Romantic Hausa Novels

A Dalilin Matar Uba Part 1 Complete Hausa Novel

Reading file: A_Dalilin_Matar_Uba_Part_1_Complete_Hausa_Novel.txt

Chapter 32 of 35

*PAGE 99...100*

Isma'il ya shiga har falon su Xeey ya kirata! Wani sanyi a zuciyarta taji Dan yaushe rabon da ta tsaya gata ga Isma'il suyi hira, Dan haka hijab dinta ta dakko tadan fesa tirare bame karfi ba tasa lipstick a labenta ta fito cikin compound din gidan! Tana waige waige ta INA zataga Isma'il, jin muryanshi taji cikin natsuwa yace" Sweetlove I'm here, kallonshi tayi tana murmushi ta karasa inda yake!
Kujeru ne guda biyu awajen suka zauna suna fuskantar juna! Gaisheshi ta fara yi tana kallon wani gefe! Isma'il yace'' Sweetlove kove kallona nakeso kiyi bawai kindinga kallon wani side ba! Rufe idonta tayi da hannu tace" I can't, wani kunyrka fa nkeji! Isma'il yace" okay tunda kunyata kikeji bari na tafi duk randa kika shirya magana dani sai ki nemeni! Yana magana irin soyayyar nan ta dabaibayeshi! Mikewa yayi tai maza ta janyo riganshi tace" Sweethrt I'm sorry, don't go itama tana magana amarai
raice kamar mejin bacci

Nan fa suka fara hira kowa na fadin yanda yakeji da yai missing din Dan uwanshi, Isma'il yace nafasha missing dinki har hrt problem nasamu, Xeey tai murmushi tace" lol nasan yanzu zaka sama sauk'i insha Allah, Isma'il yace ai tun randa naganki naji hrt dina ya dena mun zafi, Yana magana seda yakai k'arshe yai kasa kasa da murya yace" I LOVE You! Wani ajiyar zuciya taji Dan tabbas tayi missing din Isma'il dinta, nan dai suketa hirarsu har Afrah ta dawo itama daga tadin ta gansu tace" a mind dinta wato dama missing din junane yasa dukansu suka fita daga hayyacinsu ji yanda sukai kyau, tana wannan tinanin ne har ta shiga daki abunta,
Sunata hira har 10:30 Xeey tace" Sweethrt kazo ka tafi gida fa dare nayi! Isma'il yace" ai nan gidan mune idan naga damar kwana anan zan kwana tace" uhm nasani amma ai kar su Hajiya sui tinanin wani Abu ko? Isma'il yace" See you yanzu ai zan ma tafi amma in tina maki wani Abu? Tace" eh yace kin tuna kina karama kizo dakina INA bacci sedai in ganki a kan gado lokacin yarinta na damunki ko? Ai bata jira ta bashi amsa ba guduu tayi ta shige fallo, shikam binta da kallo yayi Dan komai tayi burgeshi takeyi kuma tabbas ba wanda Xeey ta dace dashi sai Shi, Dan haka ya girgiza kai yai smiling ya tafi, ya fito daga gatey din kenan sukaci karo da musaddiq shima ya dawo daga zance wajen Fatima! Shan hannu sukai musaddiq yace" dakyau abokina sai mun hadu gobe nan sukai sallama, Isma'il ya wuce gida, musaddiq kuma ya shiga gida

Bayan Isma'il ya shiga gidane seya manta be amsa number din Xeey ba Dan haka ya kira musaddiq yace" ya turomai da number din Xeey, musaddiq yace bazan turo ba, abokina lalle na lura Xeey dinnan seta saka ka manta da komai ae Isma'il yace hahaha Eh din naji nidai ina jira! Ya katse wayar, ba ai minti 2 be sega number nan musaddiq ya turo mai, Yana ganin number Isma'il ya kirashi yace" Nagani thanks ka cece rayuwar abokinka da yau bazan iya bacci ba! Musaddiq yai dariya yace se yanzu nagane Ashe dai duk xeey dinnan ne ta sa abokina Rashin walwala, Isma'il yace" oho dai sai gobe, katse waya Isma'il din yayi ya jefa gado sannan ya shiga toilet yayi wanka ya bude firij ya dauko lemon yasha sannan ya fara tura ma xeey din text Dan gani yake 11:20 tayi bacci...text din kamar haka!

_If I could chose between loving you and breathing I would use my last breathe to say I LOVE YOU._

_You are the sun in my day, the wind in my sky, the waves in my ocean, and the beat in my heart. I Love you So Much._

_Everyone says you only fall in love once, but thats not true, because every time I see you, I fall in love all over again._

Seda ya tura mata texts guda uku yace bari nabarki haka sweet dreams, ya kashe phone dinshi shima yai bacci
Chan darene Xeey ta farka zatai nafila seta duba wayarta taga karfe nawa! Tana bubawa taga texts Dan karamin tsaki tayi tace" to waye wannan seda taga ma karanta tsab, ta kara yin tsaki tace" mtsww sai yasa na tsana whatsap dinnan ba dama ai adding dinka a grp wasu mazan sun dinga biyoka kenan _a tinaninta wanine a GRP chat batasan Isma'il bane_ dan Haka tai reply kamar haka!
_Malan sai kayi hakuri inada Wanda nakeso, kawai kaga number mutun ka wani mai text daga yau kar in sake gani, Wani ya rigaka tai sending, toofaa_ sannan ta shiga toilet tai alwala tai sallah ita kadai tunda Afrah tana off!

Bangaren Isma'il kuwa Yana tashi yai alwala yai sallah be komq bacci ba karatun qur'ani yayi, gari na waye yasa ruwa a heater, yai wanka ya shirya sannan ya kunna wayarshi! Yana kunnawa yaga text ya shugo karantawa ya farayi! Gabanshine yai mugun fadi, yaji duk bazai ma iya zuwa office din ba nan ya fada gado!!!........

Hope you're enjoying the story

Ummiey Xeey
[1/21, 10:34 PM] ©REAL UMMIEY XEEY: *_ ∆°°••~❣_💞••💙💓❤💛
*A DALILIN MATAR​​​​*
*UBA​​​​*
*_ ∆°°••~❣_💞••💙💓❤💛

```​​​​​​​​​​​​STORY & WRITTEN BY​​​​​​​​​​​​```
*​​​​Ummiey_Xeey Abakson​💋​​​*

*​​​​♻EXCLUSIVE WRITER'S FORUM​​​​*
_[ɦօʍɛ օʄ քɛaċɛ, ɦօռօʊʀ aռɖ sʊքɛʀ աʀɨtɛʀ's]_

*​​LIKES AND DROP YOUR COMMENTs​​*
FB..#https://www.facebook.com/Exclusive-Writers-Fans-E-W-F-1922297541423276/

```​​​​​​​​​SADAUKARWA GA____​​​​​​​​​```
*​​​​MARIAM TIJJANI ADAM​*

*NABILANCY* Ina tayaki murnan kammala littafin ki me suna kallon kitse akema rogo, Allah ya kara Basira🤙🏼

Chapter Navigation

Use this section to move to any chapter without going back to the top.