Sanadin Caca Book 2 Complete Hausa Novels By Sadi Sakhna
Reading file: SANADIN CACA 2.txt
Chapter 40 of 42
∆∆∆∆
Sumaimah (pov)
Yau kwana na uku kenan a wajennan,har yanzu banga hajiyah Mammah ba duk da nasan itace ta bada umarnin a kawoni wajennan,sai wannan mai aikinnata mara imani,jinake da inada dama zan iya yimata komai.
Jikina kaman an jefani cikin ruwan zafi haka nake jinsa,hannuna na saka a kan É—an cikina,tausayinsa nakeji sosai,yunwar da suke barni da itah abinci sau É—aya,ga kuma rashin bacci da azaba,nasan dukka sai ya shafeshi..
Hannuna na É—aga sama ina addu'ar sirri ta Allah ya kawomin mafitah.
Yau har an kai hantsi amma bata zo ba,komai yasa oho. Duk da zata cutar dani amma abincin datake bani shima wani abunne.
Hannuna na kalla wanda aka ɗaureni da sarƙa zuwa jikin ƙaramin gadon dayake ɗakin,to wai tukunna ma nan inane. Gidane mai kyau amma ba kowa a ciki,ko a wanne garine wanne ƙarnine oho.
Jan jiki nake na isa bakin window gidane mai kyau sosai, amma ginin na É—an dane . babbane sosai kuma bakowa,ko ihu zanyi baza'a gane ba.
Wani hawayene ya zubomin kan kuncinah. Ƙarar buɗe ƙofar naji hakan yasa na juyah da sauri,nasan ma wacece tazo....
Ga mamakina wazan gani ya shigo,hajiyah Mammah ce itada kaltum. Wani murmushi tayimin kaman na matar arziƙi,ja da baya nake harna danganta da bangon ɗakin. Ƙirjina banda bugawa babu abinda yakeyi.
"Ohh kinsanma mai kikayi kenan,tunda daga shigowa har jikinki ya fara karkarwa,bansan ke wacece ba inata nemanki,sai gashi kin nunamin kanki da kanki a ruwan sanyi. Kece makasudin karyewar komai nawa,kama daga rushewar ƙungiyata,yaron dana tsana nake son yabi duniyah,shine kika zauna dashi a matsayin miji harda yaro koh?".
Kujera kaltum ta miƙomata ta zauna tana yiwa Sumaimah kallon ɗan tsako.
"Yanzun zaki faÉ—amin inda kika saka kwalbar da kika É—auka kokuma saina miki abinda nayiwa wacce ta gabaceki tukunna"
Kimm Sumaimah tayi da taurin zuciya ga ido a soye tana kallon hajiyah Mammah,vatace komai ba amma kana ganinta kasan batada niyyar yin magana.
Abinda kaltum ta azabtar da itah ta nuna mata,kuka ta saka tana shashshafa jikinta.
"Bazaki samu abinda kike nema ba har abada."
"Nikuwa zan samu,kinsan harda na nuclear information É—in zaki bani,shi ya manta mai yasameshi a baya,amma keda kike matarsa nasan bazaki gagara sani ba. Zaki ce in inaso na kasheki,amma karki manta nasan raunin mu mu mata......kaltum shigomin dashi"
Tana faɗin hakan Kultum ta fita sai gata da sayyid ta riƙo hannunsa,yaron sai kuka yake yana ƙiran deeja,idonsa cabb da hawaye.
Deejah ce ta shigo wani ƙaton mutum ya hankaɗota ɗakin itada inna larai,dukkansu jikinsu ya baci ka shatar duka.
Zaro ido Sumaimah tayi tareda jan hannunta wanda yake É—aure,jikinta yana rawa ta kalli hajiyah Mammah tana jijjiga kai.
"Karki tabamin ahalina,kada ki kuskura ki tabamin ahalina,su basumiki komai ba,ki barmin su"
Kuka take tana fincikar hannunta zata isa wajenda su Deejah suke.
