Sanadin Caca Book 2 Complete Hausa Novels By Sadi Sakhna
Reading file: SANADIN CACA 2.txt
Chapter 13 of 42
SADI-SAKHNA CEH
09035784150
ku tuntubeni domin biyan kuɗinku ko ƙarin bayani.
*SANADIN CACA*
-BOOK 2 (PAID)
Mallakar *SADI-SAKHNA*
09035784150
Bismillahir-rahmanir-raheem
Ki biya kan ki karantamin na biyu dan Allah. ga number ta nan mai son littafi na É—aya yayi min magana zan bashi shi kyautane.
Sister's duk wacce batayi anfani da sabulun mg's ba ko kit dinsu inamai shaidamuku anbarku acan baya domin duk wnd yajaraba mg's sai sanbarka duk wani Mai tantama Akan kayan gyaranjiki toh tabbas yacire sabulun mg's domin yahadu bakarya zegyarajiki yafidda dattin fata Dama duk wani matsalan fata duk Wanda kefama da matsalan fata walau pimples ko spot, sunburn acne,stretch mark dama dukkan wani prblm yajaraba mg's bi'iznillah komai zaizama labari bayan jikinku yy fresh zaisa jikinku yy smooth yadinga glowing,gawanda basa San anfani da Mai zaku iya using mg's batare da kunbukaci wani Mai b🤗nd wnn new soap din💣ne,😯 bama cika Baki kujaraba kugane ma idanku domin ance gani yakoriji Kuma siyan daya maida kudi gida
You can check pic👇for the soap reviews🥰
Soap price:4k
maiso yy mgn
08062991549
07046881166
07067210195
Call 08064532391
Instagram:glow_with_mgs
Facebook: mg's skincare
Masu bukatar cream Shima munadashi harda ma complete set nagyaranjiki
Small 14k
Babba 16k
Munatura Kaya kowani gari dayardar Allah Amma delivery is not free
Be part of the glow teamðŸ˜karkubari abaku lbrðŸ‘
*BOOK 2*
...12...
"Okay let's go to the deal,(Aha bari muje yarjejeniyah),zan faɗamaka wacece matarka,sannna kuma a ina take,amma da sharaɗin saika daina binciken da kakeyi a yanzu na ƙungiyar BC,duk cewar nasan idan na kacigaban babu abinda zaka samo saidai ka sake saka rayuwar a halaka karo na biyu.
Dan haka ka ajiye case É—innan ka kama wani daban,idan kayi hakan ka tsira kuma zaka san inda matarka take"
Wani kallon kinsan mai kike fada Ahmad yayiwa hajiyah maryam,saida tagama bayanin kafin yayi É—an murmushi.
"Amma da kikayi wannan maganar ke kanki kinsan idan zan yarda da ita kokuma akasin haka, babu abinda zaisa na daina wannan aikin matuƙar ba kama wanda suke da hannu da shuni a ciki nayi ba. Batun sanin inda matata take,dama bawai saninnata ne maƙasudin abinda yasa nake nemanta ba,bazaki san dalilin ba kuma,dan banyi maganar da kowa ba bare ki sani"
Tashi yayi cikin bacin rai zai fita daga office É—in,magana tasake yimasa hakan yasa ya tsaya da fita.
"Bazaka daina ba....koda kuwa na kusada kai zasu cutu akan hakan,koda kuwa abinda zaka tono É—in bazai maka daÉ—i ba?"
"Ban damu da daÉ—insa da kuma rashinsa ba,indai zanyi nasara hakan ma kaÉ—ai ya wadatar"
"Hmmm yaro man kaza,kanada masoya a boye,haka zalika kanada maƙiya ma a boye,abinda yake zai bayyana maka maƙiyanka amma kuma zai cutar da boyayyun masoyanka,tunda kace kaji ka gani na amince da zabinka,i like to see you try"
Ƙarisa maganar tayi tana ɗan sosa biro a goshinsa,bayan ya fita ajiyar zuciya tayi tareda lumshe ido.
"Shin ya zanyi da yaronnan ne ni maryamu,gabaÉ—aya narasa taya zan juya akalarsa daga kan abinda yake shirin yi"
Ƙirane ya shigo ta wayar office,hakan yasa ta ɗaga da sauri.
"Halle jikin nasreem ne?"
"Eh ranki ya daÉ—e,yanzu haka ma ana nemanki da gaggawa"
"Ohk ganinan zuwa"
Tana kashe wayar tafita daga office É—in da gaggawa,wani corridor ta bi da gudu har tana tuntube.
ÆŠaki na biyar a bangaren hagun ta shiga.
Likitocine guda biyu akanta,da kuma wasu mata masu uniform ruwa kalar omo.
