Sanadin Caca Book 2 Complete Hausa Novels By Sadi Sakhna
Reading file: SANADIN CACA 2.txt
Chapter 5 of 42
A ranar aka sallamemu muka tafi gida,kasancewar na farfaÉ—o kuma babu wata matsala.
Tunda mukaje asibitin ammi ce kawai taje,shima ina kwance bansan taje ba.
Ranar daza'ayi dakan yaji dama ban saka a raina za'ayimin komai daga gidan mu ba. Inna ce ta yankamin kaji guda biyu wanda take kiwo a can ƙyauyensu.
Abin suna kuwa dama tun cikina yana ƙarami ta siya ta ajiye a garinnasu,ana gobe suna aka kawoshi,ragone amma ba babba sosai ba,saidai kuma baza'a ce masa ɗan ƙarami ba.
A zaune nake ranar sunan da safe ina bawa sayyid abincinsa,hankalina gabadaya ya karkata kansa,maganar Shareefah naji tamkar a sama,yaushe ta dawo na faÉ—a a raina,don ita a boarding take makaranta.
"Mashaallah ƙawata da beautiful baby,sauƙata kenan a garin naji wannan labarin."
Murmushi nayi cikeda jin daÉ—in ganinta.
Gaisawa mukayi na yaushe gamo,miƙa mata yaron nayi sai tubarakallah take cewa,ba yabon kai ba kam kowa yaga yaronnawa sai ya faɗa,kyakykyawa dashi gashi ba rama a jikinsa.
Nima kuma lafiyata ƙalau,iya kula muna samu a wajen inna sosai,dan ranar sunan ma lace ta ɗinkamin ja mai kyau.
Lokacin dana ga abubuwan da tayi mana har kuka saida nayi,domin abun ya bani mamaki sosai,abinda inna takeyimin ko mahaifiya ta iyakaci.
Anyi daÉ—i anyi ba daÉ—i dukka a taron sunan,har aka watse kowa yakama gabansa,aka barni dagamu sai halinmu.
Washagari da safe hayaniyar a da ake a cikin gidanne ta tasheni,dan yanzu na dawo É—akin inna kafin nayi arba'in.
Muryar inna ce da kuma gaji suna sa'insa.
Wai gaji ce ta tashi da sassafe ta ɗauko wuƙa zata fara aikin naman suna,ita kuma inna tace bata yadda ba. Duk aikin da akayi a gidan babu wanda ta taya sai wannan.
"Amma dai gaji bakida kunya,tunda muka dawo daga asibiti ƙafata tana ciwo,amma baki tayani da komai ba na aiki sai yanzu,dayake nama ne zaki fito sassafe kifara gyarawa"
"Ohh kura kika maidani komai,kina nufin kice saboda namane shiyasa nazo nake tayaki?"
"Ahh to da ba haka bane,kinyi wani aikinne bayanshi,dan haka ki barshi zamu gyarashi nida Deejah,tunda na da bai kashemu ba na yanzu ma bazai kashemu ba da ikon Allah"
"To shikenan dama ba'ayi muku gwaninta,saikuje kuyi kayanku gayyar tsiya arna a idi,uban É—an ma ya gudu ya barku ai ballantana wani"
Ni dariyama abin ya bani danaji maganganunnasu,narasa meyasa gaji bata jin kunyar yin wani abun.
Gidannamu kenan ko yaushe wasu abubuwan zasu zama tarihi oho,ji nake a jikina kaman wasan yanzu ma aka fara.
SADI-SAKHNA CEH
09035784150
ku tuntubeni domin biyan kuɗinku ko ƙarin bayani.
*SANADIN CACA*
-BOOK 2 (PAID)
Mallakar *SADI-SAKHNA*
09035784150
Bismillahir-rahmanir-raheem
Ki biya kan ki karantamin na biyu dan Allah ðŸ™ÂðŸÂ¼ ga number ta nan mai son littafi na É—aya yayi min magana zan bashi shi kyautane.
