Sanadin Caca Book 2 Complete Hausa Novels By Sadi Sakhna
Reading file: SANADIN CACA 2.txt
Chapter 7 of 42
Tafiya hausawa suka ce yankin azaba,Musamman da mutum bai taba yiba.
Ba ƙaramar wahala nasha ba kafin mu isa,ga kirjina har yanzu bai daina ciwo ba na yayen da nayi.
Sallahr azahar da la'asar mukayi nida wata mata mai ƴaƴa biyu a tashar bayan mun sauƙa.
Sai surutu take yimin,irin mutananne masu magana,ganin ban bata lokaci sosai ba yasa ta koma yi da Æ´aÆ´an ta.
ÆŠari biyu na É—auka a cikin kuÉ—ina na siya lemo da biredi,wata Æ´ar ta sai kallona take kaman zata cinyeni,wasu yaran fah dama haka suke da kwaÉ—ayi.
Bayan nasha miƙa musu sauran nayi da sauri suka fizge har suna haɗawa da hannuna..
Tashi nayi na É—auki kayana na nufi wajen masu taxi,ina ji tana min godiya ko waigawa banyi ba,abin yabani haushi sosai,Æ´aÆ´a kaman goyon gwauro.
Kaman dama jira suke da sauri suka nufoni,kowa ya ƙokarin wajen ganin shi ya karbi kayana,nidai da ido na bisu,kafin na bi wanda yayi nasarar karbar kayannawa.
"Hajiya ina za'a kaiki?"
Shine maganar sa ta farko bayan na shiga motar,ban san me zan ce masa ba,dan haka na miƙamasa takardar da inna ta bani. Ajiyar zuciya na saki ganin ya gane address ɗin jikin takardar.
Kai tsaye kuwa ya kunna motarsa domin ya kaini.
"Hajiya kuÉ—inki É—ari biyar ne"
"Ehh É—ari Takwas kuma,kaman za'a bar gari dani?"
"Hhhh hala wannan ne zuwanki garin abuja na farko,ai haka abin yake"
"To shikenan nidai ka kainin tukunna"
Dama dubu ɗaya ce ta sauramin ɗaka da waje,dan haka ba musu ba miƙamasa ita ya vani ɗari biyu.
Jingina kaina nayi ta jikin motar tareda lumshe ido,na gaji matuƙa gaskiya yau..
Sama sama naji yana min maganar cewar mun iso,ashe har bacci ya fara É—aukata ban sani ba..
Fitowa nayi nida jakar kayana,bakina buÉ—e ina kallon tangamemen gidan da ya ajiyeni a gabansa..
Na dade a tsaye ina kallon gidan,har van lokacin daya ja motarsa ya tafi ba,har na juya zan tambayeshi anya nan ne kuwa,naga wayam babu shi babu labarinsa.
Ohh ni Sumaimah ina na kawo kaina haka?
Nayiwa kaina wannan tambayar.
Kafaɗa a sanyaye na ƙarisa bakin get ɗin naman jikina ta ciki yana rawa.
Na saka hannu zan ƙwanƙwaƙwasa kenan naji muryar wani mutum yana min magana. Sanye yake da wandon sojoji da t-shirt a jikinsa.
"Hey madam what are you looking for?"
(Baiwar Allah wa kike nema?)
Ohh ance ilimi rahama ne kuma babba baiwa ce,koda baka buƙatarsa a sannan kayishi watarana zakaga amfaninsa,cikeda ƙwarin gwiwa na mayar masa a harshen nasarar da yayimin magana dashi.
"Um sir am looking for Inna ladiyo,she is maid in this place"
(Malam ina neman inna ladiyo ne,tana aiki anan)
Ganin na mayar masa amsa yasa ya rage yimin kallon walaƙancin daya faramin daga farko. A haka muka yi ɗan magana dashi har nake cemasa ni ƴar uwarta ce.
Budemin gidan yayi na shiga,abinda banyi zaton zaiyi ba.
