Romantic Hausa Novels

A Dalilin Matar Uba Part 1 Complete Hausa Novel

Reading file: A_Dalilin_Matar_Uba_Part_1_Complete_Hausa_Novel.txt

Chapter 3 of 35

*PAGE📄31__32*

Yalwa tace kiramun Ita kiga yanda zaki Fara, Sa'adatune ta tashi zata fita kiranta, "yalwa dariya tayi tace ai seta rainaki wlhi, Daganan zaki kwalla mata kira basai kin wahalar da kankiba....

"sa'adatune ta kwalla wa Xeeeyxeey kira har sau Uku, xeey nachan na bacci Bata jiba a fusace yalwa ta tashi ta shiga dakin ta bubbuga gado tace kee bakiji *MATAR UBANKI* na kiranki Bane?

Firgigit Xeey ta tashi tace hajiya wlhi banji bane tace to maza kije tana kiranki, Xeey da bacci be gama sakenta ba ta nufa Dakin Hajiya sa'adatu Ta sama waje ta tsugunna yalwa ta Bude baki tace ke haka wai aka koya miki Kinbar bayi duk wari maza kije ki wanke kuma kina gamawa Ki share wajen flowers duk Yayi datti ko kina jiran masu aikine bayan kina kwance ba abun da kikeyi,

"xeey Tace Ok bari naje na wanke ta tashi ta nufa bayin ta tsugunna kenan ta tino da furucin matar Nan wai ba'akoya mata bane, dazu kuma tace haka aka koya musu tarbiya? Hawayene masu zafi suka fito daga idonta amma ta daure wata xuciyan tace karki kuka tunda ba *MATAR ubanku* bane tace miki haka, dan haka tai abun da zatai ta gama ta koma daki time din la'asar yayi tayi alwala tai sallah ta dakko uniform dinta tai musu sallama Ta tafi islamiya..

"Yalwa tace to kinga abun da nayi dai nida ba matar gidan ba; haka zaki dinga mata da ita da kaninta dan ke basa'arsu bace "hajiya sa'adatu Tace to indai wannan ne ba damuwa sosai karkiji komai munanan zan baki labari uwar dakina. Sukaci abinci sukai Sallah yalwa Ta tafi gidanta.....

*WASHE GARI*
tun asuba sa'adatu ta tashi amma taki tashin su xeey, dama akwai abun data ayyana a xuciyanta dan haka Ta tashi ta dafa ruwan tea dinta tana da bread da kayan tea a daki taci ta koshi ta koma baccinta hankali kwance....

"Abba ne ya fara tashi yaga gari duk yai haske, Allah yasama ran sunday ne ba school da yau kam bazasuje school ba, Kofa yai ma xeey knocking itama ta window taga gari yayi haske sosai, bude kofa tayi Tace bro yau mun makara ka bugawa anty kofa bari nai alwala nai sallah...

"Abba ya tafi yaje yana mata knocking budan bakinta tace waye ke bugamun kofa kamar yana neman abu a wajena..

"abba yai smiling yace anty mun makara tace toh naji ai tun tuni na farka kasan ku yan gayune bakwa tashi da wuri sai gari yai haske,

"abba yace laa Aunty ko sallah fa bamuyi ba da munyi sallah se mukai 10am indai weekend ne yana magana da raha,

"sa'adatu tace sai kayi kuma karka sake damuna kana jiko,

_Abba yai matukar mamakin maganganunta bece komai ba ya wuce yai sallah yazo yai wanka ya zauna yafara nazarin maganar *MATAN UBANsu* tsaki yayi dan abba yarone bameson damuwa ba, laptop dinshi ya dakko ya fara dube dubenshi, Har 10am beji Ance mai ga breakfast ba dan haka ya tashi ya nufa Dakin Xeey,

"A kwance ya sameta da alama bacci takeyi dan ba karamin gajiya tayi Jiya ba, yace sist nifa yunwa nakeji tace haa Aunty batai breakfast Bane bro? Yace banga alama ba gaskiya Tace ok bari naje na tambayo yace ok Sist

Fitowa xee tayi taga ko ina duk datti, da alama bata gyara Ko inaba, dakin step mum din taje ta tura tai sa'a a bude yake shiga xeey tayi ta gaisheta ta amsa a wulakance tun daganan Jikinta ya fara sanyi, Tace amm uhmm Aunty bamuga Abincin break fast din muba,

wani harara sa'adatu ta jefo mata tace sannu mulkakko da mai dama an ajiyeni ne dan na dinga muku girko or what, To banyiba kuma Bazan yiba infact duk aikin gidan nan ke zaki dingayi, Ba ruwan masu aiki, Munafukan yara kawai,

Me sukai kuma na munafunci kuma, wani kuka xeey ta sake a dakin Dan batasan me sukai mata ba lalle rashin Uwa gaskiyane, Jin kukantane Yasa Abba ya shugo dan ganin me ya faru, Yana shuguwa suka hada ido da Sa'adatu dukda yarone tadan tsorata dan namiji duk kankantarshi na mijini, karfin hali tayi tace fitan mun a daki, kaima kazo munafuncin kenan, Kamar zaiyi magana seyai shuru yace xeey sorry Allah nanan, ya fita a gidan dan abba nada zuciya dukda yarone,

Xeey kam itama tashi tayi ta nufa dakinta kanta ta chusa cikin pillow ta fara Kuka me tsananin taba zuciya, sedataci kukanta ta gama sannan ta tashi ta gyara ko ina dan idan ma batai abincin break fast ba su zasu wahala ita da bro dinta dan haka ta sama xuciyarta Salama akan yanzu dole ta dinga girki, wunin ranar aiki taci sosai dan badama Ta zauna se sa'adatu ta jajubo mata aiki........

Bayan kwana biyu ran da dad zai dawo kuma sukaga Akasin Haka, Ranar Tun asuba Hajiya sa'adatu ta Tashi tai duk wani aiki da tasan mijinta zai yaba, Su xeey da abba sukace Allah sarki mamansu, Tace abba yaje yai wanka xeey ma haka ta dakko musu kaya me kyau suka sa tasa musu abinci sukaci sosai kamar ba ita kwanakin biyu baya ba ta chanza musu kai mata akwai makirci wallahi....

"itama taci kwalliyarta tace suzo su zauna dad yau xe dawo, basuce mata komai ba sukazo suka Zauna suma...amma Se kallon juna abba da xeey sukeyi dan kowa nada abun cewa a xuciyarsa......

*TEAM XEEY*
[11/7, 6:55 AM] Ummiey Xeey Abakson💋: *_ ∆°°••~❣_💞••💙💓❤💛
*A DALILIN MATAR*
*UBA*
*_ ∆°°••~~❣_💞••💙💓❤💛

```STORY & WRITTEN BY```
*Ummiey_Xeey Abakson*💋

*♻EXCLUSIVE WRITER'S FORUM​*
[ɦօʍɛ օʄ քɛaċɛ, ɦօռօʊʀ aռɖ sʊքɛʀ աʀɨtɛʀ's]

*LIKES AND DROP AND YOUR COMMENTS*
FB.. #https://www.facebook.com/Exclusive-Writers-Forum-E-W-F-1922297541423276/

*OCTOBER 2017*
_SHORT STORY_

```SADAUKARWA GA____```
*MARIAM TIJJANI ADAM*😍

*°°°•••YAR GATA NAH•••°°°*
💞💞💞
When I See Your Smile.
And Know That,
It Is For Me,
That Is When I Will,
Miss You The Most..
*I MISS YOU MY REAL KHADY*

Chapter Navigation

Use this section to move to any chapter without going back to the top.