Trending Hausa Novels

Sakar Makafi Littafi Na 3 Complete Hausa Novel

Reading file: Sakar Makafi Book 3 Complete Hausa Novel.txt

Chapter 10 of 31

By
*GARKUWAR MARUBUTA**SAƘAR MAKAFI*
Page 97
Na
*Aysha Aliyu Garkuwa*

Assalamu alaikum jama'a ta jama'ar arziƙi fatan muna lfy ya gida da yaranmu.
Matan alkhairi mata masu duniya, akwai garaɓasa fa ta musamman da na watannan na maulud promo haɗine na musamman kashi da ban da ban, akwai naku na manyan mata, da kuma amare bazaaawara ko budurwa, da masu joge ɗanyen jego ko barden jego.
08069423567 gata inda zaku yi min magna ta WhatsApp,
Set É—in kayana mataki biyu ne.
Na forƙo daga 40k ne zuwa ƙasa shine ƙananan 40k 35k 30k 25k 20k 15k 10k Akwai Maganin Infection sadidan yar uwa ba haufi, shi kuma set 10k.
Sai kuma manyan set É—in hajia taho kiji daga 50k 60k 70k 80k 90k 100k 120k 130k 140k sa sha kundum uban makiya 150k ne yar uwa.
HaÉ—ine na musamman.
Kana akwai kayayyakin turaren wuta dasu Humra da kulacca suma haka farashinsu yake.

Idan kin sayi kaya in dai set É—in kayanki yakai daga 50k 60k 70k 80k zan biya miki rabin kuÉ—in Delivery, daga 90k 100k 120k 130k 140k 150k to free delivery ne, Ni zan biya Miki.

