Sanadin Caca Book 2 Complete Hausa Novels By Sadi Sakhna
Reading file: SANADIN CACA 2.txt
Chapter 10 of 42
Ahmad (POV)......
Tunda na tashi na kasa daina mamakin abinda ya faru jiya,ina cikin aiki da daddare naji tamkar an lullubamin bargon bacci ƙarfi da yaji.
Ko dai kai duk yanada alaƙa da ban warke ba? No amma shi bayamin haka,saidai na ɗanji ciwon kai daga baya kuma ya tafi.
Bayan nayi sallahr asuba ban koma ta kan aiki ba,sai kawai na kwanta..
Ƙarar wayata ne ya tasheni,anan naga irin makarar danayi,tara da wasu mintunan duk ina gida?.
A gurguje na shirya na fito daga É—akin,hankalina na kan agogon hannuna naji nayi gware da itah,itace dai wannan yarinyar ta jiyah. Kallona ta cigaba dayi kaman najiya,duk da tasan na hanata,kuma ba kallon tsoro takemin ba kona shakkah,kallo takemin kaman wacce ta sanni.
Tun jiya naso na koreta,amma data roƙeni saina tsinci kaina da kasa korar tata,ko wani abu tayimin kai kafin tazo aikin.
To yanzu kuma komawata É—akin a wajen takarduna na ganta,mai yakaita wajen su?
Yawancin masu aikin gidannan basu iya karatu ba,amma kuma ita batayimin kamada Æ´ar kyauye wacce batayi karatu ba.
Inda bincike takeyimin da zata tsorita da ganina,amma maimakon haka saima yimin kallon na cika ƙorafi da tayi.
"Ohhh sauri fah nake zan tafi wajen aiki,meyasa kuma na tsaya a mota ina tunanin da bashi amfani"
Yau bazan shiga cikin gida ba,idan na dawo na shiga.
Tafiya nake sa sauri na daidai misali,yau banbi da cikin gari ba,hanyar baya na ɗauka domin nayi,saboda kar cinkoso ya riƙeni.
Daidai zan wuce ta gaban wani hotel,na tsaya ganin wani ƙira ya shigo wayata.
Kaman ance na ɗaga idona,Mulaifah na gani itada wani zasu Fito cikin hotel ɗin. Kenan anan ta kwana? Mammah kuwa tasani,kai ba lallai tasani ba,nasan wayo zatayimata takawo uzurin ƙarya da gaskiya ta faɗa.
Kayan jikinta ma na fara kalla,babu ko É—ankwalin a kan ta sai wani gashin doki kaman ba musulma ba.
Ga wasu riga da wando damammu,shi kansa wanda take tareda shi É—in bayyi kama da musulmin ba,in ma shine to ba hanyar daidai yake bi ba.
Aski ne kansa mai irin wani wajen akwai wani wajen babu,ya saka wata sarƙar gwal a wuyansa.
Sai dariya suke ya wani rungumeta tamkar matarsa,wani ƙululun baƙin cikine ya turnuƙe a zuciyata.
Hada alaƙa danayi da itah shine ya sakani jin haushinta,babban wani abin takaicin ma wai hakan takeso na jata cikin rayuwata. Koda batada irin wadannan abubuwan ma ita ba tsarina bace ballantana kuma yanzu.
Ina kallonsu suka shiga mota,saida suka bace kafin naja tsaki nima naja tawa motar.
Ni inaga cikin barrack ma zan koma da zama,bansan yanzu ko Abbah zai barni ba.
Fitowa nayi daga motar bayan nayi parcking,office É—in Abbah na nufah.
Nazo shiga office É—in kenan naji kamar muryar Sameer yana magana da Abbah.
"Abbah wlh dagaske nake maka,duk da cewa darene amma fa ni kamar shinagani a cikin waɗannan mutanen,shima naga ya tsaya yana kallona da mamaki. Shi yafara ciremin hula kafin nima nacire masa,zanyi masa magana kenan naji an ƙwaɗamin ƙasan bindiga a kaina,har na jimasa ciwo ma a gefen cikinsa na dama"
"Ya isheni wannan zancen Sameer,kai kanka kasan wannan ba abune da hankali zai É—auka ba,É—an uwanka bazai taba aikata abu irin wannan ba"
"Nasani Abbah shiyasa abin yabani mamaki,amma wlh....."
"Ya isa haka kaje zanyi bincike akai,koma ya ake ciki duk zakaji,shin kungama abinda kukene naga ka dawo jiya da daddare?"
