A Dalilin Matar Uba Part 1 Complete Hausa Novel
Reading file: A_Dalilin_Matar_Uba_Part_1_Complete_Hausa_Novel.txt
Chapter 31 of 35
*PAGE 97....98*
baban Su musaddiq yace" ubanta ai nanan ko? Akace Eh nan suka mik'e zasu tafi gidan Su baban Xeey, dukansu sun fita Se Xeey da Isma'il wani kallo yai mata da ita kanta tasan she's missed him, Yana mata kallon shima ya fita itama tabiyo bayanshi!
Mota suka hau suna tafe Afrah se Jan Xeey da hira take wai she's lucky gaskiya! Musaddiq yace ki tsaya wasa yarinya kema karki fito da miji, Isma'il kam shuru yayi se kallon Xeey yaketayi ta mirror, ita ko Xeey in banda fargaba da tsoron fitinar matar ubanta da zasuje ta tadda ba abun da takeyi...minti kadan suka karasa gidan tofaa!
Saukowa sukayi su mazan suka tsaya a waje Matan suka shiga mezai faru! Hajiya Sa'adatu tana ganin Mariam Tijjani gabanta yai mugun fadi, batama lura dq Xeey ba tace was Maryam" oh yau kinmun gayyane to ku fitar mun a gida maza maza, sudai mu mummyn Afrah kallonta suka tsaya sunayi sukace ba shakka wannan muguwar *matar ubace* Mariam tace" matsalarki, hajiya Sa'adatu tace" matsalar ku dai chan tunda Xeey ba dawowa zatai ba ta mutu!!! Maman Su Afrah ne tai dariya tace lalle kuwa kudirinki yau ya karye ga Xeey nan bata mutuba da ranta! Kallon Xeey tayi tsab tabbas itace wani mugun faduwar gaba taji, Alhaji baban Xeey, Yana daki yanajin an ambato Xeey wuf ya fito, Xeey na ganin babanta da gudu taje ta rungumeshi sai kuka, jin gidan ya kaure ne da maganganu da koke koke mazan suka suka shugo, hajiya Sa'adatu taga yau karyarta ya kare a Fasa kuka ba Wanda ya saurareta, Maman Isma'il binta da kallo tayi tace" makira!!!
Nan Baban Isma'il yace" Alhaji ba zamu mukazoyi ba, kamar daga sama Alhaji yaji ya dawo dai dai bisa adduo'in da yasha, baban Isma'il yace" tabbas mun DDE da nemanka da inda kake, nan dai suka bashi labarin from A to Z na wahalar da Xeey tayi *a Dalilin matar uba* nan baban Xeey yaci kuka yace ba da saninshi bane, har suna hada baki sukace tabbas munsani sai yasa mukai maka uziri! Yqnzu munzo maganar auran Isma'il ne da Xeey mun yanke komai in kuma kanada magana ne kayi
Nan baban Xeey yace" ai sungama mai komai, hajiya Sa'adatu tanajin labarin Xeey zatai aure nan fa fara wasu kururuwa tana Fasa kayan dakinta, sukai banza da ita Ashe dai Hajiya Sa'adatu ta hau kace ne. Kaikayi ya koma kan mashekiya kenan Alhamdulillah!
Bban Xeey yace gaba da musu godiya sukace bakomai" yace" abarmai Xeey, Sukace a'a zasu tafi da ita Dan bazasu bari wannan matar ta sake ma Xeey lahani ba Dan haka sukace an tsayar da biki nan da Wata uku, yayi murna sosai sunfito shima ya futo wajen neman Yar uwanshi.....suna fitowa sega Sa'adatu ta rugu da gudu waje ta tara bola se tsalle takeyi, kowa sedai ya kyalleta yace" Allah ya kyauta Dan kana ganinta kasan mugun abun da tai ya koma mata
Dan haka suka tafi da XEEY shima yabar mata gidan har abada yaje nemen yan uwanshi da basu labarin nan me dadi!
