Sanadin Caca Book 2 Complete Hausa Novels By Sadi Sakhna
Reading file: SANADIN CACA 2.txt
Chapter 2 of 42
Wannan kenan a shafin farko na littafin SANADIN CACA BOOK 2.
SADI-SAKHNA CEH
09035784150
ku tuntubeni domin biyan kuɗinku ko ƙarin bayani.
*SANADIN CACA*
-BOOK 2 (PAID)
Mallakar *SADI-SAKHNA*
09035784150
Bismillahir-rahmanir-raheem
Ki biya kan ki karantamin na biyu dan Allah ðŸ™ÂðŸÂ¼ ga number ta nan mai son littafi na É—aya yayi min magana zan bashi shi kyautane.
Ina ƴan mata dakuma Matan aure masu muradin burge mazajensu da ɗinkuna zuƙa zuƙa. *PHEEDY TOILORING DESIGN* ,suna gabatar muku da ɗinkuna kala kala wanda sukayi daidai da zamani.
Zaku samemu a kan wannan layin waya kamar haka
09167130115
Wato a manhajar whatsapp. Domin ganin kalolin samufurin aikinmu kuma ku tuntubemu a INSTAGRAM da kuma TIKTOK a @pheedyxacks_ragtrade
Muna maraba daku a kowanne lokaciðŸ™ÂðŸÂ¼ðŸ™ÂðŸÂ¼ðŸ™ÂðŸÂ¼ðŸ™ÂðŸÂ¼ðŸ¥°ðŸ¥°ðŸ¥°ðŸ¥°ðŸ¥°ðŸ¥°ðŸ¥°ðŸ’ƒðŸÂ»ðŸ’ƒðŸÂ»ðŸ’ƒðŸÂ»ðŸ’ƒðŸÂ»ðŸ’ƒðŸÂ»ðŸ’ƒðŸÂ»ðŸ’ƒðŸÂ»ðŸ’ƒðŸÂ»
*BOOK 2*
...2...
"Mammah Mammah kina ina ne?"
TafaÉ—a da sauri bayan ta shiga sashen Mammah É—in.
"Meyafaru haka kike xubamin wannan ƙiran uhm ?"
Mammah tafito daga É—akinta hannunta É—auke da carbi da hijabi a jikinta kaman kullum.
Zama tayi akan kujera,wanda daman abinda Mulaifah takeso kenan ta É—ora kanta a cinyarta.
"Mammah bakiji labari ba Ahmad ya dawo ashe bai mutu ba duk tsawon lokacin,Allah yayi zamu kasance tare ashe shiyasa ka aurena ya mutu"
Shuru Mammah tayi kaman mai tunani kafin tacigaba da shafa kan Mulaifah wanda yake kan cinyarta,ganin tayi shuru batace komai bane yasaka Mulaifah juyawa ta kalleta.
"Mammah bakice komai ba,bakiyi mamakin dawowarsa bane?"
Murmushi tayi irinna manya kana ta É—ora da cewar.
"Ahah ba haka bane,waye bazayyi tunanin abin al'jabi irin wannan ba,amma kuma babu abinda yafi larfin Allah,dan haka wannan ba abin mamaki bane dan ya faru,saima na farinciki da Allah yadawo mana dashi garemu. Ina yake yana cikin gidane?"
"Ahah wai fah Abbah ya turashi abroad a duba lafiyarsa"
"Ehh to hakanma yanada kyau,amma ya kamata a a tura wani nasa ya kulada shi,ba a barshi shi kaÉ—ai ba gashi ba cikyakykyiyar lafiya ba,barin abbannaku yashigo muyi maganar,sainaje ganin jikinnasa.."
"Yawwa Mammah in zakije nima zan biki na ganshi,i can't wait to see him"
"Uhmm Mulaifah kenan kefah kike rawarki kike kiÉ—anki,sanin kanki ne amadu bayason ana haÉ—ashi dake,wancan karon ma abbanku ne yayi masa dole shiyasa ya amince da aurenki,yanzu kuwa kinsan ba lallai ya yarda yasake maimaita wannan hukuncin ba"
Kukan sakarci Mulaifah tafara jin abinda Mammah ta faÉ—a.
"Wai Mammah haba meyasa kike haka,shima nasan yana sona,ko ba yayi zan sakashi yayi yanzu,sannan nasan zaki roƙi abba ya dawo da maganar aurenmu koh?"
"Ni ban miki wannan alƙawarin ba,so kike ayita shiga haƙƙinsa,yaji da halin dayake cikima na halin waccar matar,yanzu babu wannan zancen,in ya dawo yanaso toh,idan kuma bayaso to ni zan tsaya masa"
Tashi tayi daga cinyarta tana mata kallon mamaki ganin da gaske fah Mammah take akan maganarta,kuma dama tasan hakan zata faru,dan duk zamanta Æ´ar lele a wajen Mammah to bazata haÉ—a kanta da Ahmad ba,sanda yana nan idan kaga yana fira da sakin fuska to a sashennata yake.