"Ahah bamu gama ba,jirgin yau da yamma zanbi na koma"
"To kaje Allah ya taimaka"
Ina nan tsaye a bakin ƙofar kamar gunki naga Sameer ya fito daga office ɗin,kallon rashin yarda yayimin kafin ya raba ta gefena ya wuce.
Zancena suke,kaddai zancen Sameer gaskiya ne kai, ciwon dana tashi na gani a gefen cikina na dama na shafa,kasancewar rauni ne mai girma tabonsa babbane.
Kaina ne naji yana juyamin,hakan yasa na fasa shiga office din na nufi nawa kawai.
SADI-SAKHNA CEH
09035784150
ku tuntubeni domin biyan kuɗinku ko ƙarin bayani.
*SANADIN CACA*
-BOOK 2 (PAID)
Mallakar *SADI-SAKHNA*
09035784150
Bismillahir-rahmanir-raheem
Ki biya kan ki karantamin na biyu dan Allah. ga number ta nan mai son littafi na É—aya yayi min magana zan bashi shi kyautane.
Ina ƴan mata dakuma Matan aure masu muradin burge mazajensu da ɗinkuna zuƙa zuƙa. *PHEEDY TOILORING DESIGN* ,suna gabatar muku da ɗinkuna kala kala wanda sukayi daidai da zamani.
Zaku samemu a kan wannan layin waya kamar haka
09167130115
Wato a manhajar whatsapp. Domin ganin kalolin samufurin aikinmu kuma ku tuntubemu a INSTAGRAM da kuma TIKTOK a @pheedyxacks_ragtrade
Muna maraba daku a kowanne lokaciðŸ™ÂðŸÂ¼ðŸ™ÂðŸÂ¼ðŸ™ÂðŸÂ¼ðŸ™ÂðŸÂ¼ðŸ¥°ðŸ¥°ðŸ¥°ðŸ¥°ðŸ¥°ðŸ¥°ðŸ¥°ðŸ’ƒðŸÂ»ðŸ’ƒðŸÂ»ðŸ’ƒðŸÂ»ðŸ’ƒðŸÂ»ðŸ’ƒðŸÂ»ðŸ’ƒðŸÂ»ðŸ’ƒðŸÂ»ðŸ’ƒðŸÂ»
*BOOK 2*
...10...
"Wayyo bayana"
Na faÉ—a ina kama kunkumi,gaskiya na dade banyi aiki mai yawa irin wannan ba.
Mopar na É—auka da bokitin ruwan dattin na fita dasu. Dawowa nayi ina kallon gyaran,gaskiya ya burgeni sosai,kalar kitchen É—in ya fito sosai kaman ba shiba.
Saidai ba girki za'ayi a cikiba,dan babu kayan abinci ma a ciki,na faÉ—an ina sunkuyar da kai.
Hanyar sashenmu na nufa nayi domin na tsaftace jikina,ga ƙura ga kuma dama ina son yin wankan..
Rana tayi a lokacin,dan har an fara kiran sallah a wasu masallatan na anguwa.
Hanyar cikin gidan na nufah,anan na haÉ—u da wannan wacce taje sashen Ahmad jiya.
Motarta ta buÉ—e ta fito,hannunta É—auke da key É—in mota tana kakkaÉ—awa..
Murmushi take da alama tana cikin yanayi mai kyau kenan,bata kuladani ba tashige cikin gidan. Nima yafimin,dan tun haÉ—uwar da mukayi jiya haka kawai naji bana sonta.
"Sumaimah ina kika shigane,daga zuwa gyaran sashe ɗaya sai yanzu kika dawo? Kizo to inna ladiyo tana nemanki,an ƙara miki aikin sashen hajiya maryam,mai aikinta bata nan ta tafi gida anyi mata rasuwa,kuma naji ana cewa wai aure zatayi"
"Kai aure kuma,yanzu shikenan aikina ya ƙaru?"
"Ohh da kinace a iya gyaran waccan wajen za'a baki dubu ashirin,nida kika ganni nan bayan wanke wanke ina gyaran sashen Æ´an biyun gidan"
"Suwaye kuma Æ´an biyu ohh sorry ashe inna ladiyo tafaÉ—amin yanda gidan yake da mutanen,wacce tashigo yanzu itace Mulaifah koh?"
Naƙarisa maganar a hankali kar a jiyoni.