Tafiya nake kaman baƙyauye a kano,jinayi na bugi wata mace karaff.
Saurin maido da hankalina nayi jikina,wanda ya tafi da kalle kallen dogon ginin dayake gabana..
Macece matashiya amma tafini daga gani,tana sanye da kayan sojoji itama a jikinta,wai nan gidan sojoji ne ne,na faÉ—a a raina..
"Sorry am sorry madam,banganki bane"
Hakuri nake bata,amma ko kulani batayiba tayi hanyar wajen da wata tamfatsetsiyar mota take fake a gefe.
Ganin hakan yasa da sauri na shige wata ƙofa da na gani.
Wata mata na gani zata wuce,dattijuwa ce tana É—auke da wani bokiti a hannunta. Tayimin kamada Æ´ar aiki,amma kuma kayan jikinta ko wata mai wadatar a garinmu albarka,koda yake wazai haÉ—a da nan da can.
Saurin isa gabanta nayi ina yimata alamar ta tsaya.
Da mamaki take kallona,ganin bata sanni ba..
Amfani nayi da shurunta na gaisheta,Amsawa tayi a gajarce tana min kallon mai ke tafe dake?
"Uhm dama inna ladiyo nake nema,an aikoni wajenta ne"
"Waye da aikoki?"
"Inna mairo ce daga DABAGAYI,dan Allah kinsanta?"
ÆŠan murmushi tayimin na manya tareda cewa.
"Nice ai ladiyon,mairo ce ta aikoki innar goje?"
Jijjiga kai na fara tamkar ƙadangare,tareda jin farinciki ganin yanda kayana ya tsinke a gindin kaba.
Alama tayimin akan na biyota,muna tafiya ina kalle kalle har muka isa inda nayi tunanin muhallin masu aikine.
"Ki ajiye kayanki ki huta,zanje wani waje na dawo,idan hajiya taƙiraki ko wani a gidannan karki kuskura kice masa mairo ce ta aikoki,kicemusu ke ƴar yayana ce daga Zarawa"
To nace mata daga nan ta fice,komai yasa zan boye oho.
SADI-SAKHNA CEH
09035784150
ku tuntubeni domin biyan kuɗinku ko ƙarin bayani.
*SANADIN CACA*
-BOOK 2 (PAID)
Mallakar *SADI-SAKHNA*
09035784150
Bismillahir-rahmanir-raheem
Ki biya kan ki karantamin na biyu dan Allah ðŸ™ÂðŸÂ¼ ga number ta nan mai son littafi na É—aya yayi min magana zan bashi shi kyautane.
Ina ƴan mata dakuma Matan aure masu muradin burge mazajensu da ɗinkuna zuƙa zuƙa. *PHEEDY TOILORING DESIGN* ,suna gabatar muku da ɗinkuna kala kala wanda sukayi daidai da zamani.
Zaku samemu a kan wannan layin waya kamar haka
09167130115
Wato a manhajar whatsapp. Domin ganin kalolin samufurin aikinmu kuma ku tuntubemu a INSTAGRAM da kuma TIKTOK a @pheedyxacks_ragtrade
Muna maraba daku a kowanne lokaciðŸ™ÂðŸÂ¼ðŸ™ÂðŸÂ¼ðŸ™ÂðŸÂ¼ðŸ™ÂðŸÂ¼ðŸ¥°ðŸ¥°ðŸ¥°ðŸ¥°ðŸ¥°ðŸ¥°ðŸ¥°ðŸ’ƒðŸÂ»ðŸ’ƒðŸÂ»ðŸ’ƒðŸÂ»ðŸ’ƒðŸÂ»ðŸ’ƒðŸÂ»ðŸ’ƒðŸÂ»ðŸ’ƒðŸÂ»ðŸ’ƒðŸÂ»
*SANADIN CACA*
-BOOK 2 (PAID)
Mallakar *SADI-SAKHNA*
09035784150
Bismillahir-rahmanir-raheem
Ki biya kan ki karantamin na biyu dan Allah ðŸ™ÂðŸÂ¼ ga number ta nan mai son littafi na É—aya yayi min magana zan bashi shi kyautane.
