Trending Hausa Novels

Sakar Makafi Littafi Na 3 Complete Hausa Novel

Reading file: Sakar Makafi Book 3 Complete Hausa Novel.txt

Chapter 9 of 31

By
*GARKUWAR MARUBUUTA*https://chat.whatsapp.com/F93CYFGSIWA3ewhl8cCAYW
Barkanku da zuwa zauren A.A GARKUWA FOUNDATION inayi mana fatan alkhairi, fatan wannan haɗakar tamu na taimako zata kaimu ga Jannatul Firdausi, *Ga Ramadan ya ƙarato mai akwai da mai niya, taimakon sadaka ga ma buƙata ciyarwa ko shayarwa in Allah ya hore mana kamar yadda muka yi last year ga account da zamu fara tara kuɗin ga mai niya 5843176522 Moniepoint Aysha Aliyu Garkuwa*
jama'ata kune ƙarfina, domin su jama'a Rahama ne, ba haushe yace hannu ɗaya baya ɗaga jinka, yan uwa ita sadaka bata yawa kuma bata kaɗan ko Naira 500, 1k 2k 3k 4k 5k har zuwa 10k 20k 50k 100k kai har 1million zuwa sama in Allah ya baka iko, kai koda Naira ɗarice kike bayar zamuyi farin ciki da ita, kuma ajiyace maidaraja, wacce Allah ne zai bamu sakamakonta kada ki/ka raina abinda ke hannunki domin manzon Allah S.A.W yace muyi sadaka koda da tsagin dabino ne! kada kuma muyi tunanin sadaka zata raunata dukiyar mu ko ta hanamu ci gaba, kada kuma muga sadalar tayi yawa in kina da hali ko 1M kika bayar akwai ma buƙatan da in za'a raba musu zasu iya neman ƙari ma. Kuma Manzon Allah yace, ita sadaka tana kashe masifa kamar yadda ruwa ke kashe wuta, Allah Ubangijin talikai shi zai yi mana sakayyar al'khairi da zamu wanzar duk ƙanƙantarshi, Allah ya bamu ikon haquri da zama da juna, Allah ya bamu ikon taimako, ya kuma sa mana a mizanin kyawawan ayyukanmu ya taimakemu fiye da yadda zamu ke taimakawa jama'a. mu haɗa hannu da hannu mu ciyar da mabuƙata a Ramadan. Afwan In nayi miki/maka wani kuskure cikin rashin sani da ajizanci na d'an adam a gafarceni🤝🙏🏻
A taimaka domin Allah

