Trending Hausa Novels

Sanadin Caca Book 2 Complete Hausa Novels By Sadi Sakhna

Reading file: SANADIN CACA 2.txt

Chapter 8 of 42

____∆∆∆____

Ya yage takardu sunfi guda biyar yana zubarwa,kansa ya kulle ya rasa ma mai zayyi.
Kansa ya riƙe tareda jan gwauron numfashi.
Kwanansa uku kenan da zuwa office amma yagagara yin komai kaman nada,abubuwa da dama sun canja ciki harda tsarin wajen,abun yana cin zuciyarsa ganin duk yanda yakeson aikinsa ya tafi a gaggawa amma abu ya gagara. Duk ƙoƙarin daya dungayi a baya ya tara shaidu duk sun tafi kaman anyi ruwa an ɗauke.
Kansa ya É—ora a kan kujerar yana jinata a hankali idonsa ya rufe.
Yaji alamar buɗe ƙofa wani ya shigo,tun kafin ya bude ido yace.
"Eemran mai Abbah yace,ya bamu izinin binciken wanann gidan?"
"Am sorry sir amma har yanzu ya ƙi saka hannu,a cewarsa wai bai kamata ka fara babban aiki irin wannan ba daga dawowarka"
"Hmmm kaida Neelah ku fara aiki cikin sirri,bazan iya tsayawa da aikinnan ba"
"Amma yallabai akwai hatsari muyi batareda sanin sama ba"
"Hatsari ya wuce wanda nake ciki,kullum hankalina a tashe yake da tunanin a kowanne irin sakanni za'a iya sake farautar rayuwata ba, shin akwai abinda yafi haka hatsari Eemran?"
Duk yanda yake boye damuwarsa tun bayan dawowar tasa,amma kana kallonsa zaka san baƙaramin dauriya yake ba.
"Hakane kam ogah lamarin abin abun a dubane,nida Neelah Inshaallah zamu iya ƙoƙarinmu wajen ganin komai bai sake zuwa da matsala ba.
Wanda suke aikata waÉ—annan abubuwan da sannu zasu zo hannu.
Hular sa ya É—auka ya É—ora akan kayan uniform É—innasa,wanda suka sake fito da jarumtarsa a fili.
Yau baizo da drivernnasa ba wai mai ɗakinsa ta haihu,dan haka da kansa ya tuƙo bai ɗauki wani drivern ba,domin dukkansu ba yarda yayi dasu ba,yasan duk yaran hajiyah maryam ne.
BuÉ—e motar yayi zai shiga,tsayawa da shiga motar yayi sanadiyyar wani akwati daya gani a wajen zaman drivern..
Kaishi yayi É—ayan sit É—in,sai bayan ya zauna kafin ya É—auko shi ya buÉ—e..
B'era ne matacce a ciki sai wata wasiƙa da jan ink.

