Trending Hausa Novels

Sanadin Caca Book 2 Complete Hausa Novels By Sadi Sakhna

Reading file: SANADIN CACA 2.txt

Chapter 4 of 42

SADI-SAKHNA CEH
09035784150
ku tuntubeni domin biyan kuɗinku ko ƙarin bayani.

*SANADIN CACA*
-BOOK 2 (PAID)

Mallakar *SADI-SAKHNA*
09035784150

Bismillahir-rahmanir-raheem

Ki biya kan ki karantamin na biyu dan Allah 🙏🏼 ga number ta nan mai son littafi na ɗaya yayi min magana zan bashi shi kyautane.

Ina ƴan mata dakuma Matan aure masu muradin burge mazajensu da ɗinkuna zuƙa zuƙa. *PHEEDY TOILORING DESIGN* ,suna gabatar muku da ɗinkuna kala kala wanda sukayi daidai da zamani.
Zaku samemu a kan wannan layin waya kamar haka

09167130115
Wato a manhajar whatsapp. Domin ganin kalolin samufurin aikinmu kuma ku tuntubemu a INSTAGRAM da kuma TIKTOK a @pheedyxacks_ragtrade

Muna maraba daku a kowanne lokaci🙏🏼🙏🏼🙏🏼🙏🏼🥰🥰🥰🥰🥰🥰🥰💃🏻💃🏻💃🏻💃🏻💃🏻💃🏻💃🏻💃🏻

*BOOK 2*
...4...

.......BAYAN WATA BAKWAI.

