Trending Hausa Novels

Sanadin Caca Book 2 Complete Hausa Novels By Sadi Sakhna

Reading file: SANADIN CACA 2.txt

Chapter 33 of 42

*SANADIN CACA*
-BOOK 2 (PAID)

Mallakar *SADI-SAKHNA*
09035784150

Bismillahir-rahmanir-raheem

Ki biya kan ki karantamin na biyu dan Allah. ga number ta nan mai son littafi na É—aya yayi min magana zan bashi shi kyautane.

*BOOK 2*
...31...

Anyi sati guda da Ahmad ya gane cewar Sumaimah tanada cikinshi,kuma har zuwa yanzun hankalin sa bai kwanta ba,har mafarki yake mijinta yasaka masa wuƙa a wuyah,abinda yake bashi mamaki kuma mijinnata kamarsu ɗaya dashi,saidai yana zuwa masane a salo na daba.
Yau ma tun Dare abinda ya kwana yanayi kenan,da asuba bai koma bacci ba,karatun qur'ani yayi tareda neman gafarar Allah bisa wannan dumbin zunubi nasa.
Da wuri ya fita daga gidan, gabaÉ—aya abubuwa sun isheshi.
Lokacin dayaje office babu kowa a headquarter sai masu shara da gyare gyare,aikin dayake kansa ya dauka ya fara,ko zai rage abinda yake cikin ransa.
Wajen misalin ƙarfe sha biyu yaga kira a wayarsa,sunan Musbahu yagani,dama yana expecting kirannasa tun jiyah amma shuru.
Yana É—agawa sallama sukayi yace masa.
"Yah Musbahu naƙira ka baka ɗaga ba,gobene fah za'ayi bikin baku matsayin"
"Oga wanann yayan da kake ƙirana dashi na kasa sabawa dashi,gani fah a ƙofar headquater bansan office ɗin ka ba"
"Okay ka tsaya ganinan zuwa yanzu"
Ajiye aikin dayake yayi ya fita daga office É—in,binsa wani squad na ma'aikata sukayi,dama yana ciki,babu wanda yaga ya fito tunda suka zo.
Da sauri sauri ya fita harabar wajen,daga nesa ya hango Musbahu a tsaye wajen da ake parking motoci.
Tun daga nesa daya ganshi ya taho daga wajen suka yi gaisuwar musabaha.
"Barkanka da zuwa muƙarisa"
"Lahh ogah da basai ka shigo bama,in ka yimin kwatance ma zanzo"
"Ahah karka damu ƙarisa,bayan abinda yake tsakaninmu inayi maka kallon aminina ne"
Tafiya suke suna tattaunawa har suka isa,ruwan sanyi yabashi don shine abinda yakeda shi a office É—in.
"Ga ruwa kasha hanya,barina ƙarisa wannan saimu tafi gida kaci abinci"
"Zan sha ruwan dai abinci kam daka barshi,dan har nayi booking na hotel,muna gaisawa zanje na sauya kaya sai mu haÉ—u. Har yanzu ina kiran wayar ta ma baya shiga,bansan meyasa ba. Hmmm inaga akwai matsala........."
Jim Musbahu yayi daya faÉ—i hakan,wanda hakan yasa Ahmad bashi dukkan nutsuwar sa donjin wacce matsala ce.
"Basa garin,daga innan da Deejah dakuma Sayyid,na tambayi matar gidan kuma tana cemin wata baƙar motace tazo ta daukesu wancan watan zuwa nan abuja,bansan waye ba ,amma jikina na bani ko gidan da Sumaimah take aikine"
"Amma kana gani wanne wajene haka,mai ya faru dukka suka tafi gabaÉ—aya,basusan inda suke ba address É—insu?"
Cikeda damuwa Ahmad yake tambayar,gaba É—aya hankalinsa ya tashi. Ji yake duk laifinsa ne dabai nemeta ba,gashi har ta shiga duniya neman aikatau saboda rashin abinyi.
Rarrashinsa Musbahu ya fara yi ganin yanda hankalin sa ya tashi,don yasan kansa yake ɗorawa duk laifin abinda ya faru. Shikansa ba ƙaramin tausaya masa yayi ba,ace ka yi rayuwa da mata harta haihu amma baka sani ba,to amma meyasa ya kasa tunawa.
