Trending Hausa Novels

Sanadin Caca Book 2 Complete Hausa Novels By Sadi Sakhna

Reading file: SANADIN CACA 2.txt

Chapter 31 of 42

SADI-SAKHNA CEH
09035784150
ku tuntubeni domin biyan kuɗinku ko ƙarin bayani.

*SANADIN CACA*
-BOOK 2 (PAID)

Mallakar *SADI-SAKHNA*
09035784150

Bismillahir-rahmanir-raheem

Ki biya kan ki karantamin na biyu dan Allah. ga number ta nan mai son littafi na É—aya yayi min magana zan bashi shi kyautane.

*BOOK 2*
...29...

Bayan mun shigo gidan fita nayi daga motar ya nufi wajen parcking,ina nan tsaye ina kallon ƙyauye naga ya wuce ta gefena,baicemin na biyoshiba nabi bayansa da sauri,wani falo muka wuce kafin mukazo wani daban. Bai shigaba da hannu ya nunamin na shiga,shikuma yayi wani wajen daban.
Kaman wata baƙuwar kaza haka na kutsa kai ina rarraba ido.
Wazan gani inna ce da deeja dakuma Sayyid.
Suman tsaye nayi ina kallonsu,har deeja ta rungumeni banyi motsi ba,wannan wanne irin bazata ne haka. Nayi kaina tambayar,in suna haka tsaf zasu saka kaina yin kwancewa.
"Innaaa......"
Shine kawai abinda nasamu faɗi,dariya sukayi tare,har matar danake tunanin matar ƙanin hajiyah Maryam ɗince,wacce suke cewa Hajiya Shukurah.
"To anan dasu bazaki iso ba,duk mamaki ne yanaki motsawa"
Da sauri nazo inda inna take na rungumeta da ƙarfi,kukan Sayyid naji yana jan hijabi nah.
Juyawa nayi na tsura masa,kama naga yanayi da hajiyah Maryam,kodan nasan yanzu jikantane,amma idon kam na ubansa ne. Tureni yake yana tiro baki,waina matsa a jikin inna. Dariya abin yabani,wannan kam halin babansa ne.
Hannu nasa na ɗaukeshi,zuciyata cike dason yaron,wai dana riqeshi saina tuno labarin hajiyah Maryam,gaskiya ba ƙaramin azantuwa tayi na sosai.
Kallona yake yaƙi sakin jikinsa dani,deeja tana matsowa ya miƙa mata hannu. Dariya abin yabani,wato har ya mantani kenan. Inna na kalla tareda haɗe rai.
"Inna kiga ya mantani,laifinki ne bakya bashi labarina"
"Ohh jimin,labarinki ma kike cewa,keda kika figeshi a nono kika gudo saboda duniya tamiki zafi,kuma ma dakike can É—in wani rainonsa kike daya miki zafi. Kinshigo gidan mutane ko gaishesu bakiyi ba kina ta danki koh"
Maganar da tayine yabani kunya,kuma fah ban gaisheda matar gidan ba.
Cikin rusunawa na gaisheta,dariya tayi kafin ta amsa.
"Lahh kada ki damu Sumaimah,ai kinyi kewarsune shiyasa. Dan ma kada ki damu anan zasu zauna"
Kallon inna nayi da sauri,anan zasu zauna kaman yah. Ta gano wanne tunani nake,saita bani amsa.
"Nice nake neman wacce zata tayani aiki,shine Anty Maryam tacemin daman tanason inna ta dawo da aiki,sune suka zauna a sashen hajiyah Mammah suka raini Ahmad itada Inna ladiyo. To bazata manta dasu ba har abada."
Cikeda murna dakuma mamakin dama ashe inna tasan Ahmad tun yana ƙarami na kalleta.
Murmushin manya tayi kafin tace.
"Kiƙara mata godiya har deeja zata saka a makaranta,dama nayi tunanin tafiya da itah zan koma garinmu,to saiga mota wai ƙira daga hajiya,shine muka taho"
Bayan na gama godiyar wani abune ya fadomin.
"Inna meyasa zaki tafi garinku"
"Hmmm wata shida kenan da gaji ta matsawa baba audu kan cewar ya siyar da sashenmu,yanzu haka wanda suka siya sun matsa mu tashi"
