Sanadin Caca Book 2 Complete Hausa Novels By Sadi Sakhna
Reading file: SANADIN CACA 2.txt
Chapter 42 of 42
Bayan munje naso na kwana biyu amma Ahmad yaƙi,saboda inaso na zaga danginnamu, duk da a baya basu nunamin ƙauna ba,amma badansu zanyi ba ai.
Haka ina gani mukayi kwana É—aya muka kamo hanyar dawowa, zuwa gidana kuma cikin dangin mahaifiyata,wacce yanzu nasan asalinta.
Bayan shekara biyu da haihuwar ƴan biyuna dukka mata, Maryam da zainab wanda ake ƙiransu Islam da ilham. Dukkansu babu mai kamata,Neelah islam ta iyo,ilham kuma hajiya Maryam har jikin.
Cikin ƙoshin lafiyah na rainesu har na yayesu,lokacin kuma Sayyid yashiga makaranta,wanda yadawo hannuna da zama. Dan so nake nayi masa tarbiyyah yanda ya kamata bata iyayen zamani ba.
Bayan yayennasu makaranta na shiga Jami'a,zan karanci Qur'anic science,dan inada burin sanin ilimi a fannnin,a lokacin ne nayi planing na haihuwa,soyayya kawai muke sha nida mijina Sannan kuma ina samun lokaci na yarana sosai.
****
Ina faka motar dana kasheta shigowa cikin gidan nayi,da islam naci karo ta dawo daga sashen inna larai,wandonta ya jiƙe da fitsari,jijjiga kai nayi dam takaci,magana saita siyarka amma tana fitsari a wando.
"Daga ina kike islam?"
"Gujin inna nake Unni"
"Ina É—ayar taki?"
"Tana bacci gujin inna"
"Kekuma kina yanda kikaga dama koh,yayah fah yana gidan Ummee ko wajen inna "
"Bashu dawoba da abbah"
"Hmm wuce to muje nacire miki wannan wandon"
Saida na gyara mata kafin nashiga kitchen a gurgune,ina cikin yi naji muryar Ahmad a falo shida yaransa.
Jallop É—in taliya nayi na fita da itah.
Sannu da dawowa nayi masa kafin na juya zan shiga É—aki..
"Hayatee ke bazaki ci abincin bane zaki tafi yau?"
"Ahah banajin yunwa beb wanka ma nakeson yi,kuci abincinku kada ya huce"
"Ahha baki isa ba dawo ki zauna,banason zama da yunwa,zona baki a baki"
Zaro ido nayi bayan na zauna a gefensa,ganin zai bani kunya a gaban yara na saka hannu mukaci tare.
Kallonsa nake yanda yake sakawa su ilham abincin a baki. A raina nace Alhamdulillah da wannan baiwar da dddaÉ—ar rayuwa.
Nima sainace ALHAMDULILLAH a fili tareda ajiye alÆ™alaminah. Kuyi haÆ™uri ta katse littafin a haka,banida zabine exam ta matsoni. Da fatan zaku fahimta. Kowa in bai masa ba yasake maimaita Æ™arshen a kundin hasashensaðŸ˜Â.
Godiya ga dukkan makaranta,musamman masu binsa yana da'irar rubutu na gode da kasancewa dani nagode sosai.
Taku a kullum SADI-SAKHNA ke muku sallama da BISSALAM. sai mun haɗu a wani sabon littafin wanda babu rana a yanzu gaskiya. Saboda sabuwar rayuwa na shirin tunkarata ta aure,ina barar addu'ar ku Allah yasa yazomin da sauƙi. Nagode.
THAMMAT BIHAMDULLAH......âœÂðŸÂ¼
Chapter Navigation
Use this section to move to any chapter without going back to the top.