Tun a wajen kowa yai sallama dan no need su koma gidan su Afrah! Maman Isma'il da babanshi suna tafe suna hiransu, Mariam ma haka, baban su musaddiq shima tare da matarshi, se Musaddiq da yake driving dinsu Afrah, Zeey da Isma'il suna tafe suna hira basu tsya ko inaba se gidan su musaddiq nan kowa ya huta
*BAYAN SATI DAYA* hankalin kowa. Kwance matsalar dake damun kowa Allah y kawo karshenshi, itama yanzu Afrah Ta sama wani lecturer Abdulrasheed Yana sonta dan aure sai yasa duka aka tsayar da bikinsu rana daya! Kowa abun yamai dadi Matuka!
Akwai wata ranane Isma'il yazo gidansu musaddiq suna zaune musaddiq yace" abokina bari inzo mu tafi ko? Isma'il yace" ina kenan fa? Musaddiq yace" wajen Fatima mana! Isma'il yai dariya harda rik'e ciki yace" tab yau soyayya zansha da baby Xeey kullun nazo tare muke hira all yau nida itane! Musaddiq yace" ohhh nikam kaga tafiyata, Yana fitowa yaga Afrah da saurayinta lecturer Abdulrasheedl! Shidai yai gaba Isma'il ya shiga har falon Su Xeey ya kirata!!!!!!!!!
Kuci gaba da biyoni
Ummiey Xeey Ce
[1/21, 10:34 PM] ©REAL UMMIEY XEEY: *_ ∆°°••~❣_💞••💙💓❤💛
*A DALILIN MATAR*
*UBA*
*_ ∆°°••~❣_💞••💙💓❤💛
```STORY & WRITTEN BY```
*Ummiey_Xeey Abakson💋*
*♻EXCLUSIVE WRITER'S FORUM*
_[ɦօʍɛ օʄ քɛaċɛ, ɦօռօʊʀ aռɖ sʊքɛʀ աʀɨtɛʀ's]_
*LIKES AND DROP YOUR COMMENTs*
FB..#https://www.facebook.com/Exclusive-Writers-Fans-E-W-F-1922297541423276/
```SADAUKARWA GA____```
*MARIAM TIJJANI ADAM*
*101...102*
Gabanshine yai mugun fadi, yaji duk bazai ma iya zuwa office din ba nan ya fada gado!!!
Shuru Shuru musaddiq yaga Isma'il bezo office ba Dan haka ya dauka wayarshi ya kira! Har ya gama ringing ba'a daukaba, ya sake kira chan Isma'il ya dauka muryanshi har wani shakewa yakeyi, Musaddiq yace" Isma'il what's wrong? Isma'il saboda bugun kirji ya kasa cewa komai! Musaddiq ya sake tambayarshi, shuru jin shurun da yayine yace" a office dinsu yna zuwa! Ko 20 mins ba ai ba Sega musaddiq gidansu Isma'il, direct dakinshi ya wuce ya sameshi kan gado se nishi yakeyi! Musaddiq ne ya tallabo Isma'il Yana tambayarshi meya faru! Isma'il yace" aboki shine zaka cuce rayuta Ashe Xeey da wqnda takeso zata aura! Musaddiq yace" bangane ba kamar ya akwai Wanda Xeey takeso, to inma akwai ni bansaniba gaskiya! Isma'il ya nunawa musaddiq text din da Xeey tai ma, zare ido shima yayi yace what Wlhi bansaniba!
Nan take musaddiq ya kira Zeey yace" suzo su sameshi gidan su Isma'il, shida Afrah Xeeyy tace" okay nan suka sanar da Mummy tace sai sun dawo amma karsu Dade! Suna fitowa suka sama me adaidata har kofar gidan su Isma'il ya saukesu! Suna shiga basuga kowa a pallow dinbba Dan haka direct dakin Isma'il suka wuce! Suna shiga sukaga Isma'il na numfashi sama sama kuka Xeey ta fara tace please Sweethrt karka mutu!