A zaune take tasaka tsinin ciki a gaba da kwanon abinci akan cinyarta..
Ta kumbura tayi ƙatuwa,ga wani uban girma da cikinnata yayi kaman an saka babban mutum a ciki.
Hankalinta kwance take cin garin kwakin kaman ance ta cinye kan wasu su shigo.
Tun daga zaure take jiyo hayaniya tsakanin kursiyyah da Deejah,wanda abune da ya kamata ma su saba dashi,duk sanda aka sakasu sharar gida ko É—iban ruwa sai sunyi faÉ—a. Kuma duk yawanci Deejah ce take dukan kursiyyah,gaji tayi masifar har abin ya isheta,tunda ta kula Deejah ba rage mata takeba,gashi batajin maganar kowa idan bata Sumaimah ba.
Yanzun ma kaman kullum shigowa sukayi kursiyyah tana kuka da fashashshen botiki a hannunta,sai Deejah wacce tashigo tana ciccije baki,itama da botikin a hannunta amma bai fasheba.
Hanyar ƙofar su kursiyyah tayi,yayinda Deejah kuma ta iyo inda Sumaimah take zaune tasaka kujera a bakin ƙofar goje.
Da kallo ta bita na alamar tambaya,amma sai tayi biris kaman batasan mai take nufi ba.
"Mai kikayi mata naga kun shigo tana kuka,waye yafasa bokitin hannunta"
Tun kafin Deejah ta buɗe baki tayi magana sukaji muryar gaji tana masifah,fitowa sukayi da tana riƙe da hannun kursiyyah.
"Wannan wanne irin iskanci ne,komai aka ga dama sai ayimaka in kayi magana ace kai jarababbene,to wlh bazai yiyu ba,babu wanda yake ban ci ballantana sha. An kawo bare yazo ya kanainaye gida hadda yin aure,saboda bala'in da aka sakashi a gaba ya gudu ana shirin shekara babu shi babu É—uriyarsa,hakan bai isaba sai itama matar da batada gindin zama a gidan ta kawo wata É—osun É—osa nan tana takurawa Æ´aÆ´an gida? To bazai yiyu ba haka sam"
"Kai gaji kai gaji,waini kam yaushe zaki girma ne ki daina waÉ—annan abubuwan"
"Dakata Mairo dama nasan zakice haka,barni nayi na more,duk tsiyata dai da masifah ta ban kori mijina da baƙin hali ya tsallake ya barni ba"
"To ita wanene yace miki guduwa yayi ya barta,in ma guduwa mai naki na wannan magana"
"Heee to in ba guduwa yayi ba fatalwa ya koma a gidan yake rayuwa idon mu baya ganinsa,wayasani ma ko cikinne ba nasa ba ko kuma lasarsa take da daddare shiyasa ya gudu"
"Gajiiiiiiii!!!!! Duk abinda zaki faɗa ki faɗa,amma ki daina sheganta min ɗa ko kuma yimin sharrin maita,dan bazan yarda da wannan ba,akan hakan zan iya kaiki ƙara"
Hakan da Sumaimah tafaÉ—a ya razana ta,domin tariga tasani duk lokacin data kai Sumaimah bango bata jin shakkar maida mata martani.
Duk da haka da masifah tana cinta bata yi shuru,ta É—age gefen zani sai masifa take.
Deejah wacce take tsaye abin yayi mungun isarta,gashi Sumaimah ta hanata idan gaji tana masifa ta tanka,shiyasa babu yanda zatayi tai shuru.
Dafe goshi Sumaimah tayi tana jin gaji wacce take ta bambami akanta,marar ta taji kaman wani abu ya keta mata,hakan yasa ta ajiye kwanon hannunta tareda da dafe wajen.
Muryar inna taji tana magana.
"To ikon Allah Sumaimah ruwa fah kike zubarwa,ko haihuwa ce kai?"
Bin wajen da inna ta kalla tabi ta kallo itama,kaman dama wacce take jira a gane,nishi ta fara tana kama ciki. Komawa É—aki inna tayi da gudu ta É—auko kayan da suka shirya na haihuwar..
Tunga ne ya ƙira mota aka sakata zuwa asibiti,dan dama sunce idan zata haihu a kawota asibiti kar a barta a gida. Saboda tun cikin yana ƙarami jininta ya hau,bai sauƙa kuma sosai ba har zuwa lokacin.
Kai tsaye É—akin labour aka wuce ta ida,harta fara fita daga hayyacinta..
Ƙarbarta nurses sukayi zuwa ciki,ganin yanda numfashinta yaka sama sama.
Inna ban kuka babu abinda takeyi,Tunga ne da Deejah basuyi kuka ba,saidai fuskarsu ta nuna tashin hankali.
Nurse ce tafito daga cikin É—akin fuskarta É—auke da murmushi.
"Mashaallah ta sauƙa,saidai jikinta yayi laushi yana buƙatar kulawa."
"To amma mai ta haifa?"
Inna ta tambaya cikin nuna damuwa.
"Ta samu É—a na miji,amma shima bazaku samu ganinsa yanzu ba,saboda baya motsi sosai"
"To mashaallah Allah ya rayashi bisa sunnah,itama Allah ya bata lafiya. To yanzu kuma me dame za'a buƙata wa ita mai jegon?"
"Eh to a yanzu kam babu,yawwa kada a yi mata wanka da ruwan zafi,za'a rubuta maganin da zatayi amfani dashi"
Har ta tafi dawo tayiwa innan tuni,saboda tasan halin taurin kai irinna mu na mutanen ƙyauye.
"To shikenan Inshaallah zamu kiyaye,mun gode sosai sosai"
Yanzu inna sai murna take kaman ba ita bace take kuka ba É—azu.

