Trending Hausa Novels

Sakar Makafi Littafi Na 3 Complete Hausa Novel

Reading file: Sakar Makafi Book 3 Complete Hausa Novel.txt

Chapter 27 of 31

By
*GARKUWAR MARUBUTA**SAƘAR MAKAFI*
Page 114
Na
*Aysha Aliyu Garkuwa*

A.A GARKUWA FOUNDATION saka abinda Allah ya baki a wannan tallafin ciyar da bayin Allah ma buƙata a wannan wata mai albarka watan Ramadan da zaku shiga taimaka da abinda Allah ya hore miki 5843176522 Moniepoint Aysha Aliyu Garkuwa, mu haɗa hannu shi zai bada ƙarfi da karfe mu haɗa abu mai yawa mu zama sanadin tsaida zubar hawayen wasu, musa murmushi ya meye gurbin kukan da wasu keyi mu cire wasu cikin matsi da kekkyawar niya da fatan muma Allah ya ciremu cikin matsi na gidan duniya da ƙiyama. Taimaka domin Allah shine mai biyanmu da sakamakon da babu irinsa a duniya. Please ya uwa a taima ita sadaka bata yawa bata kaɗan ibada group na da duk muke haɗa abinda Allah ya hore mana kuma a ciki nake lissafin duk abinda aka samu da kuma nuna duk abin aka haɗa dan ku tabbatar saƙonku yaje ga ma buƙatan*