ÆŠaya daga cikinsu ce taga shigowar hajiyah maryam É—in,da sauri ta matsa domin bata damar kallon yarinyar da take kan katifar.
Cije cije take da fizge fizge,gaba É—aya bata cikin hayyacinta,fatar bakinta duk tayi jawur saboda cizonta da take kaman zata cireta.
Ƙarisawa gabanta tayi a hankali daidai lokacin da likitar tayi mata wata allura..
Sauke numfashi tafara tana jan nishi kaman mai alamar fitar rai,can kuma sai tayi shuru kaman wacce ta mutu,da alama bacci tayi.
"Naga tayi bacci da wuri,kenan yau da sauƙi ba kaman jiyaba da muka kai dare?"
Hajiya Maryam tayi maganar cikin tausayawa,kaman ba itace take izza ba.
"Ehh hajiyah mun samo allurar da tayi daidai da jikinta yanzu,Inshaallah zata samu sauƙi"
"Mashaallah hakan yayi, aikinku yana kyau,ya dai sauran marasa lafiyan,da fatan suna samun sauƙi"
"Eh suma da sauƙi,mai siyo maganin ma yanzu zai dawo,jariran har yanzu jikinsu da zafi"
"Bakomai kada ku damu,kudai kuyi abinda ya dace,duk abinda ake buƙata ba matsala bace"
Tashi tayi tasake kallon wacce take kwance akan gadon cikeda tausayi.
"Hmmm wanda sukayi raping É—inki saisun biya ba É—aukar bashi,babu wanda zai sha idan yashiga gonata"
Lokacin da tayi maganar ta dawo ainihin kalarta,fita tayi da sauri kanajin takun takalminta ƙwass ƙwass harta bar wajen. Wani sashen tasake shiga,wanda su kuma duk yarane a wajen suke wasa.
Suna ganin tashi go suka fara rige rigen isa wajenta,da alama su basa tsoranta kaman sauran mutanen waje.
..........
Yau banje sashen Ahmad gyara da wuri ba,yayi fadan har ya gaji amma ko a jikina,dokokinsa indai ba wasu muhimmai ba babu wanda nake bi a ciki.
Tafiya nake ina kalla kalle,nazo daidai wuce na shiga sashensa kenan naji murya dr Saleem yanamin magana.
"Malam Sumaimah barka da safiyah,ko nace safiya,da naga shabiyu ta kusayi"
"Ahh habadai da saura,ya naganka a gida baka tafi wajen aiki ba"
"Uhm na dawone,abu na É—auka yanzu zan koma"
Uhm kawai nace fuskata É—auke da murmushi na wuce,shikam ya fita zakka a gidannnan a kirki.
Fulawar dana yanka nake murzawa a hannuna harna isa sashen,kaman nawa kai tsaye na wuce.
Babu wani datti sosai saboda gyaran dayake samu daga gareni,sannan kuma ba zama ake ba sosai.
Sama sama na gyara ko ina kafin na dawo falon ina kallonsa,kana gani kasan bana mace bane,ga waje har waje amma fayau babu abubuwan daukar ido a ciki.
Fita nayi lambu na cinko fulawowi wanda suke cikin tukunya na saka a ƙofar inda ya dace.
Labulayenma sanjasu nayi daga farare zuwa jajaye,irin carpet É—in falon.
Yaraf na zube a kan kujerar falon ina maida numfashi,nikaina gyaran yayi min kyau ba kadan ba.
Gumi naji yana yankomin saboda motsa jikin danayi,gashi bangama ba inason saka room fresh da turaren banÉ—aki.
Yunƙurawa nayi na tashi na shiga ɗakin.
"Fadi ba'a sakani ba,sai gwanintar da ba godewa nake. Ohh kodayake zan samu lada a matsayinsa na mijjna.
Bayan na gama komai har zan fito daga banÉ—akin sainaga yayimin kyau sosai.
Wata zuciyar ce tace nayi wankana kawai a nan basai na tafi ba,uh uhm anya kuwa.'kiyimana da sashen mijinki ne ba laifi kikayiba.
"Uhm mijin da bai san daniba? Baridai na ɗana naji mai akeji,wannan sabulan daga gani zasuyi ƙamshi"
Hannuna na miƙa na murɗa wata makunna dannaga ko tana aiki,ban zata ba saiji nayi ruwa daga saman banɗakin ya yimin wankan rashin shiri daga sama har ƙasa.
Ahhh ajiyar zuciya naja,ina kallon yanda kayana suka jiƙe jaraff.
Wayyo ni wlh ba haka naso ba. Cire kayan nayi na matsesu na shanya a jikin glass É—in inda aka zagaye domin wanka.
Ruwa na haɗa mai ɗumi nayi wanka a cikin bahon,ina ciki idona yana kallon sama inda wasu ƙofofi suke,gabaɗaya bantaba kulada su ba sai yanzu dasukamin wanka.
