Romantic Hausa Novels

A Dalilin Matar Uba Part 1 Complete Hausa Novel

Reading file: A_Dalilin_Matar_Uba_Part_1_Complete_Hausa_Novel.txt

Chapter 27 of 35

*PAGE 91__92*

*WASHE GARI*
musaddiq ne ya fito daga wanka ya dauka phone dinshi ya kira Isma'il yace gashinan Zuwa! Isma'il yace okay.
Ba'ai minti talatin ba Sega musaddiq Yana shugowa mummy yaci karo da ita ya gaisheta tace" yasu hajiya da sauran yan uwanshi? Yace" sunanan Lafiya Alhamdulillah, sannan ya wuce dakin abokinshi, ya sameshi shima yayi wanka Alhamdulillah jiki yayi kyau sedai ya rame sosai, musaddiq yace" haba friend kaga yanda ka koma kuwa? Wai meke damunka? Kullun sedai kace kanka na ciwo? Ai ko ciwon kan akwai abun dake janyoshi kamar ba doctor ba ka bari ciwo zai maka illa?

Isma'il smiling kawai yayi yace" abokina time yayi da zan sanar dakai koma menene amma yanzu muje gidan su Fatima mu dawo! Musaddiq yace" anqi wayon kaga just tell me koma menene I promise you zan temakeka! Isma'il yace" Aure nakeso gashi banda wanda zan aura! Musaddiq yace' banganeba

Isma'il yace" yap Wanda nakeso batanan! Musaddiq yace karka damu, indai wannan ne cikin sisters dina ka zaba daya indai kanaso! Isma'il yace huh kace su 2 ne ni kuma daya nake gani kullun, musaddiq yace" dayar ma tananan zaka ganta, yace okay _isma'il karya yai mai just karya tsanant bincikene ya akai yaga memo din gidansu yaji labarin Xeey ta mutu ko sun tsinta sai yasa yai shuru........_) Isma'il ne yace" okay mu tafi ko? Musaddiq yace yap nan suka tashi suka nufo gidan su Fatima budurwan Musaddiq, an tarbesu tarba na azo a gani nan iyayan fatima sukace indai da gaskene su turo Dan yanzu haka aiki takeyi ta Gama service, sukace insha Allah za'a turi.... Ikon Allah cikin kankanin lokaci har soyayya me karfi ta kullu tskanin fatima da musaddiq
"Musaddiq na dawowa gida ya sanar da iyayanshi, sukace Alhamdulillah, akasa ranar Daza'aje kai kayan sa rana! Musaddiq hankakinshi a kwance amma daya tino halin da abokinshi yake duk sai yaji wani wani

*Bayan kwana bakwai*
An ansa Bikin fatima da musaddiq *Wata UKU* Isma'il yayi kuka sosai na rashin masoyiyarshi Xeey, Har ya hakura! Ikon Allah kenan inji Isma'il yace" a mind dinshi ba ddewarku da mutun bane aure sega wani daga baya tazo ya aureka, gadai musaddiq nan tun da suke bai taba jin yayi labarin budurwa ba se gashi cikin lokaci kadan komai y kankama, Allah sarki isma'il..Musaddiq yanzu da Fatima kuma kullun cikin waya Suke sun bala'in shakuwa sosai!!!!!

