Sanadin Caca Book 2 Complete Hausa Novels By Sadi Sakhna
Reading file: SANADIN CACA 2.txt
Chapter 32 of 42
*SANADIN CACA*
-BOOK 2 (PAID)
Mallakar *SADI-SAKHNA*
09035784150
Bismillahir-rahmanir-raheem
Ki biya kan ki karantamin na biyu dan Allah. ga number ta nan mai son littafi na É—aya yayi min magana zan bashi shi kyautane.
*BOOK 2*
...30...
A jirgi É—aya Musbahu suka taho shida Ahmad,zaibi normal jirgi ya hanashi akan zasu taho tare. Don a dan wannan wata ukun da sukayi sunyi sabo sosai,wanda duk sanadin labarin Matar sa ne.
Bayan sun sauƙa kowa jawo jakarsa yayi suka fito.
"Toh general ni daga nan zan hau motar gida"
"Ahhh habadai,kazo muje gida mana ayi ka huta in yaso gobe saika wuce,sannan ya zancen .......dakace zaka haÉ—ani da itah,gashi numberta tunda ka bani kullum saina gwada amma ban sameta ba"
"Shiyasa nakeson tafiya gida ai general,saboda nasan inna tasan inda take zata bani address ɗinta. Sannan karka damu na gode da dukkan halaccinka,inna dawo nayi maka alƙawarin zanzo har gida,saimu je inda take tare."
"Yaushe zaka dawo,nan da sati biyu za'ayi bikin nasararku"
"Eh kafin lokacin zan dawo Inshaallah"
Sai bayan da Musbahu ya shiga motar garinsu kafin driver yazo É—aukar Ahmad zuwa gida.
Sashensa ya wuce direct ta ƙofar baya,dan tun abinda ya faru yakejin kamar shida ƴan gidan basu hada wani jini na azo a gani ba. Mahaifinsa ne ɗan uwansu to baya raye,dangin mahaifiyar sa kuma na can wani gari daban,daɗin daɗawa kuma basa Ga maciji da su.
Ɗan tsayawa yayi daga bakin ƙofa yana kallon yanda aka gyara ɗakin,Sumaimah ce ta faɗo masa a rai,yasan babu mai wannan aikin sai itah.
ÆŠaki ya wuce ya ajiye jakarsa ya watsa ruwa.
Falon ya fito yana dadanna waya,daga idon da zayyi suka haÉ—a ido da saleem,wanda yake hakimce akan kujera yana kallon yayannasa.
Hade ido yayi ya kafeshi dasu kaman shine babba,abin ba ƙaramin mamaki yabawa Ahmad ba.
"Kaikuma fah ya haka'
"Dole ka tambaya mana yah Ahmad,yanzu baka gidannan tsawon wata uku ka dawo amma ka wuto sashenka kawai,Æ´an cikin gida nacan suna zancen"
"To so what suyi maganar ma,dama sun damu dani ne,kaima in zancen dazakamin kenan to kama hanyarka kayi waje"
Jijjiga kai Saleem yayi tareda jan numfashi,yana son yayannasa kuma wani lokacin baya ganin laifinsa,yanayine yasakashi zama hakan.
Wajen dining ya nufah ya buɗe kulolin,ƙamshin abincine ya bugeshi saida ya lumshe ido.
Zama yayi ya zuba abincin yaci yayi nak,ko ci kanka baicewa Saleem ba,yayinda shikuma ya zuba masa ido yana cin abincin kaman ya samu tv.
"Hmmm kana cewa ba ruwanka da yan aiki gashinan kuma kazo ka ci abincin mai aikin gidan.
Ni inaga ƙoƙarinta ma,da ciki tayi maka wani gyaran sashe da kuma abinci,saikace mijinta"
Yana cikin goge bakinsa ya cakk jin abinda Saleem yafaÉ—a,ciki ciki kuma wanne iri .
"Saleem mai kake cewa cikine da wa?"
"Sumaimah mana mai aikinka,ohh da kanace budurwace,naga dama ka fara nuna kishi akanta,tun wuri gwanda ka bari,naji an ce cikine da itah,mijinta yazo ganinta sai gata da ciki,lallai wannan miji ya iya bugu sosai"
Wani zimmm kan Ahmad yayi,a ransa yana ta maimaita Allah yasa dagaske na mijinnata ne bashine ba.
