Trending Hausa Novels

Sakar Makafi Littafi Na 3 Complete Hausa Novel

Reading file: Sakar Makafi Book 3 Complete Hausa Novel.txt

Chapter 3 of 31

By
*GARKUWAR MARUBUTA**SAƘAR MAKAFI*
Page 90
Na
*Aysha Aliyu Garkuwa*

Su Saddiga dake ta mata tsiya mamy ta tsare da ido tana faÉ—in.
"Malam yace ku shirya da yamma kuje ku duba Mujahid da hannu wai ashe ya fame a can taraba yanzu an medashi asibiti.
To sukace kana sukaci gaba da hira. Da yamma bayan sun gama shiryawa ne Mamy ta kalli Fariyda dake rungume da Zaitoon data ƙi sakinta tace.
"Banda ke a tafiyar”. Murya sanyaye tace.
"Toh”. Ta koma ta zauna sukuma suka tafi.
Bayan fitansu ne Mamy ta shiga É—akinta tana cewa.
"Zo nan”. to ta kuma cewa tare da bin bayanta har lau bata bari sun haɗa idoba, tana shiga Nasir na shigowa kusan a tare suka shiga bedroom ɗin a bakin gado suka sameta, haka yasa suka zauna kan carpert dake gaban gadon bayan sun gaisa da Nasir ɗin ne ta kalli Fariyda ta kuma kalli Nasir a hankali tace.
"Dama ina son ganinka”. Gyara zama yayi haɗe da cewa. "To Mamy gani”. Fuska a haɗe tace.
"Me ka sani game da auren Fariyda da Mahmoud da zuwansu Taraba dan Sadiq yace min tabbas kasan da Mahmoud suka tafi kainema kace masa ga motar da zasu shiga”.
Ita kam Fariyda tuni ido ya ciko da hawaye murya na rawa tace.
"Mamy wlh ban san shi bane, saida muka shiga har ya rufe motar na gane shine, kuma nayi ta roƙonsa ya sauƙeni yaki wlh bada sona ya kaini hotel ba”. Ta dire mgnar cikin kukan kunya da takaici, fuska a haɗe Mamy tace.
"Baki da gsky akwai abinda kuke ɓoye mana keda Mahmoud ɗin ki gaya min ko in saɓa miki”. Da sauri Nasir yace.
"Mamy kiyi haƙuri bai saketa bafa ni ya nuna min saƙon da ya tura mata a ranar da abin ya faru”. Cikin tuhuma Mamy ta tsare Fariyda da ido haɗi da cewa.
"Ke ba kin tabbatar mana ya sakeki ba har dacewa ba idarsa a kanki”. Kai ta sunkuyar a hankali tace.
"Nima ban san ba saki bane dan ban buɗe saƙonba saida mukaje Gembu da ina cemasa ai ya sakeni shine ya buɗe min saƙon yace in karanta in gani nan ne naga ashe bai sakeni ba”.
Nannauyan numfashi Mamy ta sauƙe haɗe da cewa. "Tashi kije kula da yaranki Abbansa da kansa zai karɓo miki takardar sakin yanzu kam tunda ba son juna kukeyi ba ai ba amfani barin auren je ɗakinki”. Ganin Nasir zaiyi mgna ne yasa Mamy saurin dakatar dashi.
A hankali ta yunƙura ta miƙe har taje bakin ƙofa sai kuma ta juyo dan jin Mamy na cewa.
"Bani wayarki nan”.
Tana kallon idon Mamy ta miƙa mata wayar ba tare da ta juyaba.
Kashe wayar Mamy tayi tana ajiyeshi gefenta tace.
"Jeki”. Cikin nauyi da cushewar tunanin menene manufar hakan ta juya ta fita ta nufi ɗakinta inda yanzu ba Raihana ita kadai ne.
Shi kuwa Mahmoud tunda Abba ya fita ya zame ya zauna a wurin ya riƙe kansa.
Haka yasa Ummi ta miƙe ta fita hakama Goggo Dada dan sun rasa abin cewa.
Sulaiman kuwa kai yake É—an jujjuyawa yana kallon Salim dake cewa.
"Abba ya bani tsoro ya kafe sosai, kuma bai kamata ba, a barshi da matarsa mana tunda yana sonta”.