0005388578 Jaiz bank Aisha Aliyu Garkuwa.

*SAƘAR MAKAFI*
Page 97
Na
*Aysha Aliyu Garkuwa*

"Yah Naser ina son zanje gidan Aunty Rashida nefa ba gida zan komaba kuma kaga tafiyar da nisa”. Fuska ya tsuƙe hadi da cewa. "Ke shiga mu tafi kina ɓata min lokacin fa ba inda zakije sai kin warke”. Ganin yadda yayi mgnar cikin haɗe fuska ne yasa ta shiga.
Suna isa gida ko kashe motar baiyi tana fita ya juya ya fita.
A hankali ta jingina da jikin motar Baba Malam tana mai kallon motar dake gefe wacce bata santaba.
ÆŠan tsugunawa tayi dan jirin da take É—an ji, wayar Mahmoud ta zaro a jakarta, kiran Amina ta gani har 3 sai kuma miss call É—in Saddiqa da text message É—inta É—aya text message É—in ta buÉ—e.
"Ban sani ba ko kina tare da Mahmood, ga Amina tazo, Mamy nata kiran Yah Nasir ta gaya masa kiyi maza ki dawo tana kiransa baya ɗagawa kiyi sauri ki dawo kar ta gane”.
Tana gama karantawa ta miƙe ta nufi cikin gidan.
A parlour ta samesu Mamy na ganinta tace.
"Shike nan ma gata ta dawo ina Nasir ɗin ya wurgar da wayarsa ne”. Tana isa gaban Aunty Amina data tashi tsaye rungumeta yayi tare dasu Zaid dake jikinta.
“Allah sarki Fariyda kina kewarmu yadda muke kewarki kuwa.” suna zama Fariyda ta lumshe idanta tace.
"Aunty Amina kullum sai na tunaki hakama su Ummi”. Idon da Mamy ta kafeta dashi ne yasa tayi shiru. Aunty Saddiqa data miƙo mata goran Admiral ta kalla tare da amsar goral ta ɓalle marfin tasa a baki.
Har lau Mamy ido ta zuba mata kamar mai son gano wani abun.
Aunty Amina tace.
“Autan Ummi yace min baki da lfy, su Hafiz ma da suka zo Huzaifa yace min Mom Aunty Fariyda bata da lfy ta rame ta zama shiru-shiru”. Sassayar gyatsa tayi haɗi da gyara zamanta tace. "Zazzaɓi nefa kawai kuma shi Alhamdulillah da sauƙi”. Cikin kulawa tace.
“Allah ya ƙara sauƙi su Ummi sun gaisaki”.
Amin Mamy da Saddiqa suka faÉ—i.
Amira ne ta fito daga kitchen ɗin Mamy riƙe da wormars a kan table dake gabansu ta jera.
Shigowar Aunty Amarya da Aunty Sadiya ne yasa parlour kacamewa da hira. Amira ne ta zuba musu abinci, basu tashi ba har Saida aka kira azahar. A hankali Fariyda ta miƙe da hand bag nata a hannun ta bedroom ta wuce tana faɗin.
"Aunty Amina ku gama cin abinci ku shigo muyi salla”. Tana kallon Saddiqa data ƙara musu abincin tace.
"Toh”. Tana shiga bedroom ɗin kiransa na shiga wayarta, da sauri ta maida ƙofar ta rufe haɗe da zaro wayar ganin kiran layin Yah Amin da yayi saven nashi da My blood yasa ta amsa kiran tare da zama kan gadon murya a narke ta amsa kiran sunanta da yake yi a hankali.
“Farriyhah! Babe! My Angel!!”. Ido a lumshe tace. “Na'am Appiyn menene?”. Murya a karye yace. "Ina sonki ina son ganinki please ki taimaka min mu haɗu a asibitin”. A hankali tace.
“Ai naje ma har na dawo”. A hankali ta sauƙe numfashi mai sanyi jin yadda ya saki numfashi mai haɗe da sheshheƙa murya na rawa yace. "FARRIYYHAH ya zaki min haka meyasa baki kirani ba, bazan iya bafa na fara gazawa so kike in kai kaina ga halakane ji nakefa kamar marata zata fashe wlh komai na iya faruwa dani”. Ya ƙare maganar murya na rawa, a hankali cikin tausayawa tace.
“Appiy nimafa ina son ganinka to amman bani da yadda zan yi, ina gayawa Mamy zanje asbiti kawai ta kira Yah Nasir da sassafe yazo muka tafi asbitinsu koda aka gama min nayi nayi ya barni in taho ni kaɗai yaƙi yace Mamy tace ƙafata ƙafarsa wai duk nayi lagwai-lagwai kar inje in faɗi a hanya saida ya dawo dani gida, ban shigaba na tsaya zan kiraka kuma sai Aunty Saddiqa tace min Aunty Amina tazo shiyasa na shiga gida ban kirakaba sai yanzu na shigo ɗaki akan zan kiraka kafin inyi salla kai kuma ka kirani nima ina son ganinka ina son gaya maka wani abu ina son in ganni kusa da kai ina son inji ɗumin jikinka shine kaɗai naji ya cire min sanyin da nakeji ranar da kazo”. Ta ƙare maganar cikin narkekkiyar muryar mai tafe da sautin sassayan kuka, hakan yasa jikinsa mace wa cikin ɗimuwar jin tana kuka da son sanin halin da take ciki yace. “Farriyhah kina sona? Kina son rayuwa dani? Kinyi missing na? Kina son Papi kusa dake? Please Farriyyhah tell me”. Murya a narke tace. "Yesss Appiy to amman ya zanyi Abba baya son zamanmu tare Mamy ta hanani fita”. Numfashi mai zafi ya fesar cikin nemo mafita da madogara yace.
