Romantic Hausa Novels

A Dalilin Matar Uba Part 1 Complete Hausa Novel

Reading file: A_Dalilin_Matar_Uba_Part_1_Complete_Hausa_Novel.txt

Chapter 16 of 35

*PAGE 67__68*

"Mariam kam tinanin waye take, Dan ji tai gabanta na ta faduwa, hajib ta danko ta saka sannan ta fito taje waje Dan ganin waye!!!
Isma'il kam yana tsaye a waje se tinani barkatai yakeyi ji kawai yai an bude gate, daga kan Da zaiyi sukai four eye's da Mariam, ba shiba har ita seda kwalla ya fito ma kowanninsu

Karasawa tayi a hankali ta kalleshi tace" Isma'il dama kana Raye? Zan sake ganinka, Isma'il wani ajiyar zuciya yayi sannan tace *aunty Mariam* Baki fushiba, wallahi tun da na tafi school ko na dawo tsoron zuwa nake kar inji mummunan labari,

Mariam tace" Allah sarki ai da ka dinga zuwa wallahi, Isma'il yace uhm bazaki ganeba ya labarin Zainab fa (Xeey)

Mariam tace uhm mu shiga daga ciki wannan labarin bana tsaye bane, ko gaisawa ba bamuyi ba, Isma'il yace ohh INA kwana, ya kwana 1000, tace Alhamdulillah mu shiga dai daga ciki, sannan suka shiga, tana tafe yana binta a baya, koda suka shiga cikin dakin drinks ta kawomai, yace" Aunty yaushe zan Iya shan wannan banji labarin inda xeey Tah takeba, Mariam " tace karka damu, sannan ta dauka phone dinta kirar infinix ta kira *Mijinta* Take sanar dashi Isma'il din Xeey fa yazo, tace Allah sarki, ki gaisheshi, duk yanda kuka tattauna idan nadawo zanji, tace" OK sannan ta kashe phone din

Wani Jan numfashi tayi tace" Isma'il, shi ha kalinshi ma gaba daya yana can wani wajen yana tinani, yace" Ammm Aunty, yanda ya amsa ya bata tausayi amma seta share!

Isma'il ne yace yaya dai aunty har yanzu ba labarin Xeey ko?
Mariam ta fara magana kamar haka, Isma'il wallahi kasan dai halin da ma tafi ka barta, Wannan *matar uban* babban makirace wannan abun ba wai na hankali bane, Asiri tai ma kowa na dangin Alhaji, Dan rannan ma naje gidan mahaifiyarshi tace rabonsu dashi har sun manta, kaga kenan Xeey se yanda Allah yayi!!

Wani Jan numfashi shima yayi, yace ya Salam, yanzu kema Baki da labarin xeey kenan, Tace" wallahi kuwa yanzu sedai muita addua Dan kwanan nan INA yawan mafarkinta,

Isma'il yace" ya Allah ka bayyanar mana da baiwarka, idan kuma ta mutu, ya Allah kajikanta da rahama, Mariam ta amsa da Ameen
Ta k'ara da cewa kaga da duk time din da suka kashe mahaifiyar xeey an Tona mata Asiri da ba haka, Isma'il yace lol aa mu barta, k'arshe da zaizo da yardan Allah, ahaka dai suka taba hira, sannan suka CE zasu jajirce wajen nemo xeey da kuma adduan Allah ya bayyanata, Ameen

Bayan sun gama maganar ne sukai Sallama, Isma'il kamar yasa kuka Dan baijin dadin komai a rayuwarshi, just imagining yake yanda rayuwarshi zata kasance ba tare da xeey ba, dakyar ya Iya daga kafa yazo wajen motarshi, Dan wani jiri da ciwon kai yakeji, Mariam ta lura da Hakan amma ta dake, tace mai kawai karya damu, yai murmushin karfi Hali yace insha Allah aunty, sannan ya shiga cikin motarshi

Yana driving ne yaji wani sanyi ya kamashi, idonshi sun kankance kamar Wanda yasha kuka, nan danan ya sama wani waje yai parking, jikinshi ba inda be rawa, ganin bame temakonshi ne, kuma beso mummy tasan halin da yake ciki idan ya kona gida, ya daure ya ya tada motar, Tafiya kadan yayi ya sama wani chemist, yai parking ya shiga akai mai alkurai, aka bashi maguguna, sannan ya tada motar shi be zarce ko inaba se gida
Yana shuguwa, suka hada ido da mummy dukda beda lafiya karfin hali yayi yayi ya sake mata wani murmushi yace" my sweetest mum, ganin yana cikin fara'ane itama hankalinta ya kwanta tace Allah yasa andace my love

Yace" Wallahi mummy a a amma insha Allah za'a dace tace" Allah yasa yace Ameen Hajiya ta, nan ya zauna yaci abincin rana dukda yanajin zazzabi ya daure yana shiga daki magani yasha ya fara bacci....! Wannan kenan

Alhaji (Mijin Mariam Tijjanj) bayan ya dawo suna zaune a pallow suna nunawa junansu soyayya, Alhaji yace yauwa madam ya kuka karke da Isma'il nan ta kashe duk yanda sukai da Isma'il, mijin Mariam yace" Allah sarki wallahi tausayi yake bani, Allah ya bayyanata tace Ameen...nan na barsu sunata soyewa!!!!

Ummiey Xeey Ce
[1/3, 8:30 AM] Uβ“‚miey XeeyπŸ‘„: *_ βˆ†Β°Β°β€’β€’~❣_πŸ’žβ€’β€’πŸ’™πŸ’“β€πŸ’›
*A DALILIN MATAR​​​​*
*UBA​​​​*
*_ βˆ†Β°Β°β€’β€’~~❣_πŸ’žβ€’β€’πŸ’™πŸ’“β€πŸ’›

```​​​​​​​​​​​​STORY & WRITTEN BY​​​​​​​​​​​​```
*​​​​Ummiey_Xeey Abaksonβ€‹πŸ’‹β€‹β€‹β€‹*

*​​​​♻EXCLUSIVE WRITER'S FORUM​​​​*
_[ɦօʍɛ Φ…Κ„ Φ„Ι›aΔ‹Ι›, Ι¦Φ…ΥΌΦ…ΚŠΚ€ aΥΌΙ– sΚŠΦ„Ι›Κ€ Υ‘Κ€Ι¨tΙ›Κ€'s]_

*​​LIKES AND DROP YOUR COMMENTs​​*
FB..#https://www.facebook.com/Exclusive-Writers-Fans-E-W-F-1922297541423276/

```SADAUKARWA GA____​​​​​​​​​```
*​​​​MARIAM TIJJANI ADAMβ€‹πŸ˜β€‹β€‹β€‹*

Dedicated to my dear mamieys... *Aishan Umma, Aisha a muhd And Aysha yar'adua*
_...Allah ya saka muku da alheri, Allah ya biyaku duniya da lahira, Allah yasa Ku fi haka, INA sonku irin Baki bazai Iya fada dinnan ba_ *Team Ana tare*

Chapter Navigation

Use this section to move to any chapter without going back to the top.