*SAƘAR MAKAFI*
Page 96
Na
"Aysha Aliyu Garkuwa*

Tsura masa ido yayi lokacin da ya isa front seat ɗin buɗe ƙofar yayi haɗi da masa alamun ya fito. Fuska ya kuma tsukewa cikin tafasar zuciya da tsanar jidda ke ƙara tunzurashi da tona masa zafin nesan tashi da matarsa da akayi murya a kausashe yace.
"Bazan shigaba dan bana son ganin yarinyarna na tsaneta Yah Ahmad ka gayawa Bappa Lawan bafa na son Jidda na tsaneta tsana mafi muni kar ya bari a haɗa auren nan, in kuwa suka bari aka haɗani zama da wannan mayyar yarinyar nan a inuwa ɗaya a matsayin mata da miji wlh tallahi zanyi abinda zai raba zumuncinmu zai haɗa faɗa da gaba a tsakanin iyayenmu bare kuma mu dan bana sonta!!!”. Ya ƙare maganar da ƙarfi haɗi da taune lip ɗinshi na ƙasa da dukan zucinyarsa da hannunsa na dama na hagu kuma ya dafe kansa.
Tamkar wanda aka dasa haka Yah Ahmad ya zama sai kallonsa yake ba ƙibtawa numfashi mai nauyi ya sauƙe jin Mahmoouud yana sauƙe wasu numfarfashi da sukafi kama gurnanin mayunwacin zaki a hankali ya maida idonsa kan Mahaifinsa da tunda yayi parking ya iso wurin bisa dukkan alamu daga masallaci yake a hankali yake jinjina kansa yana kallon Mahmoud cikin sanyin halinsa da natsuwa yace.
"Saƙon nakama ya isa inda ka aikeni ai Mahmood Bappa Lawan ɗin yaji da kunnensa”. Manyan idanunsa da sukayi jazir ya tsaida kan mirror ɗin motar, ido cikin ido sukayi da ƙanin Mahaifinsa cikin ko ɗar ya ɗan rusunar da kwayar idonsa kaɗan haɗi da ci gaba da taune lips ɗinshi.
Shi kuwa Bappa Lawan kai ya jinjina ba tare da yace musu komaiba yayi cikin gida.
Da sauri Yah Ahmad É—in yabi bayansa.
Washe gari da yamma gidan Baba Malam. Ido Mamy ta zuba wa uban kayan da Hafiz da Huzaifa suka jibge mata a tsakiyar parlour. Kayan masarufi ba abinda babu a ciki, ido ta maida kan roll ɗin Admiral dake gaban Fariyda a ƙalla sun kai goma manya shida ƙanana huɗu sai zuma mai kyau taceciya a gora 24. Aunty Saddiqa ta zubawa Fariydan ido tana kallon yadda take kwance kan 3 seatter tayi lip ta naɗe ido a narke sunyi wani kala na musamman su ba mai jin bacciba ba kuma mai mayeba ba kuma wacce idonta biyuba suna lumshe da alamun zazzaɓi da ɗan kasalar jiki. Numfashi ta fesar a hankali tace.
“Hmmmm masu abu da abunsu ba dai Admiral ba to gashi nan kisha kiyi wanka gashi kuwa harda zuma.” numfashi ta ɗan fesar haɗi da lumshe idonta sai kuma ta buɗesu a hankali ta sauƙesu kan Hafiz dake rungume da Zaid Huzaifa kuma na riƙe da hannun Zaitoon kan cinyarsa ya ɗaurata ya fara lasa mata zuma a baki. Mamy kam katton ɗin su Pasta indomie shinkafa ɗanye da gumi mai manja su maggi sugar madara millo Lipton coffee take kallo baki buɗe sai kuma ta kalli buhun da Hafiz ya ajiye can gefe na nama numfashi ta sauƙe a hankali tace.
"Ke Fariyda da Mahmoud yazo me kika ce masa da ya libgo wannan uban kayyakin ya turo mana”. Cikin sanyi da tsoro tace.
"Mamy wlh ba abinda nace masa nima ganinsu kawai nayi”. Kwaffa Mamy tayi ta juyo kan Hafiz tace. "Kai Hafiz duk wannan kayan na menene wai”. Yana murmurshi yace. "Mamy yace mu kawowa su Zaitoon nefa”. Saddiqa tace. "Su Zaitoon ne nama buhu guda shinkafa buhu buhu ai wannan ko bikinsu za'ayi iyaka kenan”.
Kai Mamy ta jinjina tace.
“Bari in kirashi inji dalilinsa”. Daga nan ta juya ta nufi parlour Malam inda nan ta baro wayarta.
Da sauri Hafiz ya miƙe haɗi da cewa.
"Kai Huzy tashi mu gudu kar mamy tasamu maida kayan nan, dan in muka maidasu Our Uncle zai karya mana agara”. Da sauri Huzaifa ya miƙe yana faɗin.
"Aunty Fariyda Mom tace in gaya miki ranar Tuesday zata zo”. Ya ƙare maganar yana bin bayan Hafiz kai ta gyaɗa mishi haɗi da cewa.
“Kujira Mamy kadafa ku tafi”. Da sauri Saddiqa tace. "Kuje kawai”.
Ido Baba Malam ya zuba wa Mamy har saida ta kai ƙarshen jawabin a hankali ya ɗanyi gyaran murya cikin dottakun yace. "To ai tunda yaransa na gidan nan bamu da ta cewa, tun basu kai haka bama kin san haka yake yi kuma ba yadda banyiba in hanashi yaƙi bare kuma yanzu da yake ganin harda matarsa na gidan”. Kwaffa Mamy tayi tace.