Ina ƴan mata dakuma Matan aure masu muradin burge mazajensu da ɗinkuna zuƙa zuƙa. *PHEEDY TOILORING DESIGN* ,suna gabatar muku da ɗinkuna kala kala wanda sukayi daidai da zamani.
Zaku samemu a kan wannan layin waya kamar haka
09167130115
Wato a manhajar whatsapp. Domin ganin kalolin samufurin aikinmu kuma ku tuntubemu a INSTAGRAM da kuma TIKTOK a @pheedyxacks_ragtrade
Muna maraba daku a kowanne lokaciðŸ™ÂðŸÂ¼ðŸ™ÂðŸÂ¼ðŸ™ÂðŸÂ¼ðŸ™ÂðŸÂ¼ðŸ¥°ðŸ¥°ðŸ¥°ðŸ¥°ðŸ¥°ðŸ¥°ðŸ¥°ðŸ’ƒðŸÂ»ðŸ’ƒðŸÂ»ðŸ’ƒðŸÂ»ðŸ’ƒðŸÂ»ðŸ’ƒðŸÂ»ðŸ’ƒðŸÂ»ðŸ’ƒðŸÂ»ðŸ’ƒðŸÂ»
*BOOK 2*
...7...
Ina nan zaune a bakin katifa naji alamar shigowar mutum.
Inna ladiyo ce ta dawo hannunta É—auke da kwanon abinci.
Tashi nayi na karba a hannunta kana na ajiye a tsakar É—akin.
"Sannu na barki ke kaÉ—ai koh,naje kawo miki abincine,sannan munyi magana da hajiya yanzu.
In kinci abinci kizo zatayi magana dake,ki kula sosai nasan mairo ta fadamiki haka koh?"
Daga mata kai nayi alamar ehh,daga nan ta juya ta fita,zama nayi a gaban kwanon kafin na bude a hankali.
Sakwarace a ciki da miyar ganye,kafin nasaka hannu ma sai ƙamshi takeyi.
Ban bata lokaci ba na saka hannu bayan nayi bismillah na fara zubawa cikina.
Duk yanda naso na cinye malmalar sakwarar guda biyun kasawa nayi,dan ina cin guda ɗaya naji na ƙoshi,ta biyun kada na taba..
Kwanon na tattara wai zan fita dasu,a nan gizo ke saƙar ina zan nufah a wannan tangamemen gidan haka..
Wani mutum na hanga a gefe dani na tambayeshi hanyar kitchen,gyaran wasu fulawowi yakeyi,da alama aikinsa kenan.
"Baiwar Allah ta ina zansan inda hanyar madafa take,wannan ai sai su ladiyo,amma naga sunayin wancan corridor da yayi dama"
Godiya nayi masa daga nan nayi wajen daya faÉ—amin.
Tafiya nake ina Addu'a a raina har na samu kaina a wajen dana tabbatar madafar ce,duk da bayyimin kama da wanda na saba gani ba. Wannan waje haka ƙato.
Kwanon hannuna na ajiye akan wani tebur dana gani a gabana,har na juya zan fita naji muryar wata matashiya.
"Ke daƙiƙiyar inace dazaki ajiye kwano a wajen da ake yin girki,ko kyauyen cinki bai nuna miki canne wajen wanke wanke ba"
TafaÉ—a tana nuna min wani waje mai dan rami da famfo a wajen,wanda ni sai yanzu ma na kulada shi.
Maida kaina nayi kan fuskarta,budurwa ce ko kuma nace ƘARAMAR BAZAWARA(littafin ummu najam amarsisi nayi miki miss).
Domin daga ganinta bazata fini ba.