“So sorry my Angel stop crying My Happiness in sha Allah zan yi maganin matsalar mu in this week wlh zamu rayu a tare babu abinda zai rabamu bana son jin kukan ki, kiyi haƙuri in sha Allah zakiji ɗumin Appiyn ki, gaya min me likita yace meke damunki”. Tana sauƙe sheshheƙan kukan tace.
"Maleria ce kuma sun bani magani nasha”. Cikin jin gamsuwa da shawarar da zuciyarsa ta bashi da gamsuwa da ita yace. "Dole nemafa ki kasance kusa dani, na sanki bakya son shan magani, ina tsoro kar ciwo ya illata min ke, Please babe dan kin sha maganin?”.
Cikin sanyi tace.
“Nasha Mamy ta bani ai”. Cikin rashin gamsuwa yace. "Okay ba matsala tashi kiyi salla”. Bayan sun idar da salla ne sukaci gaba da hira har sai ƙarfe biyar Aunty Amina tace.
"Zan tafi.”
Aunty Saddiqa tace. “Tun yanzu”. Tana miƙewa tsaye tace.
“Yamma tayi gashi zan biya in ɗauko Hafiza”. Fariyda ne tace. "Tana gidan su Ummi ne”.
Amina tace. "No wai birthday party ɗin ƙawarta Zahra Muhammad manga taje, kuma bazan barta ta kai dare ba”. Kai Saddiga ta jinjina ita kuwa Fariyda a hankali ta ɗan jingina kanta jikin kujera haɗi da lumshe idonta, numfashi mai nauyi ta fesar haɗi da gyara zamanta dan tunaninta ya hasaso abinda yake burin Yah Amin kafin mutuwarsa.
Daga nan suka raka Aunty Amina har wurin motarta.
Ummi ne ta kalli Samira dake ta murna tsugune gaban Mahmoud dake tsaye bisa dukkan alamu alwala yayi kuma da shirin fita yake dan ga car key a hannunsa.
Cikin girmamawa tace.
“Uncle Mahmoud ngd matuƙa Allah ya saka da al'khairi Babana ya yarda zanci gaba da karatu yace min kaine kayi kishi magna kuma in sha Allah ba zan baku kunya ba”. Yana gyara zaman hular kansa Ba yabo ba fallasa yace. "Bani zaki godewa ba, ki godewa Allah da Auntynku Farriyyha itace ta matsa ni banma san bakici gaba da karatuba sai da ta gaya min”. Ido Goggo Dada ta zuba masa hakama Ummi sai kuma suka kalli juna yana kallon Huzaifa daya fito kitchen da plate a hannunsa cike da indomie kwaffa yayi yace.
"Ka kusa tafiya Qatar acan zakaje kayi karatu na gama komai saura fitar visa ɗin ka, kaje can zafin ƙasar tasu zai narka maka uban kitsen da yasa maka teɓan nan tea ya koroshi waje da sintirin karatu”. Cikin kwaɓe fuska yace.
"Uncle ni wlh Istanbul nake so ko Canada”. Yana kallon Hafiz da yake amsar plate ɗin yace. "Ai sanyi zai ƙara kumburaka ka fashe a waɗannan ƙasashen”. Dariya Hafiz ya saka harda riƙe ciki sai kuma yayi maza yayi shiru.
"Ummi zan tafi”. Ya faɗa yana jiran addu'arta. Ummin tace.
“Allah ya kiyaye hanya”. Ummi ya faɗa Goggo Dada tace. "Gidan Salim zaka jene dan tun ɗazu da suka fita shida Sulaiman ban kuma jinsu ba”. Ummi tace.
"A'a ai gidan Amina suke sunje suga kayan lefen Sulaiman ɗin ne kinsan tace ta gama haɗa komai”. Bai kuma ce musu komai ba ya fita.
Bayan an idar da sallan magrib ne Baba Malam da ya juyo a hankali yana fuskantar sahun forko cikin mamaki yake kallon Mahmoud dake cikin sahun forkon a kuma saitin inda yake haka yasa suna fuskantar juna gaba da gaba, kanshi na ƙasa yake tasbihi kamar yadda kowa keyi hakan yasa shima Malam yaci gaba da yin tasbihi.
Koda akayi addu'a cikin natsuwa duk kowa ke miƙewa yana yin nafila.
Koda suka gama da yawa sun fita cikin Masallacin sai kaÉ—an daga cikin wasu na tasbihi hasu kuma qur'ani mai girma suka É—auka suka fara karatu dan jiran lokacin sallan isha, haka shima Mahmoud Qur'anin ya É—auka ya fara karatu.
