Romantic Hausa Novels

A Dalilin Matar Uba Part 1 Complete Hausa Novel

Reading file: A_Dalilin_Matar_Uba_Part_1_Complete_Hausa_Novel.txt

Chapter 4 of 35

*PAGE 📄33___34*

_ Suna Zaune a pallon su ne da yasha gyara ko ina se kamshin turaren Dan maiduguri yakeyi.

"daddy ne ya kira Xeey a waya yace mun sauka fa wani tsalle xeey tayi tace Aunty daddy is back, itama murmushi tayi tace Yeah Dama yace 10AM zasu sauka, malan mukhtar ai sunje dakkowashi, "Abba ma smiling yayi dan atleast Zaiga beloved dad dinshi...

Suna zaune suna kallo sukaji alamun an bude gate, da gudu suka fito dan yiwa dadynso Oyoyoo, ware hannunsu Dad yayi alamun oyoyo suma haka Sukazo se murna sukeyi,

"Hajiya sa'adatu kam bata fitoba tana ta lekensu ta window tace Zakuci ubankune yara.... Lolx..

__tana zaune dad ya shugo wani murmushi ta sakar mai hade da juya ido alamun tayi missing dinshi, Shima dad murmushi ya mayar mata dashi, yazo ya sama waje ya zauna a kujere xeey na hannun dama Abba na hannun hagu, Sake AC akayi dan dad yace ya gaji gashi yunwa yakeyi dan haka ya sakko kasa ya baje yaci abinci sosai, sannan yanata kollon yaranshi Sun dan rame amma yai tinanin ko duk rasuwar mahaifiyarsune dan besan abun dake faruwa ba, Yasa yai shuru:

"bayan yaci abinci suka taba hira sosai sannan ya shiga wanka daganan ya wuce daki dan hutawa, yanajin sanyin Ac bacci ya kwasheshi,

"hajiya sa'adatu bayan mijinta ya shiga daki ta tattara ko ina ta sake Saka wani tilaren tai wanke wanke tadan dora mai Doya dakwai na Anjuma dan best food din alhaji kenan.. Abba da xeey kam se kallon ikon Allah suke suma ba daman magana,

************ bangaren ismail kuwa be zama sosai dan zirga zirga yakeyi sosai yanzu Dan ya kusan barin kasar zai tafi Egypt karatu, Ismail ne yau zaune a daki yau kusan 4days bega xeey ba kuma ko ya kira numbernta Akashe dakko drawing dinnan da yayi ya kalla Yace a Zuciyanshi soon to miss you my baby sister, kawai yaji kwalla na shirin zubomai wata xuciya tace haba Ismail kaida namijine be dace daga tinanin mace ka fara kuka ba dan haka ya dakko wani *memo* guda biyu ya fara rubuta Love words duk abun da ya rubuta a daya seya rubuta a daya duka memon Rubuta iri dayane Sak sedai daya ismail ne daya kuma Xeey

Seda ya gama Tsab ya fesheshi da turare kamar wata mace yace insha Allah se randa zan tafi school zan baki ya bude wani dan karamin kit din da dad dinshi ya siyo mai mekyau, Ya saka dawowa kan gado yayi rub da ciki se tinanin Xee yake xuciyanshi na fadamai indai beganta yau ba akwai matsala.....

___Da daddarene su xeey suna pallow sega wani yaro yace wai ana kiran Xeey inji ismail, Ta tashi ta dakko hijabinta tace yanzu zata dawo,

"sa'adatu kam tana ganin ta fita xuciyarta tai sanyi tace yanzu zan shirya miki makirci dan dama na tsaneki ballema inganki da wannan Ismail din... dakin Alhaji ta shige tana salati tace kazo ka gani da idonka, tun randa ka Tafi xeey kullun seta fita wajen dan iskan ismail dinnan kullun da daddare, Alhaji yaji wani mugun takaici ya fito dan ganema idonshi...

"sukam su ismail Suna waje suna hira dan bakaramin missing din junansu sukeyiba, yaganta da hijab har kasa yace inyee an girma tace wlhi, yace bari na gwadaki a xuciyarshi ya miko hannu alamun su gaisa....kashhhh

"mikowar hannun da zaiyi yayi daidai da fitowar su Alhaji da sa'adatu; Tace kagani ko da idonka inji sa'adatu, wani wawan mari alhaji ya sakar wa xeey yace ta wuce gida, Ya juya kan ismail din yana ta mai maganu marasa dadi dai

Harga Allah ismail yasan ba haka yake nufi ba, sedai kawai yacewa Daddy yayi hakuri bazai sake kula taba, Su kai gida shima yayi gida yaje daki be fadawa kowa ba kuka yayi sosai sannan yai xuciya yace bazai kara kula xeey ba...

Shin kuna ganin HAKAN ZAIYUWA?? For comment Only

+2348164640126

Ita kam xeey tun da suka dawo gida daddy se fada yake mata, Abba kam yanzu ya tsinke da al'amurar matar uban su, dan duk wani makirci tsab zata iyashi yanzu ma karyanta kawai ta je ta hada, dan ya tabbata abun da sa'adatu ta fada ba gaskiyane bane,

"Daddy se fada yake mata tayi kuka sosai, Ita ba kukan marin takeyi ba a a kukan yaushe sa'adatu zata dena musu karyane? Hakanan tai kuka ma'ishinta sannan daddy ya cigaba da lallashinta kuma akan karta sake kula ismail irin sune masu Hurewa yan mata kunne sedai su gama lalata musu rayuwa,

"xeey tace daddy wallahi Ba haka Bane ni nasan waye ismail, Daddy ne ya katse ta da magana Yace Ki rufemun baki be kamata ina magana ba kinayi

"sa'adatu ta sundumo baki tace kagani ba ai ya riga ya gama hure mata kunne duk bazataji maganar muba, ta Dada da cewa Alhaji ga shawara mubar wannan ung dan Kar aje A bata mana suna, Dan yanda naga yana magana kamar muna fiki Allah dai ya tsare be gama bata......

Bata karasheba Alhaji ya katseta yace ki dakata Hajiya... Nan tai shuru,

abba saboda takaici barin pallon yayi ya shiga daki dan shima be yarda xee xata aikawat wani mugun aiki ba,

Bayan dady ya gama mata fadane xeey ta shiga daki.....

*XEEY XEEY CEH*
[11/7, 6:55 AM] Ummiey Xeey Abakson💋: *_ ∆°°••~❣_💞••💙💓❤💛
*A DALILIN MATAR*
*UBA*
*_ ∆°°••~~❣_💞••💙💓❤💛

```STORY & WRITTEN BY```
*Ummiey_Xeey Abakson*💋

*♻EXCLUSIVE WRITER'S FORUM​*
[ɦօʍɛ օʄ քɛaċɛ, ɦօռօʊʀ aռɖ sʊքɛʀ աʀɨtɛʀ's]

*LIKES AND DROP YOUR COMMENTS*
FB.. #https://www.facebook.com/Exclusive-Writers-Forum-E-W-F-1922297541423276/

*OCTOBER 2017*
_SHORT STORY_

```SADAUKARWA GA____```
*MARIAM TIJJANI ADAM*😍

Dedicated to my twin.... *FATY AXLAND😍 rabbi ya kara daukaka da group dinku na REAL PURE MOMENT OF LIFE WRITER'S...❤* _I CARES IRIN SOSAI DINNAN_

Chapter Navigation

Use this section to move to any chapter without going back to the top.