Romantic Hausa Novels

A Dalilin Matar Uba Part 1 Complete Hausa Novel

Reading file: A_Dalilin_Matar_Uba_Part_1_Complete_Hausa_Novel.txt

Chapter 13 of 35

*PAGE📄 61__62​*

"Ismail yace ba fariyaba nhahaha xeey bazata taba kada Niba koda maza 1000 zasu taru

_Wani dariya Fahad ya saki yace kaji masoya nikam bari na fita na zaga gari Dan naga kai ka ​hau jirjin so​

Ismail yace naji din, jirani na watsa ruwa mu fita tare Dan zama mutun daya ba dadi, Fahad yace alright my frnd, nan Ismail ya shiga wanka, be dadeba ya fito, yasa wani riga me dogon hannu se wando blue jeans yamai kyau sosai, kafin su fita ne ya dakko *MEMO​* ya duba yai smiling sannan yai kissing din memo din

Fahad kam kallon shi ya tsaya yi yace lol...love wan kill person, Ismail yace eh din naji, let's go, suka kama hanya dan fita shan iska

*​A KADUNA KUMA​*
Mummyn Ismail itama kullun addua take ma d'anta, in Alherine Allah yasa su hadu da xeey inba alheri bane Allah ya ciremai sonta, Dan tsoro takeji kar d'anta ya kamo da heart problem...!

Bangaren Su xeey kuma, Alhamdulillah sauk'i na samuwa, Dan kullun se hajiya tai mata adduoi

Safiyar ran jumma'a, bayan hajiya tai ma xeey addu'a kamar yanda akace mata, yayan Afrah na shirin fita office, daddyn su afrah kuma yana daki Dan yazo Hutu,

Ihu sukaji me karfi a dakin xeey, gaba dayansu suka fito, yayan Afrah kuma daga shi sai towel ya fito daga wanka lolz.. daddy ne yace kallekafa, nan kunya ta kamashi ya koma daki ya sa jallabiya hahaha
Bayan yasa jallabiya se kunya yakeji kamar bazai fitoba, hakadai yayi ta maza ya fuske ya fito, koda ya shiga room din su xeey, yanda yabar su mommy haka yazo ya taddasu

"Xeey CE tarik'e kanta se kuka takeyi,

Mummy ce taje kusa sa ita ta kamata tace menene y'ata?

Daddy ne yace" yace in banda abunki hajiya, yarinyar da bata magana taya zata amsaki?

Kawai jin maganar da basui tsammani ba sukaji *XEEY* tace "inajinku inane nan?

Duka dakin suka hada Baki sukace *Alhamdulillah* *Alhamdulillah* Sannu xeey, kuka ta k'ara tsakewa tana cewa wayyo kaina, wayyo kaina, kowa na dakin tausaya mata yayi, mummy kam har da Yar kwallanta,

Daddy ne tace " haba hajiya meye na kuka, ai godewa Allah zamuyi tunda Gashi ta fara magana, shikam yayan Afrah tsayawa yayi yana ganin ikon Allah... _tabbas duk Wanda ya r'ike Allah zaiga haske_

Xeey kam in banda kuka ba abun da da takeyi, mummy CE tace hana y'ata kidena kuka mana

Daddy ne ya kalla xeey cikin tausayawa yace" Hajiya ki barta ta koka, Allah kadai yasan wahalan da ta tsince kanta, Mummy CE "tace Hakane amma Dan Allah ki dena damuwa muna tare dake,

Xeey binsu da kallo kawai tayi ta daga kai alamun To, sannan suka bar dakin, pallow dukkansu sukaje suka zauna,

yayan afrah kuma se jinjina abun yake, Dan kar ayi bashi, ya dauka wayarshi, ya kira frnd dinshi, yake sanar dashi bazai Iya zuwa office ba, abokinshi yace OK Allah yasa dai lafiya, yace" eh lafiya lau sai dai Monday idan mun hadu, nan sukai Sallama
Daddy ne yace ha'a my son meyasa bazakaje office dinba

Yayan afrah ya shafa keya yace uhm dad banso ayi banine, nasan zamu bukaci jin labarinta

Daddy yai murmushi yace kai my son, mummy ma itama maganar ya bata dariya

Suna zaune a pallow din xeey kam na daki, se kallon dakin takeyi, tashi tayi ta zaga ko ina na dakin, wani babban hoto ta gani a Dakin enlargement, wata kyakkyawar yarinya tagani, a zuciyarta tace to WACECE WANNAN?

ganin bame bata amsane yasa ta k'ura wa pic din ido, can kuma ta tino da Dan uwanta Abba da mahaifirta, dasu Ismail da auntyn ta Mariam Tijjani, nan ta saka wani kuka me taba zuciya

Su mummy kuma suna pallow, ta dauka waya tai dialing number Afrah, take CE mata wani babban farin ciki ya samemu, bata ida magana ba sukaji kukan xeey tuni, suka rude suka nufa dakin da Xeey take, shiga sukayi suka sameta a gefen gado, mummy CE ta dafata tace Y'ata ba kuka bane solution kinji, kiyi shuru

Ku ci gaba da kasan cewa dani

*Ummiey xeey CE* kema kowa fatan Alheri
[1/3, 8:30 AM] UⓂmiey Xeey👄: *_ ∆°°••~❣_💞••💙💓❤💛
*A DALILIN MATAR​​​​*
*UBA​​​​*
*_ ∆°°••~~❣_💞••💙💓❤💛

```​​​​​​​​​​​​STORY & WRITTEN BY​​​​​​​​​​​​```
*​​​​Ummiey_Xeey Abakson​💋​​​*

*​​​​♻EXCLUSIVE WRITER'S FORUM​​​​*
_[ɦօʍɛ օʄ քɛaċɛ, ɦօռօʊʀ aռɖ sʊքɛʀ աʀɨtɛʀ's]_

*​​LIKES AND DROP YOUR COMMENTs​​*
FB..#https://www.facebook.com/Exclusive-Writers-Fans-E-W-F-1922297541423276/

```​​​​​​​​​SADAUKARWA GA____​​​​​​​​​```
*​​​​MARIAM TIJJANI ADAM​😍​​​*

```Dedicated to my dear bilkisu BK😍 nagode da soyayya Allah ya bamu tare```
*Allah ya Baki lafiya me amfani, Allah yasa kaffrane*

Chapter Navigation

Use this section to move to any chapter without going back to the top.