Trending Hausa Novels

Sanadin Caca Book 2 Complete Hausa Novels By Sadi Sakhna

Reading file: SANADIN CACA 2.txt

Chapter 34 of 42

*SANADIN CACA*
-BOOK 2 (PAID)

Mallakar *SADI-SAKHNA*
09035784150

Bismillahir-rahmanir-raheem

Ki biya kan ki karantamin na biyu dan Allah. ga number ta nan mai son littafi na É—aya yayi min magana zan bashi shi kyautane.

*BOOK 2*
...32...

"Am sorry am sorry please i....i can't..........."
Bata gama bayanin ba taji ya rungumeta ta baya.
"Relax"
Shine abinda ya raÉ—a mata a kunne cikin sanyayyar murya.
Rage sautin muryar kukan tafara tana jan zuciya a hankali.
"Ki daina wannan kukan ya isa haka,tun É—azu kikeyi zai iya affecting É—inki, nasan kina tunanin cewa zan takuraki ne saikin faÉ—amin dalili,bazanyi hakan ba zan baki lokaci daga nan idan kin kwantar da hankalin ki ki faÉ—amin gaskiya. Yanzu godiya kawai zanyi ga Allah daya warwaremin matsalata a kusa,Alhamdulillah daya kasance kece."
Nagode da fahimtarka da kuma daÉ—aÉ—anan kalamanka,Inshaallah zan sanar dakai dalilina nayin hakan,kuma nayi ne saboda lafiyarka tawa da kuma ta É—ana,amma bawai don son rainaba"
"Uhm naji,amma duk da haka bazan gamsu ba sainaji mai nene dalilin. Sannan koba komai ni shaidane na kuladani da kikayi da kuma bin hanya mai hatsari wajen ganin kin karemin mutuncina,duk da nasan hadda kishi a lamarin"
Ƴar dariya tayi kaɗan a cikin kukan tareda ɗora hannunta akan nasa,daidai lokacin kuma cikinta yayi motsi.
Daidai wajen ya É—ora hannunsa tareda sakin ajiya numfashi.
"Am sorry for calling you illegal blood.....ƙanin sayyid koh,inada yaro amma bansani ba"
ÆŠaga masa kai tayi tareda murmushi.
"Kayi haƙuri hakan Yazama dolene,nagaji da tsayuwa zan tafi idan na huta in mun sake haɗuwa zan faɗamaka mai yake faruwa,amma kafin sannan dan Allah kada ka faɗawa kowa ni wacece indai ba Neelah ba"
"Taya kikasan Neelah?"
"Labari mai tsayi"
Juyowa yayi da itah tareda share hawayen kan kumatunta.
"Dama haka kike da saurin kuka,shine ya ceceki da kuma tunawa danayi halinda kike ciki,amma da sai raina ya baci sosai"
"Kaima kanada laifi"
TafaÉ—a tareda kallon cikin idonsa.
"Wanne laifi nayi,saboda nakasa ganeki?"
"Ahah ba wannan ba,kafin lokacin da hankalin ka yadawo,na daÉ—e ina zaune a gefenka tareda jiran ka tashi,amma daka tashi baka tasheni ba sai kawai gani nayi baka nan ka tafi ka barni. Kuma nasan ka ganni a wajen gadonnaka"
"Naganki kam,kuma na yarda laifina ne,amma na amshi hukuncina tunda na zauna da matata tsawon lokaci bansan ita bace"
ÆŠan yin baya tayi zata faÉ—i ya riqota tareda tambayar miye.
"Jiri nake É—anji ne,barinaje na kwanta"
Hannunta take ƙoƙarin cirewa daga nasa,amma yasake riƙota.
"Ina zakije barina kaiki É—aki ki kwanta,kinci abinci ma kuwa?"
"Naci saidai inna tashi a bacci na ƙara,ahah ka bari na tafi ɗakinmu,inna zauna anan za'a zargi wani abun,nayi maka alƙawarin zan dawo daga na tashi"
"Nikuma banmiki alƙawarin barinki ki tafiba,domin hankalina bazai kwanta ba. Muje ki kwanta kuma anan sashen,bake ba komawa can kin dawo nan. Har sai kin faɗamin dalilin dayasa karna faɗawa kowa ke matata ce"
Yana gama faÉ—in hakan ya cirata sama zuwa É—akinsa.
Tun tana mutsu mutsun ya sauƙeta har tayi shuru ta haƙura. (Ku tashi mafarki ne😀😀😀)
