Sanadin Caca Book 2 Complete Hausa Novels By Sadi Sakhna
Reading file: SANADIN CACA 2.txt
Chapter 36 of 42
Bayan an gama jan jinin an É—aura mata kafin aka barsu suka shiga.
Zuwa lokacin anyi mata allurar bacci.
Fatee ce a zaune a gefen kanta sai su Sameer a tsaye,Sumaimah kuma na gefe a zaune.
Can kaman an É—an daÉ—e ta fara juya kanta kaÉ—an kaÉ—an.
Fatee da Maimuna ne suka ɗan ɗagota tareda saka mata pillow ganin tana ƙoƙarin tashi.
Idonta akan Ahmad ya sauqa wanda shima ita É—in yake kallo cikeda soyayya irin ta É—a da mahaifi.
Sannu sannu su Sameer suka mata,fatee kam rungumeta tayi tana kuka.
"Mommy bakida har haka amma baki faÉ—amin ba har kwanciya fah kikayi"
"Kin damu ki sani ne,miye ya dameki banda kanki uhm"
Hajiyah Maryam tafaÉ—a tana dafa kanta..
"Habadai mommy you know i love you"
"Umm naji i love you too,yanxu dai É—agani bake kaÉ—ai bace a É—akin koh?"
Ƙin matsawa tayi saida ta tureta tukunna,sai turo baki take kaman zai faɗi.
"Sannu Ummee jikinnaki yanzu"
Ahmad yafaÉ—a a nutse cikin kulawa.
Murmushi tayi tareda É—aga masa kai.
"Ummee ya jikin?"
"Alhamdulillah Sumaimah....kinci abinci kuwa?"
"Ahah"
"Tabb Ahmad ka É—auketa ku tafi gida taci abinci,batayin awa uku ma bataci ba,cikin jikinta mai neman abincine"
"Ahah yau banajin yunwar zan zauna har a sallameki saimu tafi"
Cikeda rigima tayi maganar,wanda hakan yasaka hajiyah Maryam haÉ—a rai.
"Ahah ku tafi nima yanzu zan tafi idan jininnan yaƙare,uhm yau kuma a wanne bawan Allah aka ɗauka?"
"Mommy yah Ahmad ne yabayar,yaushe kuka shirya dashi da har yabaki jini kuma ya kawoki asibiti,ga waccar mai aikin sai wani kula kike da ita kamar wata mai muhimmanci"
"Buge bakin Fatee hajiyah Maryam tayi tareda cewa.
"Ƙaniyarki da ce mata ƴar aiki,tunda har kunga ya haka yakamata kusan mai yake faruwa.
Ahmad ɗanane na fari kafin na haifi Maimuna,sannan ita kuma matarsa ce wacce ya aureta a lokacin da yayi shekara biyar baya nan. Tanada ɗa mai sunan mahaifin Ahmad kuma yayan babanku wato Muhammad,ana ƙiransa da Sayyid.. (Ta faɗa tana kallon Sumaimah. Wannan suma itan suka kalla cikeda mamaki)
Wannan shine abinda baku sani ba,sauran boyayyun labaran kuma sai daga baya. Sannan wannan maganar banaso tabar wajennan,akwai wanda sanin hakan a wajensu daidai yake da shiga hatsari dukkanmu"
∆∆∆
"Sani kuma na nawa Maryam,lallai kin raina wayona da kuma abinda zan iya sosai"
Hajiya Mammah ta faɗa wacce take zaune gabanta dauke da ƙwaryah wacce take ganin abinda yake faruwa a ɗakin asibitin.
Muje zuwa..........
SADI-SAKHNA CEH
09035784150
ku tuntubeni domin biyan kuɗinku ko ƙarin bayani.
*SANADIN CACA*
-BOOK 2 (PAID)
Mallakar *SADI-SAKHNA*
09035784150
Bismillahir-rahmanir-raheem
Ki biya kan ki karantamin na biyu dan Allah. ga number ta nan mai son littafi na É—aya yayi min magana zan bashi shi kyautane.