Ta ƙare maganar da sakin numfashi mai haɗe da nishi. Cikin sauri Salma da ta sunkuyo kasa cikin ƙwarewa a matsayinta na Nurse tace. "Alhamdulillah Fariyda yi nishi ga kan baby fa”. Cikin rawan jiki mai tafe da zufar azabar naƙudar lokaci ɗaya ta fara nishi haɗe da cewa. "Salma bazan iyaba kira min mijina zan mutufa, kin matan Dr Hairan tace bazan iya haihuwa da kainaba”. Da sauri ta durƙusa ƙasa haɗe da jawota ta jinginata ta bayanta cikin kwarewa tace. "Yi nishi Fariyda ai ba abinda Allah bazai iya yiba saunawa Doctors ke cewa mutum bazai rayuba kuma ya rayu da izinin sau nawa suke cewa mace bazata iya haihuwaba kuma Allah ya bata ta haihu da kanta, in sha Allah addu'ar da Malam da Mamy ke miki da Appiey bazasu faɗi ƙasa banza ba Please yi nishi”. Da ƙarfi ta saki nishi dan yunƙurin aman da yazo mata, kar-kar jikinta ya saki rawa nishi ta kumayi haɗe da rumtse idonta ta riƙe hannun Salma da karfin tsiya. "Hehhhhmmmm suka saki ajiyar zuciya da dogon numfashi a tare lokacin da kukan Babe ya cika bathroom ɗin.” dai-dai lokacin kuma Mahmoud ya shigo parlour da gudu ya nufi bedroom ɗin sai kuma kawai ya kutsa cikin bathroom inda yake jiyo kukan Babe.
Salma na ganishi tace. Alhamdulillah Appiy riƙe min ita.
Da sauri ya durƙusa dirsham a ƙasa ya tallabota haɗe da leƙa fuskarta cikin wani irin gigitaccen yanayi da rawan jiki da murya yake kiranta. "Babe hello my Angel kina jina da gaske kin haihu. Salma da gaske tanhaihu”. Cikin farin ciki Salma tasa hannunta ta ɗago babe haɗe da cewa Mahmoud. Appiyn naɗe rigarta nan”. Da sauri ya fara tattare rigar, cikin sauri Salma ta kifa Babe kan cinkinta. Sai kuma ta sunkuyo ta ɗan keƙa ƙasa, da sauri ta miƙe da sauri Mahmoud yace. "Lfy ina zakije mutafi asibiti ko Salma”. Tana fita tace. "No Appiy first Aid box zan ɗauko yanzu zan dawo ba matsala fa”. Jim kaɗan da fitar ta dawo riƙe da First Aid box ɗin. Cibiyar ta yanke haɗe da ware ɗan kwalinta ta ɗago Babe daga kan cikin Fariyda dake lumshe da ido tana maida numfashi naɗe baby tayi cikia ɗan kwalinta ta miƙawa Mahmoud tace.
"Fita bedroom dashi bari in tayata ta gyara”. Da sauri ya miƙowa Goggo Dada da Huzaifa yaji kukan Babe ya gaya mata yasata shigowa. Aiko da sauri ta rungume Baby tana salati haɗe da cewa. "Alhamdulillah ina Fariyda ita da waye ne a ciki”. Da sauri ya juya ciki yana faɗin. "Ita da Salma ne. Ganin yaƙi matsawane yasa Salma fito ta fara gyara Babe ta gogeta fes da Baby oil.
Saida ya tayata tayi wanka kana suka fito Goggo Dada kuma ta shiga ta gyara bathroom fesa tuni ko ina ya É—auki kamshi.
Salma ta kalli Humaira data shigo da sauri ganin Babe ya sata yin Sujudul shukur haÉ—e da cewa.
"Alhamdulillah yar uwata lallai tabbas Allah yayi gskya munga sirrin Hasbunallahu wa ni'imal wakheel”. Salma na kimtsa yar kekkyawar Babe mai masifar kama da Aunty Amina tace. "Ai kuwa wanda yace ya zai yi ya mance Allah ne.” ta ƙare maganar tana miƙawa Humaira yarinyar da take cikin fararen kayan sanyi masu taushi. Shi kuwa Mahmoud Fariyda ya kuma tallabewa ganin har yanzu tana lumshe idone yace. "Mu tafi Hospital a dubaki”. Salma tace. "Eh amman a bata tea tukuna”. Cikin hamzari Humaira ta fita.
Tare suka dawo da Ummi da kanta ta haÉ—a mata tea kusan fiye da rabi tasha.
Daga nan suka tafi Hospital ita da Goggo Dada da Babe da Salim.
Ummi ta kallesu cikin natsuwa tace. "Karku gayawa kowa tukuna sai sun dawo asbitin. Salma miko min mahaifar saiku ƙara gyara ɗakin. Ke kuma Humaira mu tafi kitchen.”
Ƙarfe takwas dai-dai suka bar gidan.