Dukkansu sun nuna alamar tausayi banda Deejah wacce ta haÉ—e rai tana hararar hajiyah Mammah.
"Meyasa kika yiwa Anty Sumaimah haka,mai tayi miki zakiyi mata haka. Uhmmmmmmm(taja numfashi tareda rufe ido).
Baƙin ruhi,ke baƙin ruhi ce,sannan kuma kina amfani da baƙin ruhi......yana kusa ina jiyishi,kin haɗa ruhinki dana Jinsin nas'ass(jinsin aljanune rabi mutum rabi aljani). Mayaudara kana marasa amana"
Bayan ta gama bayanin buÉ—e idanunta tayi ta kalleni. Nasan mai take shirin yi dan haka nayi mata magana.
"Deejah mai kike haka,kada ki kuskura ki koma gidan jiyah,bayan wahalar da kika sha muma muka sha,ban yadda ki koma wannan rayuwar ba"
"Ba komawa zanyi na,tarayyar danayi dasu na tun ina yarinya ne,duk da mun rabu dasu tunda na zabi mutane akansu,amma hakan bashi ya hanasu yimin alƙawarin taimako daya sashi jinsunsu ba. Karki hanani,bake kaɗai suka taba ba,sun tabamin sayyid wanda bazan iya haƙuri ba,yanzunnan zan dawo,zan arawa Harƙeelah jikina na wani lokaci. Kada ki damu tanada mutunci,itace ta cinye kazar inna rammah"
Tana gama maganar tayi Murmushi,kallon mu tayi ta kalli Hajiyah mammah ma kafin ta rufe ido..
Yin hakan keda wuyah ta ta faÉ—i a wajen kaman matacciyah.
"Mai take aikatawa,harƙeelah badai .......aljanar daji bace"
Zaro ido hajiyah Mammah tayi tareda zare wuƙah zata cakawa Deejah,ganin ta tura mata tsafi amma yaƙi cinta.
Ihu nayi tareda runtse ido na,shikenan zata kasheta shikenan........
Jin shuru ne yasani buÉ—e ido,Abbah nagani ya riqe hannun hajiyah mamman,idanunsa sun kaÉ—a sunyi jajur. Bayansa neelah ce,yah Musbahu Ahmad da kuma su Sameer. Iyah Fatee ce kawai babu saisu inna ladiyo da ummi.
Wani daÉ—ine da fatan nasara ya jiyarceni,saidai me.
SADI-SAKHNA ce
09035784150
*SANADIN CACA*
-BOOK 2 (PAID)
Mallakar *SADI-SAKHNA*
09035784150
Bismillahir-rahmanir-raheem
Ki biya kan ki karantamin na biyu dan Allah. ga number ta nan mai son littafi na É—aya yayi min magana zan bashi shi kyautane.
*BOOK 2*
...38...
Fincike hannunta tayi tareda ja da baya tana kallonsu da mamaki,nasan na ganinsu a bazata ne.
"Menene haka Mammah,me nake gani haka da idona ba wanine ya faÉ—amin ba "
Cikin karayar zuciyah yake maganar.
"Meya kawoka wajennan,karka yadda da abinda ka gani ba gaskiyah bane,duk komai inayine domin É—auka maka fansa da kuma sama maka É—aukaka,kaima kasan bazan cutar da kai ba ai"
"ÆŠaukar fansa wacce iri da kike shirin kashe wani"
"Ɗaukar fansa irin wacce ta kashemin mijina,Ta kashemin abokiyar zamana,ta kashemin surukaina da mahaifina,ta rabani da ɗana . ina kallon sa amma ban isa amsa sunan mahaifiya a gareshi ba,ta haɗani Da cutar da bansan wacce iri bace,ta tursasamin auren ɗanta saboda barazanar da takemin da rayuwar dangina. Ta so kashemin ɗana da bata samu nasara ba ta sanadiyyar haka ya shiga duniya. Ya dawo da mata da ɗa. Hakan bayyi mata ba kuma tanason kashe matar da kuma ɗanta harma da danginta kaman yanda tayimin. Wannan ne fansar da take iƙirarin faɗa"
Da hajiyah Maryam ta gama bayanin ba iyah wanda basusan mai ya faruba,har wanda suka sani ma ta basu tausayi.