Shine wasi wasin da Musbahu yakeyi,wanda shima Ahmad yayi irinnasa.
Sun dade suna zance duk akan matar tasane,saikuma wanda yake damunsa aransa na Sumaimah.
"Bakomai Musbahu karka damu,Inshaallah Allah zai bayyana su. Yanzu dai muje gida tukunna daganan sai mu wuce gidan tv bada information ɗinsu,da kuma radio,maybe idan sunji ko wani yasansu ya ƙira. Ga matsalar babu hotunansu."
A motar Ahmad suka fita daga headquater zuwa gidansu.
Direnct sashensa ya wuce dashi basu shiga cikin gidan ba.
Shidai Musbahu binsa yakeyi a baya,don ya damune ma yabiyoshi,sannan shima yana da buƙatar son ganinsu,musamman Deejah wacce yakejin kaman nauyin kulada itah a kansa yake.
A falo yamasa iso ya zauna,motsin mutum yaji a kitchen,sannan kuma babu abinci a dinning,sai sannan ya tuna ya rage awa guda hadda rabi akan lokacin dawowarsa,ajiyar zuciya yayi yasan abinci take,koba komai zata fiddashi kunya,da har yayi niyyar kuwa hanata yi masa aiki,yanzu ma daga ya samu matarsa sai Yanda zayyi da case É—inta.
Kitchen É—in a yashiga ya sameta a kan stool tana wanke kwanukan da tayi amfani dasu,a gefe kuma ta jera kayan abincin a kan tire,da alama tagama gyara wajen take kafin ta tafi.
Aikinta take a hankali ko kuladashi batayi ba,hakanne yabashi damar ƙare mata kallo,tayi fari tayi ƙiba fiyeda da,wanda kuma yasan cikinne ya sakata,don gashinan yafito a jikinta,dayake doguwar rigace a jikinta,kuma ta fara kamata saboda cikin.
Kyau tayi masa a hakan,inaga matarsa take masa wannan hidimar da cikinsa a jikinta. Inama matar dayake ta nema ce. Wani runtse ido yayi tareda jijjiga kai,ahah wannan matar wani ce wanda yaci amana.
Tabon dayake zuciyarsa na abinda ya aikata ne ya dawo sabo.
Jinginar dayayi a jikin ƙofar kitchen ɗinne yasaka ƙofar yin ƙara,wanda kuma ya ankarar da Sumaimah wacce kanta yake sunkuye,kallonsa take da alamar mai ya dawo dashi a lokacin.
Lokaci guda ya tsime tareda yin gyaran murya.
"Nayi baƙo ne mun dawo dashi,zan ɗauki cup ne na shan ruwa,sannan idan kin gama abincin ki kawo shima yanzu"
Yana gama faÉ—in hakan ya É—auki cup biyu a inda ta jera ya fita,itadai da kallo kawai tabishi tareda tabe baki.
Gabaɗaya ya dagula mata lissafi da ƙamshin jikinsa,wanda yake rikitata,aman da take ji ɗazu ma yakoma.
Bayan ya fita cigaba tayi da wanke wankenta,saida ta gama kana ta É—au kwanukan abincin da saka su plate da komai zata kai musu.
Lokacin data shiga da Ahmad suka haɗa ido,saboda shine yake facing kitchen ɗin,shikuma baƙonnasa ya bawa kitchen ɗin baya,magana taji sunayi akan yaɗa labarinta ko za'a sameta,har zuwa taje ta ajiye kayan abincin akan dining table, juyowar da tayi zata tafine idonta ya sauƙa akan Musbahu,yayinda shima itan ya kalla a lokacin daidai yakai gorar ruwa bakinsa.
Dawowa yayi dashi da sauri tareda zare ido.
"Sumaimah!!!!"
"Yah Musbahu"
Itama ta faÉ—a cikeda mamakin ganinsa a nan É—in.
Ahmad ne ya kalleshi tareda cewa.
"Kasanta ne?"
"Itace fahh dama kuna tarene tuntuni?"
"Itace wa,muna tareda itah a ina?"
"Mai kake nufi,bakasan wacece ba,ko aljana ce kai ni kaÉ—ai nake ganinta,Sumaimah ce fah matarka wacce ka bari ka tafi. Itace muke nema"