"Ehh itace kinga ni inada aikinyi ba surutu ba,maza kije ki kai mata abinci,babban falo ma yana cikin sashenta,ke zaki dunga kulada shi keda Kultum"
"Wacece kuma Kultum?"
"Inkin fara aikin zaki santa ai,tana aikin kulada kaiwa abinci da kuma gyara sashen hajiya Mammah"
Wai da alama fah saina maida hankali,naga alamar bansan abubuwan gidan ba sosai,ta wani bangaren kuma naji daÉ—in yin aiki a sashen hajiyah maryam koba komai zan gano wacece ita..
Falon nata na shiga,babu kowa sai wata mata tana rubutu a system ɗin gabanta,farace kamar mamar tasu,tasa ƙaramin glass a fuskarta,ko ba'a fadaba nasan itace Maimuna,don Fatee itace ƙaramace ba kaman wannan ba,shekarar ƙarshe take a jami'a.
"Barka da rana hajiyah"
NafaÉ—a ina rusunawa,É—agowa tayi ta kalleni tareda yimin murmushi.
"Yawwa barka,amma kidaina cemin wannan hajiyar,anty Maimuna ma ya isa,kece wacce zata ƙarbi Amina kenan?"
Duk da bansan wa take nufi ba amma nasan wacce ta tafi take nufi.
"Eh nice"
"Ayya ki fara aikinki kawai,karki damu dani,amma ki fara da gyara ciki tukunna"
To nace tareda shigewa ciki,nazo buɗe ƙofar kenan naji ana magana sama sama.
"Hmmm kinji wata sabuwa kuma du,wai yanzu abin ya koma kan wa zai aura,aure ma yanzu bai isa yayi ba,saboda hakan matsala zai jawo. Ni na gaji da wannan abun sam"
Cikin masifah take maganar,mutum bazai gane haushin maganar takeji ko kuma haushin shi mai yin auren ba.
"Ta mutu mana ni mai ya shafeni dama yarinyar ba sonta nake ba, tunda ya dawo iya shegenta yafi na da,nakula baya son ita take rawarta take kiÉ—inta...............har yanzu babu wani zance ina gameda akwatinnan?
Gwanda ma da bai bayyana ba,dama banason yashiga wannan shugaba na ukun ballantana kuma hannun ta,to amma a ina kikega yake?........
Uhm mtsw wancan ba? shima so yake ya kawomin ciwon kai........,kedai ki cigaba da kulada abinda yake,nayi tunanin daya dawo zai bar wannan aikin ya kama wani,amma na kula taurin kaine dashi,zanyi magana dashi nayi masa gargaɗi idan yaƙi dainawa kuma bansan me zanyi ba gaba"
Maganganun sun isheni haka,a da inda zare mai baki kala kala,amma bansan a ina suke ba. Yanzu kuma na fara kamo bakin zarurrukan. Babu makawa dasaka hannun hajiyah maryam a dukkan komai dayake faruwa,harma da waccar ƙungiyar duk da saka hannunta a ciki.
A zuciye na tura ƙofar na shiga ɗakin,na manta ma da cewar itace fah mai juya komai.
Juyowa tayi ta sauri tana kallona,nayi saurin sauƙar da kaina ina rarraba ido.
"Ke kuma fah daga ina?"
"Uhm nice sabuwar mai aikin nan sashen"
"Ohh kuma shine kikayimin wannan shigowar tamkar an koroki"
"Kiyi haƙuri hajiyah,uhm barina farada banɗaki"
Cikeda tsoro da roƙon Allah yasa kada tace komai nayi hanyar banɗaki da sauri,saida naga na shige na maida ƙyauren kafin naja ajiyar zuciya,wayyo ni Sumaimah nakawo kaina ga hallaka.
Bayan nagama gyaran na fito kenan daga É—akin naga wata tashigo falon da sauri tana kuka kaman anyi mata mutuwa.
"Mommy mommy wayyo mommy"
Da ƙarfi take maganar,anty Maimuna tunda ta daga ido ta kalleta tacigaba da abinda take,da alama kenan ta saba hakan.
Hajiya maryam ce ta fito daga É—akin tana kallon Fatee.
Tana ganinta kuwa da sauri tazo ta rungumeta tareda ƙara sautin kukanta.
Nidai gefe na koma ina kallon ikon Allah.
"Yau kuma meya faru,ke wai bakya girmane uhm kullum kina cikin rigima?"
