Trending Hausa Novels

Sanadin Caca Book 2 Complete Hausa Novels By Sadi Sakhna

Reading file: SANADIN CACA 2.txt

Chapter 38 of 42

___A bangaren Kultum kuwa ganin tabiyo sawu bataga komai yasa ta koma,a hanyar juyawar tata aka kawo haske.
Jini tagani ya tako tun daga cikin É—akin hajiyah Mammah zuwa waje,zaro ido tayi tareda shiga É—akin da gudu.
"Yau waye ya shigo sashennan?"
Shine abinda ta faɗa a razane,musamman da taga akwatin da yafi rayuwar hajiyah Mammah kanta daraja a ƙasa a buɗe,hannu ta ɗora a ƙirjinta ta dafe.
"Nashiga uku waye ya shigo cikin É—akinnan haka"
Waya ta ɗauka hannunta har rawa yakeyi ta ƙira hajiyah Mammah.
"Hajiyah hajiyah akwai babbar matsala fah,wani ya shigo ɗakinki ya buɗe akwatinki na ƙarƙashin gado"
"Akwati kuma dama a bude na barshi,waye yasamu key É—in dakina,babu wanda ya sani banda Mulaifah,ita kuma batasan inda na saka akwatin ba"
"Hajiyah babu komai a cikin akwatin,sai wata fashashshiyar kwalbar an takata É—akin duk jini"
"What jini kuma? Ganin nan dawowa yanzunnan,akwai kwalba biyu a ciki ina suke?"
"Ga É—aya mai zan abu ta fashe,É—aya kuma bata nan"
"Wayyo nashiga uku,ganin nan dawowa yanzunnan driver zai dawo dani a darennan,amma ba Mulaifah bace tayi?"
"Ba ita bace,tana bacci a É—akinta, wani ne fah ya shigo,na bishi ma yagudu É—azu"
"Kuma mai kike da kika daina binsa,koma waye sai ya karbi hukuncin lalatamin shirina na tsawon shekara da shakeru,ganin zuwa idan wanda ya É—auka ya lalata kwalbar ko wanne lokaci hajiyah maryam zata iyah tashi"
"Mammah keda waye kike magana haka naji hankalin ki a tashe?"
Maimuna ta tambayeta ganin yanda take haÉ—a gumi,itah mai sunan tazo wajen jinya amma gabaÉ—aya hankalin ta na wani wajen daban..
"Inason komawa gidane yanzunnan Æ´ar nan,an samu matsala,ciwon zuciya na ya tashi,dama yakan yimin idan naga mai jinya. Ko zaku kulada itah kafin......."
Lahh karki damu Mammah kije gidan kawai,sha ɗaya tayi bazan iya tuƙin dare ba,amma bari na faɗawa Saleem ya maidaki gida"
Godiya ta dungayiwa Maimuna har tagama ƙiran Saleem ya kaita gidan.
Shiga tayi wajen hajiyah Maryam wacce akayi wa allurar bacci tana kwance tamkar gawa,kuka tayi a gunnata da kuma wasu surutai kafin ta fito suka tafi..
Sai sannu suke jeramata tana saiƙe nishi ɗaɗɗaya..
Har bakin sashenta Saleem ya rakota kafin ya wuce nasu part É—in,dama jini ya bata masa kaya daya taimakawa likita wajen sakama hajiya Maryam na'urar iska.
Tana ganin yabar wajen ta jefar da gyalen jikinta tareda miƙewa tsaye.
Kultum wacce ke falon a tsaye sai ganin tayi kamar an jefo ta ciki.
Hancinta ta ɗaga sama ta shaƙi iskar ɗakin kafin ta buɗe ido..
"Koma wacece zata gane kuranta,abinda ta ɗauka yafi ƙarfin sata"
"To amma hajiyah wannan data fasa babu komai,Sannan wacce ta tafi da itah inta fasata fah itama"
"Wacce ta fashe aikin dana yiwa Maryam ne,a yanzu bazan ƙara amfani da jininta na dawo da ƙuruciyata ba,Sannan ina buƙatar ƙarin ƙarfi da gaggawa,domin idan wani abu yafaru da kwalbar Harsheelah nasan kaina zata dawo,domin kullum burinta shine taga raunina"
