Trending Hausa Novels

Sakar Makafi Littafi Na 3 Complete Hausa Novel

Reading file: Sakar Makafi Book 3 Complete Hausa Novel.txt

Chapter 19 of 31

By
*GARKUWAR MARUBUTA**SAƘAR MAKAFI*
Page 106
Na
*Aysha Aliyu Garkuwa*

Assalamu alaikum jama'a ta jama'ar arziƙi fatan muna lfy ya gida da yaranmu.
Matan alkhairi mata masu duniya, akwai garaɓasa fa ta musamman da na watannan na maulud promo haɗine na musamman kashi da ban da ban, akwai naku na manyan mata, da kuma amare bazaaawara ko budurwa, da masu joge ɗanyen jego ko barden jego.
08069423567 gata inda zaku yi min magna ta WhatsApp,
Set É—in kayana mataki biyu ne.
Na forƙo daga 40k ne zuwa ƙasa shine ƙananan 40k 35k 30k 25k 20k 15k 10k Akwai Maganin Infection sadidan yar uwa ba haufi, shi kuma set 10k.
Sai kuma manyan set É—in hajia taho kiji daga 50k 60k 70k 80k 90k 100k 120k 130k 140k sa sha kundum uban makiya 150k ne yar uwa.
HaÉ—ine na musamman.
Kana akwai kayayyakin turaren wuta dasu Humra da kulacca suma haka farashinsu yake.

Idan kin sayi kaya in dai set É—in kayanki yakai daga 50k 60k 70k 80k zan biya miki rabin kuÉ—in Delivery, daga 90k 100k 120k 130k 140k 150k to free delivery ne, Ni zan biya Miki.