*BOOK 2*
...34...
Ciza yatsa tayi tareda jan hannunta a iska ƙwaryar ta bace.
"Ba abinda ta faɗamusu daya danganceni,ita kuma waccar matar Ahmad wacce na daɗe ina nema naganta amma ya ƙi nuna fusakarta har yanzu,saidai neman ta daga baxayyi wahala ba,tunda nagano tana tareda su"
Kaltum ce ta kalli hajiyah Mammah tareda cewa.
"Meyasa to ba'a ganin fuskarta,da alama wajen da muryar ta É—aukema sunan ta aka ambata,ko wata shu'umar ce kai itama?"
"Ahah ruhinane yayi rauni,kullum hakan zai cigaba d kasancewa idan ba ban kawar da waÉ—annan mutanen ba"
"Ki shirya yau inada meeting,zan É—ora wani a kujerar bello"
"Toh amma shugaba ya za'ayi da neman matar shi ........."
Wani dariya tayi tareda cewa.
"Ki ƙaddara na sameta,tunda har duk yaran gidan da kuma ita kanta Maryam tasan wacece,to samun bazai mun wuyaba,samota kamar nayine"
"Gobe zamu koma gida, sannan ina so darennan na kafe ruhin Maryam,Æ´aÆ´an ta su zaba,ko rayuwarta kokuma su rufe wacece matar Ahmad"
Wata ƴar tsana ta ɗauko a gefenta, an caccaka allurai a tsakiyar ƙirjinta,ga kuma zarruka an ɗaureta dasu. Zaren tafara ja tana wasu kalamai,lokaci ɗaya ɗakin ya turnuƙe da duhu. Kultum na ganin haka ta fita daga ɗakin da gudu,saboda tasan idan wannan ruhinnata ya fito daga akwatin suka haɗa ido,kwana zatayi tana mafarkin sa.
Zagaya ta yakeyi yana wani ƙugi,yayinda itakuma idonta ya rufe tana ta karanto wasu surkulle.
Can kaman wani lokaci ta tsaya da abinda take tareda da fara tari har jini yana zuba.
Wani rishi ruhinnata tayi wacce kamarsu É—aya da itah.
"Hahahhaha nace miki kin tsufah ki musamu,banda kina aiki da jini domin maida ƙuruciyarki da tuni bazaki kai wannan shekarun kina aiki damuba. Kuma kinsan dokar aiki,duk ranarda kika kasa iyah damu to jininki mallakinmu ne.......uhmmm zayyi daɗi kuwa,munasan gubataccen jini ahhhhhhhh"
Tana cikin maganganunnata mai kamada raÉ—a hajiyah Mammah ta daka mata tsawa.
"Ƙarya kike,banga ranar da zaki fi ƙarfina ba,ke baiwata ce kaman yanda dodo ya bani saboda ki yimin aiki. Dolene saina gama cika burina,sai na gama ɗaukar dukkan fansana tassss"
Tana faÉ—in hakan ta É—akko wata kwalba a cikin akwatin,ja ce wani abu yana juyawa a cikin ta yana walwali.
Baki ta saka ta zuqo abun zuwa cikinta.
Lumshe ido tayi jin ƙarfin dayabi jikinta. Buɗe ido tayi jajaye dasu suna fesar da wani jan haske.
"Yanzu na umarceki daki je ki riƙemin Maryam,ruhinta nake so yakasa sukuni a jikinta sam"
"Ahhhhhh ruhinki ya amshi buƙatarki kuma zai cika"
Tana gama faÉ—in hakan ta bace a iska,
Sauƙe ajiyar zuciya hajiyah Mammah tayi tana kallon kwalbar da take hannunta.
"Ina so na kasheki,amma saina samu wanda zan cigaba da zuqar jininsa tukunna. Yanzu dolene ki kasance a wannan halin har sai nagama da wannan yarinyar tukunna."
