Sanadin Caca Book 2 Complete Hausa Novels By Sadi Sakhna
Reading file: SANADIN CACA 2.txt
Chapter 39 of 42
A asibiti kuwa hajiyah Mammah na tafiyah Ahmad ya shigo asibitin.
Anan suka kwana a wajen hajiyah Maryam É—in har gari ya waye.
Har zuwa lokacin hajiyah Maryam bata tashiba,sai kace matacciyah haka take. Ƙarfin allurar ya ƙare yaci ta tashi amma har yanzu shuru. A.M Aliyu ne ya kwana a kujerar da take gabanta,iyah dare ɗaya amma damuwar da take fuskarsa bazata misaltu ba.
Su Sameer Ahmad da Maimuna suna tsaye a gefe guda,babu mai cewa komai kowa da abinda yake sakawa.
Sallama akayi a ƙofar shigowa ɗakin,Saleem ne ɗauke da kayan karyawa,sai kuma su inna larai itada Hajiya Shukurah.
Gaishe gaishe akayi na kwanan mai jiki.
"Gashi wannan inji inna ladiyo wai na Sumaimah ne,itace mai san É—anwake"
Ya faɗa yana ajiye wata ƙaramar coolar a gefe.
"Sumaimah kuma,jiya fah yah Ahmad ya maidata gida,ko ba gida ka mayarta ba kai?"
Fatee ta faÉ—a cikeda mamaki tana kallon Ahmad.
Shima da mamakin yace.
"Gida na mayar ta mana,saida ta shiga ma kafin na wuce"
"Eh ta koma gida,amma inna ladiyo tace wai bayan sun gama fira sun kwanta,data tashi ƙarfe biyun dare bata kanta ba. Tayi zaton ko tana wajenka shiyasa bata nemeta ba"
"Nida ban kwana a gidaba taya za'ace tana wajena,Sannan side É—ina ma a kulle yake,kuma batada key É—in wajen yanzu. To ina taje kenan?"
Ahmad yayi tambayar a razane.
Kowa hankalin sa ne yadawo kan wannan sabon lamarin,kafin kace me Ahmad yafice da gudu daga É—akin.
Saleem ne yabi bayansa suke tada mota zuwa gidan.
A ƙanƙanin lokaci suka isa,tareda security na gidan aka shiga nemanta,amma babu ita babu labarin ta a gidan.
Don ba kowa a gidan daga su inna ladiyo itada ummi sai kuma hajiyah Mammah wacce a cewarta ta kwana batada lafiya ciwon zuciyarta ya tashi.
Wasa wasa har dare babu Sumaimah babu alamarta,ga hajiyah Maryam ma har yanxu bata motsi,saidai ta buÉ—e idonta tana kallon sama kawai,daga haka babu abinda takeyi.
Yanda sukaga rana haka suka dare aka waye,kowa in ka ganshi kaman ya tashi a jinya saboda tashin hankali.
Ganin sun raba kansu a asibiti da kuma gida ga ciwon hajiyah Maryam an tabbatar musu bana asibiti bane,hakan yasa suka dawo da ita gida aka malamin da zai mata na islamic. Suna dawowa gidan da safe sai gashi yazo,yasha manyan kayansa wai hajiyah Mammah ce tayi masa Magana akan zai fara mata magani.
Maimuna ce da Fatee kawai a gidan saisu inna,sauran mazan dukka basanan suna wajen case É—in neman Sumaimah,wanda aka watsa a media ma amma har yanzu babu takaimaiman labarin ta..
A zaune yake ya zurawa waje É—aya ido,bai taba sanin haka take a cikin ransa ba sai yanzu,bai san wanne irin so mai zurfi yake mata ba sai yanzun,gaba É—aya nutsuwarsa bata tareda shi saboda batannata.
Wayarsa ya ɗauka ya danna ƙiran Maimuna,don itace mai kulada hajiyah Maryam ɗin.
"Hello y kuke ya jikinnata,ta farka ne?"
"Ahah bata farka ba har yanxu,mai maganin da aka turo ma yazo ya fara yimata"
"Waye kuma ya turo mai magani?"
"Hajiyah Mammah ce mana,dama tun a asibiti da Likitoci suka ce ayi na gida tace zata nemo mai magani"
"What mai magani daga wajenta,ganinan zuwa yanxunnan,zan taho da mai maganin,munyi magana dama dashi. Ki tabbatar baki bar mutuminnan shikaÉ—ai da ita ba,Sannan kada ki kuskura ki bari ya tabata har sai nazo tukunna"
Cikeda mamaki ta amsa masa da toh.
Yana kashe wayarsa ya É—au key É—in motarsa zuwa gidan.