Miƙewa Mahmoud ɗin yayi haɗe da sauƙe numfashi mai nauyi cikin sauri ya sa hannunsa duka biyu ya riƙo kansa sai kuma ya ɗan jingina da ƙofar parlour, ido Salim ya zuba masa, Sulaiman kuwa hannunsa ya kamo yana faɗin.
"Kana lfy”. Cikin cushewar numfashi da zuciya yace.
"Eh lau nake”. Daga nan ya fita parlour ya haura upstairs.
Su kuwa Parlour Ummi suka dawo nan sukayi ta bawa Ummi haƙuri a kan tasa baki.
Wunin ranar dai haka sukayishi ba daÉ—i.
Washe gari da rana Amina tazo.
Goggo Dada ne ta bata labarin duk abinda ya faru, cikin damuwa tace.
"Kuma yanzu shi Abba sai ya raba auren bayan sun fara son junansu, dan Allah Ummi kiyi magna kar a cutar da Mahmoud wlh yana masifar sonta gashi ya rufe kansa yaƙi buɗewa yanzufa sau huɗu kenan ina zuwa ina Knocking ƙofar bedroom nasa yaƙi buɗewa”. A hankali Ummi tace.
"To ya zanyi Amina Mahmoud shi ya jawa kansa ni yanzu in nace zanyi mgna laifin kaina zai dawo kawai mu zuba musu ido shi da ɗansa da zuciyoyinsu da halinsu iri ɗaya wa zai shiga tsakaninsu”.
Cikin sanyi Goggo Dada tace. "Wallahi Mahmoud ya sani kuka, ni tun a ranar da ya karya Mujahid na gane azabar kishine ke son haukatashi, abubuwan da yake kuma shine ake kira da mahaukacin masoyi mai mahimmancin so, da kam tabbas baya sonta amman tunda suka dawo India nasa lamarin ya sauya. Amman ba komai muyi ta tayashi da addu'a Allah yayi masa zaɓi mafi alkhairi”.
Haka dai suka wuni tattaunawa.
Shi kuwa Mahmoud sai washe gari da safe ya shigo bayan sun dawo masallaci, a parlour Abba ya samesu bayan ya gaidasune yamiƙe zai fita.
"Zauna”. Abba ya faɗa ba tare da ya kallesa ba.
Ummi kuwa da Goggo Dada har yanzu idonsu na kanshi ganin yadda ya zabge a kwana uku ana ya zama tamkar majinyaci yayi fiyaw idonsa tamkar garwashi, a hankali ya zauna gefen Sulaiman, da sauri Goggo Dada ta fara haÉ—a masa tea. Abba yace.
"Sai yaushe zaka koma bakin aiki ko dai zaka bar aikin ne dan na lura kusan wata uku kenan yanzu baka wani zuwa aiki”. A hankali Goggo Dada tace.
"Yaya to ai watanni biyun kam duk yana India ne jinyar Zaidu”. Fuska a tsuke yace.
"To daya dawofa tunda ya dawo sau biyu yaje in aikin ne baya so masu bukatarsa da yawa, dan Aminullah ya mutu shi ya nuna ban kai da shiba ai ina da Salim da Sulaiman da Ahmad ko da su sunada gefen da suka riƙe mana zan iya sa Saleh ya baro Istanbul ya dawo ya rike aikin nasa”.
Hmmmm Ummi tace haɗe da yin ƙasa da kai ido na cikowa da kwalla.
Ita kuwa Goggo Dada mug ɗin data haɗa masa tea ta miƙa masa tace.
"Babana karɓi kasha da zafinsa”. Kai a sumkuye yace. "Ina azumi”. Sai kuma ya ɗan kalli Abba da yake kuma cewa. "In baka son aikin ne ka rubuta takardar ajiye aikin ka kawo min”. Kai ya ɗan jujjuyawa a hankali yace.
"Abba zanje zanyi duk abinda Yah Amin yake yi har sai ranar da nima na bar duniya”. Ido na cika da ƙwalla Sulaiman yace.
"Abba yau Alhamis ne gashi yana azumi gobe kuma jumma'a ayi haƙuri a barshi ya huta gajiyar hanya sai ranar Monday ya koma bakin aikin, dan Allah kasan bai saba yin driving ɗin long journey ba”. Yana cire kansa da kallon Ummi data miƙe ta fita yace.