0005388578 Jaiz bank Aisha Aliyu Garkuwa.

Cikin sassarfa ta nufi gaban motar da mutanen suka shiga, sauri ta ƙara ganin har sun rufe marafen murar ne yasa tasa ɗan gudu tana ɗaga musu hannu, cikin zafin nama Mahmoud ya riƙo hannunta ya fizgota baya, dan saura ƙiris wata motar tayi kanta, da ƙarfi ta abka jikinsa dan fizgota da yayi da ƙarfi.
Cikin sauri ta fara mutsu-mutsun ƙwace kanta. Ido cikin suka fara kallon juna saboda jin ya sake ta yana faɗin.
"Ke Farriyyhah me hakan?”. Ido na cikowa da ƙwalla ta buɗi baki cikin rawan murya tace.
"Appiy wlh tallahi ƙam....” da sauri ta rufe idonta tare da kame jikinta wuri ɗaya haɗi da fara rawan sanyi sabida tsawar daya daka mata cikin fusatacciyar murya yace.
"Kada ki kuskura kice min komai, karki yadda ki ƙara buɗe baki kice min kinga Yah Amin kada ki ƙara wannan kuskuren”. Shiru tayi tana mai tsuma har lau idonta a rufe sai hawayen daya fara silalo mata.
"Ke wai kin fini sanin Yah Amin ne ko kin fini sonshi ne? Ko mahaukaci kike son maidani”. Kai take ta jujjuyawa ba tare da ta ƙara yunƙurin buɗe baki tayi masa magnar dake manne akan lips ɗinta ba. Show dake ƙara sauka da kuma dare dake ƙara yin nisane bai hana hada-hada ba a wannan lokacin saboda sun ɗauki Valentine Day da mahimmanci manya da yara duk ana cikin nishaɗi da annashuwa, saɓanin zuciyar Mahmoud da ta cika da fargaba da ruɗani, hannunta yaja ya fara tafiya dole ta bishi ba gardama har suka isa wurin da mai taxi ɗin su yake. "Uhmmmm”. Ta sauƙe nannauyan numfashi lokacin da suka shaga taxi ɗin.
A hankali ta fara buɗe idonta da har yanzu hawaye ke silalo mata, so take ta juyo ta inda yake amman tsoron ganin kwayar idanunsa takeyi. Ganinsu a cikin Toronto Pearson international airport Guide. Yasata kuma takurewa wuri guda a Waiting area suka zauna bayan ya gama musu komai. A hankali ta ɗan juyo kanta ta inda yake zaune, ido ta zuba mishi ganin yadda yake zaune ya ɗaura guiwowin hannunsa duka biyu kan cinyoyinsa yasa tafukan hannunsa duka ya riƙe kansa gam, hannunsa duk karkarwa sukeyi hakama kafafunsa. Jin an fara kiran passengers na Turkish Airlines ne yasa ta ɗan kuma kallonshi tunda dama tasan can suka nufa. A hankali ta miƙe tsaye ganin ya miƙe ya nufi hanyar fita, bayanshi tabi ba tare da tace masa komai ba.
A hankali suka shiga Air Canada Express.
Bayan shigarsu da kamar 26 minute ƙarfe daya dai-dai Flight nasu ya ɗaga. Duk da tazara mai yawa dake tsakanin Toronto to Istanbul tafiyar 9.5 to 10.5 hours kasan cewar manyan country's yasa ana iya samun direct flight ba tare da anyi transit in another country ba. Numfashi mai sanyi ta fesar haɗe da gyara zamanta ta lumshe idanta hakan ya bawa sabbin hawayenta daman zubowa duk da dannar kanta da take yi amman ta gaza danne sheshheƙan kukan da ya kwabce mata a hankali cikin sasssyan sautin da shi kaɗai ke iya jinta. Shi kuwa Mahmoud jingina kansa yayi jikin seat nashi ya rumtse manyan idanunsa da ƙarfi har lau jikinsa tsuma yake yi.
Bacci mai nauyi ne yayi awon gaba da ita a cikin kukan da take yi. Shi kuwa Mahmoud kanshi ya kuma kifawa jikin seat ɗin gabansa yana taune gefen lip ɗinshi na ƙasa.
Ƙarfe shida dai ta farka. A hankali ta ɗago kanta tana mai motsa lips ɗinta a hankali alamun addu'ar tashi daga bacci take yi. Ganin haske ne ya tabbatar mata gari ya waye duk da a sararin samaniya suke.
