A Dalilin Matar Uba Part 1 Complete Hausa Novel
Reading file: A_Dalilin_Matar_Uba_Part_1_Complete_Hausa_Novel.txt
Chapter 11 of 35
*PAGE 📄 53__54*
*I LUV YOU WITH OUT YOU MY LIFE IS OUT OF CONTROL* "to ko na dawo dai na fasa fitar ne", A cewar Alhaji, sa'adatune ta wani sake murmushi hade da cewa" yi tafiyar ka babu komai.
yana tafiya ta kira Aminiyarta ta shaida mata abinda Alhaji ya bata shewa yalwa ta saki tace gani nan zanzo a bani rabo na, "Maganar yalwa ta b'atawa Sa,adatu rai amma saita hakura saboda yalwa zata raka ta wajen wani boka, Ba' dauki lokaci mai tsayi ba sai ga yalwa ta iso haka, Sa,adatu ta cikata da kayan kwalama da mak'ulashe sai da taci tayi Kat sannan "tace Sa,adatu dauko min rabo na, Sa'adatu ranta Adan bace tace" bari nayi miki transfer na 1million
"yalwa ta d'an bata rai tace haba ina laifin 2 million kinga wahalar dana sha wajen binne abubuwan da Boka ya bayar da wanda yace a boye inda wani bazai gani ba koya taba haba sa,a
" Sa'adatu tace To yalwa bari na baki 2 din a zuciyarta kuma tana fadin kinci na karshe don da Kaina zan rinka tafiya ko don sirri na
********
"Xeey ce kwance a bedroom tana ta sharar baccin ta mummy ce ta shigo da garwashi a hannunta ta zuba Habbatussada ta turarawa Xeey, Wani zabura XEEY tayi ta mike tana shirin kuka, mummy CE still ta r'ikota ta fara mata adduoi sannan ta samu ta lafa, abun yaba mummy mamaki sosai, tace dole mu dage da addua Dan da alama Zamu sama nasara sosai
*********
*After 4months* haka DAI aketa adduo ana samun nasara sosai sedai Xeey bata magana is like abun ya taba mata brain sosai, Afrah kam yanzu ta tafi service komai mummy ke mata se big bross yana Dan temaka mata abun da be gagaraba
__Ismail kuwa ya dawo hutu, tun da ya shugo garin yaji bemai dadi sosai Dan yasan ba ganin Xeey zaiyiba, koda ya shugo area dinsu ya shiga gidan mummy tamai oyoyo ta kawo mai abinci yaci yashiga toilet yayi wanka ya fito ya shirya yasa wani light blue shadda yayi kyau sosai..
Pallow yazo ya zauna ya dakko remote ya r'ike, mummy CE ta shugo ta sameshi taga yayi shuru da alama ya sunduma cikin tinani, "mummy CE ta kora mai ido ta tausaya mai sosai Dan tasan sure! He's thinking of Xeey..
"Dafashi tayi tace look my son, Dan Allah kayi hakuri, I told you several time's without number nace ka rage tinani ba abun da zai karama sedai cikin kai, just be praying for her, Allah ya hadata da alheri a duk inda take,
"Ismail ne yayi wani ajiyar zuciya yace Hakane mum, wallahi ADALILIN da yasa kikaga INA yawan tinata shine when I was in school INA yawan mafarkintane, kuma ba'a yanayi najin dadi nake ganin taba sai yasa,
"Tunda yake magana mummy idonta ya cika da hawaye Dan tasan Sabon da sukai da ita sai yasa take tausayamai, " tace nasani my love, nima zanci gaba da tayaka da addua, ai Xeey tamuce so please ka sake ranka insha Allah nima zan temakama wajen tayaka Neman inda take ko a Raye ko amace _Mummy ta fadamai wannan maganar ne Dan kwantar mai da hankali Dan ita Sam da za ace ta nemo inda Xeey SUKE bata saniba_
Wani murmushi Ismail yayi Dan ba karamin jin dadin maganar mahaifiyarshi yaji ba, yace thanks mum I'm proud of you, itana tai smiling tace me too Allah ya k'ara tsaremun my son "yace Ameen mum
Kwanar Ismail biyu, Kullun seyayi dialing number room mate dinshi na school, *musaddiq*
Yauma Zaune yake a pallow yana shan coffee dayar hannunsa r'ike da phone, dialing number musaddiq yayi again yaji abun da ya tsana _the number you dail Does not exist please try again letter_ yani tsaki yaja yayi da shuguwar mummy, har gabanta ya fadi tana Allah yasa ba Xeey ya tinoba,
Zuwa mummy tayi ta zauna kusa dashi tace my love meke faruwane naga kana tsaki, " Ismail yace wallahi mum number din frnd dinnan nawane na kira naji be shiga shine abun ya batamun rai, Mum tace eyyah sorry kuma bakasan address dinsuba ko?