*Bari mu leka wajensu Hajiya'a Sa'adatu*
Tana Zaune tayi tagumi duk abun duniya ya isheta, Alhaji kuma kamar a mafarki yaji ya tashi! Kallon cikin gidan yyi ko ina duk datti, tsawa ya daka mata yace" ubanwa kika barma gida haka? Jikinta na rawa Dan yanzu tasan karyanta ya kare, tsinstiya ta dakko ta fara share ko ina, kallonta yayi yace" ina yarinyata Xeey??? Ina kika kaita? Gabantane yai mummunar fadi! Tace" uhm uhm Allah yai mata rasuwa yace" What? Cikin karfin hali da makirci irin na mata tace'' Alhaji kashafa jinya ne kusan shakaru nawa? Wani harara ya sake mata yace" innalillahi wa inna ilaihi rajiun! Sannan yai shuru duk abun duniya ya isheshi, sannan ya k'ara da cewa" yan uwanafa? Tace ai duk kwanciyarka Jinya ba Wanda yke zuwa! Yace" da gaske? Tace kwarai kuwa! Yace" Allah yai miki Albarka! Makirar mata karya tamai amma ita ko ajikinta....tundaga wannan lokacin Alhaji be sake tambayar ko waba duk da a zuciyarshi Yana tinaninsu har kukan Zuciya yakeyi....wannan Kenan!!!!
BAYAN KWANA BIYU
Isma'il ya fara zuwa aiki jiki yayi kyau, ranar suna zaune da musaddiq ya kalla Isma'il yace wow kaga yanda kayi kyau? Kamar kaine zaka angonce!

Isma'il yace haha kaidai kai kyau angon fatima, musaddiq yace" lolx Allah dai ya kaimu yace" Ameen suna zaune ma sega fatima ta kira nan Isma'il ya amsa wayar ya na mata tsiya yace daga kwanciya ciwo se Kamuwa da Soyayya" Fatima" tace uhm Kaidai ka Sani!"

Bayan sun gama wayar ne Musaddiq yake ma Isma'il tsiyan yaushe rabon da gidansu tun kafin ya fara ciwo! Isma'il yace wlhi kamar ka shiga raina yau nakeson Zuwa dama zance mu tafi da wuri Dan gidanku zanyi dinner! Musaddiq yace haba Aboki ko kaifa! Tun wuri suka tashi suka biya ta gidan su fatima suka gaisa sannan suka wuce gidan su musaddiq, Isma'il na shiga yaji gabanshi yayi mugun fadi! Ya dake! Suka shiga ya gaishe da mummy, Ta amsa ta kara da cewa ya yaji da jikin yace" Alhamdulillah, Kwalla musu kira tayi tace" ina kuke kuzo ga abokin yayanku sannan ku taho mai da drinks! Afrah ta zumbura baki tace ba abun da zan dakko dan hka Xeey tana fitowa kitchen ta wuce ta dakko drinks, yayin da ita kuma afrah already tazo falon ta gaisheshi ta zauna! Suna Zaune gaba dayansu Sega Xeey rik'e da wani plate ta daura Apple juice da cake da ruwa! Itama tana dosowa taji gabanta na fadi Dan haka ta sunkuyar dakai a tinanina kallonta akeyi! Zuwan gabanshi da zatai ta ajiye kenan suka hada ido da Isma'il zare ido tayi shima ya mike yace" Xeey!! Nan ya fadi sume itama XEEY a sume dukansu rikicewa sukai musaddiq ya dauka Isma'il sai mota suma Afrah suka suntumi Xeey sai mota basu wuce ko inaba Se hospital

Kuci gaba da biyoni...

Ummiey Xeey ce
[1/21, 10:34 PM] ©REAL UMMIEY XEEY: *_ ∆°°••~❣_💞••💙💓❤💛
*A DALILIN MATAR​​​​*
*UBA​​​​*
*_ ∆°°••~❣_💞••💙💓❤💛

```​​​​​​​​​​​​STORY & WRITTEN BY​​​​​​​​​​​​```
*​​​​Ummiey_Xeey Abakson​💋​​​*

*​​​​♻EXCLUSIVE WRITER'S FORUM​​​​*
_[ɦօʍɛ օʄ քɛaċɛ, ɦօռօʊʀ aռɖ sʊքɛʀ աʀɨtɛʀ's]_

*​​LIKES AND DROP YOUR COMMENTs​​*
FB..#https://www.facebook.com/Exclusive-Writers-Fans-E-W-F-1922297541423276/

```​​​​​​​​​SADAUKARWA GA____​​​​​​​​​```
*​​​​MARIAM TIJJANI ADAM​*
```Wannan shafin nakune masoyan Littafin, Ummi XEEY na gaisheku tare da fatan alheri a gareku```❣❣

Chapter Navigation

Use this section to move to any chapter without going back to the top.