Trending Hausa Novels

Sakar Makafi Littafi Na 3 Complete Hausa Novel

Reading file: Sakar Makafi Book 3 Complete Hausa Novel.txt

Chapter 25 of 31

By
*GARKUWAR MARUBUTA**SAƘAR MAKAFI*
Page 112
Na
*Aysha Aliyu Garkuwa*

A.A GARKUWA FOUNDATION saka abinda Allah ya baki a wannan tallafin ciyar da bayin Allah ma buƙata a wannan wata mai albarka watan Ramadan da zaku shiga taimaka da abinda Allah ya hore miki 5843176522 Moniepoint Aysha Aliyu Garkuwa, mu haɗa hannu shi zai bada ƙarfi da karfe mu haɗa abu mai yawa mu zama sanadin tsaida zubar hawayen wasu, musa murmushi ya meye gurbin kukan da wasu keyi mu cire wasu cikin matsi da kekkyawar niya da fatan muma Allah ya ciremu cikin matsi na gidan duniya da ƙiyama. Taimaka domin Allah shine mai biyanmu da sakamakon da babu irinsa a duniya. Please ya uwa a taima ita sadaka bata yawa bata kaɗan ibada group na da duk muke haɗa abinda Allah ya hore mana kuma a ciki nake lissafin duk abinda aka samu da kuma nuna duk abin aka haɗa dan ku tabbatar saƙonku yaje ga ma buƙatan*

