A Dalilin Matar Uba Part 1 Complete Hausa Novel
Reading file: A_Dalilin_Matar_Uba_Part_1_Complete_Hausa_Novel.txt
Chapter 14 of 35
*PAGE 63__64*
Kuka Xeey take yi mai ratsa zuciya, mummy ce ta rungume ta tana shafa bayanta ta sigar lallashi har aka samu tayi shiru tana ta sauke nannauyar ajiyar zuciya sannan daddy yace" ki daure ki sanar damu wacece ke?
kokarin tattara nutsuwar ta waje daya tayi sannan ta kwashe labarinta tun daga farko har karshe mummy ce ke zubda kwalla sannan ta sanar da Xeey a halin da suka tsince ta da kuma bata labarin Afrah ta fada mata itace silar zamanta a gidan nan sannan tace ki kwantar da hankalin ki Xeey kici gaba da addu,a komi yayi zafi maganin sa Allah kuma nayi miki alqawari insha Allah Indai Kina tare dani ba zaki yi kukan Maraici ba, kuka Xeey taci gaba dayi tare da kuma rungume mummy.
*********************
Mariam ce zaune a pallow ta rasa meke mata dadi firgigit ta mike tace wai meke faruwa ne yaushe rabon dana je na naga lafiyar niece dita *Xeey*anya banci amanar zumunci ba nayi wa kaina adalci kuwa hawaye masu zafi ne ke bin kuncinta tashi tayi ta dauki wayarta ta latsa number mijinta ringing daya aka dauka ta bayyana masa zata ganin *Xeey* amsa mata yayi da ta gaida mata su, da isar ta gidan horn daya tayi gate man ya bude mata ta shiga parking tayi tare da knocking kofar pallow hajiya Sa,adatu ce ta bude mata tare da watsa mata kallon wulaqanci meya kawo ki gida na ina ce babu komai naki a gidan nan *Xeey* ce kike takama da ita ko kuma ta dade da tafiya yawon duniyar ta don haka bani da lokacin ki juyowar da Sa,adatu zata yi
*Mariam* ta wanke mata fuskanta da Mari ta hagu ta dama wanda saida taga wuta, kuma ta kara da cewa" shegiya kin kashe min yar uwa sannan kice bakisan inda yata take ba wallahi ba zaiyu ba duk inda take ki fito min da ita kafin 24hours fuuuuuuuu taja motar ta tabar gidan
Hajiya Sa,adatu kam tsaye tayi r'ike da kunci tana ajiyar zuciya zabura tayi ta dauki waya ta kira yalwa cikin minti 10 sai ga yalwa ta iso labarin duk abinda ya wakana da tsakanin ta da Mariam tayi jinjina kai yalwa tayi tare da kyabe baki tace babban magana...!
Sa'datu tace" dan Allah ki temakeni, Yalwa tace" kinsan bakya gayawa Alhaji wannan magana ba Kinsan sharadin boka ne wannan don dakin fadi abinda ya shafi waccan matacciyar zance zaisha bambam ayi babu ke hakuri zaki yi, tunda yanzu da zance Ki kawo wata dubu Dari saiki ce baki da Ita da kinga aiki da cikawa.
Da fitar *Mariam*bata tsaya a ko ina ba sai gidansu daddyn Xeey (mahaifitar babban xeey) Sallama tayi da fara,a hajiyar ta tarbe ta tare da bata juice da ruwa mai sanyi gaisawa suka yi sannan Mariam ta sanar mata da abinda ya faru tsakanin ta da hajiya Sa,adatu shiyasa tazo neman Xeey ko tana nan kuka hajiyar ta saki tana fadin *innalillahi wa,inna ilaihirraji,un*wallahi na manta da wata Xeey *A DALILIN MATAR UBA*yanzu an rusa mata rayuwa ni rabon dana sa daddyn nata a idona harna manta saboda yafi shekara daya dana sashi a ido kuma duk wata hidima da kika san yana yimin Sa,adatu ta hana shi kannansa ma da suka je gaida shi cewa yayi bai sansu ba yanzu muje muyi ta addu,a duk inda *Xeey*take Allah ya bayyana mana ita yau na sake shiga wani tashin hankalin ni khadija.
*************************
Daddy ne zaune a Office sai juya biro yake ya rasa meke yi masa dadi ya tafi tunani amma ya rasa wai meye ke faruwa dashi??? Wunin ranar bai iya tabuka wani abun kirki ba gida ya dawo Sa,adatu ta tarbe shi cikin kissa daga mata hannu yayi alamar ta dakata saroro tayi dakinsa ya shige tare da murza key zaga dakin ya rinka yi ba tare da ya sami solution ba
***********************
*xeey*ce kwance a pallow tana kallon TV amma zuciyarta ba nan take Kallo ba tana can wajen tunanin daddyn ta Aunty mariam da isma,il dinta Wanda hawaye ke biyo kuncinta wanda bata san yana zubowa ba Maganar da kisa sunan yayan Afrah haba my beloved sister meke faruwa ba zaki karbi nasihar da Mum ta miki ba hadiye kukanta tayi tare da cewa yaya bawai ban amsa nisihar bane wallahi wani Abu nake tinawa sai yasa
Yayan Afrah yaj itausayinta sosai yace........
Ummiey XEEY
[1/3, 8:30 AM] UⓂmiey Xeey👄: *_ ∆°°••~❣_💞••💙💓❤💛
*A DALILIN MATAR*
*UBA*
*_ ∆°°••~~❣_💞••💙💓❤💛
```STORY & WRITTEN BY```
*Ummiey_Xeey Abakson💋*
*♻EXCLUSIVE WRITER'S FORUM*
_[ɦօʍɛ օʄ քɛaċɛ, ɦօռօʊʀ aռɖ sʊքɛʀ աʀɨtɛʀ's]_
*LIKES AND DROP YOUR COMMENTs*
FB..#https://www.facebook.com/Exclusive-Writers-Fans-E-W-F-1922297541423276/
```SADAUKARWA GA____```
*MARIAM TIJJANI ADAM😍*
_Dedicated to my dear sweet heart, Khady fresh💞..thanks for your love and support_
Chapter Navigation
Use this section to move to any chapter without going back to the top.