Romantic Hausa Novels

A Dalilin Matar Uba Part 1 Complete Hausa Novel

Reading file: A_Dalilin_Matar_Uba_Part_1_Complete_Hausa_Novel.txt

Chapter 30 of 35

*PAGE 95...96*

Adai dai lokacin da Afrah ta shugo taga mum Isma'il rungume da Xeey itama me ya faru tace" shi kam musaddiq in banda murmushi ba abun da yake Dan shi kadai ne zai iya bada labarin komai!!!!

Mummyn su Afrah tace" yanzu dai burinmu su sama Lafiya komai me sauk'i ne tunda Allah ya kawo k'arshe abun, maman Isma'il din tace hakane hajiya! nan ta wuce da Xeey bayi tai fitsarin,
Bayan Xeey ta fito daga bayin jiri taji Yana debanta ta sauri ta fisge ta fada gado! Maman Isma'il t tausaya mata matuka! Around 10pm ne Isma'il ya farka daga baccin da yakeyi! Addua yayi tare da bude ido, yace Alhamdulillah Dan wani karfi yadanji a jikinshi, su mamanshi da babanshi yagani sukai mai Sannu! Daddynshi da yaga jikin nashi da sauk'i yace shi zai koma gida tunda duk matane wajen gobe zaizo, Hajiya tace" Okay

Da fitarshi Afrah taje kusa dq Xeey tana ta bata hakuri akan ta dena kuka koma menene duk da ita Afrah batasan meke faruwa ba! Zeey tace ok nan tai shuru, misalin karfe 11ne kowa ya sama inda zai kwanta se bacci, Isma'il ne Yana kwance se hamdala yakeyi Dan wani natsuwa yaji a jikinshi kamar ba abun da yake damunshi, ranshi fess yayi bacci

Cikin dare ne Xeey ta farka tanajin yunwa, mikewa tayi ta kunna filatar dakin taga kowa na bacci, kuma motsinta besa kowa ya tashi ba dan sun gaji gaskiya! Takawa tayi ahankali taje daidai gadon da aka kwantar da Isma'il, K'ura mai ido tayi taji inama ya farka yanzu suyi magana koda sau daya ne, Hakanan ta dinga kallonsa seda ta kusan 20mins akanshi sannan ta wuce ta eba abinci tashi ta sha ruwa sannan ta koma kan gadon itama se hamdala takeyi dan Taga Sahibinta....

*WASHE GARI*
tun Wuri Dr musaddiq ya tashi yaje tai dressing na doctor, suma suka tashi nan nurses suka shugo suka basu medication dinsu na 8am...Alhamdulillah jikinsu da sauk'i dama ba wani ciwo bane suma ne kowa yaji sauk'i sai son barka!
Musaddiq ne zaune suna hira da Isma'il a office din su Dan yanzu Isma'il kunyar su Maman Afrah yakeji Dan be iya zama a ward din da aka kwantar dashi! Suna zaune ne Fatima Zahra ta kira musaddiq tana tambayarshi me yasa kwana biyu baya picking ko reply din text idan ya gani, Musaddiq yace afuwan babban Aminina ne ba Lafiya, Tace" Allah sarki, Allah ya kara Lafiya may be inshugo dubashi, yace" Ameen Ok...Isma'il yace" Angon Fatima, musaddiq yai dariya yace kai kumafa??? Nan dai suketa hiransu

Kwanan Su Isma'il biyu aka sallamesu dukansu aka tsayar da magana Iyayan Isma'il zasuzo Gobe Dan fayyace duk abubuwan da ke tsakanin Xeey da Isma'il, Da kuma yanda akai Xeey tazo gidansu musaddiq!

