Trending Hausa Novels

Sakar Makafi Littafi Na 3 Complete Hausa Novel

Reading file: Sakar Makafi Book 3 Complete Hausa Novel.txt

Chapter 24 of 31

By
*GARKUWAR MARUBUTA**SAƘAR MAKAFI*
Page 111
Na
*Aysha Aliyu Garkuwa*

"Abba na kayi haƙuri ka yafe min kasa min al'barka da fatan alkhairi. In sha Allah bazan ƙara yin nesa da kaiba kuma bazan ƙara yin duk abinda baka sona amman dan Allah kayi haƙuri ka barni da matata wlh ina sonta”. Sunkuyowa Abba yayi ya kamo kafaɗunsa ya ɗagasa haɗe da jawosa jikinsa ya rungumeshi da ƙarfi haɗi da ɗan dukan bayansa yana faɗin. "Allah yayi muku al'barka ya raya maka yayanka ya sauƙi matarma lfy ya baku zaman lfy na har abada, kada ka sake yin nesa dani”. Cikin jin dadi su Ummi Goggo Dada dasu Salim suka shigo. Haka yasa Abba sakinsa.
Yana kallon Fariyda dake ɗan ture Zaitoon da Zaid tana faɗin. "Ai ba ruwana daku, kuna ganina baku kulani ba”. Sai kuma tayi shiru jin duk sun maƙalo wuyanta suna kissing Cheek ɗinta a tare.
Cikin farin ciki Abba ya kalli su Ummi dake ta hamdala sai kuma ya kalli agogon hannunsa yace. "To mu tafi ai duk kun gama shiryawa”. Daga nan duk suka juya suka fita.
Ummi da Goggo Dada a motar Abba.
Huxy da Samira da Mamanta a motar Hafiz. Mahmoud kuwa car key É—insa ya amsa a hannun Sulaiman Baban Samira na gaba Fariyda da Humaira da Salma a bayan tare dasu Zaitoon.
Salim kuwa shi da Sulaiman da Bala da Kabiru....
Bayan an idar da salla ne sun dawo lfy lau Parlour Ummi suka wuce baki ɗayansu matan. Abba ne ya kalli su Salim haɗi da cewa. "Kuzo mu fara yanka”. To sukace haɗe da juyawa dan sauya kaya. Hafiz ne ya kalli Mahmoud daya nufi Upstairs da sauri yace. "Uncle Mahmoud yanzu mune a side dinka ai ku Abba yasa an shirya muku komai sabo a part ɗin Uncle Amin.” da sauri Huzaifa yace. "Bari inje in karɓo maka key yana hannun Ummi”. Ganin yadda Abba ya zuba masa idone yasashi yin ƙasa da kai haɗe da sauƙe nannauyan numfashi. Amsar key ɗin yayi haɗi da matsowa kusa da Abba a hankali yace. "Abba Nagode Allah ya ƙara lfy da nisan”. Yana amsar wuƙar da Salim ke miƙa masa yace. "Amin Ya Allah. Kuyi maza ku fito muyi layya akan lokaci”. A hankali ya kusa kai cikin part ɗin da tun saura kwana biyu rasuwar Yah Amin da ya shiga bai kuma shigaba sai yau. Ido ya lumshe a ya kuma buɗesu yana kallon tsari da zubin komai na ciki an sauyashi hatta pentinma an sauya komai na ciki sabone dal daga sama har ƙasa hatta kitchen ba abinda ba asaba.
Bedroom nashi ya shiga cike da salama da farin ciki ga na salla gana al'barkar Abba da yafiyarsa gana gani su Zaid ga kuma daÉ—in kasancewa cikin Æ´an uwa duk da ba wani hira yake yi da suba.
Riga da waondo 3 quarter ya saka kamar yadda su Salim suka saka, Abba kuma jallabiya ce a jikinsa, kamar yadda shariya tafi so kowa da kanshi yayi yankan shi, sai na matarsa dan tun su Ummi sunce bazasu iyaba shiyasa Abba ke musu kullum Abba nayin nasa dana Ummi da Goggo Dada, Sai baban Samira yayi nashi dana Maman Samira, sai Salim yayi nasa dana Salma sai Sulaiman yayi nasa dana Humaira a karshe Mahmoud yayi da na Fariyda.