Tara dai-dai Baba Malam da Alhaji Habu mahaifin Mujahid da kuma kanin babansa suka iso parlour Abba bayan sun gaisa ne sun gabatar da kansu da abinda ke tafe dasu cikin girma da kamala Abba ya kalli ƙaninsa Bappa Lawan da Sulaiman yace. "Mun baku kuma in kun shirya yau za'a ɗaura auren, sai mu basu mako ɗaya suyi yan shirye-shiryensu da yan bukukuwansu next week akai mishi matarsa”. Cikin Mamaki Sulaiman ke kallonsu sai kuma ya maida idonsa kan ƙanin Baban Mujahid ɗin da ya zaro rafan kuɗi yan dubu dubu yace. "In dai sadakinmu ya cika a ɗaura ga dubu ɗari uku sune kaɗai cash in kuma za'a karbi transfer sai inyi”. Da sauri Abba yace. "A'a sunyi Allah yayi musu al'barka.” sai kuma ya kalli Sulaiman yace. "Je maza ka kira Baban Samira da Bala da kabiru mu samu ƙarin shaidu”. Anan take aka ɗaura auren Jidda da Mujahid.
Dai-dai lokacin kuma su Fariydan suka dawo, a hankali take maida numfashi bayan ta kwanta har yanzu bata daina jin azabar ɗinkin da akayi mata ciki da waje dan babe ta ƙarata ciki da waje.
Goggo Dada ta amshi Babe daga hannun Salim ta nufi Parlour Ummi. cikin farin ciki tace. "Kun dawo ba wata matsala ko?”. Tana nufar parlour Yayanta tace. "Babu komai sai dai sun mata allurai sun ƙara mata ruwa ƙananan leda biyu sun kuma yi mata ɗinki kam ta wahala, bari inje inyiwa Yaya albishir ko kin rigani”. Da sauri tace.
"A'a ai yana da baƙi sai dai ke zaki iya zuwa su Malam Ibrahim ne gashi kai musu yar lukutar amarya da har an bula kunne dan sauri da gaggawar gyara”. Amsar Babe tayi tana faɗin.
"Lukuta kam fa shiyasa cikin ya girma kamar biyune a ciki, Aminullah ɗin mu bai samu takwara ba”. Tana lumshe idonta tace. "Allah yasa ya samu gaba ko wurin Salim ko Sulaiman dan naga itama Humaira kwanan nan duka ta cika yawan bacci”.
Cikin jin daÉ—i tace.
"Na lura da haka”. Daga nan ta nufi parlour Abba da sallama a bakinta ta shiga, bayan sun gaisane ta miƙawa Baba Malam Babe haɗe da cewa.
"To Yaya Ibrahim ɗan kwali yaja hula ko ga amarya ta iso lfy uwartama na lfy lau”. Cikin mmki da farin ciki Abba yace. "Fariyda ta haihune?”. Cikin jin daɗi tace. "Alhamdulillah ta haihu yanzu muka dawo asbitin kuma da kanta ta haihu ba tiyataba kai babu doguwar naƙudama”. Sumbatar Babe Baba Malam yayi haɗe da cewa. "Alhamdulillah Allah ya raya yau dai muje inga Fariyda na”.
Ya ƙare maganar da miƙawa Abba Babyn nan fa sukayi ta mata addu'a da shafa kanta dasa mata al'barka.
Abba da Baba Malam, Bappa Lawan, Baban Mujahid da ƙaninsa duk Goggo Dada tayi musu jagora har parlour Fariydan suka isa, ita kuma ta fito tana tafiya a hankali. Shafa kanta Baba Malam yayi haɗe cewa. "Kinga sirri riƙe Allah ko Mamana Allah ya raya mana ita bisa imani ya baki lfyar shayarwa kuma Allah ya sauƙeku lfy”. Ya faɗa yana kallon su Salma dake kusa dashi.
Da Amin suka amsa kana suka fita.
Bayan Abba ya rakasu ya dawo ne yake shaidawa su Goggo Dada cewa an ɗaura auren Jidda yau da Mujahid sun sha mmki iya mamki Salim kuwa da Mahmoud Sulaiman ne ya gaya musu suna can parlour Salim riƙe da Babe.
Jidda kuwa da Bappa Lawan ya koma ya gaya masu an É—aura aurenta kawai sai taji kuka ya zo mata.
Aunty Amina kuwa ana gaya mata haihuwa tazo.
Su Mamy Baba Malam na komawa da labarin haihuwa Sadiq ya kawosu.
Mujahid kuwa daÉ—i kashesa farin cikin daga zuwa neman aure sai kawai aka É—aura masa auren.
Fariyda kuwa Aunty Amarya zata zauna da ita har sai anyi suna.
