A Dalilin Matar Uba Part 1 Complete Hausa Novel
Reading file: A_Dalilin_Matar_Uba_Part_1_Complete_Hausa_Novel.txt
Chapter 34 of 35
*PAGE 103...104*
Xeey na zaune Mum su Afrah tace" Xeey ya kikai shuru? Xeey tace" mum inasone naje naga dangin mahaifina Dana uwata na Dade bangansuba! Mum tai murmushi tace kaman kinsan abun da nake sakawa a zuciyata karki damu cikin yau ko gobe zamuje gaba dayanmu kinji, Xeey tai murmushi tace" nagode Hajiya!
°°°°°°°°°°°°°
Soyayya tsakanin Xeey da Isma'il ya sake kulluwa kullun sukai waya shidai a matso da auran Dan gani yake kamar baze aureta ba, 2months din da ya rage gani yake kamar shekara ne Dan haka yanzu Isma'il yamaida gidan su Musaddiq tamkar nashi! Afrah ma da saurinta Abdulrasheed soyayya ruwa ruwa kamar su Hadiye Juna! Musaddiq ma da Fatima zarah suma wani rawan kai suke Dan sun kosa su zama mata da miji.
Bayan kwana biyune su Xeey da mummy da Afrah suka shirya suka kai Xeey dangin mahaifinta, kowa da yaga Xeey be gane taba, yanda tai kyau fatarta se kyalli yake, dama bayan wuya sai dadi, nan dangin Alhaji Abdallahi sukaiwa mum Afrah godiya sosai bisa kokarin da tai musu, tace" bakomai ai yiwa kai ne, kaima bakasan waye zai temake kaba wata rana sukace" maganarki hakane game tinani, seda suka gama gaisawa sunci sunsha sannan akai musu jagora gidan *MAHAIFIN XEEY*
Suna shiga da Sallama sabuwar *matar ubanta* hajiya Aisha ta amsheshu hannu bibbiyu Nan, tana ganin Xeey taji yarinyar ta kwanta mata arai! Nan Xeey ta gaisheta itama Xeey taji a jikinta tabbas Wannan matar uban NATA tanada kirki Dan haka ta rungume Xeey tace" zan share miki hawaye insha Allah, kiyi hakuri ki manta komai kinji? Tace bakomai nagode sosai, _matar ubanta Hajiya Aisha tace"_ Ashe ansa bikinki ko? Xeey tana rufe ido tace" eh wlhi, hajiya Aisha tace" ikon Allah rana daya Da za ai da na yarinyar yayata, Sunanta fatima! itama ta sama miji sunanshi musaddiq! Mum Afrah tace" doctor musaddiq? Hjiya Aisha tace" eh tabbas shi, Mman Su Afrah tai murmushi tace" Ai yaronane, duka abun ya basu mamaki sukace Ikon Allah kenan, abun Yama kowa dadi nan Hajiya Aisha ta kira wayar yayanta tace" ai ga mahaifiyar musaddiq nan, Ashe ita ta rik'e yarinyar mijina! Maman Fatima Kabbara tayi tace" Allahu Akbar, Allah kenan me yin yanda yaso! kan kace meye lbari duk ya kaurad'a dangi mum din musaddiq ita ta rik'e Xeey, Xeey kuma matar ubanta kanwar Maman Fatimane Wanda musaddiq zai aura..
Hajiya Aisha tace" abarmata su Afrah su kwana biyu mana! Mum musaddiq tace" bakomai ai ana tare Allah ya saka da alheri, tace" Ameen, musaddiq yamma yayi yazo daukar su yaji wannan labarin me dadi nan ya kira Isma'il shima kwarai yayi murna yace Allah ya albarkace mu gaba daya, nan akabar su Xeey sedai sukai kwana biyu sannan suka koma!
Hajia Aisha ba karamin tsaraba tai musu ba na kayan mata, tace tunda bikinsu ya kusa ba zama zasui ba, su dage su temakawa Kansu, yanzu ba lokacin wasa bane
Akwana atashi ba wuya saura *kwana uku* bikinsu, kowa anmai kaya na gani na fada musaddiq da Isma'il iri daya sukai akwatinansu da kayan ciki, yyin da Abdulrasheed kuma shima yai kayanshi daidai gwargwado bana karyaba.
*Agurguje* ana saura kwana biyu yan uwan mahaifiyar su Xeey su Mariam Tijjani tazo, kunsan kanuri ne Dan haka itama ta zo musu da kayan gyaran jiki da sauransu....Masha Allah, Amare kam sunyi kyau matuka sai ma ranar!
Ranar bik!, Gida cike da yan uwa da abokan arziki
Ummiey Xeey
[1/21, 10:35 PM] ©REAL UMMIEY XEEY: *_ ∆°°••~❣_💞••💙💓❤💛
*A DALILIN MATAR*
*UBA*
*_ ∆°°••~❣_💞••💙💓❤💛
```STORY & WRITTEN BY```
*Ummiey_Xeey Abakson💋*
*♻EXCLUSIVE WRITER'S FORUM*
_[ɦօʍɛ օʄ քɛaċɛ, ɦօռօʊʀ aռɖ sʊքɛʀ աʀɨtɛʀ's]_
*LIKES AND DROP YOUR COMMENTs*
FB..#https://www.facebook.com/Exclusive-Writers-Fans-E-W-F-1922297541423276/
```SADAUKARWA GA____```
*MARIAM TIJJANI ADAM*
Chapter Navigation
Use this section to move to any chapter without going back to the top.