Sai Kabir da Bala sun nasu gida jensu suka kai, haka yasa sune akan shanu.
Cikin iyawar da Abba ya horesu duk suka gama yanka aka barwa mahauta da suka kira fiÉ—a kasan cewar suna da yawa tuni aiki yayi nisa.
Huzaifa ne ya shigo riƙe da roba cike da hanta a ciki. Ummi tace. "Kai Huzaifa baka koma gidanku ba, wa zai taya Dadynku aiki”. Yana miƙawa Humaira robar yace. "Yah Hafiz ya tafi ai, kuma shi Daddy fa komai nasu aikine keyi, ni ki barni anan Our Uncle ma yace kar in tafi”. Fariyda tayi sauri janye su Zaitoon dake maƙale da ita ta ture gefe haɗe dasa hannunta ta karɓi robar. Humaira na isa wurin ta miƙa mata hannu tana kallon Fariyda ta yunƙura zata tashi tace. "Ina zakije”. Miƙewa tsaye tayi har lau robar na hannunta tace. "Kitchen mana zanje inyi gashin hantar buɗa bakin”. Da sauri Salma ta ɗaga Zaitoon dake ɗaga mata hannu tace. "To dan Allah waya saki, koma kiyi zamanki zamuyi komai”. Fuska ta kwaɓe tana kallon Goggo Dada da har yanzu basu gaji da kallon cikin da mmkinsa ba tace. "Zauna Fariyda ai yanzu kam kina da masu taya aiki ke dai ki huta”. Tana kallon Hantar dake wanke fes an yankashi sala-sala tace. "Goggo Dada wata na suke samun ladan yi muku girki na azumi duk su sukayi ni kuma yau kaɗai su hananin samun ladan dan Allah kice su bari zanyi wlh ban gajiba tun jiya da yamma fa muka iso a Abuja fa muka kwana ai ba gajiya”. Murmurshi Ummi tayi tace. "Salma ku barta tayi mana gashin ku tayata bare maggi da yankan albasa”. Da sauri tace. "A'a Ummi ni dai su huta iya na yanzu kam zanyi komai”. Daga nan ta nufi kitchen Samira na biye da ita a baya.
Salma tace. "Huzaifa in anyi wani a kawo mu fara rage aikin”. Goggo Dada tace. "Ai ba wani aiki Salma acan wajen mahauta ne suke gyaran kayan cikin kinsan sunfi kowa iya aikin har kitse hanjin suke su wanke komai su yayyanka su tsane ana kawowa kawai sai ɗaurawa a wuta. Na shanu dana Abba duk rabawa sada ake harda jan naman a yau”. Numfashi mai sanyi Humaira ta sake a hankali tace. "Ni dama ban iya gyaran kayan ciki ba, in inayi sai nayi ta amai bana son ƙarninsa”. Ta kare magnar tana shaƙar ƙamshin dake fitowa daga kitchen ɗin.
Cikin 40 minute Fariyda tayiwa hantar kekkyawan gashin tukunya mai ɗan romo-romo. Wermers ɗin da Samira ta jera mata ta ɗauka, na Abba dasu Goggo Dada da Ummi ta fara sawa, ta haɗa da bread data soya da kwai ta da tea sai fruits data sa Samira ta gyara plate biyar. ta shiryasu kan Tray. "Ɗaki ki kaiwa Ummi.” ta faɗa tana zubawa a Wermer uku masu kyau, ko wanne ta haɗa. Nasu Mahmoud ta shirya a babban tray tasa musu komai, kira min Humaira ta fadawa Samira data shigo.