Da sauri Zaitoon ta gyaɗa mishi kai, sai kuma ta ɗan buga kanta kan cikin. Da ƙarfi Fariyda ta ɗan saki ƙara haɗe da rumtse idonta a take jikinta ya fara rawa dan dukan cikin da Zaitoon tayi da kanta ya shigeta.
Innalillahi Ummi ta faɗa tana matsowa kanta, shi kuwa Mahmoud da sauri ya sunkuyo kanta yana faɗin. "Babe taji miki ciwone”. Kai take jijjigawa har lau jikinta na rawa, ita kuwa Zaitoon kuka tasa haɗe da fara shafa cikin da ɗan hannunta tana faɗin. "Corry Ammey Corry”. Humaira ne ta ɗagata haɗe da rungumeta tana faɗin "Zaitoon kinjiwa Ammey ciwo”. Salma kuwa da Goggo Dada sai sannu suke mata, a hankali ta buɗe ido jin Mahmoud ya sunkuyo zai ɗagata yana faɗin "Mu tafi Hospital kawai Goggo Dada zomu tafi”. Da sauri tace. "A'a Appiy barni ya bari”. Salma tace. "A'a Fariyda adai je asbitin”. Tana gyara zamanta tace. "Allah kuwa ya sake kun gani”. Ta ƙare maganar da miƙewa tsaye ta nufi hanyar fita.
Da sauri yabi bayanta.
A parlour ya sameta kwance kan 3 seatter tayi shiri taune da lip ɗin ƙasa. Jin yana shafa cikin ne yasa ta buɗe ido rungumo wuyansa tayi haɗe da cewa. "Appiy zan daki Zaitoon in ta sake min haka zata kashe min yaro da ƙaton kanta tun yana ciki zata illata min ɗana”. Murmurshi yayi cikin raɗa yace. "So sorry ta baki haƙuri ai nima na bayar a madadinta, kuma ban yarda a dukar min ƴataba ba, Lil Amin ɗin ne duk yabi ya takura mana ya hanamu rungumarki yadda mukeso shiyasa ta dake shi. A hankali tace. "Ni dama ai na lura kafi son su Zaid da cikin nan”. Da sauri ya kauda zancen da cewa. "Jiya kika gudu part ɗin Sulaiman kika kwana a can kika barni ni kadai”. Tana shafa kanshi tace. "Na sani ai dama baka wani damu da Lil Amin ba”. A hankali ya kai bakinshi dai-dai kunnenta cikin raɗa yace. "Bana son kainama kamar yadda nake son su Zaid, so duk yaran da zamu haifa ki koya musu haƙuri kada ki nuna musu bana sonsu, ina son Lil Amin ina mararin zuwansa duniya amman bai kai son da nakewa su Zaitoon ba, My Angel koda bamu ƙara haihuwa bafa su Zaid sun ishemu”. A hankali tace. "In sha Allah ba zan nuna musu hakaba amman kaima kayi ƙoƙarin boye tsananin son su Zaid”. Yana zura hannunsa cikin rigarta yace. "In sha Allah zan gwada hakan”. Ya ƙare maganar da manna lip kan caɓɓullenta...
Murmurshi
Salma tayi tana kallon Salim daya kunnawa su Zaitoon Tom and Jerry haɗe da ajiye musu kayan wasansu ya kamo hannunta yace. "Muje ki biya bashin da kikaci jiya da dare”.
Sulaiman kuwa suna shiga parlournsa a hankali yace. "Zo ki kwanta in miki massaging nasan kin gaji da zirga-zirga gashi bakuyi bacciba jiya”....
A hankali Fariyda ke maida numfashi tana ɗan ƙara narkewa a jikinsa tace. "Appiyn yaushe zanje gida ina son ganin Mamy da Malam, gashi banje naga Baby Yah Naser ba”. A hankali yace. "Jibi nefa suna ki bari sai jibin da kaina zan kaiki gidan malam daga nan sai kusha suna da dare zan ɗaukoki”. Tana ɗan tura baki tace. "Ba kace Malam yace in dai ka yarda inja mota in jaba”. Yana gyara mata kwanciya yace. "Eh tun kafin in saya miki motar mukayi mgna”. Da sauri tace. "To ka huta zanje da motata in nuna musu ita su sa min al'barka”. Yana kallon cikin yace. "Zaki iya driving a haka ki bari in kaiki mu gaida Malam ai yafi”. Kissing lip ɗinta yayi yaci gaba da cewa. "Kuma nafi son sai motocin da na sayawa Matar Salim da Sulaiman sun iso kafin ki fara jan taki”. Da sauri tace. "To na yarda amman da mota ta ɗin zamuje kuma ni zan ja in yaso sai ka dawo da ita”. To yace mata yana jaa musu duvet.
Ranar suna kusan duk gidan Malam É—in suke, gidan Yah Nasir É—in Kuma Aunty Sadiya ne da tawagar yan uwanta.
Tunda suka shigo gidan Sadiq ya zubawa motar ido har Saida yaga Salma da Humaira sun fito daga baya rungume dasu Zaid, ya matso da sauri ganin Mahmoud ya fito front seat.
