Sanadin Caca Book 2 Complete Hausa Novels By Sadi Sakhna
Reading file: SANADIN CACA 2.txt
Chapter 3 of 42
Kaɗo ya sace abu amma ya manta,mai yafi haka takaici🤔
SADI-SAKHNA CEH
09035784150
ku tuntubeni domin biyan kuɗinku ko ƙarin bayani.
*SANADIN CACA*
-BOOK 2 (PAID)
Mallakar *SADI-SAKHNA*
09035784150
Bismillahir-rahmanir-raheem
Ki biya kan ki karantamin na biyu dan Allah ðŸ™ðŸ¼ ga number ta nan mai son littafi na É—aya yayi min magana zan bashi shi kyautane.
Ina ƴan mata dakuma Matan aure masu muradin burge mazajensu da ɗinkuna zuƙa zuƙa. *PHEEDY TOILORING DESIGN* ,suna gabatar muku da ɗinkuna kala kala wanda sukayi daidai da zamani.
Zaku samemu a kan wannan layin waya kamar haka
09167130115
Wato a manhajar whatsapp. Domin ganin kalolin samufurin aikinmu kuma ku tuntubemu a INSTAGRAM da kuma TIKTOK a @pheedyxacks_ragtrade
Muna maraba daku a kowanne lokaciðŸ™ðŸ¼ðŸ™ðŸ¼ðŸ™ðŸ¼ðŸ™ðŸ¼ðŸ¥°ðŸ¥°ðŸ¥°ðŸ¥°ðŸ¥°ðŸ¥°ðŸ¥°ðŸ’ƒðŸ»ðŸ’ƒðŸ»ðŸ’ƒðŸ»ðŸ’ƒðŸ»ðŸ’ƒðŸ»ðŸ’ƒðŸ»ðŸ’ƒðŸ»ðŸ’ƒðŸ»
*BOOK 2*
...3...
Uhhhh tasake yunƙurin wani aman a karo na ba adadi.
Tun ranar da mijinnata ya bata tamkar wanda aka buÉ—e sabon babin rashin lafiyarta.
Duk abinda taci saita amarshi,sati É—ayane kacal amma duk ta rame da fita hayyacinta.
A gari kuwa dukka ya ɗauka cewar goje ya gudu ya bar Sumaimah,wasu ma har suna cewa dan ya ƙasa riƙeta ne ya gudu ya barta..
Murna da farincikin hakan har da su inna rammah a ciki.
A bangaren innar goje kuwa tana iya ƙoƙarinta wajen kulada Sumaimah,haka shima Tunga koyaushe yana kan hanyar kawo magani.
Tun inna tana cewa ya huta harta daina.
Gobe monday hutun da makaranta suka bawa Sumaimah ya ƙare zata koma,duk da sunce zata iya ƙarawa,amma yanzun da take tsaka mai wuya itada ɗan cikinnata,tana ganin batada mafita saina tayi karatun.
Koda gojen bai dawo ba kaman yanda mutane suke faɗa mata,a ƙalla yabiya mata kuɗin karatunta har ta ƙarisa.
Tashi tayi daga wajen aman magar magar ta nufi sashen innan,gaba É—aya jitake duniyar ta fita mata a rai,meyasa duk lokacin data fara mafarkin daÉ—i saita farkane kam.
Inna tana kallonta ta ajiye tukar tareda binta da ido har tazo ta zauna a kan tabarmar tana fitar da numfashi.
Kallon ta inna tayi cikeda damuwa,tunda suka dawo daga asibiti bayan kwanansu biyu basu ga goje ba,har yanzu Sumaimah bata cewa kowa komai ba,haka gaji zatazo gulma tayi ta magana,amma daga inna har Sumaimah babu wanda yake kulata.
Kallon inna take da zurun zurun idanuwanta kafin tayi magana cikin dishashiyar murya.