Yauwa ɗauki wannan nasu Uncle Sulai ne nasan a parlour ki zasuci ki kai musu can, sai kizo mu muci a nan”. Ta faɗa lokacin da Humaira ta shigo Zaid na biye da ita a baya. Ɗaukar tray ɗin da yake dauke da wermers biyu ɗaya na gashi ɗaya na bread da kwai sai ɗan tray fruit sai flacks ɗin tea. Har taje bakin ƙofa tace. "Sai ki ajiye musu cups da spoon and fork. Ki tabbatar kin shiryar komai fa kyau irin na amare”. Dariya tayi tace. "Ba abinda zakice min ba kin gudu da mijinki baki tsaya kuka ga aurenmu ba”. Murmurshi tayi tana miƙawa Samira na Babanta da Mamanta sai nasu Bala tace. "Ai shi yasa ni yanzu zanyi huɗubata”. Salma data shigone ta ɗauki nasu tana faɗin. "Kun fa san guntun azumin rabin yin nan na ranar salla yafi azumin wuni wuya ni ku cika min ciki da ƙamshi”.
Abba da Goggo Dada da Ummi a parlour Abban.
Su Salim kuma a parlour Sulaiman.
Su kuma su Humaira Salma ce tace. "Mu tafi part ɗin Fariyda muje ki ga kayanki mune mukayi miki zaɓi collors”. Huzaifa kaɗai aka bari a parlour Ummi.
Washe gari da safe aka fara aikin jan nama, kan kace kobo tuni gari ya É—auki kamshi tako wani sashi masu kuÉ—i sun baiwa masu rongomin karfi shi yasa ko ina aka wadata.
Fiye da rabi duk sun rabar sadakane sai wani da akasa a freezer sauran kuma duk aka soya sai É—an dambun da akayi wanda za'a kaiwa Hajja Goggo.
Yau kuma parlour Humaira suke tun bayan sallan isha har sha biyu na dare suna can basuma san dare yayi nisa ba. Salma ne rungume da Zaitoon Humaira kuma rungume da Zaid ita kuwa Fariyda cikinta ne gabanta, fruit ne a tsakiyarsu suna É—an ci haÉ—i da hira.
Su Mahmoud kuwa Parlour Abba suke suna ta tattaunawa kan kasuwancinsu da kayan da suka iso da wanda ke hanya. Koda suka fito parlour Ummi suka shiga ganin ba kowa ne yasa duk suka fito kowa ya nufi part É—insa.
Kai tsaye upstairs ya wuce, wanka yayi haɗe da sa pajamas masu taushin gaske ya sauƙo ƙasa yana baza kamshi.
Shiru parlour ba motsin komai sai na Ac dake aiki, wutan ya kunna, yana mai ƙarewa parlour kallo, a haka ya nufu bedroom ɗinta ba ita ba yaran, haka ya duba ɗaya ɗakinma. A tsakar farfajiyar gidan ya tsaya haɗe da zaro wayarsa ya fara kiranta. Sai lokacin ma ya tuna wayarta na ɗakinsa. Hango Salim na shigowa ne yasashi meda wayarsa aljuhu haɗe da tsaida idonsa kan gajeren wondo da singlet dake jikin Salim sai ƙamshi yake alamun yayi wanka. "Me haka zaka fito ba suturar kirki kamar gayan bread”. Hararansa yayi haɗe da cewa. "Yarinyar nan fa bata koma ba”. Kanshi ya ɗan shafa yace. "Itama Farriyyhan da ya kamata ace tana samun hutu bata nan”. Salim yace. "To ina suke?”