Babu kaman A.M Aliyu wanda jikinsa yake rawa yana jijjiga kai. Ko a mafarki bai taba ganin mai mugunta irin mahaifiyar tasa ba.
"Mai yasa kika aikata hakan,mai suka menene dalili,na taba cemiki inason waÉ—annan abubuwan?"
"Yimin shuru rufemin baki,nizaka muzanta kuma ka yarda da itah,to ka tabka babban kuskure"
Wani kalamai ta fara faɗa jikinta yana fitar da hayaƙi,yayinda jikin hajiyah Maryam ma yafara bada hayaƙin.
Dukkan mutanen wajen jada baya sukayi, ganin abinda takeyi.
"Dukkan ku babu wanda zai fita daga nan wajen, dolene na ƙareku na........"
"Kece bazaki fita daga nan wajen,miye na amfani da tsafinta tana jikin wani,ki karbeta mana kawai"
Deejah ce take maganar wacce gashin kanta ya tashi yana filluwa a iska,nuna hajiyah maryam tayi da yatsa,take ta fara girgizawa tana wujijjiga.
Baƙin hayaƙi ne yafara fitowa daga ƙirjinta yana haɗuwa.
Kalle kalle hajiya Mammah tafarayi na inda zata shiga,ita kanta tasan idan babu kwalbar a hannunta Harsheelah dama haka takeso.
Shigewa jikinta hayaƙin yayi,lokaci guda kuwa tafara komawa tsohuwarta,jikinta yana yanƙwanewa kamar an zuƙe ruwa a leda.
"Wayyoo banda tsufah banason tsufah bazan tsufa ba,jini jin nakeso Harsheelah zata kasheni inna tsufah haka mukayi da ita.
Wajen da kaltuma take ta nufah tareda kafa hakoranta a wuyanta,ihu tasaka take ta faɗi ƙasa kamar wacce ta mutu.
Jikinta ne yafara dawowa yanda yake. Murmushi tafarayi fusakrta babu alamar nadama a jiki.
Muryar aljanar tata ne yafara amsa kuwwa.
"Ko kiso kokuma kiƙi lokacin ki ya ƙare,koda kin karbi jini dan kiyi ƙarfi toh hakan bazaiyi tasiri akaina ba saboda ba na hannunki,Sannan kwalbar a rufe take bare ki dubani....wannan ƙonawar da akamin a jikin matar nan duk saikin fanshe shi yanzunnan"
Tana gama maganar ta shige jikinta da karfi,wani ihu ta fasa nan da nan jikinta yafara fidda gashi kaman biri.
Durƙushewa tayi a wajen tana wata irin karkarwa da kuka kaman karashiyah.
Bayan komai ya lafa faÉ—uwa Deejah tayi,da sauri Musbahu ya tareta yana jijjiga ta.
Ahmad ma wajen Sumaimah ya nufah yana ƙoƙarin cire sarƙar da take hannunta.
"Akwai key a jiki,gashinan Sayyid yana miƙa maka"
Sumaimah ta faÉ—a cikin raunin jiki.
Juyawa yayi indayaron yake miƙomasa key din daya ɗauka a ƙasa.
Tsurawa yaron ido yayi yana kallonsa ko ba'a fadamasa ba yasan jininsa ne.
Karbar key ɗin yayi ya buɗe hannayenta sarƙar tana zubewa ya riƙeta a jikinsa,ganin yanda jikinta yayi laushi.
Kallon kallo suke na kewar juna.
"Habibtee ruwaaaa"
Daga wannan maganar ta sume a hannunsa.
A hankali nake buÉ—e idona na saukeshi akan farin fentin É—akin.