Bayan na gama fitowa nayi daga cikin bahon,towel ɗinsa da nagani a lanƙaye na saka,hankalina kwance na fito daga banɗakin ina kallon goge gashina da hannun towel ɗin,ɗayan kuma na riƙeshi a ƙirjina.
Nama bushe dan tun É—azu naketa yarfe kayan su samu su bushe,dan ma nasan ba dawowa zayyi yanzu ba sai an yamma.
Dana shigo É—akin kaina a sunkuye yake bamma kula da mutun dayake tsaye a dakin ba yanamin kallo ido buÉ—e.
Daga ido nayi na kalleshi nace.
"Ohh harka dawo yanzu,banyi zaton zaka dawo da wuri haka ba"
Ganin bai bani amsa ba kuma yana kallon jikina da mamaki yasa na tuna mai yake jikina saida na kalla,narasa meyasa nakasa tsintar kaina da jin kunuyrsa,kodan nasaba da ganin a haka dayake a baya?.
"Shin kekuwa mutum ce,kirasa inda zakiyi wanka sai a sashena,hakanma ki saka min towel,sannan na shigo ko a jikinki cewa ma kike wai nadawo da wuri,babu ko damuwa a ranki?"
"Am sorry kayi haƙuri,wani waje na murda bayan na gama aiki,shine sai ruwa ya zubo ya jiƙemin kaya,tun ɗazu nake yarfesu amma basu bushe ba, shine na ari towel ɗinka,kuma na fito hakanne saboda nasan bazaka dawo yanzu ba"
"Ohh yaushe aka saka min dokar bazan dawo ba sai lokacin da kika dibamin"
"Nibance karka dawo ba"
Wata harara ya zabgamin tareda nuna min ƙofa.
"Zoki fice daga sashennan,dariya yabani ganin yanda yake iya ƙoƙarinsa wajen bai kalli inda nake ba,nikuma sainaji kaman nayi amfani da hakan.
Jin shuru banzo na wuce ba yasa ya É—aga ido ya kalleni,kaman mai tsoron kar a kamashi yana kallona É—in.
"Ba magana nake miki,wanne wane irin salon karuwanci ne?"
Dumm gabana ya buga yayinda wani ƙululun baƙin ciki ya turnuƙeni,karuwanci ni ya ƙira da karuwa.
"Karuwanci, nika ƙira da karuwa???"
Hawayene suka cicciko a ido na,yayinda muryata tafara rawa.
"Uhhhh karuwanci....bakaga karuwanci ba ai,bari kaga ainihinsa"
Sakin zanin jikinnawa nayi ya faɗi a ƙasa,wanda kuma akan idonsa,runtse ido yayi tareda juyawa gefe.
Takawa nake cikin ƙunan rai naje tagabansa zan wuce,dagani sai pant.
Hannuna naji ya damƙo daidai lokacin dana kai hannuna zan buɗe ƙofar ɗakin na fita. Manta komai ai ba hauka bane,kuma nima ba dutse bace,abubuwan sun fara isa ta haka.
"Ke bakida hankali ina zakije a haka?"
Duk da naji haushin maganar daya yabamin amma ta wata fuskar naji sanyin ganin duk da bai tunoni ba amma yana kishina..dama kuma abinda nakeso naga yayin kenan bawai fitar zanyi ba.
"Zan fitane nayi karuwanci wanda kace inayi"
"Mtsww ki koma kisaka kayanki,Idan ma so kike a ace daga wajena kike to hakan bazayyi aikiba"
Juyowa nayi na kalleshi,wanda yayi saurin É—auke hannunsa daga damtsena yana ja da baya.
Har sannan baya kallon inda nake,dama bawai burina kenan ba a yanzun.
"Zan saka towel din amma da saiKa yarda zaka banni na zauna har sai kayana sun bushe,kokuma ka tambayomin ummi tabani kayana. Inkuma kanada kayan mace toh?"
Bai bani amsa ba sai zuwa inda towel yake da yayi ya É—akkoshi,dawowa inda nake yayi ya rufashi a jikina,cikeda bacin rai yake kallona tareda yin magana a kusan fuskata.
Kisaka kije ki É—ebo kayanki Ga nan dryer kiyi amfani da ita ki busar dasu.
Yana gama faÉ—in hakan ya fita daga É—akin.
Juya ido nayi tareda komawa banÉ—akin na É—auko kayana.
Atampa ce riga da zani,dayake cotton ce har yanzu a jiƙe suke.
ÆŠakkosu nayi na dawo É—akin na kunna dryer,ni bamma kawo wannan tunanin ba.
Chapter Navigation
Use this section to move to any chapter without going back to the top.