Sanadin Caca Book 2 Complete Hausa Novels By Sadi Sakhna
Reading file: SANADIN CACA 2.txt
Chapter 21 of 42
Duk wajen babu wanda ya kulada abinda ya faru sai hajiyah Maryam,Saleem da kuma Sameer.
A tare nida ummi muka bar wajen,ganin yanzu lokacin sune na tattaunawa.
"Kai nifah masu kuÉ—i suna bani mamaki,to shi wannan zama a ci abincin menene amfaninsa ne?"
Ƴar dariya nayi kafin nace.
"Uhm kowanne ɗan adam yanada tsarin yanda Allah yayi masa rayuwarsa ummi,su wannan ce hanyar da suke bi wajen haɗuwa da ƴan uwansu,bakya ganin waccar ƙanwar babannasu har daga maiduguri tazo?"
"Uhm ummi dan Allah zoki kai wanann yarinyar tana ta kuka mana"
Lokaci guda ta haÉ—e fuska,
"Haba inna ladiyo kinsan fah banason shiri da yarannan,ita É—in menene bazata rike yarinyar nan,su waÉ—annan masu kuÉ—in malalata ne"
Kallon yarinyar nayi wacce take ta tsala kuka gata ƙarama. Da kuma ummi wacce take zuba mita.
Kodan nima uwa ce,haka kawai na tsinci kaina da jin tausayin yarinyar.
"Inna kawo ta na kaita,tanata kuka bakinta har ya bushe"
Daidai shigata cikin falon najiyo muryar Alhaji Aliyu.
"Dukka nayi magana dasu kuma sun amince,kuma tunda ba abune na fari ba,kuma akwai halin yin na yanke wani satin za'a É—aura musu aure"
"Sati É—aya yayi kaÉ—an,a matsayina na matar gidannan kuma mai iko da komai to ban yarda ba"
Kowa kallon hajiyah Maryam yayi,jin yadda tayi maganar a dake.
"Meyasa zakice haka,menene dalilinki na ƙin amincewa"
"Maimuna ta yimaka zancen akwai wanda suka daidai ta zaizo wajenka,sai kace sai kayi tunani,haka Fatee kafi kowa sanin soyayyar da suke da Sadeeq amma baka bawa abin hankalin ka. Meyasa sai wannan da bawani damuwa yayi da abinba kake ƙoƙarin saishi zakaga kawai yayi iyalansa?"
Sakin baki Alhaji Aliyu yayi,ya rasa meyasa hajiyah Maryam take masa irin wannan tsanar,yana zure cin zarafinta in suna su kaÉ—ai amma a bainar jama'a abin da cin rai.
Cikin fushi Aina'u ta ajiye cokalinta tareda fuskantar hajiyah Maryam..
"Wai Maryam mai yake damunki,meyasa bakya iya boye zafin kishinki da hassadarki akan rayuwar Ahmad,kodan saboda kinga shine babba ba Æ´aÆ´an ki ba shiyasa?"
Ƴar dariya hajiyah Maryam tayi kafin tace.
"Baƙin ciki da kishi,na me kenan. Inda ɗansa ne shi da saiki cemin zanyi kishi kokuma nayi baƙinciki,amma babu wanann tunda ba ɗansa bane."
"What maryam wannan wane irin shirme kikeyi haka?"
"Shirme haka kike gani shirme nake? Ahmad ba ɗan Alhaji Aliyu bane, Maimuna itace ƴarsa tafari,idan kuma baki yarda ba ga nan uwarki da kuma yayannaki ki tambayesu. Dan haka batun nayi masa baƙinciki ki ajiyeshi a gefe,in kinga yaci gadon Alhaji Aliyu to ƴaƴana ne dukka suka mutu"
Tana gama faÉ—in hakan ta tashi daga kan kujerarta hankalin ta kwance ta bar wajen.
Idone ya koma kan Ahmad,wanda ya rumtse cokalin dayake hannunsa ƙam kaman zai maidashi cikin hannun,bakinsa yana rawa ya kalli AM Aliyu da jajayen idanuwa.
"Abbb......abba shin dagaskene abinda matarka take faÉ—a?"
Runtse ido shima AM Aliyu yayi,saboda bashida ƙarfin gwiwar kallon idon Ahmad ɗin ya tabbatar masa da abinda yakeson sanin.
Kuka hajiyah Mammah ta rushe dashi tareda saka gefen zaninta tana sharewa.