"Fariyda ce ta ƙulla dan naga harda Admiral ya libgo har katon goma kuma ita kaɗaice take shansa kwanan nan duk shine abincinta tunda take zazzaɓin nan in ba ta gaya minshiba ta yaya zai aikosu har haka”. Miƙewa Malam yayi haɗi da cewa. "Zanyi magna da Alhaji Umar”. Daga nan ya fita.
Da dare Saddiqa na goye da Zaitoon da taƙi bacci ta kuma hana Zaid ma baccin jijjigata takeyi tana ɗan zirya da ita daga ɗakin Fariyda zuwa parlour zuwa dannin har kitchen tana maƙale da wayarta a kafaɗa da alamu da mijinta take waya.
Fariyda ne zaune kan gadon ta ɗan jingina bayanta da jikin allon kan gadon a hankali ta gyara riƙon wayar tare dasa hannunta ɗaya ta jawo duvet ɗin ta rufe jikinta har zuwa kan ƙirjinta murya can ƙasan maƙoshinta cikin sanyin da zazzaɓin daren ya fara sakar mata tace.
“Appiy ni nace maka ina buƙatar wani abu ne to? Gashi yanzu Mamy tana ta fushi da hararata tana ganin kamar nice na roƙeka”. Ta ƙare maganar tana ɗan buɗe lumsassun idanta. Numfashi mai nauyi yaja haɗi da fesa mata sautinsa a kunnenta yace.
"Allah baice sai kin gaya min kina buƙatar abinci da sha ba kafin in kawo miki, wannan ai haƙƙi nane huruminane ni kaɗai Allah ya ɗaurawa haƙƙin ciyar dake da yarana bana buƙatar kowa ya ciyar min daku my happiness ninefa mijinki ko kin mantane”. Murya a narke tace.
"A'ah”. Yana yin miƙar dake nuna buƙatar ta kusa dashi yace.
"Babe in kin mantane inzo yanzu in tuna miki cewa ni mijinki ne ke matatace Allah ya halitta min kene dan inji daɗin duniya”. A sanyaye tace.
"No Appey ban manceba na sani ba sai kazo bafa”.
A hankali yace. "Farriyyhah dole zanzo fa dan ina muradinki kusa dani, kiyi haƙuri dan Allah ki barni inzo yau kwana biyar kenan fa, Please dan Allah ki lamuncemin inzo kamar yadda nazo ranar”. Cikin sanyin jin yadda yake mgnar da iyakar gaskiyarsa a tausashe tace.
"Atieyah kayi haƙuri bazan iyaba, inajin kunya”.
Da sauri yace.
“Kunya kuma Farriyyhah to waye ma zai san nazo”.
A hankali tace.
"Kunyar Malam da Mamy na wlh ranar mafa sun gane anan gidan ka kwana ni inagama Malam yaji duk abinda mukayi a mota wlh tun ranar har yau ban yarda mun sake haɗuwa ba inajin kunyar ganinsu”.
Gyara zamanta tayi haɗi yin ƙasa da kai tana mai gyaɗa masa kai jin Muryar da yake magna da itane yasata natsuwa.
“Wlh bazan iya jurar wannan horon da hukuncin Abba ba Farriyyhah zan iya yin komaifa dan samun kusanci da rayuwa dake dasu Zaid a inuwa ɗaya, bana son Abba yaga rashin kunyata a fili amman yana ƙureni ya fara kaini matakin ƙarshen da dole zan nuna masa ina buƙatarki kusa dani”. Ya ƙare maganar murya na rawa hakan ne yasa ta fara neman hanyar kauda zance da sauri tace.
"Laa Appiy na mancefa jiya Dr Fadil yayi ta kiranka, ban ɗaukaba sai kuma yau da safe naga ya turo maka IV aurensa next week zai auri wannan mayyar mazan Fadila”. Murmushi mai ɗan sauti yayi yana danne Papi ɗinsa yace.
"Yanzu dai hankalinki ya kwanta ai Dr Fadil zai aure Fadila dama can shine yake sonta, kuma dan shine na tsaya da ita a Lagos har na amshi phone number ɗinta dan in bashi”. Sai kuma yayi ɗan shiru.
"Da dai yafi mata kam ta bar mijina ta nemi nata”.
Wani irin numfashi mai cike da jin daÉ—i ya fesar cikin happy ya katseta da sauri yace.
"Kai Alhamdulillah Farriyyhah yau Monday ko, ranar Friday ne ɗaurin auren, ranar Saturday za'ayi dinner Dr Fadil Please dan Allah dan Allah dan Allah kada kice min bazaki zo muje ba dan Allah dan Allah kada kice min a'a my princess dan Allah”. Cikin sanyi tace. "To ta yaya zan samu fita Appiy”. Da sauri yace.
"Kicewa Mamy zakije gidan Yah Nasir ai bazata hanaki ba ko, Babe ke bakiyi missing ɗina bane?”. A hankali tace. "Appiy i miss u so much, ina son inji ɗumin jikinka nasan zaiyi min maganin sanyin zazzaɓin nan da nake yi duk dare”.
Da ƙarfi yaja numfashi.