Maida kwalbar tayi cikin akwatin kana ta maidashi cikin ƙarƙashin gadonta ba tareda ta rufe ba,saboda wanda take rufewa a cikin akwatin baya ciki.
∆∆∆
Bayan gama bayanin tashi Ahmad yayi akan zai mayar Fatee da Sumaimah gida,in yaso gobe saisu dawo.
Sun fita kenan sukaji hajiyah Maryam tafara jijjiga kamar zata karya gadon da take kai..
A rikice dukka suka juyah kanta tareda da daddane sassan jikinta..
Sukam su Fatee kuka suka fashe dashi ganin abinda takeyi.
Jini ne yake fita ta hancinta,yayin idonta kuma ya koma fari soll kamar ba'a taba halittar ƙwaya daga cikinsa ba.
Ahmad ne yayi ƙarfin halin yin magana a wajen, sauran daga mai kuka sai wanda yayi suman tsaye.
"Saleem maza ƙira likita yanzunnan"
To yace cikin karyayyiyar murya ya fita.
Tun kusan magriba suke abu É—aya har dare ya fara.
Mazanne sukaje sallah,matan kuma anan gidan marayun sukayi sallah,an basu abinci ma amma babu bakin ci.
Bayan sun dawo daga masallacin wata mota suka gani ta shigo wajen baƙa.
A.M Aliyu ne ya fito daga cikin motar a razane zuwa cikin asibitin.
Ahmad ne ya kalli su Sameer.
"Waye ya sanar dashi,yaushe ya dawo garin?"
"Bansan yaushe ya dawo ba,amma ai dole dama zai san mai yake faruwa ba,abin yayi zafi sosai wanda da alama sai an fita da itah wata ƙasar"
"Uhm uhm ba abinda ya shafi wata ƙasar bane,da sannu zamu samu mafita"
Karisawa sukayi inda yake,yana ganinsu yazo inda suke da sauri,in mutum ya ganshi bazaice shine dakyakykyen sojan nan ba,lallai ba ƙaramin so yakewa hajiyah maryam ɗin ba.
Hannun Saleem ya kama tareda cewa.
"A ina aka kwantar da itan,ya jikinnata. Fatee tace wai ta daɗe batada lafiya ana ƙaramata jini,yaune yayi tsanani sosai"
Ganin yanda yake maganar a gigice ne yasa Ahmad jijjiga kai,wato Fatee ce ta faɗamasa mai yake faruwa,duk da an hanata,this thing is no more secret,dolene su ɗau matakinsa da wuri. Abin tsoronsa ɗaya wacce ake tsoron da sani tariga ta sani,abin sauƙin ɗaya batasan sunsan wacece ita ba.
"Eh batada lafiyah Abbah,ɗazu kam da sauƙi har tayi magana,daga baya abin ya rikice sosai,amma dai likitoci suna kanta domin yin nasu ƙoƙarin"
"Tun É—azun jikin ya rikice amma ba'a sanja asibiti ba,mai yasama aka kawota wannnan wajen,yakama ta in fitane ma an fara shirye shirye zuwa yanzun"
"Itace batason zuwa wani asibitin,saboda batason asan batada lafiyah,Sannan da alama jinyarta kaman bai shafi asibiti kaÉ—ai ba,hadda na musulunci za'a haÉ—a,wato islamic medicine"
"Eh to sai ayi ai dukka,yanzu dai barinaje naga jikinnata"
Yana gama faÉ—in hakan ya nufi cikin asibitin,waya ya É—auko daga cikin aljihunsa,jin ya ambaci sunan Mammah yasa Ahmad runtse ido tareda barin wajen.
Shikenan is no more sceret,duk da yasan tasan dama mai yake faruwa.