Bane! Wani tsawa ya daka mata _this is the first time da musaddiq ya taba mata tsawa ko fada kenan_ Dan yaka tai shuru! Musaddiq wurgo mata wayan Isma'il yayi yace" read waye yai wannan reply din? Ashe da Wanda kikeso ko? Very good! Tana karantawa wani hawaye masu zafi suka zubo mata tace" I'm Sorry wallahi bansan shi bane! Kuma ni banda kowa sai shi, banda number dinshine please ka yafemun Isma'il! Musaddiq yai zuru zuru yace" tabbas na tina, kuma ni ma nayi saurin hassala kema kiyi hakuru! Afrah tace" Allah sarki sorry Xeey bro musaddiq be sani bne wallahi, Isma'il daya dago kai Yana kallon Xeey datai tsugunne a gabansu yace" Xeey kiyi hakuri duk laifinane da banjira kin bni number dakankiba, kuma danai miki text ban sanar dake kowaye ba kiyi hakuri kinji!
Xeey ta share hawayenta tace" bakomai nagode sosai! Musaddiq yace" to kuma maganar an barta anan kenan ba sai kowa yajiba sukace insha Allah, nan Isma'il ya sake shiryawa kamar ba shiba maganarshi ta dawo normal heart beat din shi ya ragu suka mike sukai waje nan musaddiq yai driving suka sauke su Xeey da Afrah su kuma suka wuce wajen aikinsu
••••••••••••••
Alhaji Abdullahi (baban Xeey) tun ranar yaje wajen yan uwanshi sunyi murna sosai, da suga ganshi kuma sukaimai murnar rabuwa da wannan matsiyaciyar mata, suka tambayeshi INA XEEY din yace tananan Gidan da aka riketa suke Neman mata magani har ta warke yanzu haka ma ansa bikinta, masha Allah sukace game da sakawa marik'anta da alheri, tabbas sunyi namijin kokari suma Allah ya kara tsare yaransu Alhaji yace Ameen....Suka kara da cewa ya kamata muje mu ganta ko? Alhaji yace insha Allah, nan ya koma kusa da yan uwanshi yasai gida aka gyaramai, kasancewar shekaru sunja mai nan yasama wata mata takai 35 bata bata aureba ga ibada ya aureta.....wannan kenan
*Hajiya Sa'adatu kuwa*
Duniya ta dauka, muguntar da tayi wa xeey ya koma kanta, ko daga ina zuwa ake ana kallonta, harda aminiyarta hajiya yalwa, koda hanya ya biyo da ita sedai ta kalleta ta girgiza kai tace" muma ya Allah ka yafe mana tabbasa karshen mutun kenan mugu me asiri indai be gyara halinsaba to komun Daren dad'ewa abun zai dawo kanshi! Yanzu abun hajiya Sa'adatu ya kara yawa idan taga mutun tai ta binshi da gudu idan kuma shago ne ko wani Abu me amfani tai ta fasawa ko ta dauka dutse tai ta jifa, a unguwar ganin illan da takewa mutane yasa Aka dauketa aka kaita gidan mahaukata a kulle ta achan zata kare rayuwarta kenan, labarin Sa'adatu ya kare!!!! Allah ya kyauta yasa mui kyakkyawan k'arshe
Ummiey Xeey
[1/21, 10:34 PM] ©REAL UMMIEY XEEY: *_ ∆°°••~❣_💞••💙💓❤💛
*A DALILIN MATAR*
*UBA*
*_ ∆°°••~❣_💞••💙💓❤💛
```STORY & WRITTEN BY```
*Ummiey_Xeey Abakson💋*
*♻EXCLUSIVE WRITER'S FORUM*
_[ɦօʍɛ օʄ քɛaċɛ, ɦօռօʊʀ aռɖ sʊքɛʀ աʀɨtɛʀ's]_
*LIKES AND DROP YOUR COMMENTs*
FB..#https://www.facebook.com/Exclusive-Writers-Fans-E-W-F-1922297541423276/
```SADAUKARWA GA____```
*MARIAM TIJJANI ADAM*
Dedicated to *♡R̥ͦE̥ͦḀͦL̥ͦ M̥ͦE̥ͦ D̥ͦḀͦM̥ͦB̥ͦU̥ͦ C̥ͦE̥ͦ🥗* tnx for the love # ana tare
Chapter Navigation
Use this section to move to any chapter without going back to the top.