"Inna shin da gaskene abinda kuka fada da kawu,cewar dama bakisan waye goje ba,kawai tsintarsa kuka yi uhm"
"Ba dagaske bane Sumaimah,wannan maganar ba haka take ba,kawaidai shi abinda ya sani kenan"
"To in ba haka bane meyasa zai gudu ya barni inna,saida na kamu da sonsa kuma na É—auki cikinsa kafin zai gudu,meyasa zayyimin haka?"
"Sumaimah goje ba guduwa yayi ya barki ba,kekanki kin sani har cikin ranki bazai yimiki hakan ba,dan haka ki daina yarda da maganganun mutane yana batamiki rai"
"Amma inna......"
"Sumaimah ki daina maganar nan yanzu,domin bashine mai amfani ba,akwai wani aiki gagarumi a gabanki wanda ni kaina bazan iya taimakonki akansa ba,abinda zanyi iya yimiki ɗayane kawai,amma shima bazan miki yanzu ba saikinyimin alƙawari ɗaya"
"Wanne irin alƙawari"
"Cewar zaki fitar da komai a ranki ki maida hankalin ki kan karatu,sannan ki raini cikinki cikin koshin lafiya,idan kikayi hakan har Allah ya kaimu da rai da lafiya,nikuma zan taimaka miki kikaga mijinki,namiki wannan alƙawarin"
Ɗaga kai Sumaimah tayi alamar ta yarda da zancen innan,daga nan ta yunƙura ta koma ɗaki domin ta kwanta. Duk da batasan mai inna tasani gameda gojen ba,sannan kuma taya zata haɗata da mijinnata ba,amma abu ɗaya tasani shine ta yarda da innan ɗari bisa ɗari,kuma zatayi yanda tace ɗin.
Washagari da safe da ɗan ƙarfin jiki Sumaimah ta tashi,ba kaman jiyaba da take tamkar maza wuƙa.
Kuma tasha maganin da aka kawo mata wanda duk yawanci vitaminne da zai ƙara mata ƙarfin jiki.
Shirin makaranta tayi kana ta fito daga sashen gojen,tun ranar da suka dawo inna tace ta koma ɗakinta amma taƙi,dan haka dole ta ƙyaleta.
Murmushi tayiwa inna tareda gaisheta,fara'arta ta dawo kaman da,saidai fuakarta tayi fayau kaman wacce tayi gudawa.
Koko da ƙosan da inna tasiyo taci,taƙara shan magani kafin tafita zuwa makarantar..
A bakin ƙofar gidan ta gamuda Tunga yana jiranta akan mashin ɗin gojen,nan ma gaisawa sukayi kafin ta hau suka tafi.
A hanya babu wanda yacewa kowa komai har suka isa,saidai abu É—aya da Sumaimah ta kulada shi shine,Tunga yayi aski yasaka manyan kaya,abinda bata taba gani ba sai yanzu..
"Nagode"
Shine abinda ta faÉ—a kanta a sunkuye,harta juya zata tafi saikuma taji yayi mata magana..
"Kiyi haƙuri da abinda ya faru,nasan hakan babudaɗi amma in kika daure watarana sai labari,Sannan ina mai tabbatar miki goje yana sonki sosai,bazai taba tafiya haka kawai batareda wani ƙwaƙwƙwaran dalili ba"
"Nasani Tunga shiyasa kullum nake masa fatan alkhairi a duk inda yake,Sannan nake addu'ar Allah ya dawomin dashi watarana"
Kuka ne yakusa subce mata,dan haka cikin sauri tashige makarantar tabar Tunga a wajen.
Bayan ta shiga makarantar kai tsaye ajinsu ta nufa,SS 2,suna ma second term yanzu..
Duk inda ta wulga tsit zakaji wajen yayi kamar an É—auke ruwa,saita wuce kuma a fara gulamarta. Wannan ko kaÉ—an baya damunta,dan dama tasan zai faru to tashirya tarbarsa.