Inane nan kuma na faÉ—a a raina.
Muryar mutane biyu naji,É—aya babba É—aya ta yaro.
Waiwayar da kaina nayi na saukeshi akansu.
Ahmad ne shida Sayyid sun saka kaya iri É—ayah. Farar riga da bakin wando design.
Idan nace basuyimin kyau ba to wannan ƙaryane,shin mafarki nake kokuma da gaskene.
Murmushi nakeyi duk da kuwa rashin ƙarfi da jikina yake.
Sayyid ne yafara ganina yace.
"Abbi Unni ta tashi kalli"
Da sauri ya waiwayo inda nake,tasowa yayi zuwa inda nake yazo ya zauna.
"Alhamdulillah nagode Allah da kika tashi"
"Naga ka damu kwanana nawa a haka"
"Kwananki uku hayatee,likita yace an bawa jikinki wahala sosai,kina buƙatar hutu shiyasa baki tashi ba. Ga kuma bake kaɗai bace"
"Uhm zansha ruwa kuma yunwa nakeji"
"Okay barina baki ruwan kafin na ƙira nurse ɗinki ta duba jikinki ta kuma bada wanne abincin da zaki iya ci"
"Amma nan inane naga kaman gida amma kuma nan É—akin asibitine"
Murmushi yayi tareda kama hannuna.
"Gidanki ne kuma asibitinki ne, kina ɗauke da cikin twin baby,Sannan likita yace jikinki bashida ƙarfi yana buƙatar kulawa. Nikuma banaso ki zauna a asibiti,shiyasa akayi creating ɗaki mai dauke da duk abinda kikeso na asibiti,na ɗauka miki nurse da zata dunga kulada ke har zuwa ki sauka lafiyah"
Farincikine marar misaltuwa ya kamani ganin irin kulawar dayake bani,dama zan samu irin wannan kulawar haka.
Bayan nurse ta dubani porridge aka kawomin na wake yasha kifi. Sosai naci son cina yana nan. Ina cikin ci ne inna larai ta shigo.
"Oh kintashine uwar biyu?"
"Uhm na tashi inna,yaushe kikazo na ganki kaman kin daÉ—e"
"Lahh hala Amadu bai faÉ—amiki ba,tare muka dawo ai dan kina kwancene,a can sashen dayake daya vangaren muke,Deejah ma bata nan ta tafi makaranta data shigo"
"Mashaallah dan Allah inna kuna nan, ina ummee,ya jikinta ta warke?"
"To da sauƙi dai,amma wannan ciwon kam tunda dalilinsa ya tafi to babu shi,rashin ƙarfin jikine,jiyama tazo dubaki kina kwance"
"Ayyah amma komai yayi babu wata matsala koh inna"
"Babu komai saidai muce Alhamdulillah,dama abinda nake faÉ—amiki kenan,mahakurici shi mawadaci ne watarana.
Sumaimah yanzu kinsamu soyayyar mijinki data dangin mijinki saura kuma idan kin ji sauƙi kuje gidan iyayenki su ganki,duk da ga zaman da kukayi amma suɗin naki ne"
"To shikenan inna zanje,nagode da kika tallafeni kika zauna dani a halin ƙuncina inna,keɗin uwace wacce bazan maye mata kurbiba nagode sosai da sosai"
"Matar yallabai ance kin tashi gani nazo yimiki tijara,dama haka abin yake ashe?"
"Ummi ykk"
"Kinga rufemin baki karkice komai"
"Ummi ba haka bane,a lokacin......"
Rugumeni naji tayi tareda cewa..
"Nasani kowa yaji labarin komai Sumaimah,haƙiƙa kinga jarabawa,saidai gashi Allah ya miki sakayyah da mifificin alkhairi. Allah yabaku zaman lafiya ya sauƙeƙi lafiya"
"Ameen ummi nagode"
Chapter Navigation
Use this section to move to any chapter without going back to the top.