Su Xeey suna zuwa gida abba (baban Afrah) ya kirata yake jirgin dare zaibi insha Allah meeting din da za ai gobe zai halarta, yaji komai so ta kwantar da hankalinta tace" ok Abba
Bangaren Isma'il shima suna dawowa gida mummy se congrats suke mai, Yace" Adduan ku shi ya Bini, dama mum kullun adduan Allah yasa muga na kike, mum tai murmushi tace hakane my Son! Nan take ya Ciro wayarshi y kira Anty *MARIAM TIJJANI* Tana zaune da mijinta suna hiran soyayya Sega call dinshi, tana dubawa taga *Isma'il din Xeey* Sunan datai saving kenan da number dinshi, Alhaji mijinta yace" pick up, nan ta dannan answer ya gaiaheta cikin natsuwa, Yace" Anty Albishirinki tace" Goro Yace" Wallahi naga Xeey! Alhamdulillah tace" sannan tace ganinan Zuwa! Isma'il yace" Anty ki zamanki gobe Insha Allah ma zamu hadu a malali Ghana road gidan dq Xeey din take kenan! Tace" alhamdulillah Allah ya kaimu yace" Ameen, Nan itama ta fara hamdala kowa dai ranar ya kwana da Farin ciki banda masoya biyu Isma'il da Xeey Wanda ko gyangyadi yaqi daukarsu, Haka suka kwana cikin tinani da kaunar junansu har gari ya waye!
Washe gari kowa ya tashi su Afrah da Xeey da Maman su suka gyra ko ina Dan tarban baki! Anyi abinci kala kala misalin karfe 10am Sega Anty Mariam ta sauka a gidan su Afrah, Xeey na ganinta da gudu taje ta rungumeta tanata kuka Xeey, mman Afrah tace waye wannan Xeey? Xeey tace kanwar mahaifiyatane nan sai suketa Yana kuke kuke har sunfara labari sega yan gidan su Isma'il, nan duka falon yadau Hamdala Dan duk Wanda akeso su hadu Alhamdulillah sun hadu, kamar su Baban Afrah, Maman su, Afrah musaddiq se ita Xeey, se mman Isma'il da babanshi dashi kanshi Isma'il se Kanwar Maman Xeey wato Mariam Tijjani da mijinta, Maza manya 3 mata ma haka!
Nan aka budeu wajen da addua

Mariam ta fara bada labarin tun daga kan tasowar Xeey har irin wahalan Da Xeey tasha wajen *matar uba* yanda matar uban ta rabata da Isma'il da duk yan uwanta, Baban su Afrah yace" Alhamdulillah to muma dai nan muna zaune wannan yarinyar ya nuna Afrah yace" ta sanadiyyarta tazo gidan nan har Allah yasa suka hadu da Isma'il.....nan akaima Afrah godiya sosai da dabiun ta na gari, nan dai aka yanke shawarar za'aba Isma'il Xeey tunda soyayyar su ta Dade so ba abun da'a jira, kowa ya amince da hakan Mariam tace" wannan shawarar tayi, baban Su musaddiq yace" ubanta ai nanan ko? Akace Eh nan suka mik'e zasu tafi gidan Su baban Xeey

UMMIEY Xeey
[1/21, 10:34 PM] ©REAL UMMIEY XEEY: *_ ∆°°••~❣_💞••💙💓❤💛
*A DALILIN MATAR​​​​*
*UBA​​​​*
*_ ∆°°••~❣_💞••💙💓❤💛

```​​​​​​​​​​​​STORY & WRITTEN BY​​​​​​​​​​​​```
*​​​​Ummiey_Xeey Abakson​💋​​​*

*​​​​♻EXCLUSIVE WRITER'S FORUM​​​​*
_[ɦօʍɛ օʄ քɛaċɛ, ɦօռօʊʀ aռɖ sʊքɛʀ աʀɨtɛʀ's]_

*​​LIKES AND DROP YOUR COMMENTs​​*
FB..#https://www.facebook.com/Exclusive-Writers-Fans-E-W-F-1922297541423276/

```​​​​​​​​​SADAUKARWA GA____​​​​​​​​​```
*​​​​MARIAM TIJJANI ADAM​*

*Dedicated to All lovers of the world....❣❣❣❣*

Chapter Navigation

Use this section to move to any chapter without going back to the top.