Tunda naji abinda hajiyah Maryam ta faÉ—a na zama tamkar gunki a wajen,shin ni wannan matar wacce iri cene.
Gaba da gaba muka tsaya da taxo zata fita daga falon. Wani shu'umin murmushi tayimin bayan ta dafa kafaÉ—a kafin tabar wajen.
Juyawa nayi nabi hanyar data bi da kallo.
Bangazata naji mutum yayi yafice daga wajen,iya bayansa kawai na samu gani,tafiya yake kaman zai tashi sama don sauri..
Ohh dagani har shi sai wahala muke sha a bangare mabambamta,shin yaushe komai zaizo da saukine?.
Hankalina yayi gaba ji nayi an fizge yarinyar data ke hannuna tana kuka.
Hanyoyi biyu na kalla wanda suke hannun riga.
Wajenda Ahmad yayi da kuma wajenda hajiyah Maryam tayi.
Shin ita zanbi naji mai yake faruwa,kokuma shi zanbi domin na tausheshi akan halin da yake ciki?
Ku fadamin a comment shin wacce hanya kuke ganin yakamata tabi a ciki?😄😄
SADI-SAKHNA CEH
09035784150
ku tuntubeni domin biyan kuɗinku ko ƙarin bayani.
*SANADIN CACA*
-BOOK 2 (PAID)
Mallakar *SADI-SAKHNA*
09035784150
Bismillahir-rahmanir-raheem
Ki biya kan ki karantamin na biyu dan Allah. ga number ta nan mai son littafi na É—aya yayi min magana zan bashi shi kyautane.
Sister's duk wacce batayi anfani da sabulun mg's ba ko kit dinsu inamai shaidamuku anbarku acan baya domin duk wnd yajaraba mg's sai sanbarka duk wani Mai tantama Akan kayan gyaranjiki toh tabbas yacire sabulun mg's domin yahadu bakarya zegyarajiki yafidda dattin fata Dama duk wani matsalan fata duk Wanda kefama da matsalan fata walau pimples ko spot, sunburn acne,stretch mark dama dukkan wani prblm yajaraba mg's bi'iznillah komai zaizama labari bayan jikinku yy fresh zaisa jikinku yy smooth yadinga glowing,gawanda basa San anfani da Mai zaku iya using mg's batare da kunbukaci wani Mai b🤗nd wnn new soap din💣ne,😯 bama cika Baki kujaraba kugane ma idanku domin ance gani yakoriji Kuma siyan daya maida kudi gida
You can check pic👇for the soap reviews🥰
Soap price:4k
maiso yy mgn
08062991549
07046881166
07067210195
Call 08064532391
Instagram:glow_with_mgs
Facebook: mg's skincare
Masu bukatar cream Shima munadashi harda ma complete set nagyaranjiki
Small 14k
Babba 16k
Munatura Kaya kowani gari dayardar Allah Amma delivery is not free
Be part of the glow teamðŸ˜karkubari abaku lbrðŸ‘
*BOOK 2*
...19...
Hayaniya ake tayi a cikin É—akin taron,kaf cikinsu babu wanda yayi tunanin a haka abin zai kasance. Kowa yana faÉ—in albarkacin bakinsa.
Yayinda Sumaimah kuma aka barta a tsaye tamkar gunki a kan mashigar wajen.
Kallon kallo take bawa bangaren guda biyu,da alama ja'inja take da ƙwaƙwalwarta kan wacce hanya zatabi. Hanyar sashen hajiyah Maryam ta nufah,domin a yau kam tanada buƙatar son jin menene maƙasudin faruwar komai,menene ainihin tarihin abinda yake faruwa?.
Har takai daidai shiga sashennata,saikuma wata zuciyar ta tuna mata mijinnata,shin a wanne hali yake a yanzun,gashi bashida kowa a gidan bare ya waiwayi lamarinsa,kuma a wannan yanayin dayake ciki yana buƙatar mai zama a kusada shi.
Juyawa tayi da akalar tafiyar tata zuwa sashennasa. Tafiya take ranta cikeda abubuwa masu dama.
Kai tsaye ɗakinnasa ta wuce,a bakin ƙofar dakin ta tsayah tana kallonsa,yana zaune a tsakiyar gado ya saka gabansa can. Daga bayannasa mutum na iya gano yanda ƙirjinsa yake sama yana ƙasa.
Jan ajiyar zuciya tayi kafin tafara takawa a hankali zuwa inda yake.
