Trending Hausa Novels

Sakar Makafi Littafi Na 3 Complete Hausa Novel

Reading file: Sakar Makafi Book 3 Complete Hausa Novel.txt

Chapter 23 of 31

By
*GARKUWAR MARUBUTA**SAƘAR MAKAFI*
Page 110
Na
*Aysha Aliyu Garkuwa*

https://chat.whatsapp.com/F93CYFGSIWA3ewhl8cCAYW

A.A GARKUWA FOUNDATION saka abinda Allah ya baki a wannan tallafin ciyar da bayin Allah ma buƙata a wannan wata mai albarka watan Ramadan da zaku shiga taimaka da abinda Allah ya hore miki 5843176522 Moniepoint Aysha Aliyu Garkuwa, mu haɗa hannu shi zai bada ƙarfi da karfe mu haɗa abu mai yawa mu zama sanadin tsaida zubar hawayen wasu, musa murmushi ya meye gurbin kukan da wasu keyi mu cire wasu cikin matsi da kekkyawar niya da fatan muma Allah ya ciremu cikin matsi na gidan duniya da ƙiyama. Raimaka domin Allah shine mai biyanmu da sakamakon da babu irinsa a duniya. Please ya uwa a taima ita sadaka bata yawa bata kaɗan ibada group na da duk muke haɗa abinda Allah ya hore mana kuma a ciki nake lissafin duk abinda aka samu da kuma nuna duk abin aka haɗa dan ku tabbatar saƙonku yaje ga ma buƙatan*