.........kayi hankali da rayuwarka yaro,baka san mai kake shirin tonowa ba,hakan bazai ta'ba kyau ba,domin sakamakon dazaka gani bazai ɗauki ƙwalƙwalrwar ka ba.
Hmmm wato warning É—in a aka baka a baya bai isheka ba saika sake aikata wani kuskuren?.......
Ninke ta kardar yayi tareda sakata a aljihunsa,yayinda bandir ɗin kuma ya jefashi ta windown motar,ƴar ƙaramar tsuka yaka yana cije ƙasan bakinsa,ganin bata lokacin zayyi yawa yasa yaja motarsa zuwa gida. Wanda baya ganinsa a matsayin gidan kaman yanda wasu ke gani,dan ɗaukar wajen yake tamkar inda duk jagayen dakayi zaka dawo ka kwana da makashinka a ciki..
A hankali yake jan motar yana bin karatun dayake tashi a cikin motar har ya isa gida..
Bai samu kowa a babban falon gidan ba,wanda daman hakan yakeso,in badan Abbah ya hanashi yin amfani da ƙofar bayansa ba da babu wanda zai dunga ganinsa ma saita kama dole.
Buɗe ƙofar shiga sashennasa yayi ya shiga,an sanja masa ajiyar fulawar da take kusa da window,wanda daman yana zuci zucin ya kaita kusada rana ya manta..
Sannan an goge ko ina a falon ƙal ƙal sai ɗaukar ido yakeyi,duk da yanda yaɗebo gajiya da tashin hankali amma gyaan ya burgeshi matuƙa.
ÆŠakinnasa ya nufah da hularsa a hannu.
Jefata yayi akan gado,wanda aka sanja zanin gadon ba na É—azu bane akai.
Rigar jikinsa ya cire harda singlet É—in,domin dama ya saba duk lokacin daya dawo sai yayi wanka tukunna ya wanke gajiyar jikinsa.
Bai shiga banÉ—akin ba tukunna sai ya tsaya yana aikinnasa na kullum wato tunani.
.........
Tunda naji batun biyana 20k a wata wani ƙaimi na nayin aiki yanda ya dace ya tashimin.
Bin inna ladiyo na dungayi akan tafaÉ—amin yanda aikin yake.
Anan nakejin wanda zanyi wa aikin shine É—a na fari a gidan,mahaifiyar sa bata nan,sannan ance ya mutu a hatsarin mota tsawon shekaru,sai yanzu ya dawo.
Ba wannan na maida hankali akai ba saina halayensa da aka sanar dani.
Bayason mutane sosai, dan haka duk wacce zatayi masa aiki to fah ta tabbatar ta gama komai kafin ya dawo,kar ta bari su dunga haɗuwa itada shi a sashennasa,bayason yayi magana ayi banza dashi kokuma a bashi amsa da kai,ki tabbatar komai yasakaki zakiyi da jiki,kuma karki bar ko ina da ƙazanta. Karki yi zaton ganin sakin fuska daga gareshi,kokuma a matsayinki na mai aiki mai jini a jika kiyi tunanin zakija hankalin sa,domin dan dole yake bari mai aikin ta yi masa hidima,saboda bai yarda da ƴan gidannan ba kaff,itama mai aikin koya ya kamata da wani abun da bayaso a ranar zai koreta"
Lokacin danaji waɗannan bayanan harda wanda suka fisu saida na cika da matuƙar mamaki,shin shi wannan wanne irin mutum ne haka.
Da sauri na É—ebi abubuwan aiki na nufi sashennasa,cikin sauri sauri na gama ayyukan,domin gaba É—ayansu banga abin wahala ba.
Yanzu ma na gama kowanne sai banɗaki,shima na kammalashi,saida na duba naga na saka komai har turaren banɗaki da komai da komai kafin na buɗe ƙofar na fito.
Mutum na gani a tsakiyar É—akin ya juya bayansa,hannunsa a cikin sumarsa yana yamutsawa.
Ko ba a faɗaminba nasan shine,ƙoƙarin kawar da idona nake tareda yin istigfari a zuciyata,ganin ina matar aure na tsura wani namijin ido,hakan ma wanda ba muharramina ba. Lokacin danaji yin aiki a sashen wani namiji naji wani iri,amma da akace bazan haɗu dashi ba sainaji dama dama,gashi daga farawa yau har mun haɗu. Kai dole nayiwa inna ladiyo magana akai.
Sunkuyar da kaina nayi ina kallon ƙasa,ganin ya juyo yana kallona,ko ban ganiba nasan yana mamakin mai ya kawoni ne.
"Wacece ke,mai kike a É—akina"
Muryarce tayimin kamada wacce nasani,ohh no banason tuno shi a yanzu ba yanzu ba please.
"Ba magana nake yimiki ba,meyasa bazaki kalleni ki amsa min ba?"
Gabanane ya fara dukan miliyan miliyan..
Idona nafara É—agawa inda yaja birki a daidai kan tabon raunin dayake cikinsa da bangaren dama,wanda yayi sakk dana mutumin da bana fatan yazama irinnasa.
Saurin ɗaga idona nayi na sauƙe akan fuskarsa.
A cikin mintuna kaɗan na daskare a wajen a daidai lokacin da ƙwayar idona ta caku a cikin nasa idon. Duk da cewar komai nawa ya daina aiki amma kuma saida ƙaramar ƙwaƙwalwata ta samu damar amsa kuwwar sunansa a cikin kaina.
"Gojeeeeeeeeee"

To nima nayi nan fah mutane manzo........

SADI-SAKHNA CEH
09035784150
ku tuntubeni domin biyan kuɗinku ko ƙarin bayani.

*SANADIN CACA*
-BOOK 2 (PAID)

Mallakar *SADI-SAKHNA*
09035784150

Bismillahir-rahmanir-raheem

Ki biya kan ki karantamin na biyu dan Allah. ga number ta nan mai son littafi na É—aya yayi min magana zan bashi shi kyautane.

Ina ƴan mata dakuma Matan aure masu muradin burge mazajensu da ɗinkuna zuƙa zuƙa. *PHEEDY TOILORING DESIGN* ,suna gabatar muku da ɗinkuna kala kala wanda sukayi daidai da zamani.
Zaku samemu a kan wannan layin waya kamar haka

Chapter Navigation

Use this section to move to any chapter without going back to the top.