A Dalilin Matar Uba Part 1 Complete Hausa Novel
Reading file: A_Dalilin_Matar_Uba_Part_1_Complete_Hausa_Novel.txt
Chapter 33 of 35
*PAGE 105__106*
Ranar Daurin aure, gida cike da yan Uwa da abokan arziki, Kawayen amare ko ince yan uwa tunda ba wani kawayene da su balle ma Xeey, se kwalliya ake tayi, andaura Aure, Isma'il da Xeey, Musaddiq da Fatima, and Afrah da Abdulrasheed Alhamdulillah
Misalin Karfe 4 ne na yammacin jumma'a bayan andaura Aure aka tafi arewa House dake garin kaduna ,achan akai wani kyatattcen Party dasu Isma'il da Musaddiq suka hada tare Da Abdulrasheed cos sun mai magana ayi komai tare tunda yanzu anzama Kusan yan uwa Amince, Mutane Da dama Sunje, Ana zaune Sega amare da Angwaye, duka sunsha Kwalliya kaya iri daya Matayen sunsa kaya Milk se head maroon, mazan kuma sunsa shadda farare se hulunan Kansu Black, sunyi kyau matuka, Suka sama waje suka zauna nan aka shiga program din Da sui!
Around 6pm ne aka tashi duka akayo gida dan shirin kai amare ko wacce gidanta!
Hajiya Aisha matar Uban Xeey ba karamin kashe kudi tai ba dan ganin komai ya tafi cikin tsari, baban Xeey ma da dukkanin Su dasu ka aurar da yara kowa se Hamdala sukeyi akan wannan nauyi dasu sauke
Bayan sundawo daga wajen party ne nan kowanninsu akai musu fada har itama Fatima matar musaddiq cos ba waje daya sukeba!
Akace" su zauna da mazajensu Lafiya, sannan duk abun da sukasan mazanso basaso to karsu kuskura suyi, Nan fa Su Afrah da Xeey aka shiga gefen kuka, wai zasui missing din gida
Dare nayi aka kai ko wanninsu gidanshi, Afrah badikko aka kaita, Fatima kuma da Xeey Ung dosa aka kaisu, layinsu daya but ko wanninsu gidanshi dadan, gidan kowa ya hadu amma na Afrah yafi kyau dan babban gidane.
Tofa angwaye ankai musu amare zo kuga farin ciki ballema Isma'il, da ya shiga gidanshi musamman Alwala yyi yazo yai raka'a biyu na godewa Allah daya cika mai burinshi!
Bayan ya idar da Sallah ne yazo gefen gado yacewa Zeey ta tashi taje tayi alwala tazo su godewa Allah daya nuna musu wannan rana! Tai kamar bataji ba! Ya bude mata fuska yace" madam I'm talking to you! Tace" uhm bana Sallane yace" ohh Duk randa kika gama please ki sanar dani, tace" Alright nan ta sake jikinta sukai hira dan dama ba wani kunya tsakaninsu sun Riga sun sama tuntuni, daga hira kowa ya juya yai bacci abinshi
°°°°°°°°°°°°
Musaddiq kam Dare nayi bayan sunyi abun Da Addini yace" a Daren ya samu ya kashe arna tun Fatima na kuka yai banza da ita, Itama Afrah ranar Abdulrasheed ba kyaleta yai ba dukda tana kukan missing din Xeey yace" shifa bazai hakura ba seda ya cimma burinsa! Hankalinshi sannan ya kwanta
°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°
Kwana biyu musaddiq da Isma'il suna hutun angoncin da aka basu a asibiti, Kwana biyu basu haduba! Musaddiq ya kira Isma'il Yana cemai ya angwanci? Isma'il yai murmushi yace" batada Lafiya ae kaidai zan tambaya ya angwancin? Musaddiq yai dariya yace" alhamdulillah munanan munasha, Isma'il yai dariya yace" dakyau Nan Sukai cutting din Call! Suna gamawa Isma'il yace" yau kwananmu biyu bari naje gida na gaishe dasu hajiya! Xeey tasa kuka wai zata bishi dakyar ya lallasheta ta hakura, bayan ya fitane, Xeey ta shiga toilet tai wanka sannan ta hada musu abinci koda ya dawo yau basai ya kashe kudinshi ba yaje ya siyo musu a ostrich! Dan haka tai mai abinci lafiyayeyye!
Isma'il yaje gida ya gaishe da iyayanshi suka kara jamai kunne dai akan yanzu sedai ya kara hakuri, banda zaurin fushi da Fada! Yace" insha Allah, sun taba hira kadan mamanshi tace" ya koma gida yq barta ita kadai yace" OK dan haka ya koma gida!
_Bangaren iyayan kowa, hankalinsu a kwance se adduan samun zaman Lafiya suke musu!_
Isma'il na komawa gida yaji wani kamshin abinci ya dokar mai hanci, knocking din dakin yayi, tazo ta bude, Sanya take da wata Riga da wando tree quarter, rungumeshi tayi tace oyoyo, Isma'il Kiss yai mata a kumatu yace" I'm so happy to have you kinyi kyau sosai my love! Tace uhm tana rik'e da hannunshi, direct dakinshi suka wuce ta ciremai Riga ta bashi towel tace" yaje yai wanka, Smiling yayi yace" bazakimun ba? Tace" uhnm No, ya wuce yai wankarshi ya fito shima ya sa Riga da wando tree quarter, sukai match dukansu!!!
Rik'e mata hannu yayi suka fito pallow yace" zo mui kallo, tace" okay nan ya kunna TV tana zaune, Yana zuwa ya kwanta kusa da ita yasa kanshi a cinyarta Yana kallonta! Duk tajita wani iri dan tsoro takeji, Look at my eyes yace" rufe idonta tayi tace" uhm namanta fa bakaci abinci sweetheart Yace" naki wayon so kike in cire kai na, in abincine Naci gidan mama amma zanci naki anjuma kinji hope dai kinci naki? Tace yap naci Sosai
Hira suke sosai but ba abun da ya shiga tsakaninsu up till now Yana so ya tambaya ko tagama period but Yana tsoro kar ya bata mata rai dan hka ya kyaleta!
Suna Zaune Har aka kira magrib.........
_Hope kunajin dadin novel din....muje zuwa!!_
Ummiey Xeey
[1/21, 10:34 PM] ©REAL UMMIEY XEEY: *_ ∆°°••~❣_💞••💙💓❤💛
*A DALILIN MATAR*
*UBA*
*_ ∆°°••~❣_💞••💙💓❤💛
```STORY & WRITTEN BY```
*Ummiey_Xeey Abakson💋*
*♻EXCLUSIVE WRITER'S FORUM*
_[ɦօʍɛ օʄ քɛaċɛ, ɦօռօʊʀ aռɖ sʊքɛʀ աʀɨtɛʀ's]_
*LIKES AND DROP YOUR COMMENTs*
FB..#https://www.facebook.com/Exclusive-Writers-Fans-E-W-F-1922297541423276/
```SADAUKARWA GA____```
*MARIAM TIJJANI ADAM*
```Masu kirana na gode sosai, Allah ya saka da alheri, ku sani Ummiey Xeey na yinku irin totally dinnan```
Chapter Navigation
Use this section to move to any chapter without going back to the top.