Trending Hausa Novels

Sanadin Caca Book 2 Complete Hausa Novels By Sadi Sakhna

Reading file: SANADIN CACA 2.txt

Chapter 28 of 42

SADI-SAKHNA CEH
09035784150
ku tuntubeni domin biyan kuɗinku ko ƙarin bayani.

*SANADIN CACA*
-BOOK 2 (PAID)

Mallakar *SADI-SAKHNA*
09035784150

Bismillahir-rahmanir-raheem

Ki biya kan ki karantamin na biyu dan Allah. ga number ta nan mai son littafi na É—aya yayi min magana zan bashi shi kyautane.

*BOOK 2*
...26...

A bangaren Ahmad kuwa da Sumaimah tafita,jiyayi gabaÉ—aya duniyar tayi masa zafi,kenan daman duk tsawon wannan lokacin matar aure yakeso,wani abu mafi munin ma wai har ya kwanta da itah,wannan lamari har ina.
A daddafe ya shirya cikin kayan aiki ya bar gidan,abincin data haÉ—amasa ko kallonsa bayyi ba.
Bayan yaje office É—in ma shuru yayi tareda dafe kai,yarasa ma mai yake masa daÉ—i.
Eemran ne ya shigo hannunsa É—auke da file.
Bayan yayi masa gaisuwar sojoji ne ya ajiye masa file É—in a gabansa.
"Ranka ya daɗe mun samu maboyar inda shigaban ƙungiyar yake,yana garin DABAGAYI ne amma can cikin jeji,mun samu hakanne bayan........."
Bai gama bayanin ba Ahmad ya karbi file É—in ya fara dubawa,haba no wonder shiyasa suka rasasu,suna can inda ba'a tsammani.
"Eemran ku shirya private jet a yau zamuje wajen,i need to end this case da sauri,nasan koma menene yanada alaƙa da wani nawa,kuma da rayuwar danayi a baya,nagaji da zama cikin wannan duhun,i need to know everything"
Yana gama faÉ—in hakan suka bar office É—in zuwa headquater su.

Wajen yamma rana ta kusan faÉ—uwa suka shiga cikin jejin,a bakin wajen suka tsaya,basuda wani yawa don basu wuce su goma ba,saboda binciken na sirri ne,ko mahaifinsa baisan sun tafi ba.
Saidai sun É—ebi makamai masu hatsarin gaske.
Jejin Ahmad yake ƙarewa kallo,haka kawai ya tsinci kansa dajin kaman yasan wajen. I donsa ya rufe yaja wata iska mai nauyi,haka ido a rufen yafara tafiya a cikin jejin.
Sudai sauran sojojin binsa suke a baya har suka iso bakin wani É—utse,babu kowa a wajen,amma kuma suna jiyo motsin wasu na tahowa ta bayan dutsen.
Hakanne yasa Ahmad yayiwa tawagarsa alamar suyi baya cikin duhuwar jejin su shirya kai farmaki.
Yana nan tsaye ya saita duk wanda ya zo ya harbeshi,wasu mazajene manyan manya guda huÉ—u,kana ganinsu kaga shu'umai suka bayyana,suma tasu bingidar tana É—ane,domin da alama kaman yanda su Ahmad suka ji motsinsu suma sun ji nasu motsin.
Na gabanne yafara sauƙe bindigar tareda yiwa na bayan magana.
"Kai ku sauƙe ogah gojene fah ya dawo"
Jin sunan yasakasu sauƙe bindigoginsu tareda matsowa,gaisuwa suka miƙa masa tareda cewa.
"Ogah ya dai sai yanzu ka dawo,ai har anyi taro ganin shuru shuru baku dawo ba yasa akayi tunanin duk cikinku babu wanda ya rayu, Don 2 a ranar na naÉ—a sabon Don3 amma mu bayyi mana ba,dama muna fatan dawowarka"
Duk maganar da suke Ahmad binsu kawai yake da kallo,sai a sannan maganar wancan barawon da suka kama ta dawo masa,da kuma maganar Sameer shida Abbansu. Kenan dai a rayuwar da yayi baisani ba a wajensu yayi aiki,Allah yasa ma ba kayan sojojine a jikinsa ba da sun ganeshi.
ÆŠaya daga cikinsu ne ya dawo dashi daga tunanin daya tafi,ta hanyar jan hannunsa zuwa cikin sansaninnasu.
Suna tafe yana binsu a baya batareda yace komai ba har suka isa Wani É—aki.
Shiga sukayi ya bisu,ba É—akin kwana bane,domin hadda kujera da table a ciki.
Don 3 yaji sunce a gaisuwar da sukayiwa wanda yake kan kujerar,shima ƙatone amma bakaman su ba,saidai ya fisu murɗewar jiki.
"To ogah mai guri yazo mai tabarma sai ya naÉ—e,ogah goje ya dawo,dama matsayinsa ne a ka baka"
Daga yanda suke maganar ya tabbatar kam ba sonsa suke ba a shugabannasu.
"Wanne zancen banza kukeyi haka,kunyi farautar da aka saka kune,nida idona naga goje an soka masa wuƙa,dan haka bai tsira da ransa ba"
Matsawa sukayi daga gaban yayi arba da goje,wanda yake sanye da baƙaƙen kaya da bindiga a hannunsa.
Firgit ya tashi yana rarraba ido,ashe da gaske sukeyi dai.
Ganin yafara kame kame ne yasa Ahmad ƙarisawa gabnasa tareda yin murmushi.
"Lahh ogah kada ka damu fah,ni yanzu ma inada wasu yaran mun kafa tamu ƙungiyar,saboda lokacin da abin yafaru na bugu,na manta komai na rayuwata,iya kawai sunan ƙungiyar ne yazo kaina da kuma inda take shiyasa nazo"
Wani washe baki yayi tareda cewa.
"Ahh toh abu yayi ƙyau sosai,nayi zaton ai kazo ƙarbar matsayinka ne"
"Ahah bashi nazoyi ba,nazone dai wajen Don 2,saboda na tuna zamu haɗu dashi idan muka dawo a raye,sannan kuma nazo nuna masa mutanen dana haɗa,sun ƙware sosai a wajen iya aiki,bansani ba ko zasu samu karbuwa suma a........."
"Ahah mai zai hana,dama munyi rashin mutane sosai a harin da muka kai waccar shekarar,tunda kai ka kawosu to munsan babu matsala.
Kai me kuke jira,ku basu masauki mana shida mutanensa"
YafaÉ—a yana bawa wanda suka rako Ahmad É—in umarni.
"Goje in bazaka damu ba za'a baku masauƙi ku zauna kafin na aikawa da shugaba saƙon cewar kazo"
"To shikenan bakomai,ni barina je nayima mutanennawa magana"
Bayan ya koma wajen daya bar su Eemran bayani yayi musu akan plan É—in ya sauya,zasu saje da barayinne su san komai nasu kafin su kai farmaki.
Hakan kuwa akayi,dan har kaya suka sanja irin nasu,saidai ba kaman yanda sukayi tunani ba,zasu kai kusan kwana uku kafin wanda suke jira yazo.