Jin sautin muryarsa na tashi a hankali yana karatu ne yasata ɗan juyowa a kalleshi zaune yake riƙe da Alqur'anin a hannunsa Suratu Nisa'i yake karantawa, a hankali ta ɗan fara ture duvet ɗin da ta farka ta gani rufe da ita, cikin mamakin yadda aka rufeta da duvet kuma bataji ba yasata sakin sassayan Numfashi ta miƙewa tsaye tana kallon flight Attendance ɗinsu da suke duk mazane, cikin sanin makamar aiki yake tambayarta akwai abinda take buƙatane tana ɗan kallon Mahmoud tace masa. Ta ina Lavatory ɗinsu yake.
Da sauri ya ɗan juya bayansa haɗe da nuna mata ƴar karamar ƙofar dake nan cikin wurin da suke kasan cewar first class ne haka yasa suke da nasu na musamman.
Kai ta gyaɗa haɗe da masa godiya ta shiga, ganin Lavatory nasu tsab-tsab sai ɗan karen kamshin da yake bazawane yasa ta ɗan sauƙe numfashi haɗe da fara brush ta farayi kana tayi wanka da al'wala, bathrobe ɗin dake cikin ledansa ta farke tasa sannan ta fito.
Yar jakarta da ta jawo ta zaro tattausan riga da wondo Turkesh ta koma ciki ta kimtsa haÉ—e da É—aura Abaya a kai kana ta fito tana rollin kanta da É—an kwalin Abayar.
Turarukanta ta fesa haÉ—e da naÉ—e kayan data cire É—in ta maida ciki jakar. Wayarta ta zaro Alqibla ta duba, sannan ta gyara zamanta ta kabbarta sallan asuba.
Tana gama tasbihinta da Azkarul Sabah flight Attendance ya iso wurinsu menu ɗin kitchen ɗin suka miƙa musu dan jin me suke buƙatar a kawo musu.
Kai Mahmoud ya girgiza musu alamun baya sun komai, ita kuwa binda zata iya ci ta zaba.
Ƙarfe takwas dai-dai suka kawo matana kawo musu breakfast.
A hankali ta gyara zamanta tana ɗan kallon inda yake murya can ƙasa tace. "Inna kwana Appiy”. Ci gaba yayi da karatun da yake yi wanda tuni yanzu yana karshen Ali Imran. Numfashi ta fesar tare da ɗan ɗaukan tea ɗin ta fara sha baifi rabin cup ɗin tashaba ta ajiye haɗe da yiwa mai aikincin dake kusa dasu alamun yazo ya ɗauke tray, cikin girmamawa yake tamyarta meyasa bataci ba kobai mata daɗi bane ko tana buƙatar wani abun a dafa mata kai kawai ta jujjuya mishi hakan yasa shi juyawa ya tafi, jin idonta na cika da ƙwalla ne yasa ta saurin kife kanta bisa cinyoyinta tana mai danne kukan dake son taso mata.
Kusan one hour tayi a haka, jin ƙirjinta na mata nauyine yasata ɗago kanta har yanzu karatu yake yi cikin daddaɗan sautin da yasata lumshe idonta.
Ƙarfe sha ɗaya dai-dai na safe ta ɗan ɗago kanta jin yayi shiru, rufe Qur'anin yayi ɗin haɗe da gyara zamansa dan jin ana sanar musu yanzu zasuyi landing a Istanbul IST Airport. Bayan kamar 35 minute da ɗan sauri take bin bayansa, tana mai ɗan ƙara rufe jikinta dan masifeffen sanyin da suka baro a Toronto shi suka tarar anan ma Istanbul ɗin.
Suna fitowa daga Arrival Arda yayi sauri amsar Hand lounge É—insu dan yake hannunsa haÉ—i da masa sannu da zuwa, marfin motar ya buÉ—e yasa jakar a gaba kana ya buÉ—e musu baya, ba tare da ya kalletaba ya shiga baya, tana É—an jan numfashi sanyi ta shiga bayan Arda ya maida marfin ya rufe kana ya shiga yaja.
ÆŠumin cikin motar ne yasa ta É—an sakin numfashi haÉ—e da jingina da jikin marfun motar buÉ—e data É—inta.
Cikin sauri ta kira Humaira video call ganin tana online bugu É—aya ana biyu ta É—aga, murmurshi mai tafe da ruwan hawaye tayi ganin fuskar Zaitoon da Zaid.