Wasu kwanuka take jerawa a cikin wardrope,fuskarta a haÉ—e kaman anyi mata mutuwa.
"Daƙiƙiya? In daƙiƙiya ce ni ashe kekuma kece babbar daƙiƙiyar wacce ta daɗe ma a ciki,domin in ƴan aiki kike ƙira d daƙiƙai to kece babbarsu wacc....."
"Sumaimah ya isa haka,ke kuma Ummi bai kamata kina walaƙanta mutane ba duk sanda kika gansu,ke idan ba mai kuɗi ba to kowa ba kaman ba mutum ba haka yake a wajenki"
Wacce ta ƙira da ummin ta kalla tana yiwa faɗan,ana mata maganar ma tana wani fisfisgewa,wanann daga gani bata da daɗi,in kuwa hakane halinta to batada kirki sam..
"Inna ladiyo wai bakya ganine,ya za'ayi kawai ka kawo kwano ka ajiyeshi a wajen da ake abinci"
"To naji amma dai ai kinsan sabuwar zuwace ko aiki bata fara ba"
"Duk da ai......"
"Kinga ya isa haka,kici gaba da da gyaranki,ke kuma muje na gabatar dake a wajen matar gidan,anyi sa'a ma yau tana gidan"
To nace mata tareda bin bayanta muka fice daga wajen.
Kafaren wani hamshaƙin falo na tsinci kaina a ciki,dama irin wannan gini haka dole mutum yayi tunanin irin kayan alatunnan a cikinsa.
Wata mata ce a zaune akan É—aya daga cikin kujerun falon,ta saka wani kaya da ban wanne iri bane,amma ko daga gani kasan masu kyaune da tsada.
Abinda yafi bani mamaki shine,meyasa nakejin faÉ—uwar gaba dana haÉ—a ido da ita na farko,hmm anya kuwa wannan irin mutanen da mutum zai iya sakewa dasu?.
Tsugunnawa nayi a ƙasa kaman yanda naga inna ladiyo tayi.
"Hajiyah barka da warhaka,g ta nan na kawomiki itah,tazone domin ta samu aiki,da fatan za'a taimaka"
"Hajiyah barka da yamma"
Nima na fada cikin girmamawa,ganin ta kafeni da ido.
Can munyi shuru kaman ruwa ya cinyemu,nida inna ladiyo sai zazzare ido muke.
Jan ajiyar zuciya tayi tareda zare farin glass É—in dayake idonta.
"Ladiyo banason wani magana yanzunnan,kuma ba kin faÉ—amin zuwanta ba É—azu...huhh wancan yaron dama ya dawo gidan,naji waccar tsohuwar nayin mitar kan kan a samu masa wata mai aikin,tunda waccar mun sallameta,kuje ki nuna mata yanda zatayi,in kuma ta kuskure itama ya koreta kaman yanda ya saba toh sai tasan yanda zatayi.
Albashinki dubu ashirin a wata shin yayi miki ko kuwa"
Tun daga ambaton aikin naga ladiyo ta sha ruwan jikinta,koma menene naga da alamar wanda zanyiwa aikin bashida daɗin sha'ani,koma dai menene tunda naji batun dubu ashirin zanyi iya ƙoƙarina wajen ganin nayi nasara.
"Yayimin hajiyah nagode Allah yaƙara buɗi yasa kifi haka"
"Ameen ku tashi ku tafi toh,in wata yayi zanyi miki magana,idan har kina gidan har zuwa lokacin. Sannan kuma karki sake ki nuna masa cewar nina ɗaukeki aiki,kawai kice masa kin fito ne a jerin wacce zatayi masa aiki. Abu na ƙarshe banason ki yaudareni,Sannan ko nan gaba na buƙaci haɗin kanki akan wani abun dole zaki bani"
"Inshaallah hakan bazai gagara ba hajiya,kuma da sannu zanyi yadda kika ce"
Chapter Navigation
Use this section to move to any chapter without going back to the top.