Sakar Makafi Littafi Na 3 Complete Hausa Novel
Reading file: Sakar Makafi Book 3 Complete Hausa Novel.txt
Chapter 2 of 31
By
*GARKUWAR MARUBUTA**SAƘAR MAKAFI*
Page 89
Na
*Aysha Aliyu Garkuwa*
"Abba ke kirankaâ€. Sai kuma ta kusa kai cikin kitchen É—in gefen Fariyda da tuni ta isa gaban kaskon ta kashe wutan tare da fara kwashe babbakekken Arish É—in taÆ™i bari su haÉ—a ido da Goggo Dada hawayen kunya da takaici dake kwaranyomata take É—an sharcewa kai kawai ta gyaÉ—a jin Goggo Dada na faÉ—in.
"Ki barwa Maman Samira aiki kizo Abba na kirankiâ€.
Wani irin dum haka kunnenta da zuciyarta sukayi cike da kunya tace.
“Toâ€. Shiru parlour yayi bayan shigowarsu da Goggo Dada dake biya dashi, sai Huzaifa da Hafiz da suka fita a tare.
Goggo Dada ta haɗa tea ta miƙa kishi tana kallonshi cike da mmki dan tunda suka shigo ya zauna bai sake ɗago kanshi ba bare aga kwayar idanunsa da suke cike da jarabar masifa, sai lips ɗinshi dake rawa da zuciyarsa dake harba da ƙarfi hakan ya haddasa masa ɗan rawan jiki, so yake ya buɗe bakinsa ya gaida Abba amman ya kasa hakan dan yanayin bukatar da yake ciki in ba don kiran Abba bane kuma Goggo Dada da kanta ne ta kirashi da bazai iya ganin kowa ba a wannan yanayin in ba matarsaba ko kuma ya tsaya ƙasan shawa ruwa ya sauƙa kansa wata ƙil zaiji sassaucin fitinar da yakeji to amman ina duk hakan bai samuna sabida kiran Abba haka yasa lips ɗinshi da jikinsu duka tsuma da cushewar murya gami da rufewar ido.
Kasa amsar mug É—in tea dinma yayi, haka yasa duk suka zuba masa ido cike da mmkin shi kuwa Abba kamar bai san dashi a wurinba haka yayi duk da ya fahimci yanayin da É—an nasa yake ciki.
Sallamar Fariyda Abban ya amsa tare da cewa ta shigo, a hankali ta ta shigo cikin parlour kai a sumkuye ido cike da kunya mai gauraye da hawaye, gefen Ummi ta durƙusa tana fuskantar Abba sai dai tunda ta shigo bata kalli kowaba dan kanta a sumkuye kuma idonta a rufe dan tsananin kunya da takaicin Mahmoud ɗin, murya sarkefe da rawa da rauni tace.
"Abba ina kwanaâ€.
Cikin kulawa Abba yace.
"Alhamdulillah Fariyda, gyara zamanki zauna da kyauâ€. Kai ta gyada haÉ—i da É—an gyara zamanta kai a sunkuye sai yatsun hannunta take ta jujjuawa tana datse da lip É—inta na Æ™asa na sama kuka tana tsotsa.
Shiru parlour ba wanda ya iya kara koda motsine bare magna dan wani irin kallon da Abban keyiwa Mahmoud da har yanzu ya kasa cewa komai ko kai bai iya ɗagowa ba, hakan yasa duk suka natsu gyaran muryan da yayine yasa suka ƙara yin ƙasa da kansu murya ba wargi bare wasa ko sassaucin yace.
"Mahmoud yanzu kafi karfin gaishemu kenan?â€. Da sauri ya fara jujjuya kanshi ba tare da ya iya motsa koda lips É—inshi ba. Murya a kausashe Abba yace "Nima bana buÆ™atar gaisuwar takaâ€. Har lau bai iya mgna ba sai kai ya karya yayi tamkar wanda ke fama da azabebben ciwon wuya tun da ya shigo yake son gaida Abban amman ina ta kasa hakan saboda yanayin muradin da yake ciki.
"Ina kaje?â€. Abba ya tambaya a kausashe, shiru ba magna haka yasa ya gyara zamansa yana kallonsa yace.
"Mahmoud da kai nake ina kaje?â€. Wani irin tsuma jikinsa ya saki dan buÉ—e bakinsa da yayi zaiyi magna.
Murya can ƙasa cikin kasa danne yanayin da yake ciki yace.