Tashi tayi cikin fushi ta bar sashen Mammah,nata sashen ta nufah zuciyarta cikeda tunanin shin wanne hanya zata bi na mallakar zabin rannata.
A can kuwa Cairo dake ƙasar Egypt Ahmad a kwance yake akan wani gado,jikinsa sanye da kayan masu jinya,wasu wayoyi aka saka akannasa wanda suke shinshinar lafiyar ƙwaƙwalwartasa.
Buɗe idonsa yayi a karon farko bayan kawoshi ƙasar,wanda kwanansa uku kenan da zuwa..
Yauɗin kuma su Sadeeq sukazo dubashi harda Mammah da Mulaifah saikuma Saleem,dan dama a duk cikin ƴan uwannasa yafi shaƙuwa dashi..
Bayan buÉ—e idon yana jiyo hayaniya daga É—an can nesa,amma a É—akin kam baiji motsin mutum ba,da alama shi kaÉ—aine..
Tashi yayi a hankali tareda zubawa na'urar da take gabansa ido.
Waishikam duk sanda ya kwanta a asibiti zai farfaÉ—o ya ganshi,yaushe yazama hakane kaman juji? Ko yaushe yana asibiti?.
Ɗan ƙaramin tsaki yaja tareda fitar da ruwa dayake shiga jikinsa,saƙƙo na ƙafafunsa yagi akan gadon tareda niyyar sauƙa,amma sai ya tsaya jin abu ya riƙe masa kai,suma a wayoyin cikeda bacin rai ya cire su kafin ya nufi banɗaki,wanda yagani a yamma da ɗakin.
Fuskarsa ya wanke tareda kallon kansa a cikin madubi,ɗan razana yayi tareda ja da baya,ganin yanda ya rame yayi baƙi,ya kuma ƙara manyanta ba kaman yanda ya sanshi ba..
Shin dama da gaskene abinda Sadeeq ya faÉ—a masa,cewar shekararsa biyar da barin gida,to a ina yake tsawon lokacinnan,bacci yake tayi sai ya yanzu ya tashi? Ko kuwa wata rayuwa yayi da bai sani ba kai?.
Zullumine suka cunkushe masa kai,wanda hakan yasa ya fito daga banÉ—akin.
Cakk ya tsaya a bakin ƙofar banɗakin yana ganin tarin mutanen da suke ɗakin,wanda duk cikinsu babu wanda kallo ɗaya bai ganeshi ba,amma sai ya basar ya nufi gadon daya tashi yanzun..
Mammah ce tafara yimasa magana cikeda kulawa.
"Amadu ka tashi ya jikinnaka,babu inda yake yimaka ciwo,amma ka ganemu kuwa"
Kwanciya yakeson yi,amma ganin yanda take zubo tambayoyi yasaka shi kallonta tareda sakin murmushi ɗan ƙarami.
"Mammah na ganeku mana,ƙalau nake babu abinda ya sameni ciwon kaine shima ya ɗan sauƙa,taya zan manta ki saidai amma kin ƙara tsufa,kinfara cin goro ne"
Dariya Mammah tasaki cikin jin daÉ—in maganarsa ,kafin tace wani abu Mulaifah ta dawo kusada shi da sauri kaman zata wuce jikinsa..
"Honey ka ganeni nima?"
Wani kallon matsa ki bani waje yayi mata,ganin ta dalleshi da manyan idanuwanta yasa yayi magana cikin ƙosawa.
"Kai Mulaifah wai bazaki sauya bane,gashi a fuska kin ƙara girma amma kinanan yanda kike,saikin shige jikina kafin ki tsaya komai?"
Bataji haushin yanda yayi mata maganar ba,ƙiran sunanta kawai da yayi ma hakan ya wadatar da ita,kuma ya sakata cikin farinciki.
Shareta yayi tareda kallon Saleem wanda yake zaune a waje É—aya shida Sadeeq.
"Gentle bro kaima ka girma sosai,amma yanzu kam ka zama doctor koh,sanda nasani kana aji É—aya"
Murmushi yayi shima daya tuna lokacin.
"Ehh nagama yah Ahmad har nafara aiki ma waccar shekarar,Sameer shima yana aiki a barrack É—inku,sai Maimuna tana karatun law,Fatee kuma tana makaranta"
"Ban tambayeka ya suke ba ai,naka kawai na tambaya"
YafaÉ—a yana tsuke fuska,dukkan su kallon juna sukayi,har yanzu yana nan da halinsa,ba dama ayimasa gwaninta.
"Oh AA Hamma ni baka ganni bane komai"
Sadeeq yafaÉ—a cikin tsokana..
"Banganka ba saida kayi magana"
Yana gama faÉ—in hakan ya kwanta a gadonnasa,suna ganin haka suka fita,da alama hutu yake so.
Suna fita daga É—akin ya tashi ya koma banÉ—akin,dama yayi hakanne saboda su fita,kasancewar bai saba da zama cikin mutane ba tunda,shiyasa yajishi cikin wani irin yanayi.