Suna murmurshi sukayi harda tafa hannu Zaitoon ta fara gwarancin duk da mgnar ta ɗan fara fita yanzu. "Ammiy ajo ajo”. Kai ta ɗan jinjina haɗe da cewa. "Zanzo Zaitoon zan dawo kusa daku ko dan samun farin ciki, in sha Allah zan dawo kusa daku tun kafin zuciyata ta fashe”. Zaid ne dake ta tafa hannu yana faɗin. "Ammey ieyn Appiy Appiy Ammey an zo”. Murya a sanyaye tace. "Zanzo Zaid zan dawo dan nasan ko duk duniya basu soniba Ku dai kam zaku soni”. Humaira tayi dari tace. "A dai daina yiwa yara jan rai bayan an gudu anbi Appiny su”. Tana ƙara matso da wayar kusa da ita tace. "Na gane hakan ai kuskurene kuma zan gyara, tafiya bada izinin iyayena ba shine zunubin da na fara amsar sakamonsa tun jiya, dama ance duk wanda yace namiji ubane zai mutu maraya”. Ta ƙare maganar cikin sasssyan murya. “Hmmmmm”. Yaja numfashi mai nauyi har lau bai kalleta ba, Humaira da sam bata wani jitaba dan ɗan rufe speaker wayarta da tayi kafin tayi mgnar ne yasa tayi murmushi tana cewa. "Baki turo min pictures ɗin Valentine Day ba”. Tana kallon su Zaid dake ta kallonta suna dariya tace. "Kema kince Valentine Day, ai iya zama ranar masu masayone ni da banda mai sona ai ba ranata bace”. Salma data idar da salla ne ta leƙo fuskantar tana cewa. "Bafa na son munahinci ai mu zamu bada lbarin masoyinki ba ke zaki gaya mana ba, kun wani gudu kun buya a acan duniyar masoya kinzo kina mana iyayi”. Dariya Humaira tayi tace.
"Barta dai ke Yah Farooq mafa da Zainab sun tafi Cairo mu kadai aka bari da amarcin Nigeria”. Salma ne tai dariya tace. "Ke kada ki damu naji su Yah Salim da Sulaiman suna cewa muma zamuje umarar ranamadan, daga nan kuma zamu biya Dubai kuma a can zamu samowa su Zaid ƙanne in sha Allah. Ganin Arda yayi parking a harabar gidan da bazata taba mancewa bane yasa ta ɗan juyo ta kalli Mahmoud daya buɗe ƙofa ya fita, kai tsaye cikin gidan ya nufa.
Ita ma fitan tayi tana katse kiran tare da bin gidan da kallo dan anyiwa gidan gyara na musamman kai baka ce gidan ne bama in dai bawai kayi masa farin sani bane, da alamun an saye filin dake gefen gidan ma dan duk an shigo dashi ciki.
A hankali ta fara bin bayan Arda dake riƙe da hand lounge nasu, tafiya take yi cikin sanɗa da masifar tsoron ketra daya faɗo mata a rai, a baki ƙofar parlour ta tsaya tana ɗan waige waige. ganin haka ne yasa Arda ɗan ƙara buɗe mata ƙofar alamun ta shigo mana, kai ta jujjuya tace. "Ketra fa yana ciki ne?”. Da sauri yace mata ai oga ya sa ya ɗauki ketra ya kaishi gidansu dan dama gidan Yah Saleh yake in ba kowa a nan ɗin”. Ajiyan zuciya ta sauƙe kana ta shiga ciki.
Jakar ya ajiye mata kan kujera haÉ—i da mata sai anjima ya juya ya fita.
Ido ta ɗan fara jujjuyawa parlour sit sai sautin room heater dake ɗan tashi, da fesa wani irin ni'imtaccen ƙamshin mai daɗin shaka, komai na parlour sabone dal ba wanda ta bari wattanni baya bane komai na cikinsa farine sai ɗan goldin dake ƙyalli mai kyau sai wasu furanni flowers da aka baza daga tsakiyar parlour har zuwa can corridorn da zai sadata da ɗakin Mahmoud. Dinnin area ta ɗan matso tana kallon tsalelen table mai glass ɗin madubi da kujerunsa sai washing hands baby dake hefe sai show glass ɗin dake cike da su cups, mugs, plate, bowls and spoons da dai sauransu sai kwalaben drinks.
ÆŠan Fridge na gefe.
Kitchen ta ɗan leƙa komai na buƙata ba abinda babu a ciki kuma komai sabone har zata fita sai kuma ta buɗe ƙofar store ɗin.
Baki ta taɓe ganin komai na buƙatar girki babu abinda babu.
Juyowa tayi ta shiga corridorn tana magnar zuci. "Ni dai Allah ya sani nayi kewar iyayena da yarana bazan zauna ana fushi da gaba dani ba, komawata zanyi tun ma kafin ka dawo da halinka na baya dan bazan iya ɗaukaba yanzu, dama ai mai hali bashi fasa halinsa hali kuma zanen dutse”. Kasake tayi a cikin corridorn da akayiwa kwalliya ta alfarma da flowers masu masifar kyau da kamshi sai kuma ta buɗe ƙofar ɗakin da zatonta yana ciki.