"Ni Na turasa ne ai shi ya kai kansa ya koma bakin aiki kawai in baya buƙata ya kawo min takardar ajiyar aiki in kuma bai kawoba kuma bai jeba zaiga takardar kora”. Cikin sanyi yace.
"In sha Allah yau zan fara fita”.
Kai ya juyo yana kallonsa ido cikin ido yace
"Ka rubuta sakin ne”.
Fuska tamkar zai saki kukan hawayen jin yace.
"Banzan iyaba ban san ya akeyi ba”.
Wani mugun kallo yamasa haÉ—i da cewa.
"Kaje kotu ka biya a rubuta maka”. da sauri yace.
"To Abba”. Daga nan ya miƙe ya fita haka ranar ya wuni a office.
Washe gari ranar jumma'a ma a office ɗin ya wuni sai bayan sallan isha ya dawo yana shiga ɗakinsa ya faɗa kan gado tare da fashewa da kuka yana riƙe kansa da hannunsa duka biyu, sai kuma ya tashi zaune wayarsa ya ɗauka numberta ya kuma kira karo na sau ba adadi har lau kiran baya shiga.
Dr Nasir ya kira shi kuma yana shiga baya É—agawa.
A hankali ya kuma kife kansa kan pillow yana tuna yadda sukayi da mai gadin gidan Malam ɗin da yaƙi buɗe masa gate ya kuma hanashi shiga ta ƙaramar ƙofar wani irin kuka mai cin raine ya kwabce masa har mai gadi zai hanshi shiga gidan da yake tamkar gidansu gidan da tun yana yaro yake zuwa, a kwana huɗun nan yaje ƙafa bakwai amman kamar wani kare ake korarsa wannan tunanin ne ya sashi kuka.
Cikin rawan murya yace.
"Me Abba ya gayawa Malam da shima baya amsa kirana, meyasa Yah Nasir ma baya amsa kirana, meyasa layin Angle baya shiga”.
A haka bacci yayi awon gaba dashi.
Bayan kwana biyu kasancewar week end tunda ya dawo masallaci sallan asuba ya wuce sama ko tea bai shaba juye juye kawai yake yi a kan gadon zuciya cike da ƙunci number Amina ya kira yana mai kara wayar a kunne tana ɗagawa ya saki kuka kamar yaro, cikin tashin hankali tace.
“innalillahi Mahmoud me ya faru, kana ina? Ina Ummi? da Goggo Dada? Ina Abba?”. Kukan yake yi ba tare da yace mata komai ba, haka yasa ta miƙe da sauri ta nufi parlour Daddyn Hafiz tana faɗin.
"Innalillahi ya Ubangijin talikai ka jiyar dani alkhairi Mahmoud kayi mgnan ɗan uwana gaya min meke faruwa”. Ta ƙare maganar tana zama shiga bedroom nasa ganin baya parlour da sauri ta zauna bakin gadon mijin nata da alamu ya shiga bathroom ne.
Ajiyan zuciya taja ido na tsatshfo hawaye jin yadda yake magna murya na rawa cikin sanyi da rauni yace.
"Ina sontafa Aunty Amina ki gayawa Abba ina son matata kar su rabani da ita in dai suna son inci gaba da rayuwa, zuciyata zata buga in aka rabani da ita Aunty kizo ki tayani bawa Abba haƙuri nasan zaiji mgnarki ki zame min madadin Yah Amin nasan da yana raye da ya nema min mafita.”
Ido na zubda wahayen tace. "Mahmoud ina tsoron Abba, kuma ina son kasancewarka da Fariyda”. A hankali yace.
"Yanzu menene abin yi ƴar uwata ki nema min mafita ki bani shawara”. Numfashi mai nauyi taja a hankali ta sauƙe cikin jin tsammani tace.
"Yauwa duk duniya mutum É—ayace zata iya yiwa Abba faÉ—a ta sashi ko ta hanashi.
ga shawara ɗan uwana ka shirya kaje katsina ka samu Hajja Dada itace kaɗai babba akanshi duk zuriya ƙanwar mahaifinsane kuma surkarsa mahaifiyar matarsa kakarmu itace zata iya tankwarashi”. Numfashi ya sauƙe yace.
