A Dalilin Matar Uba Part 1 Complete Hausa Novel
Reading file: A_Dalilin_Matar_Uba_Part_1_Complete_Hausa_Novel.txt
Chapter 7 of 35
*PAGE📄43__44*
"Xeey Tace
Au Hakane, mum bari naje na saka mai nima na saka nawa "sa'adatu Tace Yawwa Yar babanta Allah miki Albarka, Tace ameen amma tayi mamaki Sosai Sosai........
"xeey ce bayan ta gama sakawa Kowa Ta dakko abincinta Tai daki Ta zauna Taci, Ashe sa'adatu na bibiyanta tana ganin ta shige daki dan Haka sa'adatu Ta shige kitchen Din ta dakko abincin abba ta barbada mai magani Kamar Yaji sannan ta rufe ta bar kicin din, "ba Ddewa sega Abba ya dawo ya kwalla wa xeey kira yace Sweet Sist, Ita kam already tayi bacci ma, Yana shuguwa Da Hajiya taji motsinshi yana kiran xeey tace mai ai tayi bacci me kake bukata ne? Ya nuna Cikinshi Alamun yunwa yakeji,
"hajiya tai wani murmushi na mugunta shi abba duk be Sani ba, dan haka ta nuna mai kicin tace abincinka nachan kaje ka dauka, ya shiga da murna ya bude yaga abinci lafiyayye Kamshi ya bade ko Ina da sauri ya dakko ya bude frigde ya dakko ruwan faro sannan yazo ya zauna a pallow Ya fara cin abincin hankalinsa Kwance....
"hajiya se lekowa takeyi Taga yaci abincin wani murna Tayi sosai harda kiran yalwa tana sanar da Ita Yafara cin abinci.. "Yalwa tai shewa tace dakyau kin kusan shuguwa Gariiiii yar matan Nan... "abba Yana taci yaji cikinshi Kamar yana dan kara kadan seya dakata dacin abincin ya dakko ruwa yasha, yana shan ruwan nan basai Ciki ya kara hautsinewa Ba, Ihu ya fara yana wayyo cikina, Wayyo cikina kutamakeni Zan mutu, da gudu Sa'adatu ya fito Ita ta kwalla Ihu yayi sanadiyyar Tashin Xeey daga bacci Itama Fitowa tayi dataga halin da dan uwanta yake ciki, Nan ta saka Kuka.
"abba kam se ihu yakeyi dakyar dai aka samu aka kaishi asibiti aka shigar dashi emergency, sannan Sa'adatu ta Kira Alhaji yazo suna asibiti abba beda lafiya, be ddeba segashi ya zo asibitin, Nan akai mai gwaje gwaje aka gano Poison ne aka Samai a abinci,
"alhaji yayi mamaki matuka yace Wayai abinci Sa'adatu tace zainab ce, Ana cikin haka kenan Rai yai halinsa Abba Ya rasu _subhanallah_ "Alhaji ba karamin Wani hali ya shiga Ba d'ansa ya rasu wanda yaci buri akansa...
Hakanan suka dawo gida akai mai suturu amma tun ranar Sa'adatu ta chanza zance ko ina labari ya karwade Ance xeey ce ta kashe dan uwanta, dan Haka Alhaji ko kallon Inda xeey take Bayayi balle yai mata magana...
__Bayan An watse ne daga zaman makoki Alhaji Ya kira Xeey yace baya sonta, baya kaunarta tunda ita muguwace karta sake tambayanshi kome, Kuma makaranta bazai sataba, Har tayi girman da zata kashe dan uwanta?