Tun da Ummi tayi musu bayani abinda ya faru tsakaninta da Abba da maganar da yayi yace wasiyyarsa ce.
A take ya fara shirye-shiryen nufar gida Nigeria, tunda ya fita bai dawoba sai gab da magrib.
Bayan an idar da sallan isha ne ya shigo ɗakinta, tana kan sallaya bata idar da sallan ishaba, bakin gadon ya zauna, haɗe da meda hannunsa duka biyu baya, hakama kanshi sai kuma kawai ya zame ya kwanta rigingine sawunshi na ƙasa. A hankali ta miƙe tsaye haɗe da matsowa bakin gadon, tun jallabiyar safe ce a jikinsa yau ko wanka baiyiba kan idonshi dake zubda ƙwalla suna gangarawa gefen kunnensa suna ɗiga har ƙasa, zama tayi kusa dashi tattausan tafin hannunta tasa ta fara goge mishi hawayen, ba tare da ya buɗe idowa ya jawota kan cikinsa da babu abinda yaci tun wayen garin. A hankali tace. "Appiy kuka fa kakeyi”. Murya na rawa yace. "Farriyyhah Abbana fa yake cewa a gaya min wasiyyarsa in ya mutu in bar duk inda nake inje in sashi a ƙabarinsa, yana ganin kamar bana sonsa nefa, Farriyyhah ina sonshi fa, shine dukkan Garkuwata tafa, bani da sama dashi a duniya”. A hankali tace. "Na sani Appiy kuma shima ya sani kana sonshi, yayi missing ɗinka ne shiyasa yace haka”. Murya na rawa yace. "Farriyyhah wlh nafi son Abbana fa akan Ummi na, amman gani yake kamar bana sonsa ji nake kamar inyi batan laya in ganni gabanshi. Kinji fa Ummi tace har kuka yake yi, yace ni yake son gani ba kira naba shiyasa baya picking call na, ni kuma ban gane hakan ba nayi zaton fushi yakeyi dani shiyasa nake tsoron komawa.” tana share mai hawaye tace. "Kayi haƙuri yanzu tashi muje kaci abinci kayi wanka, tun jiyafa baka kuma cin komai ba”. A hankali ya tashi zaune yana kallonta cikin sanyi yace. "No Farriyyhah bana jin yunwa, tashi muje Acibadem maslak Hospital, nayi mgna da MD dinsu Dr Abdullah Etoz zamuje ya haɗa mana medical report tun safe nake ta zirga-zirga a Airport amman sunce koda ƙarsamu ce komawa zamuyi dole Flight bazasu ɗaukeki ba sai mun kai musu medical report ɗin ki dana cikin”. Cikin tausasawa Fariyda ta miƙe tsaye ta fara jawo hannunsa tana faɗin.
"Ba matsala amman muje kaci abinci tukun, sai kayi wanka mu tafi”. Cikin sanyi yace. "Bana jin yunwa”. Kai ta langowaɓar cikin rauni tayi rau-rau ido a in one minute sai ga hawaye na zuba cikin sanyi tace.
"Please dan Allah ka taimaka min kaci abinci hankali na zaifi kwanciya, ya zanyi in yunwa ta kada kai kasan bani da kowa sai kai ko”.
A hankali yace. "Ok to bani Yogurt ya isa”. Da sauri tace to ta juya ta fita, zama yayi har saida ta dawo robar ya amsa haɗe da ɗan kallon yadda ta tsareshi da idone yasashi ɓalle marfin ya kafa kai saida ya shanye ya miƙa mata robar, yana gyatsa yace. "Muje”. A hankali tace. "Appiyn kayi wanka”. Bai ce mata komai ba ya shiga bathroom.
Ita kuma riga da wondon Pajamas ta zaro masa haÉ—i da fesa mai turare bayan ya fito ya kimtsa ne suka tafi Hospital É—in.
Nigeria.
"Kai Baba Malam ya jinjina haɗi da cewa Ummi. "In sha Allah ba komai kada ki damu kewar Mahmoud ɗin ne kawai ke damunsa ya huce kuma bai san ta ina zai fara cewa Mahmoud ya dawo ba”. A ɗaɗare Ummi tace. "Allah yasa haka dan ni dai kam ya bani tsoro”. Goggo Dada dake jin sune tace. "Nima dai haka nace ya hucene kawai in sha Allah ba komai.”
Bayan sun gama wayar ne Baba Malam ke labartawa Mamy abinda ke faruwa kai ta jinjina tace. "To dai ka gayawa Mahmoud kawai ya kamo hanya ya dawo, ni gskya kalamansa sun bani tsoro ya dawo kusa da mahaifinsa”. Yana kishingiɗa yace. "Tun shekaran jiyan munyi magna da Mahmoud ɗin yace in sha Allah nan kusa zasu dawo”. Tana kallon wayarta da kiran Dr Nasir ya shigo tana kara wayar a kunnenta tace.