Ina ƴan mata dakuma Matan aure masu muradin burge mazajensu da ɗinkuna zuƙa zuƙa. *PHEEDY TOILORING DESIGN* ,suna gabatar muku da ɗinkuna kala kala wanda sukayi daidai da zamani.
Zaku samemu a kan wannan layin waya kamar haka
09167130115
Wato a manhajar whatsapp. Domin ganin kalolin samufurin aikinmu kuma ku tuntubemu a INSTAGRAM da kuma TIKTOK a @pheedyxacks_ragtrade
Muna maraba daku a kowanne lokaciðŸ™ÂðŸÂ¼ðŸ™ÂðŸÂ¼ðŸ™ÂðŸÂ¼ðŸ™ÂðŸÂ¼ðŸ¥°ðŸ¥°ðŸ¥°ðŸ¥°ðŸ¥°ðŸ¥°ðŸ¥°ðŸ’ƒðŸÂ»ðŸ’ƒðŸÂ»ðŸ’ƒðŸÂ»ðŸ’ƒðŸÂ»ðŸ’ƒðŸÂ»ðŸ’ƒðŸÂ»ðŸ’ƒðŸÂ»ðŸ’ƒðŸÂ»
*BOOK 2*
...5...
*Bayan Shekara da watanni*......
"Ke maza kiyi abu da jiki,menene haka kaman bakida laka a jikinki,idan har ya iso baku gama komai ba sainayi mungun saba muku"
Cikeda masifa Mulaifah take magana,gabaÉ—aya duk ta fita daga hayyacinta,bayan wannan tsawon lokacin yaune Ahmad ya yanke shawarar dawowa gidan,dama Abbansune ya damu akan ya zauna jikinsa ya dawo yanda yake.
Kawai dai yana can É—inne,amma plan É—insa gabaÉ—aya babu wanda ya tsayar dashi,komai yana tafiya normal a tsaikaninnasu shiga abokan aikinnasa,wato Eemran da Neelah.
Yanzu ma buƙatar dawowarsa office ce ta taso shiyasa zai dawo gidan.
Hajiyah Maryam wacce ke zaune a falonta ko gezau batayi ba,tunda AM Aliyu yace mata Ahmad zai dawo daga to bata sake tari ba.
Iya Maimuna ce da Saleem kawai suke murna,saikuma murnar Fatee wanda dan taga yanda abin zai Æ™are shiyasa takeso ya dawoÉ—in. Sameer kuwa an turashi can wajen gyembu wani aiki (Zasuyi bincike akan Æ™ungiyar BB ta bombi dake cikin dajin)ðŸ˜ÂðŸ˜ÂðŸ˜Â.(uhm mutanen littafin BAƘAR AYAH) munayi musu fatan NASARA littafin na Maman Abdoul. Allah ya bar Æ™auna...........
Mammah wacce ta fito daga sashenta zuwa babban sashen gidan,jijjiga kai tayi ganin yanda Mulaifah tun safe ta gagara zaunawa,ta haÉ—a abincin da ko mutane goma bazasu iya cinyewa ba,duk wai akan mutum É—aya.
Kowa tausayinta yakeji,yayinda wasu kuma irin Fatee mamaki take basu.
Daidai misalin ƙarfe 1:30 na ranar asabar ɗin jirgin nasu ya sauƙa wanda ya taho daga Egypt ɗin.
Shine mutum na uku daya saƙƙo a jirgin,suit ne a jikinsa baƙaƙe,wanda suka dace da fatar jikinsa wacce tasha hutu mai aji. Ahh dole kam Sadeeq da Abba suce yayi baƙi farkon ganinsa da sukayi,danni ma yanzu na yarda da zancennasu.
Jakace briefcase a hannunsa ba wata babba ba,saikuma ɗaya hannun yana riƙe da trolly mai matsaikacin girma.
Fuskarsa babu murmushi kana kuma babu akasinsa,a takaice dai bazakace ga abinda yake saƙawa ba aransa.
Cikeda taƙama yake tafiyar kana ganinsa kasan babu wasa.
Tun daga nesa ya hango drivernsa na da wanda yake masa aiki,da saurayine amma yanzu ya ƙara girma.