Buɗe hannunta tayi a iska saiga wani ƙoƙo a cikeda jini ya bayyana.
Jinin da Sumaimah ta yanku a tsakiyar ɗakin ta dandala kana ta ɗiga a cikin na ƙoƙon.
Cikin ƙanƙanin lokaci aka fara zaro mata bayi kamar rediyo..
"Macee macecee da ciki a jikinta,itaceeee wacce ta kasance masomin alƙadarinki,surukar gidannan ta wannan da'rar mai samun nasara akanki idan baki kawarta ba, Sannan kuma itama jinin gidannan ce"
"Me.....me kike faÉ—i Matiful duluk. ......wacce matar kenan badai matar Ahmad ba danake nema ruwa a jallo,dama tana gidannan ne? Kuma jinin gidannan ce ta yaya kenan?"
"Hhhhhh aiki ya ganki uwar gijiyar Harsheelah,dolene ki dage in kinason cigaba da aiki da dodo,idan ba haka ba ƙarshenki ne kema yazo kamar yanda na wanda suka wanzu kafinki ya wuce"
Ganin sun fara mata dariyar ƙeta ne yasa ta kawar da ƙoƙon ,domin bashine a gabanta ba yanzu.
"Kultum ƙiramin Mulaifah inason in tambayeta,nasan dole tasan wanda ya shigo ɗakina tunda har ya samu makullina"
"Amma hajiyah da alama tayi shaye shaye yauma,ba lallai tah.........."
"Ban tambayeki yin ja'inja dani ba,babu ruwana da shaye shayenta,inta kama zan zaqulo duk abinda ke cikinta ciki kuwa harda shegen É—an da ya baje koli a mahaifarta idan zan samu amsata. Mtsw matsama kiga naje da kaina"
Bangaje Kultum tayi ta nufi É—akin Mulaifah,tana kwance tayi É—aÉ—É—ayah,ko takalminta bata cire ba.
Hajiyah Mammah na zuwa ta nuna hancinta wani hayaƙi ya fita,aikuwa cikin firgici Mulaifah ta tashi ta zauna tana sosa hanci da atishawa.
"Maza faÉ—amin wa kika faÉ—awa inda key É—in É—akina yake?"
Ganin wacce take gabanta kamar kakar tata amma kuma tafita yarinta yasa ta murza ido.
"Mtsw saida Sport G yacemin dama zanga abinda hankalina bazai É—auka ba,amma hadda zafi a hanci kaiii"
"Dallah ki ware kokuma namiki abinda yafi na hanci,don tsabar rashin sanin daidai kinada ciki kike shaye shaye koh,in kika mutu ai ke kika sani,na rasa uwarki ma ballantana ke. Ki faÉ—amin akan shashancinki wa kika bawa bayani ya shiga É—akina?"
"Uhm na'am ni.....bansani ba iya kawai gyara tace zata miki na kaya shiyasa nace ta shiga amma ni baruwana. Saboda ta gama miki da wuri har na bata fitila. Saboda kullum kina cewa na zama mai kirki"
"Wacece itah baki santa bane?"
"Nasanta mana,wai granny mai ya shiga kankine,na ganki ma kaman wata sa'a ta fahhhh"
Wani wawan hawa hajiyah Mammah tayiwa gadon Mulaifah tareda cafkar wuyanta.
"Faɗamin wacece ita,kokuma na ƙarisaki yanzunnan,matacciyah kawai"
"Wayyo Sumaimah,Sumaimah cefah mai laifina danna barta tashiga É—akinki,naga dai tanayimiki aiki sosai"
Sakin wuyan Sumaimah hajiyah Mammah tayi tareda daskarewa a wajen,meyasa ma bata taba zarginta ba duk zamanta a gidan. Kenan.......kenan......mijinnata wato Ahmad ne,kenan itace matarsa daya aura a rayuwarsa ta shekara biyar.......jinin mace mai ciki Matiful duluk ya faɗa,kuma tanada ciki.....kenan tasan mai nake ƙulllawa tsawon wannan lokacin,kallon ayaba kawai takeyi mata.
Wata dariyar takaici hajiyah Mammah tasaki lokaci ɗaya kuma ta haɗe rai ƙaman hadarin marka marka mai shirin zubar da ruwa........