Sai kuma kawai ya isa gaban Fariyda data fito da sauri Mahmoud yace. "Tsaya kada kaji mata ciwo”. Haka yasa Sadiq tsayawa gabanta yana ta murmushi ba tare da ya rungumeta ba. Malam da ya fito daga part ɗin shi da alamun Sadiq zai kashi wani wuri ne. Murmurshi mai faɗi yayi haɗe da kallon Humaira da Salma yace. "Wannan farin ciki haka na dawowar yar uwace, to ga can Zainab ma da Raihana sun iso jiya da dare suna ciki yau kun cika ku biyar ɗinku”. Sai kuma ya kalli Mahmoud da ya ɗan rusuna yana gaidashi. Cikin girma yace. "A'a mu isa ciki”. Ya ƙare maganar yana kallon cikin da Fariyda keta kiciniyar ɓoyewa yaƙi boyuwa.
A parlour Malam ɗin suka samu Aunty Amarya da sauri ta ɗan riƙe kafaɗun Fariyda data rungumeta tace. "Allahu wahidun qahar, iko sai Allah kai Alhamdulillah Fariyda na yi a hankali kada in ji miki ciwo zauna ai wannan rungumar sai Salma da batayi nauyi haka ba, ko Humaira da ba komai tukun na”. Da sauri Salma tayi ƙasa da kanta dan batayi zaton za'a gane ɗan cikinta na 3 Months ba.
Bayan duk sun gaisane Malam ya kalli Mahmoud sai kuma ya miƙawa Fariydan kekkyawan Carbin dake hannunsa, da sauri tasa hannunta ta amsa haɗe da kallonshi cikin farin cikin kyautar Carbinsa daya bata tace. "Malam ngd Allah ya ƙara girma”. Sauran yaran nashi ya ɗan kalla sai kuma ya meda kallonshi kanta cikin yaƙini yace.
"Ga Carbina na baki, ki riƙeshi ya zame miki matunin tasbihi ki yawaita yin tasbihin Hasbunallahu wa ni'imal wakheel, ki riƙeshi a cikin dukkan wani motsin da zakiyi in dai ba salla ko karatun Alqur'ani mai girma kikeyi ba to ki maida tasbihin nan ma abincin bakinki.” duk shiru sukayi suna sauraronsa cike da natsuwa Fariyda ke jinjina kai cikin kwaɗaitarwa da yaƙini Malam yaci ga da cewa. "In sha Allah in dai kin riƙeshi Allah zai kawo miki sauyi da sauƙin haihuwa”. Kai ta ƙara sunkuyarwa cikin kunya tace. "In sha Allah zan riƙeshi Malam”. Yana kallon Mahmoud yace. "Nima zanyi ta miki kuma zan gayawa mahaifiyarku zan ke tuna mata tayi ta miki, kai ma Mahmoud kasata cikin addu'o'inka ka kuma rinƙa tuna mata ta ntasbihin nan”. Cikin girmamawa yace. "In sha Allah Malam zan ƙara akan wanda nakeyi”. Kai ya jinjina masa kana yace. "Kuma Salma ke da Raihana dukanku ma ku riƙe wannan tasbihin ga duk abunda kukesa gaba in sha Allah komai zaizo muku da sauƙi Allah yayi muku al'barka”. Amin suka amsa a tare, daga nan Malam ya miƙe ya fita tare da Mahmoud sai kuma Sadiq da ya fito bayansu yace. "Big broz Aunty Salma tace dan Allah ka basu key ita zata jasu”. Kai ya jinjina kawai ya miƙa masa key Malam yace. "To shiga muje mu sauƙeka gida ko”. Cikin kamala yace. "Gidan Bappa Lawan zamuje dan su Salim sun tafi can ni suke jira”. Malam yace. "To shiga mu tafi”. Kai ya ɗan sosa yace. "Bamu gaisa da Mamy ba”. Murmushi Malam yayi yace to je ku gaisa Sadiq kuje.
Bayan sunje sun gaisane suka fito da Sadiq É—in suka tafi.
A nan parlour Malam kuwa Raihana da Zainab da Aunty Rashida dasu Adda Nana ne suka shigo cike da farin ciki.
Rungume Fariyda dake ta baza riga sukayi sai kuma duk suka kalli Khadijah dake cewa.
"Oh Allah mai iko ke dai duk ciki in kinyishi sai kiyi ta boyeshi”. Zainab ne ta shafa cikin tana faɗin. "Da tayi sa'a bata irin wannan jarabar tofe-tofen bane ai dole ta ɓoye yanzu ni da Raihana da muka ɓoye ma ai ganewa kukayi da wannan shegen tofe-tofen”. Aunty Rashida ne tace.
"Ita Fariyda da Salma dai cikinsu na sirrine”. Cikin kunya Fariyda dake jan carbi ta mike jin yadda suka fashe da dariya suna mamakin cikin a bakin ƙofar shiga suka haɗu da Mamy rungumeta tayi tana faɗin. "Oyoyo Mamy na nayi kewarki”. Cikin mmki Mamy ta ɗan ɗagota tana kallon ciki sai kuma kawai tace. "Masha Allah. Allah ya raba lfy”. Amin Aunty Amarya tace. Adda Nana tace. "Humaira kema Allah ya kawo nan kusa ku jero yaranku kamar yadda kuke a jere”. Amin sukace baki ɗayansu banda Humaira dayi a cikin ranta.
