Romantic Hausa Novels

A Dalilin Matar Uba Part 1 Complete Hausa Novel

Reading file: A_Dalilin_Matar_Uba_Part_1_Complete_Hausa_Novel.txt

Chapter 17 of 35

*PAGE 69___70*

Afrah ce ta tashi tun safe ta gama shirya kayanta tsab ta ajiye waje daya, sannan ta nufa camp dinsu sukaje akai POP Dan yau suke gama service dinsu, bayan sun gamane, nanfa yan mata kowa se Ciro waya yake anata daukar selfie, sunyi kyau matuka

Wata kawar Afrah CE tsaye tace" kai Afrah naga se sauri kikeyi ko irin damuwar zamu rabu dinnan bakiyi

Afrah ce tace" uhm damuwata tafi wannan insha Allah zamu dinga waya kuma one day I'll visit you, frnd din tace" Hakane Allah ya Barmu tare tace" Ameen
Afrah ta kalle ta tace kinsan yau in fa zanje gida, frnd din tace kai Afrah halin ki sai ke, Baki bari gobe mu tafi? Afrah tace" bazaki gane bane I'm eager to go home, frnd din tace uhm home girl, shikkenan, Allah bamu alheri sai mun hadu Afrah tace Ameen,

Koda Afrah tazo lodge dinsu bata tsaya yin komai ba yara ta samu suka tayata fito da kaya, sannan ta sama me adaidaita sahu yakaita gareji, tana zuwa tai sa'a saura sit din mutun daya aiko ta shige, mota ta fara Tafiya sejin dadi yakeyi...!

"Suna hanyane ta kira bro dinta a phone ya dauka, tace" bro guest what? Yace mene ne tell me, tace uhm I'm on my way, zare ido yayi yace kai sisto Baki bari ko gobene ki dawo, tace" uhm bazan iyaba I'm eager naganku, bro yai smiling yace aww Ashe ma kinsha missing dinmu m tace" Sosai ma, zaiyi cutting din calk din kenan tace bro! Karka fadawa kowafa sedai su ganni unexpected, bro yai dariya yace to sisto Allah ya dawo dake lafiya tace Ameen!

Tafiya suke amma hankalinta duk yana gida dan ta kosa su Isa
***********
Mariam ne zaune a daki tai tagumi ta rasa meke mata dadi, intact tama rasa yanda zata bulluwa wannan al'amarin, hawaye ta farayi sai wata zuciya tace meye kuma na hawaye, Nan danan ta share, sannan ta dakko waya ta kira wani malan akan a tayasu da addua, malamin yace addua kullun munayi, inaji a jikina yarinyar nan tana Raye, so ki kwantar da hankalinki, Mariam tace to malan nagode, nan ta dauro alwala tazo tai sallah raka'a biyu ta karanta Al'qur'ani me girma tai addu'o'i sannan ta sama wani natsuwa da farin ciki kamar ance mata anga Xeey lolx...

Bangaren Sa'adatu kuwa, yau alhaji ya dawo, tana shirin mai wani makirci, ta taso da wani rangwada, tazo tamai oyoyo, kallo daya ya watsa mata, shi besan ma yayi ba Dan gaba daya hankakinshi ba'ajikinshi yakeba, kallon da yai mata yasa Sa'adatu makalewa a kujera ba un ba un'un a tinanin ta ko Alhaji ya gane abun da yakeyi ne... Haha. Ranar wuni tayi tana zullumin abun da zai biyo baya, Dan tayi saranda taji ne Alhaji zaice, sai taji tsit..

Washe gari nayi, Alhaji na fita office, Sa'adatu tasa kafa ta fita wajen boka Dan a hassala take wai boka be mata aiki dakyau, taga alhaji na mata wani gani gani, tana zuwa ta sama boka ta fara mai masifa wai ya zai bata mata shiri, duk mak'udan kudin da take kawomai, boka kallonta yayi ya kashe da dariya yace" tunda haka kikace karki sake dawowa mun sallameki, kuma duk inda kikaje baza a taba miki aikiba

Nan danan idon Sa'adatu ya yi jajur tana ta rokanshi yace ina, ya gama magana, fitar mai ko ya bata mata rai, haka ta tafi gida jiki duk a sanyeye tana ta shiga uku!

Sa'adatu na zuwa gida kawarta ta Kira, yalwa "tace" kema in banda abunki Taya zakima boka haka, tirkashi, Allah ya kyauta, Sa'adatu tace" yanzu ba wani temako? Tace" ai kinji me ya fada ko INA kikaje baza ai miki aikiba ni ba ruwana ta sake wayan!

Sa'adatu tace ta shiga uku, kasa zama tayi ae up and down yakeyi a tsakar pallow, data gaji ta zauna tai tagumi tace" ya zanyi yanzu ni Sa'adatu.....!

**••••**
Afrah nagani wani me adaidaita sahu ya sauketa a kofar gidan su, knocking tayi gate man yazo ya bude mata, yana ganinta ya fara yan bautar kasa andawo lafiya? Afrah tai murmushi da dimple dinta ya fito tace " wallahi kuwa, me gadi yace" Masha Allah sannan ta shige cikin gidan

Tun daga kofar Pallow Afrah ke kwalla ma mummy kira, jin kirar yai yawane yasa xeey fito wa Dan ganin waye!!!

Ummiey xeey
[1/3, 8:30 AM] UⓂmiey Xeey👄: *_ ∆°°••~❣_💞••💙💓❤💛
*A DALILIN MATAR​​​​*
*UBA​​​​*
*_ ∆°°••~~❣_💞••💙💓❤💛

```​​​​​​​​​​​​STORY & WRITTEN BY​​​​​​​​​​​​```
*​​​​Ummiey_Xeey Abakson​💋​​​*

*​​​​♻EXCLUSIVE WRITER'S FORUM​​​​*
_[ɦօʍɛ օʄ քɛaċɛ, ɦօռօʊʀ aռɖ sʊքɛʀ աʀɨtɛʀ's]_

*​​LIKES AND DROP YOUR COMMENTs​​*
FB..#https://www.facebook.com/Exclusive-Writers-Fans-E-W-F-1922297541423276/

```​​​​​​​​​SADAUKARWA GA____​​​​​​​​​```
*​​​​MARIAM TIJJANI ADAM​😍​​​*

*Wannan shafin sadaukarwace ga duk wace mace me SUNA ZAINAB🍇🍇*

Chapter Navigation

Use this section to move to any chapter without going back to the top.