Kaman yanda yace Maimuna jansa tayi da wani abun har ya iso gidan.
Suna zaune an saka masa shayi yana sha,ga babbar riga yasaka ƙatuwa.
Jiran gwashin dayace a kawo yakeyi,wanda Maimuna ta É—au lokaci da gangan tana kawowa..
Da sauri Ahmad yashigo cikin É—akin,wanda saida ya razana malamin.
"Kai waye ya aikoka?"
"Uhm ni malamin sayyada ne kakarka,tana É—aukar karatu a wajena,to har aikin maganin aljanu ma nakanyi sosai,shine tace surukarta batada lafiyah nazo naga abinda zan iya yi akai"
Ya ƙarisa maganar yana Murmushi.
"Kaine malamin,a ina ka zama Zambilu? Garin ya takasa gane mai kake aikatawa har ta kawoka kayi wa wata maganin aljanu?"
Zumbur yayi ya tashi da suka haɗa ido da malam Hadi,wanda Ahmad ya taho dashi. Tsakaninsu kar tasan kar ne,dan zambilu riƙaƙƙen ɗan tsubbune mai aiki da aljanu sosai. Malamai sunsha haɗa ire irensu suyi musu wa'azi amma abu ya faskara.
"A ina kuka haÉ—u da itah harta aikoka kayiwa wata magani?"
Ahmad ne ya tambayeshi cikin kakkausar muryah.
"Iyee kunga tunda abin yazama haka inaga na manta gidan daya kamata nazo ne,sai anjimanku ni nayi nan"
Yazo da sauri zai wuce ta bakin ƙofah Ahmad ya tareshi.
"Malam zamu tafi dashi headquater,kai kuma ga nan Maimuna zata taimaka maka ku fara aikin"
"To shikenan mashaallah Allah yabamu ikon yin nasara"
Ahmad yana gama magana ya danƙi hannun Zambilu zuwa waje,kana ganin riƙon da yayi masa kasan babu mutunci a lamarin.
Bayan an sakashi a É—akin duhu ya daku wajen Ahmad kurtun sojojin suka iyo dashi yana makyarkyata,a awa É—aya har kamanninsa sun sanja daga yanda suke.
Ƙafar Ahmad ya kama yana ƙiƙƙifta ido,ba sakin fuska haka ya buge hannunsa tareda riƙo fuskarsa.
"Maza faramin bayanin ya akayi kasan Sayyadar da kake ambata"
"Iyee kamin rai aradu idan tasan mai zan faÉ—amuku zata kasheni muss har lahira"
"Sai akace maka nikuma zan ƙyaleka koh,idan kasake shafe wata daƙiƙar baka bani bayani ba saina ballemaka maƙogaro."
Yawu ya haÉ—iya tareda cewa...
"Nida itah munsan juna tun ba yanzu ba,domin nine nake bata aljanun dazasu kaita wajen ƙungiyarsu,ita kuma tana bani Abubuwa da dama,domin itace wacce shugaban aljanu ya yarada da itah saboda tafi kai mata abinda yake buƙata,hatta manyan ƙasa masu buƙatar nasara sukan shiga ƙungiyarta, mu kuma in an kawo mana bugun ƙasa aljanun dake mata aiki sunfi bada irin waɗannan bayanan..
Yanzu haka ta bani wani aiki na wata yarinya dana É—auke zuwa tsohon gidanta,idan........"
"Wacce yarinya ce?"
"Bansani ba,kawai tace na É—auketa daga cikin gidanku ne,daga nan bansan inda ta kaita ba,amma nasan halinta yanzu haka ta kasheta,in kuma bata kasheta ba to tanada wani shiri akanta ne"
"Innalillahi nasan Sumaimah kake nufi,ka faÉ—amin inda kuka kaita kafin na fasa kanka
yanxunnan"
"Na faÉ—amaka gaskiya bansan inda take ba har raina,bansani ba,amma mai aikinta ce ta sani haka itama,idan kuka bi É—aya daga cikinsu zaku sameta"
Ciza baki Ahmad yayi tareda cewa.
"Ku maidashi kuci gaba da ta'bashi yanda kukeso,saina buƙaceshi tukunna"
SADI-SAKHNA ce
09035784150
*SANADIN CACA*
-BOOK 2 (PAID)
Mallakar *SADI-SAKHNA*
09035784150
Bismillahir-rahmanir-raheem
Ki biya kan ki karantamin na biyu dan Allah. ga number ta nan mai son littafi na É—aya yayi min magana zan bashi shi kyautane.
*BOOK 2*
...37...