Wani takaicine naji yazomin wuya nah menene haka mutanennan suke nufi. Duk kuma wajen bai zama gadon inna ba,É—anta ya mutu ita tuminin takaba kawai za'a bata,sannna Ahmad ba É—an ta bane.
ÆŠakin da aka bawa inna muka koma,anan sabon hira ya buÉ—e.
Deeja na kalla tana shirya kayansu,hankalin yarinyar yabani mamaki,dan lokacin dana tafi ba wani har can bane,yanzu ta zama tamkar uwar Sayyid komai wajenta yake zuwa.
Yau jina nake tamkar an tsundumani a aljanna,abu kaÉ—an saina kallesu na sake kallonsu,jinake kamar na maidasu cikina.
Labari kuwa har raba dare mukayi munayi,nasu gaji da kuma gidanmu.
Bayan mun gama hirar Deejah tayi bacci itada Sayyid tashi nayi na shiga banÉ—aki.
Bayanna fito rigata na cire nayi sama da zanin,ina shirin kwanciya naji maganar inna.
"Shin kun daidaita ne a tsakaninku?"
"Uhmm ni dawa?"
"Zaki fara wannan juyar da maganar kamar baki gane ba, mijinki mana nake nufi"
"Ahah bamu shirya ba,har yanzu baisanni ba"
"Baisani ba ya akayi kuma naga ciki a jikinki"
Shuru nayi na rasa ma mai zance mata.
"Uhm.....inna uhmm lokacin baya cikin hankalin sa ne,wata tabashi magani sai shine"
Ganin na duburburcene yasa ta juyar da kanta tareda cewa.
"Allah ya kyauta,ya daidaita ku bisa lokacin daya dace"
Ameen nace a hankali daga nan na kwanta.
Da safe bayan mun tashi nice nayi aikace aikacen gidan dukka,bayan mun gama karyawa muna zaune hajiyah Shukurah tashigo da waya a hannunta.
"Sumaimah ga kira nan daga hajiyah Maryam waiki koma driver yazo É—aukarki"
Zaro ido nayi kaman zanyi kuka,dan har raina gidan ya isheni sosai,don ba yadda zanyi ne. Dan kwana É—aya danayi dasu inna har naji daÉ—i,gashi bangama ganinsu ba kuma zan tafi.
"Uhm hajiyah ki bata haƙuri dan Allah na ƙara"
"Ahah ki koma kici gaba da aikinki,bakya tunanin a halin da kike ciki zamanki kusada su ma hadari ne,dan haka ki koma kici gaba da kula Allah yakiyaye,matsalar hajiyah Mammah tariga tasan take a matsayin wacce tasan mai take ciki,zamanki kusan danginki zaisa ta binciko dawa kike tare."
ÆŠaga kai nayi alamar na fahimta. Badan naso ba na shirya komawa.
Naso tafiyah da Sayyid amma nasan bazan fara wannan gangancin ba mai suna gani kasheni,dan haka sallama nayi musu na dawo.
Tun a hanya naji kamar banje ba.
Watan su inna É—aya kenan da dawowa,amma bangansu sosai ba,sai nayi tabi kafin hajiyah Maryam ta barni naje.
I zuwa wannan lokacin cikin jikina ya fito,saboda girman dayakeyi nan da nan,don ya shiga wata na huÉ—u a satinnan.
Ana Sayyid saida yayi kusan wata bakwai kafin yakai haka,amma shi yanzu haka yakai kusan cikin wata bakwai a matan da basa girman ciki.
Kowa a gidan yanzu yasan inada ciki,saidai ban damu ba,saboda duk a zatonsu na mijina ne daya tafi rani.
Ita kanta hajiyah Mammah har kyauta takemin,tareda cewa mijina bai kyauta ba daya barni da ciki yasake komawa. Nidai saidai nayi murmushi nace uhm.
Bayan nayi sallahr asuba bacci nakoma mai shegen nauyi,gashi nayi wata ƙiba saboda yawan cin abinci kaman gara,cina har ya wuce na cikin Sayyid. Ummi har boye abincinta take inta ganni,inna ladiyo ce da hajiyah Maryam haka hajiyah Mammah suke bani abinci duk sanda suka ganni.