"Ba.....bba carry over HOD ɗin mu ya bani ba wai....kuma yana sane fah wannan ce shakarata ta ƙarshe,naje barrack kuma na faɗawa Abbah yace wai dole saina jira wata shekarar na gyarata,nasan da Mulaifah ce ai da yayi magana an barta ta wuce yiiiiihhhihiiiiii"
Kuka take tsakaninta da Allah har ranta.
"Hmmm wlh mommy karki yarda da zancenta,tana sane fah da za'ayi exam É—in amma tayi baccinta a gida,saboda ta saba Abbah yana magana a bata ta gyara,kuma dama tun wancan lokacin Abbah yace inta sake yin sakaci irin wannan bazai sake zuwa ba"
"Mommy karki yarda da itah wlh ba haka bane,ranar fah cikina ne yake ciwo"
"Yanzu dai duk ba wannan ba wanene HOD É—inna ku?"
"Alh sama'ila ne"
Jeki É—akinki ki huta kici abinci zanyi masa magana,yasaka miki gyarannata a first semester da za'a shiga"
"Mommmmmyyyyy........"
"Ya isa haka karki dameni,tunda bakiyi ta ba dole saikin gyara,karkuma ki dameni ki barni da abinda yake gabana"
Dariya anty Maimuna tafara yiwa Fatee wacce tacika kaman zata fashe,da tayi zaton intayi kukan basai ta gyaraba,amma tasan tunda mommy tace zata gyara to sai ta gyara É—in.
"Ke kuma zan fita idan anjima,zan duba miki shari'ar ko kin gano kanta"
"Ahah mommy a dubamin,har yanzu bangano yanda zan bi da itaba"
Gwaliyo tayiwa Fatee lokacin da hajiyah maryam taje kusada ita tana duba abinda yake cikin system É—innata.
Ohhh inda ranka kasha kallo,sudai wannan familyn basa zama waje É—aya kenan suyi shuru.
Ɗakinmu na nufa,ina shiga naji wayata tana ringing,dama jiya nayita ƙiran number Tunga amma bata shiga,ina dubawa kuwa naga shine yake ƙirana..
Da sauri na É—aga tareda yin sallama..
"Hello Tunga ina ka shiga baka É—aga waya?"
"Kiyi hakuri Sumaimah wlh munje sarin dankaline wani lungu jiyan,to basuda network wajen,ga innan dama tunda naga ƙiranki nasan su kike nema"
"Yawwa "
Muryar inna Mairo naji,bansan lokacin dana saki wani ajiyayyen murmushi ba.
"Innaaaa ina wuni ya gidan kuna nan ƙalau"
"Lafiya kalau ƴar nan ya wajen aikin,muna nan ƙalau ƙalau,gamunan ma Tunga ya kawo mana dankali mun dafa muna ci"
"Inna dama kin sani?"
"Nasan me?"
"Goje uhm......."
"Sumaimah ki bar zancennan,nasani amma babu abinda zan iya cemiki a yanzu saidai kiyi haƙuri da rufemiki danayi nasakaki a cikin duhu,amma babu yanda zanyi sai hakan"
"Bakomai inna nasan bazakiyi abinda zai cutar dani ba,amma abinkam akwai É—aure kai sosai,kici gaba dayimin addu'a toh."
"Da yardar Allah kuwa,hakan ba zai gagaraba,nasan kinga abubuwa da dama a rayuwarki na jarabawa,kuma kuma jure kikayi haƙuri,yanzu ma ki ƙara komai zai wuce nan kusa da yardar Allah."
"Ina khadija da Sayyid banjisu ba?"
Na ɗauko wani zancenne saboda kawar da wancan,a tunani na babu amfani naci gaba da faɗamata,tunda nasan hakan ba wani amfani zayyi sosai ba,saima na ƙara tada mata da hankali. A yanda naga abubuwan suke gudana na tabbatar ba laifinta bane na boyemin da tayi,hasalima tayine saboda hakanne kaɗai zabinta.
"Gasunan fah suna jinki,khadija ce ma yanzu tafita kaiwa su gaji É—aukin dankali"
"Ayyah nayi kewarku sosai,Sayyid ya daina kukan?"
"Hhhhhh ya daina mana,kijimin saikace dama ba tafiya kike makaranta ki barshi a gidaba,ya daina kuka yakama abincinsa"
"Shikenan sai anjima inna karna cinye masa katin waya,kucigaba da sakamu a addu'a"
Daga haka nayi sallama dasu na kashe wayar.
Chapter Navigation
Use this section to move to any chapter without going back to the top.