Romantic Hausa Novels

A Dalilin Matar Uba Part 1 Complete Hausa Novel

Reading file: A_Dalilin_Matar_Uba_Part_1_Complete_Hausa_Novel.txt

Chapter 29 of 35

*PAGE 93....94*

"Nan ya fadi sume itama XEEY a sume dukansu rikicewa sukai musaddiq ya dauka Isma'il sai mota suma Afrah suka suntumi Xeey sai mota basu wuce ko inaba Se hospital
Da shigarsu asibitin kasancewar duk a rude suke emergency room aka kaisu daki daya, Nan Dr musaddiq ya kirawo abokan aikinsu suka temaka mai Wajen samun kan su Isma'il, Afrah da mummy se kuka sukeyi Dan abun ba karamin tsoratar dasu yai ba, Mummy ne tace" Musaddiq tell us meke faruwane haka? Musaddiq ya kalla mummy cikin tausayi yace" its a long story, ya k'ara da cewa Matsalar Xeey tazo k'arshe, mummy tace" bata ganeba Ko dan uwantane? Kafin musaddiq yace" wani Abu kukan Xeey sukaji ta farfado daga dogon suman da tayi tanata kuka! Nan su Afrah sukayo kanta, suna tambayarta menene sedai kawai tace" Musu Shine, su Afrah sunyi tambayar shine wa? Sedai tai ta kuka, Shikam musaddiq yasan dai akwai Wanda suke soyayya to betaba ganintaba balle yace" itace Xeey din da Isma'il yake magana! Kuma haka zalika me taba ganin memo din a gidansu ba balle yace" wani Abu! Hakanan dai aketa lallashinta se Zuba kuka takeyi
*********************
Bangeren mum Isma'il taga har har kusan dare Isma'il be dawo gida ba hankalinta yadan tashi amma setai tinanin duk yanda akai ko ya raka frnd dinshi wajen tadi ne, Dan haka taci gaba da abun da takeyi amma kwata kwata bawai hankalinta ya kwanta bane, Dan wani faduwar gaba da taji tanayi....!
Su Musaddiq ne zaune a dakin da aka kwantar da su Isma'il, Sunyi shuru kowa da abun da yake sakawa a zuciyarshi, Afrah saboda kuka duk idonta ya kumbura mummy tace" taje gida tai abinci, Dakyar dai Afrah ta tafi gida taje tayo abinci!

Firgigit Isma'il ya tashi, da sauri musaddiq yazo kusa dashi Yana mai ya jiki? Isma'il yace Abokina gamo nayine? ina wannan *Xeey* din da nake baka labari? To wlhi na ganta, ya fara ware ido Dan ganin inda yake! Musaddiq yai smiling yace" Alhamdulillah abokina ba gamo kayi ba, tabbas itace ya nuna mai ita, nan wani rintse idonshi ya k'ara yi, yace" karyane Aljanace, Ya Allah ka tashar dani daga mafarkin da nakeyi! Shidai musaddiq se kwantar mai da hankaki yake cos yagane maganar da Isma'il yakeyi itace Dai Xeey din da yake ba labari! Alluran bacci musaddiq yamai sannan yazo yake sanar wa mummy" tabbas *Shi ne* din da Xeey take ambata Shine Wanda takeso! Xeey itama tanajin haka wani sabon kuka ta fara dakyar musaddiq da mummy suketa mata nasiha akan yanzu addua zatai da kuma ta godewa Allah daya nuna mata wannan ranar!

Seda mummy da musaddiq suka tabbatar da halin da Isma'il yake sannan Tace" musaddiq ya kira mahaifiyar Isma'il ya sanar da ita duk abun da yake faruwa! Aikuwa mum Isma'il tana zaune kan kujera maidiganta ya dawo kenan suna zaune Taji phone dinta yafara ringing, dubuwa tayi taga *One & Only Son* dasauri ta dauka tace" Son ina ka shiga tun dazu nake tsimayinka? Jin wani murya tayi dabana Son dintaba yace" hajiya Musaddiq ne, gabantane ya fadi tace" ina Isma'il din? Yace" ankwantar dashi a asibiti shine na kira na sanar daku! Tace innalillahi wani Asibiti? Ya sanar da ita giwa hospital, kuka hajiya ta fara tace" Alhaji kaga wannan yaron zai kashe kanshi a banza ko? Nace y hakura nace ya hakura yaqi" alhaji naji cikin azama ya tashi ya fita ya tada mota, Hajiyama ta biyoshi se kuka takeyi
Cikin minti kadan suka Isa asibitin, suna Isa musaddiq suka gani yai musu jagora har inda aka kwantar dashi

Suna shiga mum din Isma'il ta fashe da kuka ganin yanda Isma'il ya fita data hayyacinsa! Mman Su Afrah ne tazo ta gaishesu, nan mum Isma'il take tambayar ya Jikin nashi, tace da sauk'i, sun zauna jigon jigon chan Xeey ta farka zatai fitsari nan Maman Isma'il ya maido idonta Dan ganin waye!!!! Xeey tagani, nan itama ta tashi ta rungume Xeey tace"please meke faruwa ku sanar dani Wannan ba Xeey bace? Adai dai lokacin da Afrah ta shugo taga mum Isma'il rungume da Xeey itama me ya faru tace" shi kam musaddiq in banda murmushi ba abun da yake Dan shi kadai ne zai iya bada labarin komai!!!!

Hope kuna enjoying
Ku biyoni

For COMMENT ONLY
+2348164640126

Ummiey Xeey
[1/21, 10:34 PM] ©REAL UMMIEY XEEY: *_ ∆°°••~❣_💞••💙💓❤💛
*A DALILIN MATAR​​​​*
*UBA​​​​*
*_ ∆°°••~❣_💞••💙💓❤💛

```​​​​​​​​​​​​STORY & WRITTEN BY​​​​​​​​​​​​```
*​​​​Ummiey_Xeey Abakson​💋​​​*

*​​​​♻EXCLUSIVE WRITER'S FORUM​​​​*
_[ɦօʍɛ օʄ քɛaċɛ, ɦօռօʊʀ aռɖ sʊքɛʀ աʀɨtɛʀ's]_

*​​LIKES AND DROP YOUR COMMENTs​​*
FB..#https://www.facebook.com/Exclusive-Writers-Fans-E-W-F-1922297541423276/

```​​​​​​​​​SADAUKARWA GA____​​​​​​​​​```
*​​​​MARIAM TIJJANI ADAM​*

```Shout out to all my lovers na birni Dana kauye...naga comments dinku...tnx A lot Allah dai ya bar kauna ```💋

Chapter Navigation

Use this section to move to any chapter without going back to the top.