*SUMAIMAH (POV)*

Tashina kenan ban daÉ—e ba,abin yaban mamaki wai kwana nayi kass ina bacci,duk ma nasan allura ce sanadi..
Tunda na tashi ishirwa take damuna,har na shanye cikin jug nan da nan,dam ma inna ruwan zafi take bani,gashi bana so haka na daurewa na ƙarba.
Shafa cikina nayi,duk da yana nan da girmansa amma ba kaman jiya ba,wai dama duk ƙaton cikinnan dayake jana a hnayar makaranta ɗa ɗayane a cikinsa,kai gaskiya to kato ne inaga..
NikaÉ—ai nake wannan tunanin a raina,dan bansan ya yaron yake ba,yanzu ne ma wata nurse suka fita itada inna su kawomin shi.
Ikon Allah wai nice na haihu kuma É—an goje,abinda ban taba kawowa a raina ba kenan,haka wai gojen zai tafi ya barni har tsawon wannan lokacin.
Ƙarar murda ƙofa naji,hakanne yasa na juyo da kaina ina kallon mai shigowa..
Inna É—auke da yaron a hannunta,sai Deejah wacce take binta a baya.
Tahowa take amma gani nake kaman bata sauri,domin na matsu naganshi.
Hannu nasaka na karbeshi,duk da jikina bashida wani ƙarfi sosai.
Bacci yakeyi abinsa baisan ma mai duniyar take cikiba,yana kamada goje sosai,saidai kuma ban san miye ba amma akwai wani abu irinnawa a fuskar tasa.
"Anty Sumaimah dawa yake kama toh,nidai kama yakemin da wani ɗan jikin calender a ƙofar chemist ɗin anguwarmu"
Kallon bakida hankali har yanzu Sumaimah tayi mata kafin tace.
"To dama dole yayi miki kamada shi mana tunda shima jinjiri ne koh"
"Ehh to hakane,É—azu da aka shige dake inna tayi ta kuka hhjhhhh dama ashe haka take kuka,waiwai gotal kenan"
Fashewa tayi da dariya tana nuna inna da yatsa,wanda hakan yasa ta kaimata duka tayi waje da gudu.
Dariya mukayi nida innan,wai hakan ma da sauƙi tunda bata dukan yara a makaranta sosai,kuma wata shekarar nakeson sakata a JSS one,tunda nayi magana sunce zasu karbeta indai zata iya karatun. Ban faɗawa inna ba har yanzu,amma kuma kafin na haihunnan nafara koyamata karatun secondry ɗin.
"Allah ka shirya khadija"
"Ameen fah,ai wannnan yarinya sai gyaran Allah"
Inna ta faÉ—a.
"Uhm inna shin wanne suna za'a saka masa ne?"
Saida nayi maganar ne na tuno ashe bamma san sunan goje ba na ainihi,wannan shi ake ƙira gallo.
A zabure na kalli inna tareda yimata tambayar..
"Tabb inna wai menene sunan gojene na ainihi,koda gaskene sanda aka sameshi babu wanda yasan komai nasa?"
"Uhhh Sumaimah na faÉ—amiki ki daina wannan zancen,kawo yaronnan nan kigani"
Jin abinda ta faɗa yasa na ɗora mata dan akan cinyarta,cikeda kulawa da ƙauna take kallonsa har ta ɗora bakinta a kunnensa,ta ɗan dau lokaci kafin ta juyo ta kalleni.
"Nayi masa suna da Muhammad. Wato yazama Muhammad Ahmad Hamma kenan"
"Hakane sunan goje na ainihi,Allah ya rayashi,to amma taya kika san laƙaninsa?"
NafaÉ—a cikeda mamaki,dan ina cikin duhu diÉ—im da lamarin rayuwar uban É—annawa.
"Kinyi min alƙawarin bazaki ɗaga wannan zancen ba sai bayan kin haifi abin cikinki kuma kin gama makaranta,dan haka dan Allah ki bar zancennan ba yanzu ba."
Ba hakan naso ba amma nariga na yarda da hakan tun watannin da suka wuce,Inshaallah zan jira wannan lokacin har yazo.
"Amma zan iya É—an sakaya masa sunan kaman nace Sayyid"
"Hakan ba matsala Allah ya rayashi bisa imani"
Ahmad na maimaita a raina,suna mai daɗi amma ake ƙiransa da wani goje.

Chapter Navigation

Use this section to move to any chapter without going back to the top.