Duk yanda Ahmad ya matsa amma ya kasa samo wani ƙwaƙwƙwaran bayani akan inda matarsa take.
An fara samun sauƙi daga wajen hajiyah Maryam dan yanzu har tashi take amma bata magana saidai tabi kowa da ido.
Yanxu ma a zaune suke Maimuna tana haɗa mata maganin dazata sha da zuma. Tun jiya da malam hadi yazo ya ganta baice komai ba,sai magani daya bayar na wanka sha dakuma turare,dukka kuma babu wanda ba'ayi mata ba a ciki,gashi har an samu sauƙi.
Fatee bazakije makarantar bane,yakamata ki gyara caurse É—innan ki tafi services fah"
Karya kai tayi tareda kallon hajiyah maryam wacce take zaune sun data kanta da pillow.
Kallon Fatee take da alamar itama tanaso ta tafi É—in.
"Kingani ki shirya ki tafi,karki damu zata samu sauƙi sis ta tashi tacigaba da tambayarki kinci abinci kuwa?"
Ta ƙarisa maganar cikin janta da abin wasa.
Ƴar dariya tayi ta rungumeta kaɗan kafin ta kalli mommy tasu.
"Mommy ki fara magana da wuri,i miss you"
Bayan ta fita zama Maimuna tayi a kusada itah tareda fara bata maganin kaÉ—an kaÉ—an.
Tana cikin bata maganinne hajiyah Mammah ta shigo tana daddafawa.
Da Maimuna suka gaisa tana tambayarta ya jiki.
"Da sauƙi maimunatu,ya jikin ummantaku,mai maganin yana kawowa dai koh naga tana samun sauƙi"
"Eh yana kawowa,saidai ba wancan É—in bane,wani yah Ahmad ya kawo shiyake mata maganin"
"Ahmad kuma ahh gaskiya ya kyauta sosai"
"Ya jikinnaki hajiya da sauƙi dai koh? Naga kema jikin sai a hankali"
"Uhm na samu sauƙi,saina samu labarin wai Sumaimah matar Ahmad ce kuma abin jajantawar daga gano hakan saita bata,ko suwaye suka ɗauketa oho. Allah dai ya bayyanata"
"Ameen ya Allah,ni nafi tunanin koh a garin zata koma asibitine ta rasa hanya,ko ta haÉ—u da wasu bata gari,amma Inshaallah za'a ganta,koma waye asirinsa zai tonu"
"Hakane kam Allah ya bayyana tah,ni bari zan fitah da driver zamuje likita ya dubamin ƙafafuna."
"To shikenan hajiyah Mammah saikin dawo Allah ya sawwaƙe"
"Ameen Allah yabata lafiyah"
Duk maganar da suke hajiyah Maryam ta tsurawa hajiyah Mammah ido ko ƙoftawa batayi.
Ita kaÉ—ai tasan mai yake faruwa.
Hajiyah Mammah tana fita Maimuna ma ta tashi zata maida kayan abincin da aka kawo.
Riƙo rigarta hajiyah Maryam tayi tareda cewa.
"Maza ki faÉ—awa yayanku Ahmad cewar yafara aikin,ke kuma kibi hajiyah Mammah a bayah,duk motar data shiga ki faÉ—amasa wacce ce shiyasan mai zayyi akai. Yi sauri babu lokaci,kada ta tafi baki san waccece ba"
"Mmmmmommy dama ......dama kina maganaaaa wayyo Allah na gode maka amm......."
"Godiya ga Allah yana da daÉ—i,amma kiyi sauri kiyi abinda naceee"
Cikin saurin jiki Maimuna ta fitah daga É—akin domin ganin wacce motah hajiyah Mammah zata shiga.
Tana fitah hajiyah Maryam ta tashi daga kan gadon,duk da har yanzu jikinta a riƙe yake ga ciwon da ƙirjinta yakeyi,amma dai da sauƙi sosai.
Wayarta ta ɗauka ta ƙira Neelah,bugu ɗaya ta ɗauka.
"Hello Neelah kina ina,tafita yanzu Ahmad zai turamiki lokacation É—in da motar takebi ki zama cikin shiri,koda yake ma kizo ki É—aukeni mutafi zan iya inaga"
"Ahah mommy ko barshi jikinki ba zai iya jurewa ba"
"No dolene naje,ta hakane zan jawo Abbansu zuwa wajen,so nake yau yaga abinda uwarshi take aikatawa,koda kuwa hakan zai zama ƙarshen numfashina,na gaji haka"
Tana haki take maganar tareda saka hijabinta. Ta ƙofar baya ta dafah ta fita inda zasu haɗu da neelan.
Chapter Navigation
Use this section to move to any chapter without going back to the top.