"Ismail yace wlhi mum da na sani zuwa zanyi direct saidai ya ganni, mummy tace Hakane kaka damu please, Ismail yace lol mummy bazan damuba tunda muna gari daya sure wata rana Zamu HADU.. Tace Hakane nan DAI ya gama shan coffee dinshi ya fito wake zai zaga gari,
_yana fitowa yaga normal joint din da suke tsayawa da Xeey wani hawaye ya zubo mai nan danan yaji kanshi ya fara ciwo, be samu yaje inda zaijeba ya dawo gida ya kwanta kanshi Nata ciwo
*Ummie Xeey CE*
[1/3, 8:30 AM] UⓂmiey Xeey👄: *_ ∆°°••~❣_💞••💙💓❤💛
*A DALILIN MATAR*
*UBA*
*_ ∆°°••~~❣_💞••💙💓❤💛
```STORY & WRITTEN BY```
*Ummiey_Xeey Abakson💋*
*♻EXCLUSIVE WRITER'S FORUM*
[ɦօʍɛ օʄ քɛaċɛ, ɦօռօʊʀ aռɖ sʊքɛʀ աʀɨtɛʀ's]
*LIKES AND DROP YOUR COMMENTs*
FB..#https://www.facebook.com/Exclusive-Writers-Fans-E-W-F-1922297541423276/
```SADAUKARWA GA____```
*MARIAM TIJJANI ADAM😍*
*so sorry dear fans for d delay nd long suspence,in shaa Allah it has come to an end,u will be seeing my updates regularly luv u oll.💙💚💛💗💞❤🖤*
*PAGE📄 57__58*
"kamar a mafarki ta ganta a dakin da bata san ya akayi ta shiga ba, lumshe idon ta tayi tana son recall din wani abu amma ta kasa mintsinin kanta tayi taji ko mafarki take amma ina, K'ara kallon dakin tayi dakyau sannan ta kwanta lamo a gado kamar me tinanin wani Abu, tasan dai nan ba gidansu bane, Mummy ce ta shugo dakin taganta a kwance, tana ganin mummy ta taso kamar zatace wani Abu amma setai shuru, rungume mummy tayi ta fara kuka,
"mummy CE tace ikon Allah, it seems like yarinyar nan ta sama sauki fa, phone dinta ta dauka tai dailing number dady, take sanar dashi ci gaba da aka samu na Xeey, "dady Alhamdulillah yace, sannan yace tana magana kuwa? Mummy tace a a batayi,
"Daddy yace alright zanma yaron nan magana (yayan afrah) kuje psychiatric a duba kwakwalwarta, nan sukai Sallama yace soon zaidawo
Wani saurayi nagani a office yana shingide yana kallon cilin, phone dinshi naji tayi k'ara naga yana dubawa yaga *Beloved Dad* jikinshi na rawa yai picking, yace hello dad, dad yace "my son kana lafiya, ya aikin? Yace Alhamdulillah dad, yace to madallah, dama inasone idan Kaje gida zakui magana da mummy akan wannan yarinyar, tana samun sauk'i, amma bata magana, may be matsalar daga kwakwalwartace
"Matashin yaron nan yace" wallahi dad kamar ka shiga zuciyata, insha Allah zamui kokari, duk yanda ake ciki zan sanar dakai, Dad yace " nagode my son Allah ya k'ara daukaka ya tsaremunku, Yace Ameen
Bangaren Isma'il kuwa tun da ya koma school ya cire wata XEEY a zuciyarshi, bawai be tinanin ta bane aa, kawai, beso ya sama problem a heart dinshi sai yasa kome yakeyi da yaji XEEY tayi crossing zuciyarshi sedai yaita innalillahi wa inna ilaihi rajiun, Ba laifi yanzu ya kusan 1 Month a school amma kana ganinshi kasan yayi kyau yayi kiba har Yar haske yayi lolx _Hahaha INA masoya Wai shin da gaske SO mugum abune ne???_