Alwala ya ɗauro ya dawo ɗakin,domin rama sallolin da ake binsa ,ya daɗe yana yi har saida ƙarfinsa ya ƙare kafin ya dakata.
A wajen Addu'o'i ma ya daÉ—e nan ma kafin ya dakata.
Jijjiga kai ya fara burinsa kawai ya fitar da tunanin da suke cikin kansa,amma hakan ya faskara.
Ƙarar buɗe ƙofa yaji,har wanda ya shigo ɗin ya zauna bai ɗaga ido yaga wanene ba,har saida yayi magana tukunna ya gane Sadeeq ne.
"AA Hamma nasan tunani kakeyi,koma miye ka barshi ba yanzu ba,saboda a yanzu kana buƙatar hutu sosai"
Bai saurari Sadeeq É—in ba,saima magana daya farayi.
"Menene haka ya sameni,a ina nake tsawon lokacin nan,wacce irin rayuwa nayi duk bansani ba Sadeeq,ka yi tunanin ya zanji a halin yanzu,sannan rayuwar wa na shiga,cutar dashi nayi kokuma kyautata masa duk bansani ba"
"Hakane kam babu daɗi lamarin,amma babu yanda zakayi saidai haƙuri,a hankali Inshaallah zaka tuno komai,amma yanzu karka saka damuwa a ranka,idan ba haka ba zai dameka sosai.,Saboda hakannne ma yasa yace ka zauna anan kaman na shekara biyu ko ɗaya kafin ka koma gida,saboda ka huta sosai"
Jijjiga kai yayi tareda cewa.
"Bazan iya zama anan ba,bayan nasan wanda ya aikata min hakan yana can hankalinsa kwance,nikuma yasaka rayuwata cikin garari na tsawon shekara biyar"
"Wani mai kake nufi,shin kasan wanda yayi maka hakan"
"Ahah ban tabbatar ba amma nasan najikina ne yayimin,kuma komai yana alaƙa da case ɗin BC da nake a lokacin,Sadeeq abinda zan fadamaka inaso kabarshi anan harsai na tabbatar da hasashena. A binciken danayi harda hannun Hajiya Maryam a wani bangare na ƙungiyar,nagano hakanne bayan na saka na'urar bin diddigi a wayarta da motarta..
Wanda kuma tasan da hakan,amma ga mamakina bata nunamin ta damu ba,hasalima wata hidimarta tacigaba ta daban.
Sannan a ranar dazan kai wanan shaidar headquater a ranar nayi hatsari,sannan kafin idona ya rufe dukka naga wata mata da baƙaƙen kaya tazo kaina ta ɗauki na'urar a jikina. Daga nan bansake ganin komai ba.
Kafin duk wannan ya faru kuma dama na fara jin sauyi a jikina,sai nayi abu bansan nayi ba,wani lokacin saina dungajin inason na aikata abinda ba daidai ba,har shaye shaye idan naga anayi sainaji ina so nayi. Kokuma yiwa wani rauni ko lahani.
Abinnan ba ƙaramin firgitani yayi ba Sadeeq saidai babu wanda ya sani,sannan idan nace zanyi bacci saina kasa sam. Ina cikin wannan halinne wannan abin ya sameni. Wanda bansan mai ya faru ba sai jiya na dawo hankalina.
Kuma duk kacemin ina cikin wannan halin na zauna na huta?"
Muryar sa tana rawa ya ƙarisa magana,Sadeeq wanda ya zama tamakar gunki sai yanzu ya motsa jin tambayar da Ahmad yayi masa a ƙarshen bayaninnasa.
"Tabbas wannan ba ƙaramin lamari bane,amma duk da haka kayi haƙuri kasake warkewa,kafin sannan ni nayi maka alƙawarin zan taimaka maka da dukkan iyawata akan wannan abun"
"Nagode da kulawarka zan bari na huta ɗin kaman yanda Abbah ya buƙata,amma kafin sannan inason tambayarka.
Shin Æ´an team É—ina sunan nan wanda muke aiki dasu kokuwa?"
"Ehh to Eemran yana nan da Bilal shine ma a kan case É—in saikuma Neelah"
"Yawwa ka ƙira Neelah ka fadamata zanyi magana da itah zuwa gobe ta shirya"
"Uhm to zan bincika itama naji kaman ana cewa za'ayi mata transfer na wajen aikin"
"Zanyi magana da Abbah akan ya barta,dan a halin yanzu daka kai sai ita kawai na yarda dasu akan case É—innan. Zan cigaba ne daga inda na tsaya,zama na anan bazaisa na fasa ba"
"Am AA Hamma na manta ban faÉ—amaka ba,yanzu haka ma akwai wani case da akeyi da su."
"Case wanne iri?"
"Uhhm wata uku kenan da suka sace nuclear da aka kawo,har yanzu ba gantaba,an bi diddigi har an gaji"
"What nuclear,abinnasu har yakai hakane wai,they need to stop now"
Chapter Navigation
Use this section to move to any chapter without going back to the top.