A Dalilin Matar Uba Part 1 Complete Hausa Novel
Reading file: A_Dalilin_Matar_Uba_Part_1_Complete_Hausa_Novel.txt
Chapter 10 of 35
*PAGE 📄 51 52*
"Mummy ce tace wa Afrah ta dauko mata goran ruwa da cup tana kawo wa mummy ta fara karanta suratul Fatiha, Ayatul kursiyyu da ayatushshifa, sannan ta karanta aya ta 80 da ta 81 ta suratu Yunus ta lalata sihiri tana gama karantawa tace Afrah ki bata tasha sannan ki shafe mata jikin ta da sauran.da kyar Afrah ta samu *Xeey*tasha tana gama sha ta fara zare zaren ido ta sai kuma ta fashe da kuka har bacci yayi awon gaba da ita dakyar suka samu suka kaita bedroom Afrah tayi mata addu,oi ta rufe ta da blanket.
*CIKIN DARE* cikin bacci Afrah taji ana kokarin bude kofar dakinsu bude idan da zata yi taga Xeey ce keson bude dakin ta fita cikin saurin da ko ita bata san tana dashi ba ta isa bakin kofar ta sanya karfinta gaba daya ta janye *Xeey* daga jikin kofar tasa key juyowar da zata yi taga Xeey ta kwanta a kasa tana burgima tana yayyaga kayan jikinta "kuka me karfi Afrah ta saki cikin tashin hankali ta lalubi wayarta number big bros ta latsa ta gaya masa abinda yake faruwa saboda bata son ta tashi mummy a tsakar dare tace yazo ya taimaka yayi wa Xeey allurar bacci bata fi 3 minutes da ajiye wayar ba sai gashi ya iso da kyar aka samu akayi wa Xeey allurar kasancewar ta birkice tana ta buge buge bakinta yana ta motsi kamar me son fadin wani abu baifi 5 minutes dayi mata allura ba kasala ta saukar mata da wannan damar Afrah tayi amfani wajen biya mata Ayatul kursiyyu a kunnuwanta har bacci me nauyi ya dauke ta hamdala Afrah tayi ta koma ta kwanta.
__ knocking din data ji anayi shi ya farkar da ita mummy ce ke cewa Afrah kin makara fa yau har 6:00 o'clock baki yi subhi prayer ba tashi tayi gami da tattaki zuwa toilet ta daura alwala sannan tayi sallah sannan mummy ta bata ruwa Wanda aka karanta suratul bakara, fatiha,falaqi, Nasi, laqada ja,akum Wanda aka dandaqa ganyen magarya guda bakwai cikinsa tace ta shafewa Xeey jiki dashi karbar ruwan tayi ta fara shafawa Xeey kamar wadda aka mintsina haka ta tashi tana kokarin zubar da ruwan mummy ce ta rike ta tana karanta mata ayatul kursiyyu a kunnuwanta nan take kasala ta zo mata tayi luf ajikin mummy kamar ba itace take buge-buge ba bacci me nauyi ne yayi awon gaba da ita wanda ko breakfast bata samu taci ba sai around 12:00 o'clock.
*Bangaren* Isma,il kuwa kwance yake yana bacci mafarkin Xeey yayi ya ganta acikin wani katon rami mai xurfi tana ta miko masa hannu tana kiransa *isma,il Isma,il Isma,il* yayi kokarin zai jawo hannunta sai kawai duhu ya raba tsakanin su yana jin kukanta amma baya ganin ta, kuka me karfi ya saki Wanda yayi dai dai da farkawarsa fuskarsa cike da hawaye yayi sharkaf da gumi duk da AC dake kunne a dakin da sauri ya sauka kasa ya fara kuka me karfi yana kiran sunan Xeey kamar wanda aka tsikara tashi yayi ya dauro alwala ya fara nafila ya ringa yiwa Xeey addu,ar neman kariya yana rokar mata mafita a wajen Allah bayan ya kwanta bacci kaurace wa idon isma,il yayi sai juye-juye yake yana tunanin mawuyacin halin daya ga Xeey aciki kara fashewa yayi da kuka.
*H*ajiya Sa,adatu ce da daddy ke sauko wa daga step suna hira da daddy tana fari tana kasa da murya tace Alhajina da badon karka ce na fiya fitina ba dana dan nemi wani abu a wajen ka washe baki yayi tare da cewa banda abinki me zaki nema da nake dashi na hana ki kome kike so fadamin zan miki shi dama ba wani abu bane so nake ka.................
Sun kuyar da kanta tayi cikin kissa ta fara fadi ina son ka bani 50.3million ne dama zanja jari dariya Alhaji yace dama ke dan wannan kike tada hankalin ki brief case dinsa ya jawo ya rubuta mata cheque ya rubuta mata 60.5 millions ya mika mata tana gani ta gigice rungume shi tayi tare dasa tafin hannunta cikin nasa tana murza wa ta fara magana Alhajina bani da kalmar da zanyi maka godiya sai dai nace Allah ya kara mana dankon soyayya toshe mata baki da hannunsa yayi yace Menene abin godiyar wajibi na ne na kyautata wa iyali na, fari tayi da ido tace Alhaji tashi na raka ka driver na jira
Karka yi late yana mikewa ta kara narke masa tare da lumshe idon ta mai kama da bantaren mudubi lol kalmomi take furtawa kamar haka *I LUV YOU WITH OUT YOU MY LIFE IS OUT OF CONTROL* to ko na dawo dai na fasa fita ne Dan naga yau soyayya ta tashi, fari da idonta ta sake yi tace a a Alhaji yi tafiyar ka babu komai.
Ummiey XEEY
*_ ∆°°••~❣_💞••💙💓❤💛
*A DALILIN MATAR*
*UBA*
*_ ∆°°••~~❣_💞••💙💓❤💛
```STORY & WRITTEN BY```
*Ummiey_Xeey Abakson💋*
*♻EXCLUSIVE WRITER'S FORUM*
[ɦօʍɛ օʄ քɛaċɛ, ɦօռօʊʀ aռɖ sʊքɛʀ աʀɨtɛʀ's]
*LIKES AND DROP YOUR COMMENTs*
FB..#https://www.facebook.com/Exclusive-Writers-Fans-E-W-F-1922297541423276/
```SADAUKARWA GA____```
*MARIAM TIJJANI ADAM😍*
Dedicated to *IDON MIKIYA WRITERS ASSO🦅* YOU GUY'S ARE AMAZING❤
Chapter Navigation
Use this section to move to any chapter without going back to the top.