. Da yatsa Mahmoud ya nuna masa window parlour part ɗin Sulaiman na kasa inda haske yake kunne dal. Tsaki Salim yaja haɗe da kiran Sulaiman, cikin baccin da ya fara ɗaukarsa yace. "Ya dai Salim lfy kuwa”. A hatsale yace. "Ok kai bacci ma kayi kenan baka san matanmu na part ɗin ka bane ko kai taka tana wurinka ne shiyasa”. Cikin sanyinsa yace. Na dai jisu suna ta hira da nazo wucewa, nayi wanka na kwanta ku barsu su sha hirarsu mana, me a ciki dan suna nan wurin yar uwarsu”. Mahmoud yace. "Kai baka da kai ai”. Cikin sauri yace. "Sai kuma kuyi ni dai bazan je ince su tafi ba ko su bar min part nan kamar wani maye ai sai su ɗuka nine s matse kuma daga nayi musu haka zasu fara jin nauyin zuwa part na, dan haka ku haƙura kawai ku bar yara susha hirarsu ni saida safe”. Kwaffa Salim yayi yace. "Yafa kashe wayar ma gaba ɗaya, ita kuma Salma waryata na shiga bata ɗagawa”. A can parlour Humaira kuwa Fariydane ta kishin giɗan kan tattausan Turkish carpet ɗin Humaira haɗe da ɗaura kanta bisa cinyar Humaira data kwantar da Zaid kan kujerar dake bayanta. Hular Fariyda ta zame tana faɗin. "Yauwa bari in gwada miki wani kitson da naga anayiwa masu irin gashinki mai santsi da tsulɓi dan haka nema na bar farcen karamar yatsata yayi tsawo”. Salma tace. "Kuma zai mata kyau”. Fariyda tace. "Yaushe zamuje ganin ɗan Yah Naser ne kam”. Da sauri Salma tace. "Tab ai mu tun ranar mukaje wallahi yaron da Malam yake kama kin gashi a hoto ai ko Raihana ma tace zata zo suna”. Tana ɗan gyara kwanciyarta tace. "Ni Appiy yace wai ba inda zanje sai dai muje tare”. Dariya sukayi sukaci gaba da hirarsu....
Gidan Bappa Lawan da sauri Mama ta buɗe ƙofar ɗakin ta jin ana Knocking da sauri-sauri tana buɗewa Jiddan ta shiga. "Mama kalli hotunan da Hafiza ta saka dama Yah Mahmoud ya dawo ne”. Tana mustsuke ido tace. "Nima ɗazu Babanki ke gaya min ai Mahmoud ya dawo jiya da safe, naje zan gaya miki na samu kinyi bacci shiyasa na barki”. Idonta na kan cikin Fariyda tace. "Nayi bacci da wuri yanzuma na tashi fitsarine idona ya bushe na hau online kawai naga status Hafiza sai kawai ga hotonsu da Yah Mahmoud da Aunty Amina da Fariyda da ciki a wurin idi sukayi hotunan harda wai Allah ya raba lfy Mama wannan mayyar fa ciki tayi watoma Yah Mahmoud harda ciki yayi mata ma kenan? Mama yanzu dai ai sai mu koma wurin Malamin nan ba dama yace Mahmoud na dawowa muje akwai abinda zai haɗa min in shafa a fuskarta muddin Yah Mahmoud ya ganni to da kanshi zaice yanzu ayi auren”. Cikin mmkin Mama ke kallon cikin Fariyda tace. "Ai ni tun da naji sun dawo na kira Malam yace baya gari amman yana dawowa zai kira kije”.
Washe gari bayan sallan asuba suna parlour Abba suna shan tea Saida suka fitone suka taras dasu a parlour Ummi da alamun duk sun koma part ɗinsu sunyi wanka sunyi kwalli gwanin kyau da ka gani kasan ƴan uwane jini ɗaya masu kekkyawar alaƙa da shaƙuwa da fahimtar juna. Mahmoud ya ƙara matsowa kusa da ita hannunshi ya ɗaura kan cikinta da Zaitoon take ta faman daddanewa tana son turewa a hankali yace. "Zaitoon Lil Amin ya matsa miki ko ya hanaki kwanciya jikin Ammiy da kyau”...........

Chapter Navigation

Use this section to move to any chapter without going back to the top.