Sumaimah (POV)

Bayan Ahmad ya koreni daga sashensa na daÉ—e a lambu ina tunani,ina ganin fitowarsa ya É—au mota ya bar gidan.
Tunda yanzu aikin sashensa ya ƙare,lokacine daya kamata dama na farka daga yi masa abu batareda yasan koni wacece ba,yanzu zan fara aikin da hajiyah Maryam tasakani a sashen hajiyah Mammah. Domin itace sanadin dukkan waɗannan abubuwan,da badan itaba da yanzu na faɗamasa cewar nice matarsa,wani lokacin saina kusan subutar baki sai na tuna da rayuwar ɗana,idan tagano shima tarwatsa rayuwarsa zatayi kaman ta mahaifinsa.
Gyara fuskata nayi na nufi sashen hajiyah Mammah.
Tana zaune akan dadduma a tsakiyar falonta,jikinta lullube da babban mayafi kamar kullum.
Sallama nayi da amsa a nutse,tsugunnawa nayi tareda karkatar dakai.
"Hajiya barka da hantsi ya jiki jikin?"
"Lafiya kalau ƴar nan ya haƙuri da rayuwa"
Hawaye na ƙaƙalo yafara zubomin,wanda bakomai na tuna na zubar dashi ba sai korar da Ahmad yayimin ɗazu.
"Hajiyah ki taimakeni kaman yanda Allah ya taimakeki, Yallabai nake yiwa aiki,babu abinda banayi masa,yau da safennan ya koreni wai kada nasake nuna masa fuskata,na tambayeshi mai ya faru yacemin wai kawai ya gaji danine.
Gashi inada ɗa da kanwa da innata a ƙauyenmu wanda nake tallafawa,miji kuma ya tafi nema har yanzu shuru bai dawo ba"
Kuka nake kaman raina zao fice,inaji tana cemin nayi shuru amma banyi niyyar tsayawa haka ba,saina amayar duk abinda na ƙunsa kwanannan.
Saida naji zuciyata tayi sakayau kafin tanafara rage kukan ina jan majina.
Mai akinta Kaltum ta ƙwalawa ƙira,sai gata kuwa tafito daga wani ɗaki.
"Zo kalutume ga wannan yarinyar daga yanzu zata dunga tayaki aiki anan sashen na É—auketa aiki"
"To shikenan hajiyah za'ayi yadda kika ce"
"Karki damu ki dunga aikin anan sashen,saidai idan zakiyi min aiki banda gulmace gulmace,sannan banda rawar kai,duk da naga bakiyi kamada mai hakan ba dama, ki kwantar da hankalin ki zan biyaki,yanda zaki kulada ƴan uwanki,Allah yaƙara rufamana asiri"
"Ameen ameen hajiya,nagode nagode sosai,kaman yanda kika taimakeni kema Allah yayi miki hakan"
NadaÉ—e ina kwararo mata Addu'a godiya,ina cikin hakanne kaltum tasake shigowa tareda raÉ—awa hajiyah Mammah wani abu a kunne.
ÆŠan zaro ido tayi tareda sauya yanayin fuskarta.
"Kin bata maganin amma taƙi sha,mai take nufi kenan,dashi zata zauna har a sani? Kice mata ta sameni a ɗakina yanzunnan"
Daga haka ta sallameni suka shiga ciki. Ko basu fadaba nasan zancene akan cikin Mulaifah,nasan dai bazata taba faÉ—amusu ba,in kuwa suka gane kenan ya wuce wata biyu.
Ina nan zaune a wajen ina nazari naga Mulaifah tafito daga ɗakinta zata shiga na gaji Mammah ɗin,harara ta bankamin,tayi wata rama ga fari data ƙara kamar wata fatalwa.
Murmushin mugunta nayi kafin na fito daga sashen,hmmmm danma bata san nina lalata mata shirinta ba kenan.

Chapter Navigation

Use this section to move to any chapter without going back to the top.