Harkar gabanta ta cigaba tayi,tareda yin abinda ya kawota wato karatu,wanda suke magana ma da dasu yanzu ta É—auke kanta daga garesu..
Da aka tashi bata jira Tunga yazo É—aukarta ba,saboda batayi niyyar zuwa gida ba.
Hanyar kogon da goje yayi jinya ta nufah,dan ma babu nisa daga makarantar su.
Bayan tashiga ta daɗe a bakin ƙofar shigar kana daga baya ta zube wajen tareda yin zaman durshen.Kukanta tayi ta ƙoshi hankalin ta kwance,musamman data san babu mai jinta.
Sai bayan ta gama kafin ta nufi wani waje can ƙarshen cikin kogon.
Buɗe ƙasar wajen tayi har tazo kan akwatin dayake cikin ƙasar,babbane mai matsakaicin girma na ƙarfe.
BuÉ—e shi tayi inda tayi arba da wata jaka,saikuma akwatin da goje ya taho dashi a ranar da dawo É—auke da rauninnan.
Ƙurawa akwatin ido tayi,abubuwa barkatai suna mata yawo gameda shi.
ÆŠauke kanta tayi akansa tareda É—aukan jakar da take gefen wajen.
Saita tuna lokacin da goje ya ajiye jakar suna murmushi itada dashi.
Kuɗin saniyarsa ne daya siyar,saikuma kuɗinsa wanda aka bashi na bangar siyasa. Kasancewar Sumaimah tace batason kuɗin fashinsa shiyasa ya ajiye waɗannan kuɗin,a cewarsa tazo ta ɗauka duk lokacin datake buƙatar wani abun.
A lokacin da hakan yafaru Sumaimah bata kawo komai ba,saima shirmansa tada gani na ajiye kuÉ—in,sai yanzu data wayi gari babu shi tukunna komai ke dawo mata daki daki.
Maida akwatin tayi da kuma ƙasar bayan ta ɗau jakar,a cikin tata jakar ta makaranta ta saka tareda fitowa daga wajen..
Wannan gurin ya tara wani bangare na tarihinta da bazata taba mantawa.
"Mijina meyasa,meyasa sai lokacin da zuciyata ta faɗa tarkon soyayyar ka tukunna zakayimin ƙaura,a ina kake a faɗin wannan duniya,daka gagara dawowa garemu. Nayiwa inna alƙawarin cewar zan kwantar da hankalina nayi karatu Sannan na raini ɗanmu cikin ƙoshin lafiya,nasan kaima bazaka so ganina cikin damuwa ba koh?"
Ita kaÉ—ai take sambatunta na tsawon lokaci kafin ta tafi gida.
Tashi gidan kenan suka haÉ—a ido da Deejah,wacce take zaune akan tabarma gefen inna.
Jugum suke zaune babu mai cewa komai,kana ganin idon inna kasan tsoron Deejah takeyi..
Dariya abin yabawa Sumaimah ganin yanda suka zauna É—in.
"Inna na dawo....ke Deejah meyasa kike hararar inna,har yanzu bakiyi hankali ba ko?"
"Uhm ta harareni mana na dafa abinci na bata"
"Ohh gorin abinci zakiyimin,abincin ma da kaɗan kika bani,naga ban ƙoshi ba"
Kallon kallo suke kaman wasu abokan faɗa,hakan ba ƙaramin dariya yabawa Sumaimah ba.
"Ke Deejah zan faɗawa Musbahu fah abinda kikeyi,daga tafiyarsa jiya shine zaki dawo da halinki koh,to inada number sa yanzu saina ƙirashi"
"Nifah tunda nazo ban kulata ba,kawai zama nayi nace jiranki zanyi. Data gama abinci kuma saita sakamin É—an kaÉ—an"
Taƙarisa maganar tana turo baki.