“Ahhhhhhhshh Alhamdulillah thanks my Angel please ki taimaka min muje hospital a duba min ke bana son jin baki da lfy”. A sanyaye tace.
"Appiy ai gari na wayewa nake warkewa fa”.
Cikin Muryar bada umarni yace.
"Farriyyhah gobe zamuje hospital a duba minke ki shirya 4:00 pm zan zo wannan umarnine”. A hankali tace. “To Atieyah yadda kace haka za'ayi”. Shigowar Saddiqa ne yasa ta ƙara yin ƙasa da muryarta ta amsa kiran da ya fara jere mata a hankali. "Babe my Angel please my happiness help me wlh Papi ɗin ki zai hanani bacci ki bashi haƙuri”.
Tana ɗan cire idonta daga kan Aunty Saddiqa data kwantar da Zaitoon murya can ƙasan maƙoshinta a hankali tace. "Please Papi kayi haƙuri ka bar Atieyah na yayi bacci i promise in mun haɗu xan biya bashin all days da bama tare, ni dai a bar min Appiy yayi bacci kar asa masa ciwon marar nan kaji ko Papi nayi alƙawarin baka kullawa ta musamman fa in mun haɗu”. A narke yayi miƙa haɗe sakin sautin.
"Washhh thanks my Angel wlh papi ɗinki yajifa ya fara yin ƙasa, amman kin san kyan alƙawari”. Cikin raɗa tace. "Cikawa”. Yana gyara kwanciyarsa yace.
"Yesss my sugar babe Allah yayi miki al'barka bari in barki kiyi bacci kar kiyi ciwon kai”. A hankali tace. "Amin Ya Allah”. Numfashi Saddiqa ta sauƙe tana kwanciya gefenta tace. "Zazzaɓin ko naga kin fara rawan sanyi”. Jawo duvet tayi ta rufe jikinta duka har kanta a hankali tace.
“Aunty Saddiqa Appiy yace gobe zaizo muje asbiti ta yaya zan bishi muje Mamy ta hana Malam ya hana”. Da sauri Saddiqa tace.
“Ki shirya da wuri sai yah Nasir yazo ya ɗaukeki in zai fita ku fita tare dashi, shi kuwa Mahmoud ki gaya masa a waya yaje ya sameki a can nasan Yah Nasir bazai ce komai ba”. Kai ta gyaɗa alamar to.
Washe gari ƙarfe takwas dai-dai Dr Nasir yazo suka tafi kamar yadda Saddiga ta tsara mata. Suna isa Asibitin Dr Nasir ɗin ya haɗata da Dr Hakeem dan dubata, har saida suka shiga office ɗin Dr ne ta tuna da ta bar wayarta cikin jakarta kuma yana motar Dr Nasir ɗin.
“Ina zakije”. Dr Nasir ɗin ya faɗa ganin ta yunƙura zata miƙe. A hankali tace. "Zan ɗauko hand bag nane”. Kujerar data tashi ya nuna mata haɗi da cewa. "Me haɗinki da jaka ke da kike gaban Dr baki da lfy, ba abinda zai samu jakarki ki bari a gama dubaki, nima bari inje in duba nawa mutanen”. Daga nan ya fita bai jira cewarta bama.
A ƙalla awa biyu kafin aka gama mata duk gwaji da kuma fidda result ɗinta na komai da komai.
Ƙarfe goma da rabi dai-dai ta shiga office ɗin Dr Nasir ɗin da sauri ya miƙe tsaye haɗi da dawowa gaba table nashi kujerar ya nuna mata yana mai zama kan ɗaya kujerar ya zama suna fuskantar juna idonshi na kanta yace.
"Tun ɗazu nake jiranki dan sha ɗaya dai-dai zan shiga tiyata muga result ɗin naki”. Kai ta ɗan langowaɓar cikin sanyi da yunwar da takeji tace.
"Yah Naser ai maleria ce kuma ya rubuta min maganin har naje pharmacy ɗin kuma na saya”. Ta ƙare maganar da nuna mishi ledar magungunan amsa yayi ya juyesu kan table ɗin eh na maleria ɗin ne result ɗin gwajin su ya dudduba”. Cikin gamsuwa da inganci da kyan magungunan ya jinnina kai kana ya miƙe tsaye tare da cewa.
"To taso in medake zan dawo in shiga tiyata”. A hankali ta miƙe haɗi da bin bayansa tana gyara riƙon ledar dake ɗaya hannunta da wasu magungunan tabi bayansa har zuwa parking lot nasu front seat ɗin ta buɗe ta ɗauki jakarta haɗi da cewa.
"Yah Naser bari kawai zanje in shiga ɗan sahu kaje kayi aikinka kar ka makara dawowa”. Da sauri ya jujjuya mata kai haɗi da cewa.
"Ke rufa min asiri Mamy tace ƙafata ƙafarki maza shigo in maidake ganki kamar zabiya har wani yellow kikeyi kina ɗaukewa mutane ido kina tafiya kina layi jiki duk yunwa inaga shawararce ta medaki yellow nan dole sai an haɗa miki da maganin gargajiya duk kin zama wata lingabu lagwai-lagwai kamar yar yaye”. Baki ta ɗan tura a hankali tace......

Chapter Navigation

Use this section to move to any chapter without going back to the top.