"Yah Salam”. Ta faɗa tana kutsa kai cikin ɗakinshi da ni'imtaccen ƙamshi yayi welcoming ɗinta, dukkan idonta ta zuba kan gadonsa da yasha ƙawa da ado anyi rubutu da flowers Happy Valentine Day my princess. Sai kuma wani kwalin gift da yake tsakiyar da'irar heart da aka rubuta da flowers ɗin. A hankali ta hau kan gadon tare da yin rubda ciki haɗi da kife kanta kan heart ɗin kusa da gift ɗin da naɗin wasu furannin masu masifar kyau. a hankali ta fara juyi haɗe da sa hannun tana ɗaga flowers ɗin tana bazawa kan fuskarta zuwa kan ƙirjinta. Jin ana kiran sallan azahar ne yasata miƙe zaune tare da jawo gift ɗin, ta fara farkewa.
"Heyyyyhhhhh”. Taja numfashi haɗe da rufe bakinta da hannunta duka biyu gami da fiddo idonta waje tana kallon car key da Receipt ɗinsa da sunanta dake rubuce a kai kan gundarin kuɗin da ya sayi motar ta zuba idonta 80m, sai kuma ta kalli ɗan ƙaramin box ɗin dake gefe, ɗaukad box ɗin tayi haɗe da fara jujjjuyashi da hannunta ɗaya, ɗayan kuma na riƙe da car key ɗin da Receipt ɗinsa.
Ajiyesu tayi kan cinyarta kana ta buɗe box ɗin. Yan kunnen da sarka da abin hannu da zobe ne duk na asalin Gold sai ƙyalli kai ɗaukar ido sukeyi, innalillahi ta faɗa tana warware Receipt ɗinsu. Da ƙarfi ta ɗan zaro idonta a fili tace. "Yah Salam Appiy 40m duk a iya wuyana da hannuna”. Sai kuma ta jawo kolaben turarukan da ta gani a hankali ta fara feffesawa tana ɗan shaƙan numfashi.
Kwalin wayar ƙirar iPhone da ta gani ne ta jawo da sauri ta fara buɗewa. Cikin farin cikin da yasata mance yanayin da suka ciki ta fito parlour tana kiransa cikin muryar dake bayyana jin daɗin da take ciki.
wayam bashi ba komai nashi sai Qur'anin sa.
Kitchen ta leƙa nan ma babu shi, bathroom ɗin parlour nan ma bashi, da sauri ta koma corridorn ɗin ɗaya ɗakin da suka taɓa sauƙa da Yah Amin ta gwada buɗewa nan baya nan.
Jin ana sallane yasa ta koma ciki bathroom ta wuce tayi al'wala.
Bayan ta idar da sallane ta ƙara dubawa ko ina na part ɗin baya nan.
Da sauri ta É—auki wayarsa da ita ke amfani da ita, layin Yah Amin da tasan yana hannunsa ta fara kira, 3 miss call tayi masa ba'a É—agaba.
A hankali ta sauƙe numfashi tare da miƙewa tsaye tana tuno yadda yake hidimar sarin kaya da sungulan aiki da Companys da suke aiki dasu in yazo kasar wata ƙil ya fita wani aikine.
Ta faɗa lokacin data leƙa ta window taga harabar gidan ba motarsa idonta ta ɗan tsaida kan sabon gini na alfarma da aka ƙenƙena a acan ta gefen filin da aka shigo dashi.
Raihana ta kira, bugu ɗaya ana biyu ta ɗaga cikin jin daɗi take nuna mata gift ɗin Mahmoud ɗin. Suna gama waya da Raihana Aunty Saddiqa ta duba amman bata online. Haka yasa ta kiran Mamy cikin kunya take nuna mata abubuwan da duk ya saya mata harda receipt ɗinsu. Cikin jin daɗi da gamsuwa da zaman lfyar da suke ciki tace. "Masha Allah nayi farin ciki sosai Fariyda am, Allah ya ƙara buɗi da wadata ya ƙara muku zaman lfy da kwanciyar hankali ya raya muku yaranku ya baku zuriya ɗayyiba”. Cikin kunya tace. "Amin Ya Allah Mamy”. Tana ɗan kallon fuskar Fariyda da ta ɗanyi kip-lip cike da farin ciki tace. "Kiyi ƙoƙari ki zama mai kyautawa mijinki da masa biyayya da sashi farin ciki fiye da yadda yake mike, ki zame masa sanyin idanunsa kiyi haƙuri da duk ajizancin da zaizo daga garesa kiyi masa kekkyawar godiyar da zata sashi farin ciki da miki addu'ar samun janatul Firdausi”. Kai take gyaɗawa tana faɗin.
"In sha Allah Mamy”. Tana katse kiran Mamy kiran Salma na shiga tana ɗagawa tace......

Chapter Navigation

Use this section to move to any chapter without going back to the top.