Tunda ya tambayi Abbansu yaga yayi shuru,hasalima yakasa haɗa ido dashi,hakan ya tabbatar masa da abinda hajiyah Maryam tafaɗa dagaske takeyi. Wani duhu yagani,yayinda duniyarsa ta tsaya na wasu daƙiƙu,shi ba ɗan Alhaji Aliyu bane,to kenan wanene ubansa,shegene shi ina mahaifiyar sa,an ce ta mutu,waye mijinta kenan,kokuma dawa tayi tarayyah,ko tsintoshi sukayi kai.
Wannan kalaman sune suke ta yawo a ƙwaƙwalwarsa har ikon Allah yakaishi ga sashensa,babu cire takalmi haka ya hau kan gadonnasa, ƙirjinsa ya riƙe gam jin yana yimasa wani hawa da sauƙa kaman ana famfo.
Jinsa yayi tamkar shi kaÉ—aine a duniyar,bashida kowa ballantana yasamu wanda zai zauna dashi a wannan zazzafan yanayin.
Hawaye ne zafafa suka fara kwaranyowa daga cikin idanunsa. Rayuwarsa kullum cikin karbar baƙuncin sabon abu takeyi,shin yaushe wannan abin zai ƙare?.
Tsayawa yayi da tunanin jin hannu ya daga bayansa,wanene ya tuna dashi yazo wajensa a wannan halin,a saninsa dai Sadeeq bayanan kuma bai san mai yake faruwa ba.
"Lafiya kake? Karka damu komai zai wuce sai labari,hakan jarabawa ce wanda idan ka jure ka cinyeta zakaga sakamako Mai kyau"
Sumaimah ce take yimasa maganar cikin sanyayyiyar zuciya mai cikeda alamar rarrashi,duk da itama tana cikin damuwar amma yanda yakeji tasan yafi nata.
Kanta ta É—ora a bayansa tana cigaba dayimasa maganganun da tun baya fahimta har yafarajin mai take faÉ—a.
Zogin da zuciyarsa take masa ne yasashi sakin wani wahalallen nishi,jij hakan yasa Sumaimah dawowa gabansa da sauri.
Cikeda damuwa take kallon shanyayyun idanuwansa,masu cike da abubuwa kala kala.
"Ƙirjinahhhh"
Shine abinda ya tsinci kansa da furta mata a hankali.
Hannunta tasaka a saitin ƙirjinnasa kai tsaye bata kawo wani abu a ranta,idon da zare jin yadda take bugawa da matsanancin gudu fiyeda na kowanne lafiyayyayen ɗan adam.
"Tana bugawa da ƙarfi,yakamata na sanarwa Saleem da sauri"
Ƙoƙarin sauƙa take akan gadon yayi saurin riƙo hannunta.
"Karki ƙiramin kowa,banason kallon wani daga cikin ahalinnan kowaye shi a yanzu"
Kallonsa take da alamar tausayi,kaman ƙaramin yaro haka taga ya koma mata a lokacin. Batasan sanda zuciyarta ta ɗebeta da rungumeshi ba. Ga mamakin ta kuma sai taji shima ya maryar mata da martani.
Duk da cewar yasan kusancinta dashi a lokacin ba abune mai kyau ba,amma kuma samunta a gefennasa ya rage kaso mai yawa na damuwarsa,saboda abune da bai fiye samu ba. Shiyasa ya tsinci kansa da kasa hanata,saima sake sakemata da yayi.
Sun daÉ—e a haka rungume da juna kafin yasaketa tareda cikin sanyin jiki.
Kunyace takamata ta dawo hayyacinta data tuna mai ta aikata,duk da tasan hakan ba laifi amma kuma shi zaiji ya aikata laifin a ransa..
Saurin sauya iskar wajen tayi tareda sauƙa daga kan gadon. Hanyar banɗaki ta nufah da sauri tana magana.
"Uhm barina haÉ—amaka ruwa kayi wanka gumi kakeyi,kafin ka fito kuma na haÉ—amaka shayi"
Ƙofar data rufe yabi da kallo tareda jijjiga kai a hankali. Ya rasa meyasa yake idan yana tareda itah sai yarasa nutsuwarsa da taka tsantsansa,he can't imagine wai ya rungume mace kuma ba muharramarsa ba,sannan baiji dana sani sosai a ransa ba. Kodai kai bai warke ba daga halayyar daya gamu da ita a baya? Amma kuma ai bayajin son yin komai banda wannan ɗin.
Chapter Navigation
Use this section to move to any chapter without going back to the top.