Bayan kwana uku Alhamdulillah jikin maijego Masha Allah dan tana samun kulawa ta musamman a wurin Aunty Amarya da Goggo Dada, bata da aiki fari bare baƙi sai taci mai kyau tasha mai kyau tayi bacci ko tasha hira da Humaira da Salma gida kuwa kullum cike yake da yan barka, ga magungunan masu inganci tuni dinkinta yayi cib da cib.
Kullum Mahmoud ke bata magani a duk lokuta ukun da take sha, dan in ba shiba babu mai bata ta yarda. Yau Aunty Amina ma ta kuma zuwa Aunty Rashida kuma sai yau ta samu zuwa dan tana fama da É—an kaciya.
Bayan sallan isha, kai Aunty Amarya ta sunkuyar tana sauyawa babe pampers, Goggo Dada kuwa su Amina dake nuna Fariyda da Mahmood da baki ta kalla tana murmushi dan su dai kam da Aunty Amarya sun saba ganin yadda yake bata magani dole sai yasa a bakinsa ya tauna ya mata ƙotonsa baki da baki kafin ya bata ruwa ya kuma sa tafin hannunsa ya rufe mata baki yasa ɗaya hannun kuma ya tallabe kanta, saida ta haɗiye ya miƙe tsaye yana kallon lips ɗinta data turo, hannnta ya jawo ta ɗan matso bakin gadon a hankali ya manna kanta cikinsa ya fara shafawa cikin lallashi yace. "So sorry my Angel Appiy ya ɓata miki rai ko, yi haƙuri saura kaɗan maganin ya ƙare”. Salma da ta shigo da abinci a hannunta ne tace. "Ai ko sun ƙarema za'a ƙaro wasu”. Hararan Salma tayi, shi kuwa Mahmoud sunkuyowa yayi ya manna mata kiss a goshinta haɗe da cewa. "Ba mai ƙara miki kyale Mrs Salim ita za'a barwa sauran in ta haihu ta shanye mana su ko”. Humaira data idar da Salla ne ta juyo tana faɗin. "Kamar kukan Zaid nakeji”. Salma tace. "Zaitoon ce wai sai Huzy ya ɗagata suyi ta zagaye parlour”. Da sauri Aunty Amina tace. "To ya ɗagata mana ba shi ya koya mataba”. Aunty Rashida tace. "Ai na lura Zaitoon ɗan karen son jiki gareta”. Aunty Amarya na miƙawa Mahmoud Babe tace. "Ai uwarta sak ta ɗauka son jiki da raki”. Da sauri Mahmoud ya amshi Babe yana kallon Goggo Dada dake cewa. "Mu kuwa nan bama ganin son jikin Fariyda ko raki tana da gwazo”. Gira ɗaya Mahmoud ya ɗaga mata ganin tana murmushin jin daɗin yabon da akayi mata yana fita yace. "Ato Goggo Dada gaya musu dai mu dai mun san ta fara koyon jarumta”.
Dariya sukayi kana suka fara cin abinci.
A can parlour Abba kuwa, ido Abba ya zubawa Babe shi kansa yaga kamarta da Amina, Ummi tace. "Kaga kamar ko”. Yana shafa kanta yace. "Sosai ma”. Sai kuma ya kalli Mahmoud da Salim da Sulaiman da suke cin abinci sai dai shi Mahmoud Quaker Oats da ya wadatu da madara yake sha. “Wanne suna za'a raɗa mata”. Ya tambaya yana kallon su. Sulaiman ne yayi saurin cewa. “Yadda take kama da Aunty Amina, ita ya kamata ayiwa mai suna”. Da sauri Salim yace. "Kamar ka shiga raina kuwa”. Murmurshi Mahmood yayi ba tare da yace komai ba. "Kai baka ce komai ba”. Ummi ta faɗa, yana gyara riƙon mug ɗin yace. "Duk yadda sukace ai yayi Ummi”. Kai Abba ya jinjina haɗe da ɗan ɗagota sama kaɗan ya kai bakinsa kan kunnennta na dama ya fara mata kiran salla haɗi da raɗa mata sunanta.
Sai da ya gama ya kallesu duk suma shi suka zuba wa ido, murmushi yayi yace. "Ku kun sowa ƴar uwarku me suna, nima na sowa ƴar uwata nasa mata sunan Goggo Dadanku”. Murmurshi Ummi tayi tace. "Alhamdulillah Allah ya raya mana Zainabu Abu mai tagwayen suna”. Amin sukace a tare, cikin farin ciki Salim yace Please a bari ni zan faɗawa Goggo Dada”. Abba yace. "An barka”.
A can ɗakin Fariyda kuwa Humaira Salma da Aunty Rashida ne sukayuwa Fariyda zaɓin duk abubuwan suna da Aunty Amina ke nuna musu a waya.
Haka dai akayi ta shirye-shirye suna........

Chapter Navigation

Use this section to move to any chapter without going back to the top.