Ranar kam Fariyda tasha tsiya wurin yan uwanta Aunty Sadiya mai jego a take ta kira Saddiga ta fesa mata tana faÉ—in.
"Kuma da ganin cikin nan tun lokacin da akayi rikicin karya hannun Mujahid da cire mai haƙori aka sameshi da alama kafin ma tayi wannan dawowar da cikin ba wai a taraba aka sameshi ba da alama cikin ya kai 28 weeks koma 30 dan ya fito ras gata nan kusa ta rufe fuska da gyale tana ta jan carbi abinta” . Ta ƙare maganar tana miƙawa Fariyda wayar dariya Saddiga tayi tace.
"Wai dan Allah da gaske ciki gareki Fariyda amman baki gaya min ba. Please wai ya kai 30 weeks”. A hankali cikin rada tace. "29 ne fa”. Dariyar da taji Saddiqa tayi ne yasa katse kiran. Haka dai suka wuni shagalin suna Ibrahim Khalil sai dare Salma da Salim ya daɗe da koya mata mota taja suka dawo.
Bayan kwana uku Aunty Amina tazo suka wuni, da yamma duk suna harabar gidan kan babban carpert dariya Aunty Amina tayi tana kallon carbin hannun Fariyda tace.
"Ni yaushe kika karɓi ɗarikane kam hajia”.
Murmushi tayi tace. "Ai riƙe carbi ba sai ɗan ɗarika ba, shi carbi kamar tunasarwane in ka shagala, dan wlh da sai nayi salla nake tasbihi amman tunda baba Malam ya bani carbinsa ko yaushe ina cikin ambaton Allah.
Cikin gamsuwa Aunty Amina tace. "Nima dai yar izalace amman ina son harka da carbi sai dai bana fita anguwa dashi ko insa a wuya yadda mutanen namu keyi”. Salma tace. "Ai ni tun tashi na nasan Baba Malam da carbi shiyasa nasan carbi ba na ƴan ɗarika kaɗai bane suma izala akwai masu ta'ammali da carbi”.
Haka dai suka wuni cikin nishaÉ—i
har sai dare Aunty Amina ta koma....
Bayan kwanaki
Mama ne ta kalli Jidda cikin zaƙuwa tace. "Yanzu malam ya kirani yace ya dawo tun shekaran jiya yace. Kije yau kuma wai ke kaɗai zakije”. Cikin zaƙuwa tace. "To Mama yanzu ma kuwa bari in je in shirya.”.....
Jidda ne zaune gaban bokan da suke sakayawa suna da Malam ido ta zuba masa cikin tafasar zuciya da jini fuska a tsuke tace. "Malam ban gane me kake son faɗaba”. Gyara zamansa yayi haɗe da ɗaga kai ya kalli yar bukkarsa da take wari da ƙaurin hayaƙe hayaƙen da yake yi zuru zuru yayi idonsa haɗe da yin dariyar manufa da ƙeta yace. "Bari in miki gwari gwari in dai kina son biyar buƙatar samun auren Mahmood da mallakeshi, to dole ki bani kanki da abinda zan fitar da wanda zaki fitar sun zan haɗa in kwaɓa da mgnain da na tsuma da kwaro mai tauraro shi zaki shafa a fuskar ki kije kuyi ido huɗu dashi”. Cikin juyewar tunani tace. "Har yanzu dai ban fahimceka ba me kake kake nufi”. Cikin zaƙuwa ya miƙe durƙushe kan guiwowinsa haɗe da fara naɗe rigar gara ga naka da yake jikinsa. Da sauri ta rufe idonta lokacin daya fito mata da bokanyarsa da tafi kama data abarar jaki.
Da sauri ya miƙe tsaye haɗe da shan gabanta cikin fajirci yace. "Ina zakije ai abune mai sauƙi da samar da biyan buƙatar rai awannin uku kaɗai sun ishemu dan da aljani ɗan zurma zanyi aikin”. Da ƙarfi ta tureshi haɗe da nunashi da hannunta tace. "Azubullahi wlh ni na haƙura da Yah Mahmoud haƙura na har abadan bazan taɓa sabon Allah a kanshi ba, bazan yi zina mai kyau bama a bare ƙazamin zina, ni ka bani hanya in wuce ni ba fajira bace”. Da ƙarfi ya daka mata tsawar da tasata riƙe kanta cikin gskyar da ya sani ya taketa ya zaɓi kaucewa hanya yace. "Bama gwara zinaba da abinda kikeyiba tsawon shekaru biyu kuke zuwa nan keda uwarki, ku a zatonku inada ikon yin abinda Allah baiyiba ne ni ɗan damfara ne bokane batacce kuma mabiyana ne halakakku masu haɗa Allah da wani ai shirkar da kukeyi tafi zinan da kike cewa bazakiyi ba,......

Chapter Navigation

Use this section to move to any chapter without going back to the top.