"Salam Mammah muna asibiti ashe maryam ce badata lafiyah,nima dawowata garin kenan nasani......eh ba lallai ki sani ba wai bataso a sanine........ya kawoki wannan gidan marayun data gina anan aka kwantar da itan. Eh shi to shikenan Allah ya kawoki lafiyah"
Daidai ya isa wajen da su Fatee suke ya kashe wayar,duk sunji abinda ya faÉ—a.
Zaro ido Sumaimah tayi tareda haÉ—iyar yawu,batason ko yaya hajiyah Mammah tazo ta sameta a wajennan.
Tashi tayi ta gyara mayafinta kana ta kalli su Fatee.
"Anty Maimuna ni zan koma gida naji cikina yana........."
"Ahh dama yakamata ki koma gida,kar hakan zaman ya miki illah gaki bake É—aya ba,kije gida kici abinci ki hutah"
"Tom barina leƙata kafin na tafi,dan Allah idan hajiyah Mammah tazo karkuyi mata zance nah please"
Murmushi Fatee tayi tareda cewa.
"Karki damu matar bro bazamu ce komai ba,dama mai kamata kowa ya saniba sai mommy ta warke muyi miki official introduction,kina kirki kin dace da yah Ahmad,Allah ya barku tare"
"Ameen ya Allah nagode,Allah ya bawa ummee lafiya ya tashi kafaÉ—unta"
"Ameen ya Allah"
Fatee tafaÉ—a cikin rawar murya tana shirin kuka.
Tashi tayi zuwa wajen windown da take ciki.
An bar A.M Aliyu ya shiga inda taken,har sannan jijjiga takeyi,kodaga nesa ka gani kasan tana jin jiki sosai.
Hawayen idonta tashare tareda cewa.
"You are not deserve this,Allah ya baki lafiyah ya saka miki. Da sannu sai taga sakayya akan abinda takeyimiki......ina miki fatan samun sauƙi"
Sakin ƙarfen windown tayi tabar wajen.
Inda su Sameer suke ta nufah,Ahmad baya wajen.
"Saleem ina Ahmad yayi?"
Ta tambaya cikin ƙaramar muryah.
"Yaje yin wayah ne yanzu,gashi can"
Ya nuna mata É—an gefensu kaÉ—an.
ÆŠaga kai tayi tareda nufar inda yake,daidai lokacin ya gama wayar,kansa ya É—ora akan saman motarsa yayi shuru.
Cikeda tausayawa take kallonsa, a yau yagane matsayinta a wajensa,a yau kuma yake ganin kamar zai rasata,ganinta cikin wannan hali ma abune da duk wani É—a sai yayi da gaske ya daure.
Takawa tayi a hankali zuwa bayansa,hannunta tasaka ta saqalo ta bayansa kana ta É—ora kanta a bayannasa.
Shuru sukayi na wasu mintunan kafin ya É—aro nasa hannun akan nata.
"Lafiyah kike,kin gaji koh,ko yunwa kikeji,yanzu nake shirin tafiya neme muku wani abun"
"Ahah ba wannan bane,inason tafiya ne kafin hajiya Mammah ta tarar ni a nan wajen.....bayan haka ƙalau nake,kaifah ykk nasan kana cikin damuwa,amma ka daure ka jure. Kowanne tsanani yana tareda sauƙi. Sannan bawa bazai zama mai miƙa lamuransa ga Allah ba face ya jarrabeshi da gurare da dama. Idan ka jure kaci sai komai yazo da sauƙi"
"Uhm naji bayaninki,nagode da samunki. da Sannu zan cigaba da yimata addu'ar samun lafiyah,itakuma da take ba daidai ba Allah ya yi maganinta."
"Ameen ya Allah"
"Muje na saukeki a gida"
Hannayenta ya kama ya buÉ—e mata motar ta shiga kafin ya zagaya É—aya bangaren.
Tafiyah suke babu wanda yake cewa komai,kawai hannun ta yakama yana tuƙin,ɗan Murmushi tayi,dan ya kula yanason kama hannunnata.
Chapter Navigation
Use this section to move to any chapter without going back to the top.