Lallai an É—au shekaru kam,yafada a ransa.
Yana ƙarisowa ya miƙa masa jakarsa tareda bude bayan motar ya shiga.
Jingunuwa yayi a jikin kujerar tareda sauƙe ajiyar zuciya,ba ƙaramin gajiya yayi ba,tun safe bayyi wani ƙwaƙwƙwaran zama ba,saboda ciku cikun dawowar tasa.
Yayi tunanin ma zaiga su Mulaifah sunzo daukarsa,da alama basu manta yanda ya tsani yaga ana tara masa jama'a ba.
"Ya kke umaru ya bayan lokaci"
"Ahh ogah ka ganeni ne?"
"Ohh meka maidani,saboda bana nan na tsawon wasu shekaru sai akacemuku na rasa hankalina? Bama wannan ba wanne aiki kake bayan bana nan?"
"Uhm ai ogah ina fadamaka bayan tafiyarka da wata shida nayi aure,ga aka koreni daga aiki,na tuka wata kantar É—iban itace haka haka dai rayuwar ta dunga garamin,kwatsam ina zaune sai Neelah tacemin wai kana nemana na dawo aiki. Jinayi tamkar a mafarki. Nagode nagode ogah"
Da ɗan kukansa ya ƙarisa maganar,a haka har suka isa gidan suna taba hira jefi jefi.
Mulaifah tanajin shigowar motarsa gidan ta fito da gudu,dan dama tun ɗazu take leƙawa,yana fitowa daga motar yaga Fatee a gabansa,a ransa yace yaushe wannan kuma tafara murnar ganina.
"Ke kuma fah?"
"Ohh yah Ahmad murnar dawowarka nake mana,zamu sha kallon shagali a gidannan"
Kafeta yayi da ido kafin ya tureta ya wuce,yana kawar da itah yaga Mulaifah tana tsaye ta haɗe fuska,dariyar Fatee ya jiyo a bayansa,sai a sannan ya gane ashe bawai murnar dawowar tasa bace,tsokanar Mulaifah take. Tun sanda ya santa lokacin tana ƙarama haka take da rigima,ashe girman ma bai saka ta daina ba.
Tahowa yayi zai wuce ta gefenta,tayi saurin tarar sa tareda narke fuska.
"Hubby ya zaka wuce,baka ganni bane,tun É—azu nake jiran dawowarka fah"
Gaba yayi abinsa tana binsa tana surutu har suka shiga gidan..
Akan dinning ɗin da aka cika da abinci idonsa ya sauƙa,wanda yasan bazai wuce aikin Mulaifah ba,ko cewa yace mata a tsawon lokacinnan babu abinda ya koya sai cin abinci oho.
"Hubby ka tsaya kaci abinci mana"
Ganin yayi hanyar sashensa wanda sai anbi ta wani corridor a isa wajen,domin yana can ƙarshen gidan.
"Hubby ko nazo na tayaka shiryawa naga ka gaji sosai"
Tsayawa yayi tareda wurga mata wani kallo,ganin da gaske take dan sakarci binnasa zata yi,wani kallon ma amsa ce,bata san lokacin data yi burki ba.
Fatee kuwa mai take jira ta tuntsire da dariyah.
Muryar Mammah sukaji a bayansu tana magana.
"Naji ana cewa mai sunan manya ya dawo,ina yayi ne banga ya shigomin ba?"
"Mammah ya wuce sashensa,kaff a gidan ma babu wanda ya kula,har wacce tayi ta hidima har asubar ma bata samu kallon arziƙi ba"
Jimm Mammah tayi tareda cewa.
"Ƙalau yake dai koh,inaga ya gaji ne shiyasa"
Daga haka ta juya sashennata,sauƙe ajiyar zuciya Maimuna tayi tareda cewa.
"Gaskiya yah Ahmad baya kyautawa da irin wannan halinnasa,yana nan dai wato bai sanja ba sam"
Daga haka itama tabar wajen ranta cikeda haushin yayannata.