"An saka miki kaÉ—an É—in,danace ki sayomin kayan miya ai cewa kikayi bazakije ba,Sannan abincin saida na cika miki faranti,lokaci guda kika tashi dashi kega karutu"
"To kinji Deejah laifinki ne,Sannan ki daina yawan cin abinnan,domin hakan É—abi'ar jakine,ko kin daina son zama mace Æ´ar gayun"
"Inaso mana,sai ayita cemin banda hankali so nake nazama mai gayu nima,anan ma zan zauna bazan tafi ba,saina zama Æ´ar gayu tukunna"
Zaro ido inna tayi jin abinda Deejah tace.
"Anan zaki zauna? A ina kenan?"
"A É—akinki mana,aradu na dawo gidannan kuma bazan tafiba,dama yah Musbahu ne yake siyamin shayi yanzu daya tafi nasan bamai siyamin,dan haka na dawo gidannan wajen Anty Sumaimah."
"Ahah ahah bazaki zauna a gid......"
"Allah saina zauna inna,naga yah Musbahu ne yace na zo nan É—in,kuma nazo kice bazan zauna ba,kanki zan hau kome,kuma naga har gadone dake shikenan ya zama nawa"
TafaÉ—a cikeda tsalle tana shigewa É—akin,wata ajiyar zuciya inna tayi tareda jijjiga kai..
Ita kuwa Sumaimah abin dariya yabata,haka kawai sai taji zaman Deejah zayyi mata daÉ—i,koba komai zata koya mata abubuwa Sannan kuma ta tabbatar taje makaranta kaman yanda Musbahu yake fata.
Itama yayi mata abubuwa da yawa a lokacin baya,babu abinda zatayi masa sai tayashi gyaran rayuwar Deejan.
Sallah ta saka ta tayi na azahar,daga nan tasake wankan zuwa islamiyyah,tana dai cije cije ta tafi.
"Inna dagaske bakyason zama da Deejah,ko inyaso ta koma can wajena É—akin goje da zama kai?"
"Hhhh ba haka bane Sumaima,tsokanar ta nakeyi kawai,nida na zauna da goje ma wacece Deejah. Zamannata ma zayyi amfani,da alama tanada sauƙin dakuma rashin wayo,wanda zaman jejinne ya tabata. Amma idan har tagyaru za'a ji daɗin zama da ita"
"Uhm nima hakan nake tunani kuma da alama tana buƙatar wanda zai tallafi rayuwarta a wannan lokacin. Ta shiga shekara ta shabiyar fah kaman,kawai wautarta ne da jikinta yasa mutum bazai gani ba.
Yawwa bayan wannan ma dama inason muyi wata magana inna"
"Uhm ina jinki magana wacce iri?"
"Kuɗin da goje ya siyar da saniyarsa wancan watan ni ya bawa,to ban taba ba shine nake tunanin ko zamu fara sana'a dashi. Karmuje kuɗin hannunmu ya ƙare"
"Eh to kinyi maganar hankali anan,amma mai kike ganin zamuyi?"
"Uhm sana'a haka tacikin gida wacce bazamu rasa na kashewa ba,ki kuma kina ganin mu raba biyu mu bawa Tunga wani yafara kasuwanci?"
"Duk yanda kike gani zai dace kiyi Sumaimah domin hangen nesan naki abune mai amfani. Ko aune aune saimu farayi a cikin gidan,akwai wani shagon baban gojen a bakin kasuwa,ko za'a É—aga shi kai a fara sana'a ciki?"
"To shikenan zanyi magana da Tunga gobe,barina kwanta banajin daÉ—in jikina sosai"
Tashi tayi ta nufi É—akin gojen,yana nan yanda yake.
Zama tayi a bakin katifar tana ƙarewa ɗakin kallo,duk sanda tashigo ɗakin sai rayuwar da sukayi ta dawo mata akai,ko mantawa batayi.
Chapter Navigation
Use this section to move to any chapter without going back to the top.