Malam kam carbinsa yake ja cike da mamaki yake kallon Mahmoud É—in jifa jifa.
A haka har lokacin isha'i yayi. Bayan an idar da sallan isha duk mutane sun fita sai kaÉ—an masu yin shafa'i da wutiri suma duk sunyi.
A hankali ya ɗan ƙara matsowa kusa da Malam ɗin lokacin da yaga baifi mutum uku bane suka rage cikin Masallacin suma kuma suna can nesa dasu.
“Balam Barka da dare”. Ya faɗa cikin sasssyan sautin mai cike da girmamawa haɗi da rusunar da kai. Cikin kulawa Malam yace.
"Barka dai Mahmoud gida duk lfy ko”. Cikin sanyi ya girgiza masa kai alamun a'a ba lfy. Da sauri Baba Malam ɗin yace. "Subahallahi meke faruwa wani ne ba lfy ina Abbanku”. A hankali ya kuma ɗan yunƙurowa ya durƙusa kan guiwowinsa kai a sunkuye murya na rawa tafe da sheshheƙan kuka yace.
"Baba Malam nine banda lfy”. Cikin kaɗuwa jin muryar sa na rawa alamun kuka yace.
"Subahallahi Mahmoud meke damunka?”.
Sheshheƙan kuka mai sanyin ya saki hawaye na kwaranyo masa har suna ɗisa kan cinyoyinsa a hankali yasa hannunsa ya riƙo hannun Baba Malam da suka fara rawa dan fargabar ganin Mahmoud na kuka ya sashi tsoro, ido ya zuba masa jin ya fara magna murya a karye yace.
“Baba Malam banda lfy ina bukatar matata kusa dani.
Please Malam dan girman Allah da Manzonsa kuyi haƙuri kaida Abba ku taimaka min ku bani matata wlh ina cikin wani yanayi. Malam nifa ban saketa bafa ina son matata itama tana sona Malam kada ku rabamu, dan girman Allah kubani matata ina muradinta kusa dani zan cutu in babu ita kusa dani”. Tunda ya fara mgnar tsoron Malam ya juye ya zama kunya mai tsananin hakan ya haddasa masa kafewar yawun baki jin Mahmoud yaci gaba da faɗin.
"Please Malam dan girman Allah da Manzonsa kada ku rabamu kun sani aure sunnane na Manzon Allah Please ka yarje min in ɗauki matata Malam ka yarda?”.
Cikin sanyi Baba Malam yace.
“Eh na yarda kazo ka ɗauki matarka in har Mahafinka ya amince maka, kaje kayi magna dashi Mahmoud ni bani bane na hanaka matarka mahaifinka ne, dan haka kaje ka sameshi in dai har ya amince maka kazo ka ɗauki matarka da sanya al'barkarsa da amincewarsa ni bazan hanaka matarka ba”. Cikin farin cikin da ya danne jin fargarbar Abba bazai yardaba yace.
"Malam Ngd Allah ya ƙara girma, zanje in sameshi zan bashi haƙuri ya bar min matata”. Cikin dottakun ya fara yi masa nasiha mai ratsa jiki akan darajar aure da matar mutum da nuna masa illar abinda yayi a baya, ya ɗaura da mishi nasihar yabi umarnin mahaifinsa nayiwa iyayensa biyayya ya auri Jidda tunda haka Abbansa ke so”. Cikin sauri ya fara jujjuya kai murya cike da damuwa yace. "Malam bazan iya yiwa Farriyyhah kishiya ba, kuma bana son Jidda na tsaneta Malam Farriyyhah kawai nake son rayuwa da ita a matsayin matar aurena”. Da sauri Bana Malam ya fara jujjuya mashi kai cikin haɗe fuska yace.
“Idan dai har kana son Mahaifinka ya baka damar dawo da Fariydan to nasan tabbas sai ka yarda zaka auri ƴar ƙaninsa in kuma kace bazaka auri Jidda ba nasan shima bazai barka ka da Fariyda ba, sai ka zaɓa, zama dasu su biyun duka ko kuma ko kuma ka rasa Fariyda kuma nasan dolen dole zai aura maka Jidda ba yadda ka iya ka dai san waye mahaifinka ka sanshi farin sani duk kafiyarka da taurin kai baka kaishi ba, babu mai tankwari sai Allah kasan da haka ko?”. Manyan idanunsa da suka jazir ya lumshe haɗi da taune lips ɗinsa da ƙarfi cikin sauri yace.
“Baba Malam kunsanfa ina da matsala da gamayyar halittar fata, wlh Farriyyha ce kaɗai in fatarta ta taɓa tawa bana cutuwa, itace kaɗai nake kusanta ban cutuba, komai fa zai iya faruwa dani in na kasance da yariyar can”. A kausashe Baba Malam ɗin yace.

Chapter Navigation

Use this section to move to any chapter without going back to the top.