Romantic Hausa Novels

A Dalilin Matar Uba Part 1 Complete Hausa Novel

Reading file: A_Dalilin_Matar_Uba_Part_1_Complete_Hausa_Novel.txt

Chapter 12 of 35

*PAGE📄 59__60*

"Wani tsohu suka gani yana musu smiling, yace kar Ku tsorata, nima mutun ne kamar Ku, Amma Allah yamun baiwa in bazaku damuba kufito a motar, dukansu ba Wanda yaji tsoro suka fito a motar...

Gefen titi suka samu suka tsaya sannan tsohun nan yace " Kudena wahalar da kanku zuwa asibiti, wannan aikin bana asibiti bane, Asiri akai mata, So abun da nakeso daku shine, kuci gaba da turara mata habbatus saudah, Sannan suka Ku dinga yawan sadaka, yana yaye masifa da komai,

"Mummy CE tace insha Allah baba zamu ci gaba, mungode, tsohon nan " yace basai kun godemun ba, kuma Ku sama ruwan zamzam Ku bada ai mata rukiyya kullun kafin da asuba Ku dinga bata tanasha, kuma ki sama ruwa shima ki dinga karanta mata fatiha 1, ayatul kursiy 3, ahad 3, falagi3 da nasi 3, Sannan kiyi wannan adduan La'ila ha illallah, wahdahu lashari kalah, lahul mulku wa lahul hamd, wa huwa ala kulli shai in kadir 100* kullun safe da bayan sallan la'asar, kibata tanasha, insha Allah zata sama sauk'i,

Yayan Afrah yace" Masha Allah muna godiya malan, "tsohon yace karka damu, Ikon Allah ne yasa har muka hadu, zan temaka muku, nan sukaji dadi Mara misiltuwa a zuciyoyinsu sannan sukai mai Sallama, " yai musu Allah kiyaye hanya da fatan alheri...

Bayan sun kama hanyanyane, mum tai dialing number Dad take sanar dashi yanda sukai da wannan tsohon,
"Dad yace masha Allah, Allah ya temakemu, ya bamu sa'a, mum tace" Ameen

Sundawo gida duk sun gaji yayan Afrah ya kwanta bacci yai mafarkin xeey Wai gatanan ta fara magana, yaganta cikin jin dadi da walwala, firgigit ya tashi yaje wajen mummy yake sanar da ita, Tace Masha Allah, zamu sama nasara, yace insha Allah, Sannan Ya shiga wanka yasa kayan sport, ya nufa M² dake Kaduna yaje ya jijjiga jini

Bangaren Afrah kufa, itama a wannan yan k'wanakin tana yawan mafarkin Xeey, sedai ta ganta tana mata smiling, ko yanayi najin dadi Dan haka itama Afrah ta dage da addua sosai, Dan ba k'aramin tausayawa xeey takeyiba, ji take tamkar twins sis dinta ta jini,
********
Mummy kam itama adduan da wannan tsohon ya bata kullun setawa xeey koda na lokaci daya bata taba tsallakewa ba,

_akwana a tashi ba wuya yau kusan 3months kenan kullun se Ismail yayi mafarkin xeey amma seya batsar, gani yake kamar Dan yasata a zuciyarshi ce shaidan kemai yawo da hankali, yauma koda ya kwanta bacci ganinshi yayi tare da xeey a wani garden me kyau flowers sunyi Kore shar, suna zaune suna hiran masoya,

Wani flower ta dakko, ta mika mai tare da fadin _I Love you my Sweet special_

Farkawa yayi firgigit a tsorace yana fadin it's a lie, it's a lie _(Karyane, karyane)_

Wani frnd dinshi ne ya shugo yaga halin da yake ciki, Kamashi yayi ya fara karantomai ayatul kusiyu sannan ya samo yai bacci, frnd din tagomi yayi Dan duk yanda akai Ismail ba karamin cikin tashin hankali yake ba,

Ismail nata bacci, se kusan 4 na yamma ya farka, kasancewar yau Sunday, "yana farkawa, kallon friend dinshi yayi me Suna *Fahad*

Ismail ne yace "INA Xeey, INA xeey Dan Allah INA ka boyemun Xeey, ka temaka naganta kar na mutu,

*Fahad* kam sokoko yayi Dan tun da yafara maganar ido ya sakamai

Ismail ne ya k'ara da cewa Fahad Dan Allah INA Xeey??

"Fahad yace xeey kai mafarki hala? Ismail yace banganeba mafarki fa kace?

Fahad yace yes mafarki nake tinani kayi Dan ihunka naji, nima na shugo, Ismail ne yai narai narai da ido yace hmmm Ba mamaki amma Dan Allah ka tayani Neman xeey

"Fahad yace OK, amma zan kira su mummy na sanar dasu duk halin da kake ciki gaskiya

Ismail ne yace Huh ka rufamun asiri kar na bawata su mummy rai na musu alkawari bazan sake maganar xeey ba, Fahad yace" atoh wallahi ni har mamaki kake bani kan mace daya? Akwai abun Da zakai mata da wuce addua yanzu a halin da take ciki? Allah kadai ma yasan ko tana Raye kota mutu

"Ismail ne yadan bata rai Dan beji dadin maganar abokinshi ba amma hakanan ya daure yace uhm Hakane,
Amma Ina mai tabbatar maka da Xeey na Raye Dan kullun senayi mafarkinta

Fahad yace mutumina tabbas ka fada kogin soyayya ba abun da zance se Allah ya bayyana xeey musha biki, idan kuma ta kada ka ta zaba wani shikkenan sedai mu tayaka jaje _Fahad maganar yake amma cikin zolaya_

Ismail yace ba fariyaba nasan.....

*Ku Biyoni*

*Ummiey XEEY*
[1/3, 8:30 AM] UⓂmiey Xeey👄: *_ ∆°°••~❣_💞••💙💓❤💛
*A DALILIN MATAR​​​*
*UBA​​​*
*_ ∆°°••~~❣_💞••💙💓❤💛

```​​​​​​​​​STORY & WRITTEN BY​​​​​​​​​```
*​​​Ummiey_Xeey Abakson​💋​​*

*​​​♻EXCLUSIVE WRITER'S FORUM​​​*
[ɦօʍɛ օʄ քɛaċɛ, ɦօռօʊʀ aռɖ sʊքɛʀ աʀɨtɛʀ's]

*​LIKES AND DROP YOUR COMMENTs​*
FB..#https://www.facebook.com/Exclusive-Writers-Fans-E-W-F-1922297541423276/

​​​​​​​​​SADAUKARWA GA____​​​​​​​​​
*​​​MARIAM TIJJANI ADAM​😍​​*

_​KUYI HAKURI INA MAKU TYPING BA YAWA, AIKINE YAYI YAWA A OFFICE...LOVE YOU ALL MY FANS​_

Chapter Navigation

Use this section to move to any chapter without going back to the top.