"Nan xeey ta rusa kuka tace wallahi bani Bane Abba, yace ta rufe mai Baki ko ya babbalata, Ita kam sa'adatu dama basonta takeyiba Tace tunda ubanta yace ba ruwanShi da ita, itama ba ruwanta da xeey dan karta goga Mata laifi itama Ya shafeta,
_Daki xeey ta shige ta rasa meke mata dadi, Kuka tayi sosai sosai abinci ta kasa ci, komai
Ma ta kasa Yi, ga yunwa Tanaji ba dama Tace zataci abinci, seta fake ido sannan taje wajen mukhtar driver ya bata taci, Cikin kwana biyu xeey ta lalace tai baki, ta rame, ko bacci takeyi setai ta firgita kamar mara lafiya,
Rayuwa ya chanzawa Xeey ga ismail dinta benan Gashi ko kudin mota bata dashi balle taje wajen dangin mamanta, Hakanan In abu ya dameta zatai alwala tazo tai sallah ta sanar da ubangiji,
"Bangeren Ismail kam kwata kwata yama manta da wata xeey sedai a yan kwanakin nan yana yawan mafarkinta, koya tashi sedai Yai mata addua, *Musaddiq* ne wanda suke room daya dashi yake cemai Ismail, Wai meke damunkane, Like something is wrong, "ismail ne yace wlhi about that girl ne da nake baka labari Kullun se nayi mafarkinta,
"musaddiq yace ayyah Continue praying for her, Allah Yasa lafiya dai, Ismail yace ameen, har musaddiq na tsokanar sa Kodai aljanace Haka,
"ismail yace lols aa Wlhi nasanta fa sosai, musaddik yace i knw i'm just joking fa, nan suka barke da hira sosai dan dama sun saba sedai basu zauna ba, yanzu *Musaddik* yana final Year Befi twoweeks ya dawo naija ba, kullun se yayi phone call da yan gidansu....
"Akwana a tashi ba wuya Yau ne Musaddiq Ze dawo naija dan haka yan gidansu suka shirya mai abubuwa harda karamin Party na congrats din ya gama school, but yayi missing din Ismail sosai shima haka dan 3 ne a dakin but sunfi shakuwa su biyu, kamar twins in kun gansu...wannan kenan......
Bangeren Su Xeey Kam yanzu kwata kwata kota gaishe dasu bata amsawa ta koma dai kamar bango a cikin gidan muktar driver ma da yake bata abinci sa'adatu tamai warning duk randa ya sake a bakin Aikinshi, Dan haka kowa Ya fita daga harkan xeey Allah sarki Ta koma marainiya
"YALWA ce kwasam tazo dan ta kwana biyu bata zoba, Tana shuguwa taga xeey a Tsakar gida duk tabi ta wani yankwane, Yalwa dariya tayi tace Kadan ma yarinya kika gani tai shegiwarta dakin wajen aminiyarta Nan ma wani makircin suka kara hadawa akan Aiwa Alhaji asiri ya manta da xeey
Aiko nan suka fito Yalwa Tace haba Hajiya ko Abincin da kike ba mage ai kya dinga mata mana, sa'adatu tace ahaha dan dai kinsa baki da ba Abun da Zan Bata, sun fito kenan Sa'adatu Ta wurgo mata wani leda, su Biskuit ne, bread, raguwan kankana da sauransu, xeey na budewa tagani har miyanta na tsinkewa hannu baka hannu kwarya ta dinga ci abun tausayi... Su hajiya sunje sun dawo daga wajen bokan Da darrene ta aiwatar da abun da yace akan Tasawa Alhaji maganin a ruwan lipton, Tana sa mai, Yaji wani tsana na Yarshi ya kamashi, Harya koreta hajiya dai ta dawo da ita ta bashi hakuri Akan Safiya nayi tabar gidan yanzu dare yayi _kaji makirci_
Daren Xeeey batai bacci ba...........!
Ummiey XEEY
[11/7, 6:55 AM] Ummiey Xeey Abakson💋: *_ ∆°°••~❣_💞••💙💓❤💛
*A DALILIN MATAR*
*UBA*
*_ ∆°°••~~❣_💞••💙💓❤💛
```STORY & WRITTEN BY```
*Ummiey_Xeey Abakson💋*
*♻EXCLUSIVE WRITER'S FORUM*
[ɦօʍɛ օʄ քɛaċɛ, ɦօռօʊʀ aռɖ sʊքɛʀ աʀɨtɛʀ's]
*LIKES AND DROP YOUR COMMENTs*
FB..#https://www.facebook.com/Exclusive-Writers-Fans-E-W-F-1922297541423276/
*OCTOBER 2017*
~SHORT STORY~
```SADAUKARWA GA____```
*MARIAM TIJJANI ADAM😍*
_DEDICATED TO ALL MY LOVER'S UMMIEY XEEY NA SONKU IRIN SOSAI DINNAN..INA ALFAHARI DAKU A DUK INDA KUKE_
Chapter Navigation
Use this section to move to any chapter without going back to the top.