Gumin daya keto masa ya goge tareda cewa,
"Cikinnata zaikai kaman ya"
"Oho nina sani,naji dai ana cewa yayi babba kawai"
Duk da abinda Saleem ya faÉ—amasa hankalin sa bai kwanta ba.
Wayarsa ya É—auko ta gida wanda takeda layinsa na nigeria..
Ƙiranta ya farayi amma shuru bata shiga,haka har ya Haƙura don kansa.
FaÉ—awa yayi zurfin tunani GabaÉ—aya ya gagara barwa kansa cikin jikinta ba nasane,kai yasan ma nasane.
Hannun Saleem yagani yana yawo akan fuskarsa,hakanne yasakashi firgit ya dawo hankalin sa.
Tashi yayi zaune yayi hanyar ƙofar dazata shigar dashi cikin gidan.
"Ina kuma zakaje ogah ta wannan ƙofar?"
"Zan shiga na gaisar da mutanen gidanne sarkin tambaya"
Sakin baki yayi saida yaga ya shige kafin yabi bayansa,a bangarensa kuwa don ya haÉ—u da Sumaimah zai shiga.
Ba kowa a babban falon gidan sai Sameer wanda yabada hankalin sa gabaÉ—aya kan wayar hannunsa..
Jin shigowar mutum yasa ya É—aga kansa,yana ganin Ahmad ne ya cigaba da harkar gabansa.
"Don kana zargina meyasa bazaka zo gaba da gaba ka tuhumeni akai ba,saika dunga binciken hakan a bayan fage?"
Ajiye wayar Sameer yayi jin topic É—in da Ahmad ya É—auko.
"Hmm menene abin zuwa gabanka na faÉ—amaka,bayan nasan bazaka fadamin gaskiya ba.
"Taya zan faɗamaka gaskiya bayan nima a lokacin bansan ta ba? Zarginka gaskiya ne amma ba yanda kake tunani bane. Nine wanda mukayi faɗa dakai harka cakamin wuƙa"
Yafaɗa yana ƙarisa maganar tareda buɗe masa gefen cikinsa.
Zaro ido Sameer yayi,yayinda fuskarsa ta nuna rashin jin É—aÉ—in yanda yayi masa raunin,amma shima ai ya dukashi sosai.
Shuru sukayi babu mai cewa komai,sai can kafin Ahmad yace.
"In kanada kokwanto ka daina kawai gaba,ka tunkareni dashi"
Yana gama faÉ—in hakan yayi masa É—an Murmushin kwarewa.
Duk maganar da suke Sumaimah na jinsu,wacce take tsaye cak tayi suman wucin gadi,jikinta rawa yake wanda ta É—auki tiren,kaddai Ahmad ya tuna rayuwarsa ta goje,in kuwa hakane to zai ganeta tana shiga.
Har ta juya zata koma taji muryar Sameer.
"Yadai naga kin tsaya kuma zaki koma,ko kin manta wani abune,sauri nake fah zan fita"
Shigowa tayi kanta a ƙasa,ta gefen ido tana kallon Ahmad wanda ya tashi zai fita daga falon,da alama bai san zata shigo,saidai tunda ya riga ya tashi kawai ya fice.
Yazo giftawa ta gefenta tayi ƙamshin turaren datake shaƙa kafin tayi bacci a jikinsa,wannan har yafi wancar shigarta,nutsuwa da kasala ya sauƙar mata a lokaci guda,har bata san lokacin data ja dogon numfashi ba.
Sai bayan ya wuce ta dawo hankalin ta kafin ta kulada Sameer wanda yake binta da kallon mamaki.
"Yadai naga kin tsaya ido rufe kaman mai addu'ar kirista,idan bakya jin daÉ—i waye yace kiyi aiki?"
Bata bashi amsa ba sai ajiye masa abincin da tayi ta fita,gaba É—aya tunda yanxu sun gane tana aure kuma harda cikin basa yin maganar da sukeyi da,kuma ma cikin ya maidata marar magana,ga yawan gajiya.
Bayan ta fito daga falon har zata wuce taga Ahmad tsaye a bakin shiga sashensa,diriricewa tayi zata yi hanyar kitchen da sauri,sai kuma taji muryasa.
"Kizo yanzu ina son magana dake"
Daga haka ya shige ciki. Ajiyar zuciya tasake tana bin ƙofar da kallon. Banda sunan Allah babu abinda take ambata.
Tiren ta mayar kitchen kafin ta dawo zuwa sashennasa,zuciyarta cikeda zullumin yanda zasu ƙare,tasan dole yaji labarin cikinta kokuma ma yagani da idonsa.