Bayan na miƙe daga kan katifar madubi na ɗauka na kalli fuskata,taƙara fari da ƙiba,haka ma jikina. Ƙafafuna kam ba'a magana.
Wanka na shiga ina fitowa nasaka doguwar riga,daga cikin materials É—in da hajiyah Maryam ta É—inkamin saboda goyon ciki,naji daÉ—insu kuwa sosai ba kaÉ—an ba.
Ummi ce tashigo É—akin ina shafa mai,hijabi ta É—auka tasaka da kuÉ—i a hannunta.
"Ke kuma fah ina zuwa haka,nasan baki fiye zuwa aike ba,an fi tura mai gadi shikaÉ—ai"
"Hmmm wai Yallabai ne zai dawo shine inna tayimin lissafin abinda zan siyo,Sannan kuma ki faÉ—amin mai kike so zaki haÉ—amasa"
Zaro ido nayi tareda kallonta,wanne yallabaiÉ—in badai Ahmad ba,gabaÉ—aya na manta da ashe zai dawo,bana tunashi sainazo kwanciya na rungume rigarsa tukunna.
"Kinga tsaya tsaya basai kinje ba zanje"
"Ke dalla kimin lissafi naga bake kika sakani ba, yanzuma daga sashensa nake na gyara,kina bacci É—azu na É—auki key"
Kallonta nake da mamaki,nasan inna ce tasakata,itama kuma tana tausayina nasan.
Rungumeta nayi ina zuba mata godiya,ba ƙaramin daɗi naji ba data gyara ɗin.
"Nagode ummi,barinaje na dudduba sashen,sannan na gyara kitchen É—in. Kafinnan zan miki lissafin abubuwan"
Lokacin dana shiga sashen tsaf yake ta gyarashi koni zanyi iya haka.
Saidai ɗaki da kuma banɗaki dana ɗan ƙara gyarawa.
KuÉ—i da yawa hajiyah Maryam tabawa inna ladiyo na abincinnasa,ni kaina shaidace yanda take ji dashi a cikin ranta.
Hmmm koya zamu kaya nidashi idan ya dawo,shin wacce amsa zan bashi ne idan yayimin tambayar miye a jikina.
Kitchen É—in na gyara na fitar da abinda zanyi amfani dashi.
Ina cikin haka ummi ta dawo,sosai ta tayani har muka gama aikin wajen daya na rana,lokacin kam nasan anty thing a kowanne time zai iya dawowa,da sauri muka ƙarisa nabar sashen,domin banaso ya dawo ya sameni,ban shirya ganinsa a yau ɗin ba.
Lokacin da muka koma daki nayi sallah waje na samu na zauna ina haki tareda sauke numfashi,don ba ƙaramin gajiya nayi ba,jikina nauyi yakemin kwanannan.
Ruwa mai sanyi ummi ta miƙomin tareda ajiye abincin mu a tsakiyar ɗakin.
Saida na zuqe ruwan naja ajiyar zuciya kafin nace.
"Kai gaskiya ummi a tafawa ruwa,ruwa rahama ce,mai rowar ruwa ya cika marowaci"
Dariya tayi kafin tace.
"Ehh lallai yau gana mai yiwa ruwa santi,haba kema da laifinki,ji yanda kika dage kina yimaza aiki kaman wani mijinki,ko wanda kike aure bakya yimasa bautar da kike masa,Sannan abinda yabani mamaki ban taba ji kince ga salary É—in ki ba. Ko yake shima wannan mijinnaki da nice da tuni ai munyi wacce zamuyi,na taho aikatau domin mu rufawa kanmu asiri,amma shine hakan bai isheka ba ka biyoni kayimin ciki ka haÉ—ani da wahala,inama zan ganshi da sai na tsayar masa"
"Hhhhh ummi kinada abin dariyah,zaki iya tsayar masa idan na hadakun?"
"Ehh mana bari ki gani Allah ya kaimu"
Murmushi nayi batareda nasake cewa komai ba na saka hannuna a abinci.
Muna gamawa na kishingiÉ—a domin na kwanta na huta.

Chapter Navigation

Use this section to move to any chapter without going back to the top.