__Misalin karfe bakwai na dare ne yayan Afrah ya dawo daga wajen aiki, yana shuguwa ya sama su mummy da xeey a pallow, nan shima ya yada zango, ya gaishe da mahaifiyarsa sannan ya shiga kitchen ya dakko abincinsa yaci yasha, sannan suka fara magana da mummy akan cewa Gobe insha Allah Zasu tafi asibitin psychiatric aduba kwakwalwar Xeey, Mummy tace Alhamdulillah, Allah ya kaimu, nan ma suka kira Afrah suke sanar da ita duk halin da ake ciki
"Afrah taji dadi so sai, tace Allah ya temaka Yakuma rufa asiri, mummy tace Ameen
Bangaren Hajiya Sa'adatu kuwa, tun randa akafara ma xeey addu'o taji ajikinta karshenta ya kusan zuwa, Dan yanzu kome ta tambaya Alhaji setayi da gaske yake bata, kuma shi kanshi alhaji yanaji a jikinshi kamar he's missing something, se zaiyi magana kuma ya kasa
Yanzuma kwata kwata Hajiya yalwa sunyi fada da Sa'adatu Dan tun wani kudi da Alhaji ya bata, yalwa ta nema su raba tare, Sa'adatu tace itafa atafau bazasu rababa, ita da shan wuya
Sannan tace wani su raba kudi tab bazata yardaba, tun daga lokacin Sukai hannun Riga....
*WASHE GARI*
tun safiya suka tashi suka fara shiri, misalin karfe 8, yayan Afrah ya kintsa yace su fito, xeey ma ta shirya da mummy sannan suka fito harabar godin, yayan Afrah ya shiga mota sannan suka suka shiga, Ya kama hanya sai asibiti,
Sunje bada ddewaba, aka dubata aka bata magungunan, Dr din yace brain dinta ya sama problem sosai amma da temakon Allah insha Allah zatai magana, ya basu wasu magunguna sannan yace su dawo bayan sati biyu, sukai mai godiya sannan suka kamo hanya
__Suna hanyane kowa da abun da yake sakawa a zuciyarshi, "yayan Afrah yana driving kenan yaga kamar giftawar mutun nan ya tsaya da driving, da mummy da shi se Fadin *INNALILLAHI WA INNA ILAIHI RAJIUN SUKE*
"wani wawan birki yaja, mummy kam duk a rude take, Wani tsohu suka gani yana musu smiling, yace kar Ku tsorata, nima mutun ne kamar Ku, Amma Allah yamun baiwa in bazaku damuba kufito a motar, dukansu ba Wanda yaji tsoro suka fito a motar...
_Ku biyoni Dan jin yanda labarin zai kasance_
*Ummiey Xeey Abakson*
[1/3, 8:30 AM] UⓂmiey Xeey👄: *_ ∆°°••~❣_💞••💙💓❤💛
*A DALILIN MATAR*
*UBA*
*_ ∆°°••~~❣_💞••💙💓❤💛
```STORY & WRITTEN BY```
*Ummiey_Xeey Abakson💋*
*♻EXCLUSIVE WRITER'S FORUM*
[ɦօʍɛ օʄ քɛaċɛ, ɦօռօʊʀ aռɖ sʊքɛʀ աʀɨtɛʀ's]
*LIKES AND DROP YOUR COMMENTs*
FB..#https://www.facebook.com/Exclusive-Writers-Fans-E-W-F-1922297541423276/
```SADAUKARWA GA____```
*MARIAM TIJJANI ADAM😍*
Chapter Navigation
Use this section to move to any chapter without going back to the top.