Sanadin Caca Book 2 Complete Hausa Novels By Sadi Sakhna
Reading file: SANADIN CACA 2.txt
Chapter 9 of 42
09167130115
Wato a manhajar whatsapp. Domin ganin kalolin samufurin aikinmu kuma ku tuntubemu a INSTAGRAM da kuma TIKTOK a @pheedyxacks_ragtrade
Muna maraba daku a kowanne lokaciðŸ™ÂðŸÂ¼ðŸ™ÂðŸÂ¼ðŸ™ÂðŸÂ¼ðŸ™ÂðŸÂ¼ðŸ¥°ðŸ¥°ðŸ¥°ðŸ¥°ðŸ¥°ðŸ¥°ðŸ¥°ðŸ’ƒðŸÂ»ðŸ’ƒðŸÂ»ðŸ’ƒðŸÂ»ðŸ’ƒðŸÂ»ðŸ’ƒðŸÂ»ðŸ’ƒðŸÂ»ðŸ’ƒðŸÂ»ðŸ’ƒðŸÂ»
*BOOK 2*
...9...
Ban tashi sallahar asuba ba yau,saboda bana cikin tsarki,dama na gayawa inna ladiyo kada ta tashe da asubar.
Hasken rana nagani ya shigo da windown É—akin,kasancewar muna idon inda ranar zata fito.
Mutstsike idona nayi na tashi.
Brush É—ina na É—auka da toothpaste na fita waje..
A barandar naga wata fashashshen kasko na ƙasa.
Zaro ido nayi,wai dama abinda ya faru jiya da daddare dagaskene ba mafarki ba? Ƙafata na ɗago wacce nabuge a garin gudu,ɗan yatsan wajen ya kumbura yayi ja,banji zafin da yakeyimin ba sai yanzu dana kulada shi. Zatona duk abinda idona ya ganemin jiya mafarkine bada gaskeba.
Dabas nayi zaman ƴan bori a barandar yayinda na koma baya lokacin danayi arba da mata guda biyun,wanda suke sanye da riguna ja da baƙa,sun rufe kansu..
To su waye haka,mai yasa suka fito daga cikin gidan suka wuce ta nan,kuma a hakanma bata get ba ta jikin katanga. Sannan jiyan nayi ta tashin inna ladiyo na faÉ—a mata amma shuru kamar gawawwaki haka najisu. To ko gamo nayi da aljanu kai,kai amma aljanune zasu dunga zancen kowa yayi bacci,mutanene kuma nasan a gidannan suke duk yanda akayi.
Tashi nayi tareda kakkaÉ—e jikina na nufi katangar inda naga sun bace taciki.
Daga nesa babu komai a jiki,amma dana isa jikin katangar indai ba idona ƙarya yakemin ba to naga wata Da'irah (circle),a jikin katangar,anyi wani rubutu rubutu a wajen da jar kala.
Haka kawai naji gabana yana bugawa da ganin abin.
Kai gaskiya gidannan yanada matuƙar hatsari ba ƙarami bama kuwa,kaman yanda inna ladiyo tafaɗa dolene sai mutum yayi taka tsantsan Sannan ya riƙe Allah. Anan ina buƙatar yin aiki da kula da kuma ilimi.
"Inkin gama kallon ƙyauyen a jikin katanga kizo ga abincinki nan inna ladiyo tace na kawo miki"
"Waiwayowa nayi na kalleta,dan murmushi nayi mata gajere,yanda inna ladiyo tafaÉ—a nima na fara ganin hakan,halinta ne wani iri,amma batada mungun nufi koma dai menene zan bibiyeta nagani.
"Bayan haka kuma mai tace?"
Na ƙwala maganar tunda tafara yin nisa"
"Tace mutum ya shirya yaje aikinsa,idan ba haka ba kuma a koreshi kowa ma ya huta"
Dariya nayi ina jijjiga kai,in haka take to lallai zamuje da ita.
Brush É—in da banyi ba nayi,kana naje inda abincinnawa yake..
Dankalin turawa ne da ƙwai,tabbbb muma masu aiki shi zamu dunga ci?.
ÆŠauka nayi nakai bakina,babu abinda ya faÉ—omin sai inna Deejah da kuma É—ana,Allah sarki kome sukaci yanzu oho?.
Hawayene ya zubomin nayi saurin sharewa,ina kewarsu sosai da sosai.
Da sauri sauri na gama komai na fito daga sashennamu.
Kitchen É—in kai tsaye na nufah da kwanon a hannuna.
Inna ladiyo batanan sai iya ammi kawai tana wanke wanke.
Ajiye mata nayi tareda fara yimata É—auraya.
"Ummi barka da safiya ya aiki?"
"Kafinna amsamiki barmin aikina kije kiyi naki,kina ɗaukar aikinki da sauƙi amma yafi na kowa taka tsantsan,idan kika makara ko kuma kika je da wuri duk laifi zakiyi"
Ban bata amsar maganar ta ba,saima wata tambayar da nayi mata.
"Ina inna ladiyo banganta ba"
"Ta tafi kaiwa hajiya tea É—inta"
"Uhm ta fita jiya da daddare?"
Kallon ya akayi kika sani tayimin kafin tacigaba da abinda takeyi,kaman bazata bani amsa ba saikuma tace.