Da wani mungun sauri Ahmad ya kalleta a razane,ganin kallon dayayi matane yasakata sauƙe idonta,wani kuka ne da batasan na menene ba ya kufce mata,dama abinka da yanayinta ya koma na kukan.
Zuba mata ido sukayi dukka ganin yanda take ta kuka kaman an daketa.
Musbahu ne yayi ta mazan yi mata magana.
"Mai aka miki kuma kika fara kuka,zo nan ki faÉ—amin mai yake faruwa"
Takawa ta farayi kaman wacce ƙwai ya fashewa a ciki,ta gaban Ahmad ta wuce zuwa inda Musbahu yake,shidai binta yayi da kallo kaman ya samu tv. Tun daga tambayar ko kwaƙwƙwaran motsi bai ƙara ba.
"Miye ya faru da wayarki nayi ta ƙiranki bata shiga,ya akayi kike zaune da mijinki amma bai san ke bace,yana can yana nemanki. Ina kuma su inna suke,domin dana koma gida an ce suna garinnan?"
"Uhm uhm wayar ta baci banda wata kuma,su inna kuma suna gidan Hajiyah Shukurah ƙanwar hajiyah Maryam. Ta ɗauki inna ne aiki,kawu audu ne ya koresu bayan tafiyarsa (tafaɗa tana kallon Ahmad kafin ta ɗauke idonta). Tunda wai dama wajen ya zama nasa. Ina baba yake dasu Ammi?"
"Baki ƙarasa bani amsata ba Sumaimah,meyasa dakika haɗu da mijinki baki faɗamasa ke wacece ba,ko rashin ganeki da yayi ne yasa kika ƙullaceshi akan sai sanda ya sani da kansa?"
Jijjiga kai tayi da sauri tareda cewa.
"Ahah ba haka bane,ba a son raina naƙi faɗamasa ba,saidan yazama dolen,mutanen da suka yi sanadiyyar zamansa a goje suna tareda shi,idan suka sanni wacece bazasu ƙyaleni na dakuma shi,shiyasa ban faɗamasa ba"
"Mut......."
"Dan Allah kada ka tambayeni dalili yah Musbahu,inasu baba da ammi baka faÉ—amin ya suke ba.......baka ga Deejah ba tayi hankali kaman ba itah ba"
Tayi hakane domin ta kawar da maganar É—azun,duk da tasan hakan bazayyi yu ba.
Ganin kallon da Ahmad yake yiwa Sumaimah mai cikeda abubuwa da dama yasa Musbahu cewa..
"Suna nan ƙalau,yanzu dai bani address ɗin inda su inna suke,ni yanzu zan tafi,kina buƙatar yin magana dashi"
Jimm tayi jin abinda yace,amma haka ta bashi ba yanda zatayi.
Kitchen ta koma tanajin fitarsu shida Ahmad É—in.
Hannu ta É—ora akan zuciyarta wacce take bugawa fatt fatt.
A bangaren Ahmad kuwa da Musbahu yace zai tafi kasa hanashi yayi,domin a yanzu burinsa ɗaya shine jin bayani daga bakin Sumaimah,na akan me ta ƙi faɗamasa matsayinta a wajensa.
Ganin har suna shirin rabuwa Ahmad baice komai ba yasa Musbahu cewa.
"To ni zan tafi gen. Ga yanda abu ya kasance,amma ni abinda nake gani ka bita a sannu ta faÉ—amaka mai yake faruwa,ni kaina shaidane akan irin son da take maka a lokacin baya,bata haÉ—aka da komai,duk da mutane suna jin tsonka amma kaine wanda take burin komawa gareshi idan tayi nisa dashi"
Da kalamai masu dadi cikin hikima ya taushi Ahmad kafin ya tafi ya barshi,yana musu fatan shiryawa mai É—orewa.
Kaman jira yake yana tafiyah ya koma sashennasa,bai sameta a falon ba,har yaji babu daɗi kaddai tafiya tayi,sai kuma ya gano ƙofar kitchen a buɗe.
A kaban kitchen table ɗin take tsaye tana kallon window,ta bawa ƙofar baya.
"Can you explain your self please?"
Tajishi sarai amma bata juyo ba,wani kukan tasake fashewa dashi har yafi na É—axu.
"Am sorry am sorry please i....i can't..........."

Chapter Navigation

Use this section to move to any chapter without going back to the top.