Tura ƙofar falon tayi ta shiga,yana zaune akan kujera yana kallo,amma daga gani kasan hankalin sa baya kan kallon.
ÆŠauke idonsa yayi daga kan tv ya mayar kanta,tasan bakomai yake dubawa ba sai yanda ta sauya sosai. Duk da hijabine a jikinta amma dole a gane hakan.
Saida tazo kusada shi kafin ta zauna a tsakiyar falon tana kallon tiles..
Takai minti biyar a haka kafin ta É—ago,desame ita yake kallo har zuwa lokacin. Saida suka haÉ—a ido kafin yayi magana..
"Shin ban cancanci kimin bayani ba,cikin waye a jikinki. Ni kokuma mijinki? Karki bani amsar daba haka ba,domin idan kika boyemin dole zan gano gaskiya domin zanyi binciken mijinnaki a garinku nagano hakane koba hakane ba. Dan haka ki amsa min *cikin waye?*?"
Shuru Sumaimah tayi bata bashi amsa ba,banda rawa da jikinta yake ba komai..saboda yanda yake kausasa mata murya.
"Na mijinki ne?"
ÆŠaga masa kai tayi
"Na wane?"
Nan ma É—aga masa kai tayi,daka mata tsawa tayi kagin tana bashi amsa guda biyu.
"Ki bani amsa da bakinki cikin waye a jikinki"
A yanzun bude bakinta tayi tareda cewa.
"Cikinka nehhhh"
Runtse ido yayi tareda komawa jikin kujerar ya lafe,shidama hakan yayi tunani,yasan babu wani mijinta,tayi hakanne domin ta boye,kuma hakan yayi domin zai ara masa lokacin mai ya kamata yayi.
"Innalillahi wa inna ilaihi raji'un"
Shine abinda yake ta maimaitawa idonsa rufe..
Kallonsa Sumaimah tayi tareda fara hawaye tana jijjiga kai.
"Cikin shege dashi zan fara ajiye jinina a gidanmu,da wanne ido zan kalli mutane kenan,shin ke kanki mai zancemiki bare mijinki *KAICO NAH* (littafina na huÉ—u,wanda ya tara É—umin darasi kenan mai yamin magana).
Da wannan zunubi da kuma É—anyen aiki dana aikata,shi kanshi É—an na cuce shi na..........."
"Ya isa haka"
Shine abinda Sumaimah ta faɗa da ƙarfi tareda ƙara sautin kukan ta.
"Kada kasake faÉ—in hakan akanka da kuma É—an cikina,domin dukkanku baku cancanci wannan bayaninnaka ba sam,idan laifine ma nice mai laifin kuma na É—auka,sannan ciki dama ban dangantaka dashi ba,duk da cewa kaine mafi kusantuwar dashi.
Duk abinda kakeji akansa kanada damar kaji,amma na roƙeka kada kasake furtamin wannan kalmar. Ka ɗauka tamkar wannan abin bai faru ba,ta hakanne zaka manta dashi ka koma tamkar yanda kake. Sannan yanda kake daukan abubuwan ba haka suke ba.
Zan dawo aiki gobe,saidai bazan dunga shigowa ba sai ka fita,haka kafin ka dawo bazaka ganni ba,ba'a samu wata mai aikin ba shiyasa,kafin a samu zan dena."
Tana gama faɗin hakan ta miƙe daga zaunen da take tana goge hawayen fuskarta,harta kai bakin ƙofah taji maganar sa a cikin dashashshiyar murya.
"Watansa uku kenan"
"Eh"
"Lafiya kike"
"Eh"
Kici gaba da jira amma dolene zan É—au mataki akai,zan nemi mijinki akan maganar,dolene na karbi hukuncin abinda na aikata,abin yayi muni dayawa"
Wannan karon Sumaimah bata bashi amsa ba ta fita,tana jin yanda muryarsa ta karye tayi raunin ba ƙaramin tausayinsu take ji ba a wannnan alaƙar,daga itah har shi......
Fatanta Allah ya bata lafiyar cigaba da kulada jaririnnasu,Sannan kuma yabata da sauƙi.
ÆŠazun bataso faÉ—a masa cikinsa bane,gudun kada yayi bincike ya gano komai ne yasa ta amsa masa da eh É—in.
Chapter Navigation
Use this section to move to any chapter without going back to the top.