"In sha Allah yau zan tafi katsina”. Da sauri tace.
"Bazaka bari sai gobe ba yau rana tayi fa”. Yana mikewa tsaye yace.
"Yau zanje sai anjima”. Daga nan ya tashi ya kama shiri.
Ido Abba ya zuba mishi ganin ya nufasa da car key yasa manyan kaya gefen Sulaiman ya zauna yana gaida Bappa Lawan.
Shiru yayi dan da alama magna maimahimanci sukeyi Abba ne ya meda hankali kan Sulaiman yace. "Shima ɗin Malam Ibrahim dama Humaira ce yake da nufin baka, to kuma Alhamdulillah tunda kun haɗu kun fahimci juna kafin ma akai ga haɗaku in sha Allah gobe zamuje mu tsaida mgn kawai a haɗa bikin naka da na Mahmoud da Jidda kai kuma da Humaira koda zuwa 25 January ne”. Murmurshi mai cike da ɗan kunya Sulaiman yayi yana lissafi kwanakin da suke rage yau 5 January ne, kenan saura kwana 20 sati uku kenan”. Mahmoud kuwa kici-kici yayi da fuska yana aunawa Sulaiman harara sai kuma ya kalli Abba cikin girmamawa yace.
"Abba zamuje katsina”. Ba tare da ya kalleshi ba yace
"Kai da waye”. Da sauri yace. "Salim da Sulaiman zamuje”. Shiru Sulaiman yayi yana mmkin ƙarfin halin Mahmoud da yanke musu hukunci.
"Allah ya kaiku lfy ya dawo daku lfy, ku gaida min Hajja Dada na”. Amin sukace suna yunƙurin miƙewa ne yace.
"Ina jiran takardar Fariyda yau nayi maka magna ta biyu kenan kada ka sake ka bari inyi maka ta uku dan abin bazai maka daÉ—i ba.
Kuje Allah ya tsare”.
daga nan suka fito parlour wurinsu Ummi tayi mmki sosai.
Daga nan gidan Salim suka je yana fitowa yace.
"Wai bazaku shiga bane?”. Tsaki ya ɗan ja yace. "Shiga mota mu tafi”. Yana shiga bayan Hillux ɗin yace.
"Ina zamuje”.
Sulaiman dake waya da Humaira ne ya É—an juyo ya kalleshi lokacin da suka fita gidan nasa yace.
"Katsina zamuje”. Da sauri yace. "Amman dai kai Mahmoud ɗan mulkin mallakane fisabilillahi da gidana da iyalina bazaka gaya min nesa zamuje ba inje in sallameta in gaya mata sai kawai ka jawoni yanzu in mun tuntsure a hanya ai ka mana tsiya ba muyiwa juna kallon ban kwanaba”.
Tsaki yaja tare da yin parking a gefen titi baya ya dawo haÉ—i da ce musu.
"Ku jamu ni bazan iyaba kaina ciwo yake yi”. Salim ɗin ne ya amshi tuƙin.
Alhamdulillah sunje Katsina lfy sun dawo lfy sai dai ba alamun nasara dan kafin ma su isa Abba ya gane manufarsa ya kira Hajja Dada sun gama magna ko sauraronsa batayi ba.
Kiran Amina ya amsa murya cike da ƙuna yace.
"Tsohuwar nan fa yar tashashe, taƙi ta saurareni ma inaga Abba ya kirata ne ya hure mata kunne sai cemin take ba dama bana sonta ba ai anmin yadda nake sone, har da cewa na warkene, ai tasan na warke tunda taji ina neman a dawo min da matata, su Abba kuma da suke son ƙaƙabamin yarinyar nan so suke na nakasata ko?”. Cikin sanyi tace
"In sha Allah zanzo a satin nan zan gwada yiwa Abba magna ko zai fahimceni zan kuma kira Yah Ahmad da Saleh ma kasan yana jin mgnarsu.
Bayan kwana biyu..........

Chapter Navigation

Use this section to move to any chapter without going back to the top.