_____Tashi tayi daga kan kujerar tareda yin hamma,da Ahmad suka haÉ—a ido wanda shima itan yake kallo,duk da kafin sannan hankalin sa nakan system É—in dake gabansa.
Tun lokacin daya raka Musbahu ba direct yashigoba ya tsaya yin waya daga wajen aiki,yana shigowa ya sameta tayi bacci a inda suka barta. Ta gaji amma tasan dole zai tambayeta wani abun saboda baƙon lamari dayaji. Shine a cikin wannan yanayij harta samu damar yin bacci? Harda mafarki? Haba no wonder hakan yake mata kaman bashiba,ashe bada gaske bane.
"Sannu da tashi"
Ya faÉ—amata yana kallonta.
Kunya ce ta kamata ganin abinda tayi.
"Kayi haƙuri"
TafaÉ—a a sanyaye,itama tayi mamakin yin baccinnata yanzu,daga kuka kawai sai bacci.
Tashi tayi ta gyara rigar jikinta tareda É—aukar hijabinta zata tafi.
Har ta fara tafiyah taji maganar sa.
"Na zauna tsawon awa guda ina jiran ki tashi domin ki faÉ—amin dalilinki nayin haka,amma daga tashi saiki tafi?"
"Zanyi sallah ne nasan lokaci yayi"
Ba wani sallah kawai don ta samu excuse É—in fitane.
"Nan sashen baya sallah,ki shiga kiyi sallahr idan kin gama kuma kizo"
"To"
Tace ba musu tareda nufar É—akinnasa.
Daidai lokacin data idar yashigo É—akin,a bakin gado ya zauna.
"Uhmm fara bayani ina jinki,kince kinada dalilinki wanne daliline?"
"Uhmm zaka É—an iyah bani lokaci kafin........."
"Babu wannan maganar,dolene ki faÉ—amin mai yake faruwa,hajiyah maryam tasan ke matata ce"
ÆŠaga masa kai tayi da eh.
"Sannan nasan itace tace kada ki faÉ—amin,shiyasa kwanaki tayi barazana dake domin hanani yin bincike akan ta. Kuma itace ta hanaki faÉ—amin ko?"
Tashi yayi a zuciye yana faÉ—in.
"Barina je wajennata na tabbatar tunda ke ta hanaki magana,kuma kaman yanda bataso kowa sai yasan matsayinki a wajena"
Jin abinda ya faÉ—a Sumaimah batasan lokacin data tashi tariqoshi ta baya ba.
"Karkaje na roqeqa kada ka rushe abinda muke tsarawa,rayuwar mu na tangal tangal akai. Ba hajiyah maryam bace take aikata abinda kake tunani,hasalima duk duniya idan da wanda bazai cutar dakai ba itace."
Juyowa yayi yana yiwa Sumaimah kallon tana da hankali kuwa.
"Eh inada hankali kuma nasan mai nake,na roqeka kabi komai a sannu,makashinka na tareda kai amma ba hajiyah Maryam bace"
"Taya kike tunanin zan yarda da wannan maganar taki,keda bakisan mai yake faruwa ba"
"Saboda ita ɗin......ita ɗin mahaifiyarka ce wacce ta haifeka. Hajiyah Mammah ita ke ƙulla maka komai Tundaga farko. Shugabar kungiyar BC ma da kake nema itace,inada shaidar hakan domin ni jiyau ce ba ganau ba. Nasan lokacin da kake ƙungiyar a matsayin na ɗaya daga cikinsu dan haka tun ranar dana shigo ɗakinnan na farko naga takaddu akan kungiyar,anan nagano kana bincikene akai.
Sannan a ranar naci karo da hajiyah Mammah itada mai aikinta sun shigo ta jikin bangon gidannan.
Ko lokacin dakuka ci nasara akan BC an ƙira an faɗawa hajiyah Mammah abinda kayi a wajen,wanda yanxu haka babban bincikenta nakan ta gano rayuwar dakayi a bayane. Nasan hakanne saboda aikin baɗɗa kama danake a sashenta. Batun mahaifiyar ka ma hajiyah Maryam duk itace ta rabaku,ta ƙwaceka tun kana jariri a wajenta,Sannan tace idan tafaɗawa duniya kai danta ne saita kasheka........duk wanann bazaka gane ba saina baka labarin mai ya faru.
Ta gargaÉ—eni da kada na faÉ—amaka,amma ka riga ka gano wacece ni,dan haka banida zabi daya wuce na faÉ—amaka mai yake faruwa...."
Labarin abinda tasani tunda ga zuwanta gidan ta sanar masa har zuwa yanzun.