SADI-SAKHNA ce
09035784150

*SANADIN CACA*
-BOOK 2 (PAID)

Mallakar *SADI-SAKHNA*
09035784150

Bismillahir-rahmanir-raheem

Ki biya kan ki karantamin na biyu dan Allah. ga number ta nan mai son littafi na É—aya yayi min magana zan bashi shi kyautane.

*BOOK 2*
...36...

Bayan ta dawo daga sashen hajiyah Mammah banÉ—aki ta wuce,anan taga ciwon dataji da kwalbar data fashe,tafin kafarta ne ta dama ya tsage,
Wankewa tayi ta É—aure wajen kafin tazo ta kwanta,É—aya kwalbar kuma dagata tayi tana kallonta.
"Ko itama na fasata kaman yanda É—ayar ta fashe kai?. Ahah idan na fasata kuma wani abun ya shafeni fah?"
Ruwa ta tara a cikin roba ta karanta ayoyin karya sihiri a ciki,bude kwalbar tayi ta juye ruwan a ciki ta rufe.
"Bansani ba kozai karya abinda yake ciki ko ahah,amma Allah ina roqonka Allah yasa yayi aiki"
Ajiyewa kwalbar tayi a cikin kayanta kafin ta kwanta.
Bayan ta kwanta ta daÉ—e bacci bai É—auketa ba,shin abinda tayi daidaine kokuma saka kanta tayi a haÉ—ari.
Rufe idonta keda wuyah taji wata iska ta zagayeta,da guguwa ta taho amma ƙarfinta ya ragu kafin ta iso gareta, tana gudu haka ta ɗauketa zuwa wani waje mai duhu.
Buɗe idanunta tayi daga mafarkin,saidai sabanin ɗakinsu a wani waje ta tsinci kanta mai matuƙar duhu,dagane ba ɗakinsu bane saboda jin tana kwancene rairayi.
Hannunta takai kan cikinta,yana nan babu abinda ya sameshi. Tasbihi da fara da salati duk wanda ya samu zuwa bakinta.
A haka tana wannan halin har haske yafara fitowa da gabas. Tunda ta tsinci kanta a wajen take zaune bata motsaba har zuwa wannan lokacin.
Motsin takun mutum tajiyo yana zuwa,É—auke numfashinta tayi har zuwa lokacin da aka dalleta da wani abu mai haske.
"Hmmm wai dama kece ashe? Kinyi wasanki yanda ya dace,amma bari kiga naki ƙarshen yanzunnan"
Kultum ce take maganar cikeda jin haushin Sumaimah.
Jin wanda yake magana maimakon taji tsoro sai maida martani da tayi.
"Kinyi mamaki ne da kikaganice,zatonku ku kaɗai kuka iya shiri,komin ƙanƙantar allura ƙarfece,dan haka ba abar rainawa bace kuma akan iyalina babu abinda bazanyi ba. Ganin baku kasheni ba duk da kunsan ni wacece to aikin danayi a sashennata ita shugabar taki yayi mata illah sosai koh?"
Wani mari Kultum ta bawa Sumaimah mai ƙarfi.
"Hmmmm zatonki dan kinyi wannan ke wata shegiya ce,jira tazo tasameki kiga yanda zata gama da ahalin da kike komai dominsun. Ke kuma zakiga baƙar wahalar da zaki sha kafin mutuwarki"
Dunƙule hannunta tayi tareda faɗin wata kalma,nan da nan wani tururi ya kunnu a dukkan ilahirin jikin Sumaimah,tana jin zafin kuwa ta fasa wani ihu mai cikeda ban tausayi.

Chapter Navigation

Use this section to move to any chapter without going back to the top.