A Dalilin Matar Uba Part 1 Complete Hausa Novel
Reading file: A_Dalilin_Matar_Uba_Part_1_Complete_Hausa_Novel.txt
Chapter 2 of 35
*PAGE📄29___30*
Nan Hajiya Sa'adatu ta rungumosu Tana cewa yarana duk abun da kukeso zan muku ku daukeni tamkar ni na haifeku...
Alhaji har zuciyarshi yaji dadin wannan maganar Yace bari Na fita Hajiya, Xeey and Abba bye, sukace ok Dad....
"Xeey ce ta tashi duk jikinta ba kwari lallai Tayi missing din mum dinta, da kamar zatai Kuka seta tino mafarkin da da tayi akan cewa Mamanta tace cikinsu kar wanda yai mata kuka, Adduan da suke mata shi takeso dan tana ganin hasken shi, dan haka xeey tayo alwala tazo tai nafila ta zauna ta fara jero addu'oi wa dukkanin al'ummar musulmai da suka rigamu gidan Gaskiya, damu da muke duniyan Allah yasa mui mutuwan shahada ameen.....
"haka rayuwarsu ta kasance cikin jin dadi da walwala yanzu Xeey tana SS3 dan haka ta maida hankalinta sosai kan studies dinta, Abba kuma yana JS2 shima ba laifi akwai kokari,
"yanzu Xeey ta kara wayau da hankali bata cika xuwa gidan su ismail dinta ba sedai su hadu a joint din da suke haduwa kullun, Wata shakuwace ta kara kulluwa tsakanin ismail da Abba..... Yana son yarinyar amma bazai iya aurantaba cos Tafi karfinshi, kuma shi ya dauketa tamkar wanda suka fito ciki daya dan haka duk wani abu dazai bata mata rai yana gudun Shi, Saboda yace indai akan Xeey ne zai iya salwantar da rayuwarshi dan yanzu ya gane abun da yakeji gama da Xeey Ba Soyayya bace tsabagen shakuwa da Tausayinta Yakeji....wannan kenan..
__4months da rasuwar mummyn su komai ya chanza. Halayen Xeey yanzu
Kwata kwata ya sauya kamar ba itaba dan Ta natsu sosai kuma hankalinta Ya koma Kan addini sosai abisa da, Shiga ma Yanzu har kwatance da ita ake dan Hijab har kasa da safa da nikab, She's one in town ko Ina Zancenta akeyi ga ladabi da biyayya Wajen Ta sai yasa mutane da dama suke kiranta *YAR ALBARKA*
*********
akwai wata ranane Weekend su xee suna gida da abba Dad kuma Yaje Dubai suna Zaune a pallow sega hajiya Yalwa Kawar *MATAR UBAn Su* ta shugo suka gaisheta itama ta sama waje ta zauna Zee ta kawo mata drinks Hajiya sa'adatu Kam na gefe tana kallo nan suka gaisa da kawarta suka fara hira dama an kwana biyu ba a haduba...
"hajiya yalwace ta kalla Su xee cike da tsangwama tace kai dallah chan ku tashi bakusan *Matar Uban* ku Tayi bakuwa bane ko haka aka koya muku tarbiya,
"Abba ya tashi sumi sumi dan dama shi ba damuwa yayi ba ya fita yaje wajen abokinsa Suka fara buga Ball.
" Ita kuma Xeey Jin an ambato Ba'akoya muku tarbiya bane yasa ranta yadan baci Tashi tayi itama ta shiga Daki sumi sumi ta fada kan gado tace oh Ya ilahi, wasu mutanan Bakyau wallahi, Innalillahi wa inna ilaihi rahiun ta dingayi dan kar abun ya tsaya mata arai tana hakane har bacci ya kwasheta dama tayi aiki ta Gaji sosai....
__Hajiya Yalwace ta kalle kawarta tace tabdijam Sannu Uwar y'ay'a Ke yanzu hankalinki kwance kenan? Kin wani zauna da yaran miji tamkar ke kika haifesu,
"hajiya sa'adatune ta rufa mata baki tace dan Allah kiyu shuru kar Suji mu shiga daga ciki kinji, Hajiya yalwa ta tashi da wani Lukutin jikinta Tana tafiya kamar Wata 1St lady, Ita kuma sa'adatu na binta a baya har suka Shiga Dakin....
Bakin gado suka Samu suka zauna Hajiya yalwa tace Kinga sa'adatu bangane me kike nufi da yaran nan ba kin wani sasu a gaba tamkar kece uwarsu, ke bakyajin Haushi kigansu reras a gabanki,
"Hajiya sa'adatu tace uhm to ni yanzu ya zanyi dasu,
"Yalwa tai shewa tace ahayye lalle sa'ade ke yanzu ba wani abu da zaki musu kefa Matar Uba ce ba Uwarsau ba, "sa'adatu tace uhm hakane yanzu ya za'ayi, yalwa ta fara magana Tace kinga Tunda Alhajin kikeso gaba daya komai ya dawo hannunki Yanzu abun da zaki dingayi shine Idan bayanan ki dinga gallazamusu azaba idan yadawo kuma Ki nuna kinfi kowa sansu ina mai fada miki tsoro bazai sa su fada mai ba ahaka ahaka har suma A wuce shafinsu,
"Hajiya sa'adatu Tace to amma anya Zan iya kuwa, Yalwa tace meye wani bazaki iyaba kika kashe uwarsu balle su kananan alhaki, So nakefa kema ki shiga gari a dinga ce miki Hajiyan Alhaji... Makkah duk karshen wata,
"sa'adatu tace hahah sai yasa nake sonki fa akwai bani karfin gwiwa, Yalwa tadan harareta tace kima tsaya nan ina fada miki xeey dinnan tana shiga Universty Idon ta budewa zaiyi da kawaye karshe ma may be ba anan Zatai school ba kinga kuwa Da wuya ki iya juyata ko kuma karshe ma Yace ze aurar da ita kinga ba daman aiwatar da abun da nakeso muyi,
Sa'adatu tace eh kuma hakane yar uwa... Yalwa tace kiramun Ita kiga yanda zaki fara.......
``` Kuci gaba da kasancewa Dani```
Xeexee
[11/7, 6:55 AM] Ummiey Xeey Abakson💋: *_ ∆°°••~â£_💞••💙💓â¤ðŸ’›
*A DALILIN MATAR*
*UBA*
*_ ∆°°••~~â£_💞••💙💓â¤ðŸ’›
```STORY & WRITTEN BY```
*Ummiey_Xeey Abakson*💋
*♻EXCLUSIVE WRITER'S FORUM​*
[ɦօÊÉ› Ö…Ê„ Ö„É›aċɛ, ɦօռօʊʀ aռɖ sʊքɛʀ աʀɨtɛʀ's]
*LIKES AND DROP YOUR COMMENTS*
F B.. #https://www.facebook.com/Exclusive-Writers-Forum-E-W-F-1922297541423276/
*OCTOBER 2017*
_SHORT STORY_
```SADAUKARWA GA____```
*MARIAM TIJJANI ADAM*ðŸ˜
_The More I Meet U The More U Appear New.. The More I Know U The More I Want To Love U.. Each Day My Love For U Is My First Love....Bcoz, Each Day I Feel As If I Have Just Started loving U..!_
MISSING YOU MY *EMNOOR AHMERD DON*👄
Chapter Navigation
Use this section to move to any chapter without going back to the top.