Tun sunayi a tsaye har ta samu waje ta zauna,amma shikam bai zauna ba,ya kafeta da ido tunda tafara har zuwa yanxun,jin abinda take faÉ—amasa yayi kaman almara,garin ya hakan ya faru amma bai sani ba.......
Ya tafi dogon tunani lokacin data gama bashi labarin tayi shuru,sai bayan taci gaba ne tukunna ya dawo da hankalin sa kanta.
"Wannan shine dalilina na ƙin faɗamaka ni wacece,amma tsawon wannan lokacin ina cutuwa da rashin sanina da bakayi ba,musamman abinda Mulaifah tayi maka,shiyasa na jefa kaina ba tareda tunanin abinda zai faru ba. Haka ma hajiyah Maryam tana cutuwa da nesanta kanta daga gareka tsawon wannan lokacin,bugu da ƙari ga jinyar da take fama da itah tsawon shekara da shekaru,jiya ma saida aka ƙara mata jini. Jikinta yayi tsanani sosai,abinda hajiyah Mammah take ya kamata a dakatar da itah haka.
Takowa yayi a hankali ya zauna a inda take,kana ganinsa kasan jikinsa yayi matuƙar sanyi.
Hannunta ya kama tareda riƙewa a cikin nasa.
"Shin mai zance dake,kwata kwata ma miyasa ban É—ago ba da ya Musbahu yacemin sunanki Sumaimah,ban taba kawo kece matata danake nema ba shiyasa.
Kinyimin abubuwa a rayuwata ta baya,haka ma kinyimin a wannan. Abubuwan da kikayimin bazan taba misaltasu ba,dan haka godiya ma bazata iyah fitowa daga bakina ba,domin tayi kaÉ—an.
Kuɗin matane da samunsu a cikin al'umma zayyi matuƙar wuyah,nagode da kare min mutuncina da kikayi,nagode da karemin mutuncinki da kikayi,nagode da haifamin ɗana na farko duk da bana tareda ke,Sannan na goɗe da ɗaukamin yaro na biyu duk da bana a cikin hankalina da kuma sani.
Nayi miki alƙwarin nuna miki so da kuma ƴaƴana,zan nuna musu kulawar da ban basu ba a da. Nagode da shigowarki rayuwatah Sumaimah. Har ma da haƙuri dakikayi dani bansan mai zance ba,nasan ba halina da nagartata ce takai ba da har Allah ya hadani dake babu abinda zan.........."
Jijjiga masa kai takeyi ganin maganganunnasa da yawa.
"Karka ce haka,ka wuce duk yanda kake tunani a wajena,kai É—in na dabanne. Koda kana a lokacin baya kana mutunta inna a matsayin mahaifiya,lokacin da banida lafiyah ka tausayamin ka,ka siyamin magani ka sakani a makaranta dana faÉ—amaka ina so.
Sannan da muka shirya kamar sauran ma'aurata kai É—in namijine wanda yasan yadda zai bi da mace. Ko daren mu na farko ma ba.........."
Hannu ta saka a bakinta tareda yin murmushi.
Fitar da hannunnata yayi tareda cewa.
"Mai nayi a ranar faÉ—amin"
"Ahah bazan faɗaba gaskiya,ka ƙyaleni"
Riqota yayi ganin tana ƙoƙarin guduwa.
"Ina zakije bazaki faÉ—amin ba wai?"
"To ka sakeni zan faÉ—amaka"
Yana sakinta ta tashi da gudu,tana dariyah.
"Bazan faɗa maka ba,kayi zuciya ka tuno,abu ɗaya zaka sani shine .......kaƙi ka tashi kayi wanka da kyar na tasheka"
Binta yayi da sauri kafin ya fitah har ta kai bakin ƙofah.
Takalar baƙin ƙofah tayi,cikin zafin nama ya tareda kafin takai ƙasa.
Numfashi take fitarwa sama sama don ta tsorita sosai.
"Habibteee pay attention,kidaina wasa da rayuwarki da kuma na yaron cikinki kinji"
ÆŠaga masa kai tayi da toh.
"Rungumeta yayi,sun daÉ—e a haka kafin ya É—agota dayaga hankalin ta ya dawo kanta.
Kallon idonta yakeyi cikeda so da kuma kulawa.
Itama shiÉ—in take kallo cikeda so da burgewa.
"Kayi haƙuriii!!!"
TafaÉ—a cikin siririyar murya.
"Okay ya wuce amma ki kula nan gaba sosai,muje ki rakani wajen hajiyah maryam ina so nayi magana da itah"
"Toh"

Chapter Navigation

Use this section to move to any chapter without going back to the top.