"Wani lokacin dama takan fita da daddare,saida safe ta dawo kokuma ta dawo a daren, naji ance wai gidan marayu ta buÉ—e,idan abu ya faru na gaggawa takan fita ko yaushe"
Uhm gidan marayu koh,wato haka tace kenan,to amma mai kuma take itada wata da daddare jiya......ohh zargi ba kyau mutum bai tabbatar,amma biri yayi kamada mutum. Ahmad ne yafaÉ—omin a rai,anya ba saka a hannunta a tafiyarsa,su suna ganin iyah hatsarin motane yasakashi manta gida,to amma rashin baccin dayake yi a da fah,da kuma sai yani inbai abin Allah wadai ba bayajin daÉ—i.
Nasan indai itace to yanzu ma bazata haƙura ba sam,dole zata sakeyin wani abun. To amma taya zan taimakeshi wannan karonm. Idan a da ta turashi duniya na haɗu dashi yanzu zata iya turashi wani wajen daban kokuma ta rabashi da duniyar gabaɗayar.
Tunanin hakan baƙaramin firgici yasakani ba.
"Ke keee Sumaimah lafiyarki ƙalau kuwa,ya naga gabadaya annurin fuskarki ya sauya,harda kuka fah kikeyi?"
Cikeda mamaki takeyimin tambayar,shin mai zan ce mata,taya zance ƙalau nake koba ƙalau nake ba. A iya rayuwata a wannan duniyar naga abu da yawa,har yanzu ma ba wai nagama ganin bane,inda raima saidai nace yanzu nafara gani.
"Ahah babu komai ummi,barina tafi aiki,nasan yanzu kam ai ya fita"
Daga haka nayi hnayar sashennasa da sauri,a jiya haushinsa nakeji ganin ya mantani,amma yanzu tausayinsa nakeji da É—amarar taimaka masa da dukkan iyawata.
Tafiya nake tunani fall raina har bansan lokacin dana ci karo da mutum.
Goshina na riƙe lokacin da mukayi gwaren,na manta ma da sashenwa nazo.
"Bayan kallon mutum kaman zaki cinyeshi hadda rashin kallon gabanki ma?"
Ɗaga ido nayi na kalleshi,ya hade girar sama data ƙasa kaman bai taba dariya ba,uhm nasan irin wannan side ɗin,yayi kyau kuma.
Bangajeni yayi ya wuce,ohh ko gaisheshi banyi ba,gashi kaman jiya yauma na cigaba da kallonsa,duk laifin zuciyata ce,wai miyasa takemin hakane?.
Ciki na wuce,yau banyi kalle kalle kaman jiya ba, shigowata jiya nazone na niyyar aiki a biyani,amma yanzu jina ke kaman nazo masa gyaranne a matsayinsa na mijina.
Hhhh saina tuno É—akinsa lokacin dayake goje,wa zai haÉ—ashi da wannan.?
Falon bayyi datti ba,dan haka sama sama na kaÉ—eshi na shiga É—akin.
Nan ma banyi wani aiki sosai ba,iyah gyara zaman kayansa nayi da kuma shirya wasu takardu tana gani a kan wardrop.
Har zan saka sakasu a cikin drawer idona ya hangomin abinda aka rubuta a jiki.
MISSING NUCLEAR INFORMATION....criminals (BC GANG).
Ajiye sauran takardun nayi na duba iya na hannunnawa,hoton akwatin da goje yakoma dashi gida bayan sunje wannan satar nagani. BC? Itace kenan sunan kungiyar dayakewa aiki wancan lokacin,tunda gashi ance su suka sace. Ko saboda itace kai aka yimasa illa wancan karon,kuma rashin sani yaje ya Jona dasu??
"TabÉ—ijam wannan cakwakiyar da yawa take,shine yake jan ragamar case É—in,kuma bayan yarasa hankalin sa kuma yazama É—aya daga cikinsu batareda ya sani ba. Gashi ya manta rayuwar dayayi da goje bare yasan inda suke? To amma akwatin fah,shin na faÉ—amasa nasan inda yake kokuma na bari yanzu ba? No no idan nagaya masa bazai yarda daniba,bayan a yanzu yardarsa shine abinda zanso na fara samu tukunna"
Mayar masa da takardar nayi yanda take na ajiye,ban É—auke hannuna ba naji an buÉ—e kofar da sauri.
Turuss yayi daga bakin ƙofar ganin hannuna akan takardun,da sauri ya ƙariso ya wafcesu har yana haɗawa da hannuna. Kallon tuhuma yake bina dasu,wanda nasan bazai wuce na dannaga takardun bane.
"Aiki kikazo yi kokuma yimin bincike"
"Niba bincike nakeyimaka ba,kawai na tattarasu ne ganin sun wargaje a wajen"
Kaman bai yarda da abinda nace badai ya É—iba yasake fita da sauri.
Kumkumina na riƙe ina kallon bakin ƙofar inda ya fita.
"Ikon Allah dama ko daga goje ma wannan ba ƙaramin murɗaɗɗen mutum bane,uhhh kallom bai yarda dani ba yakemin"
Dafe goshina nayi kafin nima na fito daga ɗakin,har nazo fita daga sashen saikuma naga wata ƙofar bayan ɗakunan gidan,nasan bazai wuce kitchen ba. Amma to mai zayyi da kitchen bayan a kwai a can cikin gidan.
Wata zuciyar dai tacemin to jeki duba mana.
Buɗe ƙofar nayi na shiga,bansan lokacin dana toshe hanci ba saboda ƙurar da take wajen.
Ga kitchen iya kitchen amma saikace sansanin fatalwu.
Ƙarisa shiga cikin nayi ina duddubawa,babu abinda babu a ciki na kayan amfani,haka kawai na tsinci kaina dayin murmushi da bansan na menene ba.
Mopa na É—auko da ruwa,ga aiki na samu.....
Chapter Navigation
Use this section to move to any chapter without going back to the top.