A Dalilin Matar Uba Part 1 Complete Hausa Novel
Reading file: A_Dalilin_Matar_Uba_Part_1_Complete_Hausa_Novel.txt
Chapter 26 of 35
*PAGE 87__88*
D'ago kan da Isma'il zaiyi yai wa hajiyarsu musaddiq sallama kawai idonshi yai arba da *MEMO* Wani Abu yaji ra ratsa kwakwalwarshi, kasa mik'ewa yayi don a zatonshi kannan musaddiq sun gama kallon abun dake cikin memo din Nan take zuciyarshi ta fara bugawa, brain dinshi ya fara tinanin taya akai memo dinshi ma yazo gidan? Ko musaddiq ne ya dakkomai? Mum dai taga kamar Isma'il a takure, tace" Lafiya dai ko? Ko ruwa ba'a kawo maka ma sannan ta kwallawa Afrah kira ta kawo mai, Afrah najin an kirata ta fara wani yatsine yatsinan fuska wai tana Chating an wani kirata! _(Lols haka fa mata da yawa suke Idan suna chat basa so ai musu magana ko ace zo kimun kaza)_ Isma'il kamar yana ganin abun da Afrah keyi yace" uhm bakomai wlhi tafiyama zanyi nayi mantuwa a gida an aikeni ban dauka sakon ba tun safe _(wayince dan kar su gane halin da yake ciki)_
"Mum tace" ah ah gaskiyane dole ka damu, Musaddiq kuma yace" kai bro wallahi da abun dariya kke Aiken su hajiya ka manta ko? Sai na fada mata, Isma'il yace" rufamun asiri, ya mik'e kenan zai tafi sega Afrah ta taho da ruwa me sanyi a gora hade da five alive, tana kallonshi tace wow ammafa guy dinnan ya hadu sosai!
"Musaddiq ne ya kalleshi yace" to ga ruwan ka tafi dashi, kallo ya watsa ma Afrah da take ta wani iyayi yace" nop thanks! Wani haushi Afrah taji tace" mtsww dama kyawawan maza akwai wulakanci _Meelat tace" hahah dama yace Yana sonkine???_
"Afrah tsayawa a windo tayi seda taga fitar shi sannan ta shugo daki ta fada gado tace" Mtsww, Xeey tace" meya faru kuma? Afrah tace" wannan dan rainin wayon ne abokin bro musaddiq seda yaga nakawo mai ruwa sannan dan wulakanci wai bayasha! Xeey tace" hhaha wannan dan wulakanci ne gaskiya! Afrah tace" ohon mai zai sake zuwane ba abun da zan kawo ko ance in kawo! Xeey dai tace" uhm zaki hadu da yaya musaddiq kena!
"Shi ko isma'il yana Fitowa wajen motarshi ya nufa, da sauri ya tada ya fara driving, Da gudu yake Jan motar dan tinani barkatai takeyi, dan tunda yai tozali da memo hankalinshi ba'a kwanceba! Minti kadan ya Isa gida yai ma mahaifiyarshi sannu da gida sannan ya wuce daki!
Drawer ya bude dan duba memo dinshi be ganiba! To fa! Bag dinshi ya dakko ya sake dubawa nan ya Gani! Subhanallah yace" dan wani mugun faduwar gaba da yaji yanayi
Nan ya shiga tinanin taya akai to memo dinshi yaje gidan? Tinani barkatai yake tayi kan kace meye zazzafan zazzabi ya kamashi! Mum dinshi har magrib taga shuru be fitoba dan haka ta shiga dakin dan duba lafiyarshi, tana shiga ta hangoshi kan bed ya wani lullube,
Da sauri taje ta taba jikinshi taji zafi dauu, Subhanallah tace" ta dauka wayanshi ta kira number friend dinshi musaddiq ta sanar dashi yazo ya duba frnd dinshi bashi da Lafiya, Musaddiq yace" okay ganinan zuwa daki ya shiga ya dakko kayan aiki sannan ya sanar da mum dinshi tace" yai mai sannu kafin tazo, mum din Isma'il na zaune kusa dashi sai tofa mai addu'oi take Sega Musaddiq nan take yai mai allurai zazzabin ya sauka sannan ya temaka mai yaje toilet yayi alwala yai sallah har ya samu yaci abinci, sannan musaddiq yace" meke maka ciwo yanzu? Isma'il ya nuna kanshi tun daga time din be kara cewa" a ba bare a a, ganin jikinshi ne yasa Musaddiq ya kira mamanshi yace" anan zai kwana dan yanayin jikinshi dole se akwai wani kusa dashi, Hajiyarsu musaddiq tace" to bakomai Allah dai ya bashi Lafiya!!!
*Washe Gari*
Isma'il ya tashi jikinshi alhamdulillah amma musaddiq yace" karya damu basai yazo aikiba tunda jikin da sauk'i yanzu bare yaje gida ya shirya ya wuce office in akwai wani abun ne ya sanar dashi, basu gama maganar ba sega mum Isma'il tai ma musaddiq godiya sosai yace" aiit ba komai ana tare!!!
Musaddiq ne ya fito daga gidan ya tare me napep y kaishi har kofar gidan Yana shiga, ya gaishe da mum sannan yace abinci nan mmansu take tambayarshi ya jikin Isma'il din yace da sauk'i, hajiya tace" insha Allah zasuje gaidashi yace" OK mum
Misalin karfe 9am Musaddiq ya gama shiryawa ta tafi office nan abokan aikinsu ke tambayar ina Isma'il! Musaddiq yace" beda Lafiya ne, Sukace" Allah ya bashi Lafiya yace" Ameen! Nan nurses suka shugo office dinshi suka gaisheshi kuma suka tambaya yame jiki yace da Sauk'i, yace OK Ku dakko folders din mui ward round yau nayi latti, nan sukai abun daya umurcesu!
Ummiey Xeey
[1/21, 10:34 PM] ©REAL UMMIEY XEEY: *_ ∆°°••~❣_💞••💙💓❤💛
*A DALILIN MATAR*
*UBA*
*_ ∆°°••~❣_💞••💙💓❤💛
```STORY & WRITTEN BY```
*Ummiey_Xeey Abakson💋*
*♻EXCLUSIVE WRITER'S FORUM*
_[ɦօʍɛ օʄ քɛaċɛ, ɦօռօʊʀ aռɖ sʊքɛʀ աʀɨtɛʀ's]_
*LIKES AND DROP YOUR COMMENTs*
FB..#https://www.facebook.com/Exclusive-Writers-Fans-E-W-F-1922297541423276/
```SADAUKARWA GA____```
*MARIAM TIJJANI ADAM*
_Proudly dedicate this page to you guys_ *♻E..W..Forum, kunsan yanda nake sonku, baki bazai iya furta yanda nakejinku a heart dinaba..I love you with every breath💚💚💚*
Chapter Navigation
Use this section to move to any chapter without going back to the top.