"Anan zasu zo suyi salla anan kenan ko”. Malam yace. "Eh in dai sun samu damar hakan kam”.
cikin mamaki da farin ciki Mamy tace. "Kai Alhamdulillah yaushe ta sauƙa ita da waye a asbitin me aka samu”. Ta ƙare maganar dasa wayarta a amsa kuwa haɗe da matsowa kusa da Baba Malam, muryar Nasir ɗin suka ji cikin farin ciki yace. "Mamy muna gida tare da Aunty Amarya muke an samu Malam ƙalari”. Murmurshi mai tafe da jin daɗi sukayi haɗi da mahadala Malam yace. "Masha Allah Allah ya raya mana Ibrahima Khalilullah Allah ya mishi al'barka ya bawa Mahaifiyarsa lfyar shayarwa”. A tare da Mamy sukace Amin....
Istanbul file ɗin dake hannunsa wanda ke ɗauke da medical report ɗinta ya miƙawa ma'aikata Airport ɗin, cikin kulawa ya nuna masu kujerar dake bayansu haɗi da cewa su zauna. Sai da yaga sun zauna kafin ya fara buɗe takardun shafi bayan shi, ganin cikin 28 weeks ne ya sashi ɗan ɗago kanshi ya ƙara kallonta ganin waya take yi ne yasashi meda hakanlinsa kan file yaci gaba da bin dukkan bayanan da likitarta Dr Banu cosar ta bayar bisa umarnin MD dinsu Dr Abdullah Etoz. sunan hospital ɗin da sa hannun likitan ya ƙara dubawa haɗe da miƙawa ɗaya matar dake kusa dashi file ɗin.
Ita kuwa Fariydan cikin farin ciki da jin daɗi tace. "Yah Salam kai Alhamdulillah wlh ban saniba Aunty Saddiqa yaushe Aunty Sadiya ta haihu ba wanda ya gaya min fa”. Sai kuma ta ɗanyi shiru tana duba wayawar cikin jin dadi tace. "Ok jiya da dare ne ma ta haihu ga Yah Nasir ɗin ma na kirana sai yanzu ya tuna da ni. Kai Masha Allah ya raya mana bisa imani Allah ya sauƙi yan baya lfy”. Da sauri tace. "A ni bani da komai”. Kiran da matar tayi musu ne yasa ta katse kiran tare da miƙawa Mahmoud ɗin hannun, a hankali ya taimaka mata ta miƙe haɗi da bin bayan matar.
Medical personal health suka nufa hankali take taku lokacin da suka shiga cikin wurin port health É—in nasu.
File ɗinsu matar ta miƙawa Dr dake wurin haɗe da ɗan ce mata bayanin Fariyda bata da wani complications komai lfy lau ne bayanan medical report ɗinta suka bayar, amman su ɗan ƙara gwadawa dan tabbatar da watannin cikin dan kamar girmansa yafi 28 weeks ɗin da akace, kada aje ya kai 32 weeks”. Shafa cikin Mahmoud ya ɗanyi haɗe da kallon Dr da take ce mai ya naɗe rigar Fariyda scanning zasu ƙarayi. Kissing cikin yayi kana ya ɗan matsa. In 26 minute suka gama dukkan gwaje-gwajen su. Ƙarfe ɗaya dai-dai Turkish Airlines ya tashi dasu zuwa babban birnin tarayya Abuja.
Alhamdulillah tafiya tayi kyau sun isa Abuja lfy kasan cewar sai gobe da safe zasu samu jirgin Kano haka yasa suka kwana Abuja. Karfe shida dai-dai na safe jirginsu ya É—aga Abuja to Kano dan mafi akasarin matafiyan suna son samun idin sallan layyan a kanon ne.
Bakwai da yan mituna suka dira cikin birnin Kano ta dabo tumbin giwa. hannunsa riƙe da hand bag nata dan ba abinda suka ɗauko na kayansu. hannunsa ɗaya kuma na riƙe da hannunta na dama, a hankali suke fito daga Arrival ɗin. wani irin ƙyalli sukeyi tamkar taurari Abayace a jikimta irin masu faɗin gasken nan masu fita guda biyu, ta cikin Sky blue na saman kuma fari ƙal sai ɗan mayafinsa Sky blue da tayi Rollin kanta dashi dogon gashinta data tubke ya ƙarawa rolling ɗin armshi. Sai takalmin sau ciki masu taushi blue blue sai hand bag dinta ma black blue duk da girman rigar bai hana cikinta fitowa ras a cikiba ya turo gaba ya bayyana kansa wa bainan nasi.
Shi kuwa Mahmoud shigar manyan kaya yayi farare ƙal-ƙal sai aikin jikin babbar rigar tasa da akayi da zare Sky blue sai hular kansa Black blue mai haɗe da fari da Sky blue, sai takalmin sa Black blue masu ƙyalli, sai kamshi sukeyi da ƙyalli kai kace taurarune manne a goshinsu.
