Romantic Hausa Novels

A Dalilin Matar Uba Part 1 Complete Hausa Novel

Reading file: A_Dalilin_Matar_Uba_Part_1_Complete_Hausa_Novel.txt

Chapter 23 of 35

*PAGE 81__82*

"Musaddiq yaga ran Afrah ya Dan baci yace Yana zuwa, Direct room dinshi ya shiga ya cire kaya ya shiga wanka, be bata lokaciba ya fito sanye da wani light blue shirt da jeans yayi kyau sosai,

Afrah da Xeey da mum suna zaune sallamar musaddiq sukaji yace" sai kuzo mu tafi ko? Mum tace" haa! Bazaka tsaya kaci abinci ba da sauri haka?

Musaddiq yace" to sweet mum yazanyi wannan yarinyar ta matsa mun semun tafi, Afrah tace" woo waneni bro plz sit down and eat joor! Ita dai xeey binsu da kallo kawai take in abun dariyane tayi inna shuru ne tayi

Shap shap musaddiq yai having break fast dinshi, y mike ya dauka key yace musu let's go! Mikewa sukai sukai wa mummy sallama tai musu fatan alheri, da kuma Allah ya dawo dasu Lafiya sukace" Ameen

°°°°°°°°°°°
Isma'il ne zaune ya rasa meke mai dadi, phone dinshi ya dakko yai dialing numbern BABBAN AMININSHI *MUSADDIQ* ringing daya, biyu ya dauka suka gaisa!
Isma'il yace" are you at home?
Musaddiq yace" nop walhi nadan fita da sisters dinane ko zakazo ne zamu mangal plaza ne
Isma'il yace" alright sekundawo da zan zone
Musaddiq yace" Eyyah Idan nadawo zanzo ma plz regard to my mum, Isma'il yace OK agaishemun da kannan Nawa, musaddiq yace to aboki..!

Bayan sungama wayan ne Isma'il yace kai banda kirki fa yau na kusan 2months da dawowa amma banje naga Anty mariam Adam ba! (Antyn Xeey)

Mikewa yayi ya sake shiryawa sannan ya fito pallow ya gaishe da hajiyarshi, sannan ya hau kan dining yai break fast dinshi, bayan ya gama ne yace" wa mamanshi zai Dan fita! Tace" OK har ina cewa zaka kaini gidan abokinka nai musu godiya?

Isma'il yai smiling yace" I called him this morning sun fitane, mum Isma'il tace" ayyo. Isma'il yace" to zan fita mum tace" OK Allah ya tsare kar dai ka Dade please, ya matso ya rike hannun mamanshi yace" insha Allah.....!

Yana fita mum dinshi ta daga hannu tace" Ya Allah ka tsaremun yaron nan, ka bayyanar da Xeey in tana Raye, in kuma bata Raye, Ya Allah ka cirema yaron nan son Xeey... *Allah SARKI*

*ISMA'IL* ne ya fito da car daga cikin gidan, idonshi yakai ga inda suke tsayawa da xeey, Wani hawaye yaji Yana kokarin zubuwa, tuni yace" *innalillahi wa inna ilaihi rajium* ya dake zuciyarshi ya fara driving cikin natsuwa, be zarce ko inaba se gidan *MARI'AM TIJJANI ADAM* Yana zuwa Bakin gate din yai parking, ya fito ya tsaya yana tinanin taya zai fara shiga gidan, tunda gidan matar aurece be dace ya shiga kai tsayeba! Be gama tinanin nan ba Sega gate man ya fito suka gaisa, wa kake nema inji gate man"

Isma'il yace" Anty Mariam nake nema Allah yasa tananan, me gadi yace" tananan bari na shiga nai mata magana, Isma'il yace Okay...

Mariam ne zaune a hadd'andan falonta yasha kayan alatu ta ko ina, sallamar me gadi taji yace" Hajiya ana sallama dake a waje, gabantane ya fadi tace" oh ni waye toh?, kawai tace" to kace ganinan zuwa, hijab dinta ta dakko, ta fito cike da fargaban to waye wannan me nemanta?

Fitowa tayi sukai 4 eyes da Isma'il, dukansu Wani murmushi suka sake tace aww dama kaine? Maraba da zuwa ka shugo mana! Isma'il yace" wallahi kuwa, tana gaba Yana binta a baya...

Daki suka shiga ta kawo mai drinks sannan ta zaune tace" Isma'il idonka kenan dama kananan a garin nan bako ziyara, Dan yanzu ba xeey ba zumunci ko?

Isma'il yace" Anty ba haka bane wallahi ban Dade da dawowa daga school ba Alhamdulillah mun gama, ya LABARIN XEEY? GHAM gabanta ya fadi Dan taga sauyin fuskarshi, numfashi me karfi tayi tace" Isma'il wlhi har yanzu shuru ba labarinta, dukansu shuru sukai na mintoci sannan Isma'il yace" ya Salam, Mariam tace inaji a jikina zamu ganta, shidai Isma'il shuru kawai yayi Dan zuciyarshi wani tafarfasa takeyi

Yace" To Anty Allah ya amsa addu'arki tace" ameen, har ya fara fita a hayyacinsa yace mata zai tafi? Tace" Ismail ko ruwa kasha ai, yace" Hmmm Ina zan iya shan wani Abu banji labarin burin raina ba? Binshi da ido kawai tayi Dan ba karamin bata tausayi yayi ba, fita yayi da sauri yaje ya shiga motarshi da gudu yake figan motar har ya isa gida!!!

Yna shiga mum dinshi taga be cikin walwala mutuwar tsaye tayi Dan tasan meke damunshi

*Kuci gaba da biyo asannu sannu, a next page zakuji ci gaban labarin inda akaje wasu Afrah shopping*

Yours
Ummiey Xeey
[1/21, 10:34 PM] ©REAL UMMIEY XEEY: *_ ∆°°••~❣_💞••💙💓❤💛
*A DALILIN MATAR​​​​*
*UBA​​​​*
*_ ∆°°••~❣_💞••💙💓❤💛

```​​​​​​​​​​​​STORY & WRITTEN BY​​​​​​​​​​​​```
*​​​​Ummiey_Xeey Abakson​💋​​​*

*​​​​♻EXCLUSIVE WRITER'S FORUM​​​​*
_[ɦօʍɛ օʄ քɛaċɛ, ɦօռօʊʀ aռɖ sʊքɛʀ աʀɨtɛʀ's]_

*​​LIKES AND DROP YOUR COMMENTs​​*
FB..#https://www.facebook.com/Exclusive-Writers-Fans-E-W-F-1922297541423276/

```​​​​​​​​​SADAUKARWA GA____​​​​​​​​​```
*​​​​MARIAM TIJJANI ADAM​😍​​​*

💋💋Dedicated to All lovers of *UMAR M SHARIFF* wannan page din nakune Ku kadai.... 💋💋🤦

Chapter Navigation

Use this section to move to any chapter without going back to the top.