Banda mutuniyar ita ko a jikinta,yanzu ma zata sake zage dantse wajen ganin ta mallakeshi.
Hannu ya saka a kunkuminsa yana kallon falonnasa,babu komai a ciki sai fararen kujeru da Tv stand sai cerpet a tsakiya.
ÆŠakuna biyune a side É—in kowanne da banÉ—akinsa sai kitchen.
ÆŠakin farkon ya buÉ—e ya shiga wanda dama shine nasa tun kafin ya tafi..
Shima kaman yanda yake a da hakan yake,kai tsaye banÉ—aki ya fada ya watso ruwa tareda É—auro alwala.
Bayan ya idar da sallah yana tun kafin yagama Addu'o'i yaji wayarsa tayi ƙara.
Miƙa hannu yayi ya ɗauka,sunan Eemran ya gani,hakanne yasa ya ɗauka da sauri.
"Hello sir barka da isowa"
"Yawwa naga ƙiranka,shi kun samu wani abinne?"
"Ehh yanzu Neelah ta ƙirani wai ta samo wani underground a nan garin,kuma bashi da nisa da gidan ajiyar muhimman abubuwa na ƙasa,da alama dashi akayi amfani wajen satar da akayi shekara biyu da suka wuce"
"Shikenan gani nan zuwa yanzunnan"
Da sauri ya tashi kaman an tsikareshi ya fita daga É—akin.
Mulaifah wacce take zaune a wajen dinning sai jin motar sa tayi ya fita daga gidan,da alama taƙofar baya ya fita da take sashensa.
Address É—in da Neelah ta turo masa ya bi,nan da nan ya isa wajen.
Daga waje mutum zai ɗauka cewar gareji ne a wajen,sai ya shiga yaga ƙofa a wajen wacce zata kai mutum zuwa gidan ƙasan.
Tafiya yake yana nazartar ginin wajen,mutum yana gani ma yasan akwai hannun wani babba akan aikinnan,inba haka ba taya barayi zasu samu damar yin wannan gidan.
Ba wannan ne ya girgizashi ba saida yayi arba da harabar cikin wajen,yaushe aka gidannan wajen toh. Yayiwa kansa wannan tambayar.
Eemran ne da Neelah suke jajjagawa suna kallon abubuwan.
Neelah ce tafara ganin shigowar Ahmad da sauri taƙame tareda sara masa,jin haka yasa shima Eemran ya juyo yayi yanda tayi.
"Sannun ku da aiki,amma Neelah ya akayi kika san wanann wajen,bayan duk binciken da muke babu wani clue daya kawomu nan wajen?"
"Uhm jiyane nashiga napep cikin badda kama,anan yake cemin ya taba ganin wani jirgin sama ya sauƙa a filin waje shekara biyu baya da daddare,Sannan wasu mutane da baƙaƙe kaya sun fito daga ciki sun shigo garejin,hakan yasa nace ya kawoni wajen. Da nayi bincike saina na gano ashe gidan sirrine"
A dake take bada labarin babu gargada,wanda hakan yasa Ahmad jinjina mata,duk da cewar bai daÉ—e yana aiki ba hatsarin ya sameshi amma yasan itaÉ—in jajirtacciya ce,wanda ya gwada ta hanyoyi da dama tana tsallakewa,shiyasa ya yarda da ita sosai.
ÆŠakunan cikin wajen suka fara duddubawa,anan har suka shigo É—akin da goje ya zauna.
Wani dumm Ahmad yaji kansa yayi masa,tunda ya shigo gidan yakejin haka,wande Neelah tana kulada shi amma banda Eemran wanda yake ta rubuce rubuce.
"Yallabai lafiya dai naga kaman kana riƙe kai"
"Cikeda kulawa tayi magana,duk da a cikin yanayin aiki tayi tambayar"
"Ahhh bakomai kawai inajin wani yanayine gameda nan wajen,bansan meyasa ba"
A haka dai suka gama dube dubensu kafin suka sanarda headquarter abinda yake faruwa.
Chapter Navigation
Use this section to move to any chapter without going back to the top.