Sulaiman da shi kaɗai ne yasa suna dawowa yau ya zuba musu ido kamar bai taɓa ganinsu ba mamki fal cikinsa ganin cikin Fariyda yasa ya kasa rufe baki, saida suka iso gabanshi Fariyda na ɗan ƙara buɗa rigarta wai zata ɓoye cikin a hankali tace. "Uncle Sulai barka da safiya ina Humaira baka zo da ita bane”. Da sauri ya buɗe bayan mota haɗe da cewa. "Barka dai Madam ya hanya Bismillah muje suna gida ba wanda yasan kuna hanya ai”. Hararansa Mahmoud yayi yace. “Kalli gabanka”. Ya ƙare maganar da shiga baya kusa da Fariyda. Shi kuwa Sulaiman gaba ya shiga yaja suka tafi....
A hankali Mahmoud ɗin ya buɗe ƙofar parlour Ummi haɗe da kutsa kai ciki riƙe da hannun Fariyda. Ihun da Zaitoon tasane yasasu juyowa baki ɗayansu. Da gudu Zaid ya nufi kan Mahmoud yana buɗa hannunsa tamkar zai fire sama cikin karaɗi yake gwarancin Owoyo Appiy”. Ganin haka yasa Mahmoud ɗin saurin rusunawa ya buɗe masa hannu haɗe da sakin murmushin jin dadi.
Da gudu suka abka jikinsa dukansu biyu. Rungumesu yayi haɗe da miƙewa tsaye.
Humaira kuwa da sauri ta nufi Fariyda kamar yadda Salma tayi kusan a tare suka rungumeta.
Ummi kuwa da Goggo Dada kallon kallo sukeyiwa juna kamar sabbin makafi sai kuma duk suka juyo kan su Fariydan Salim ma dake gyara zaman babbar rigarsa da mmki yake kallon Fariyda da Sulaiman ke cewa su Humaira kai kubi a hankali kar kuyiwa Baby illa da wannan rungumar.
Huzaifa kuwa da gudu ya nufi parlour Abba.
Hafiz da Samira ma sai kallon cikin sukeyi.
Ita kuwa Fariyda cike da kunya ta nufi gabansu Ummi da har yanzu sun kasa koda motsawa.
Sai da ta isa gabansu ne ta ɗan rusuna da niyar durƙusawa da sauri Goggo Dada ta riƙota haɗe da zaunar da ita bisa kujerar bayanta cikin tsananin farin ciki mara misaltuwa tace. "A'a kada ki zauna a ƙasa ai zai miki wuyar tashi. Masha Allah Alhamdulillah wannan shine tsaraba mafi girma da amfani, mun godewa Allah da wannan ni'ima wannan itace tsaraba mafi ƙololuwar daraja dasa farin ciki.
Ta ƙare maganar tana shafa kanta. A kunyace tace. "Ina kwana Goggo Dada”. Goggo Dada tace.
"Lfy lau Fariyda ya nauyin jiki”. Kai ta kara sunkuyarwa cikin matsananciyar kunya tace. "Ina kwana Ummi”. Da sauri Ummi ta ɗan matso kusa da ita, kanta ta manna kan cinyoyinta haɗe da cewa. "Lfy lau Alhamdulillah”. Sai kuma ta ɗaura hannunta kan Mahmoud daya durƙusa gabansu. "Goggo Dada tace. "Allah yayi muku al'barka tashi ku isa wurin Abba kuje tare”. Jin haka ne yasa suka miƙe suka nufi parlour Abba a bakin ƙofar sukaci karo da Huxy dake ta kiciniyar gyara babbar rigarsa dan duk sun shirya tafiya idi saboda shi idin sallan layyan ana yinsa da wuri, shafa tumbinsa Mahmoud yayi haɗe da cewa. "Ina Mom ɗinka”. Da sauri yace. "Tana gida”. A tsaye suka samu Abba a tsakiyar parlour yana riƙe da carbi sai ƙamshi yake cikin shiga ta alfarma.
Fariyda da itace a gaba ta ɗan zubawa ido a karon farko yayi arba da cikinta. Numfashi mai nauyi ya sauƙe haɗe da cewa. "Lfy lau Alhamdulillah ɗiyata kun tuno su Abba, baku mancemu ba”. A hankali ta fara girgiza kai murya cike da kunya da rauni tace. "Abba kuyi haƙuri ku yafe mana, in sha Allah bazamu ƙara yin nesa da kuba”. Dai-dai lokacin Mahmoud ya shigo cikin parlour a hankali ya sauƙe su Zaid dake maƙale da wuyansa. Gaban Abba ya nufa, ba tare da ya yarda sun haɗa idoba ya rusuna a ƙasa bisa guiwowinsa haɗi da cire hularsa yana mai ƙara yin ƙasa da kai murya sarƙafe da bege, kewa, so yace.....

Chapter Navigation

Use this section to move to any chapter without going back to the top.