"Tarabaâ€. Fuska Abba ya kuma tsukewa yace.
"Kai da waye?â€. Shiru yayi yana juya kwayar idanunsa.
Fariyda kuwa cike da matsananciyar kunya ta kara yin ƙasa da kanta.
Abba ya kuma cewa.
"Nace kai da waye kukajeâ€. A hankali yace. "Sulaimanâ€. Cikin fusata Abba yace.
"Nace kai da waye kajeâ€. Murya a sarÆ™afe yace.
"Farriyyhahâ€. Wani irin kallo Abba ya watsa masa haÉ—i da cewa.
"Waye kuma Farriyyhah nace da waye kajeâ€. A hankali cikin sanyi da tsoro Sulaiman yace.
"Abba Fariyda ne yake cewa Farriyyhahâ€. A tsawace Abba yace.
"Kai na tambaya ne, ka bari shi ya ban amsa waye Farriyyhahâ€. Kanshi na Æ™asa yace.
"Faridaâ€. Dip-dip haka Æ™irkinta yake bugawa cike da kunya sai kuma ta Æ™ara rusunar da kanta.
Numfashi mai nauyi Abba ya feso murya a harzuƙe yace.
"Menene haÉ—inka da ita me yasa zaka É—auketa ka tafi da itaâ€. Shiru ba magna sai zufa daya fara tsatstsafo mishi. Rai a É“ace Abba yace.
"Eh tabbas ai yanzu ka tabbatar min cewa har yanzu kana nan da muguwar É—abi'arka ta zina da bin mata, shiyasa zaka je ka É—auketa a dole kaje ka kama hotel ka zauna da ita dole sai ka É“ata mata tarbiyyarta ka maida ita irin yan iskan Æ´an matanka mazinata nan kenanâ€. Zuwa yanzu gaba É—aya jikinsa karkarwa yake yi ido na cike da faragaba yace.
"Abba matatace faâ€. A harzuÆ™e yace.
"Matarka ni zaka gayawa matarkace dan kai mara kunya ne a nan a gaban kowa na baka umarni ka rubuta mata saki kuma kace min ka tura mata kuma da tabbacin bata da idarka a kanta ta yaya ta zama matarka. Cikin sauri ya É—ago kansa ido cike da wutan hawayen tashin hankali yace.
"Abba ban saketaba wlh matatace ba zina nayi da itaba da aurena a kanta, kayi haÆ™uri wlh ba saki na rubuta matabaâ€. Yadda yake magna muryarsa na rawa, ita kuma Fariyda duk cikintane ke ke rawan.
Shi kuwa Mahmoud da sauri ya juyo ya kalli Salim da Sulaiman cikin neman tabbatarwarsu yace. "Abba ka tambayi su Salim wlh ban saketaba kuma ga text message É—in ma ka duba date and time duk suna nanâ€. Murya a saÉ“ule su Salim sukace.
"Afwan Abba wlh bai saketabaâ€. Kallon da ya watsa musune yasa sukayi tsit.
Sai kuma ya kalli Fariyda da kuka hawayen ke zubo mata cikin kulawa yace. "Fariyda kin duba saÆ™on da ya tura miki ba sakiba neâ€.
Kukan da take dannewane ya subce mata murya na rawa tace. "Eh Abbaâ€. A tausashe yace. "Yi haÆ™uri kada kiyi kuka in dai ina raye zaluncin da ya miki a baya shine na farko kuma na karshe dole ya sakeki ina gani ai da Æ™arfi ya jaki ya dawo dake jiya da dare duk yadda kuka yi ina ganinkuâ€. Ya Æ™are maganar yana É—aukar
Jota da biri dake gefensa ya cilla masa haÉ—i da cewa. "Gashi a karo na biyu zan kuma baka umarni ka saki Fariyda ka bani shi a rubuceâ€. Cikin tsananin kiÉ—ima da tashin hankali ya fara jujjuya kai tare da durÆ™usawa kan guiwowinsa murya na rawan kuka yace.
"Abba dan Allah kayi haÆ™uri wlh bazan iya rabuwa da itaba Please Abba ko dansu Zaid a barni tare da itaâ€. Ido cike da hawaye Ummi take kallonsa cike da rauni, hakama Goggo Dada.
Salim kuwa kanshi ya riƙe yana mai jin tsoron fusatar Abba da sanin halinsa na kafiya da Mahmoud ɗin ma a wurinsa ya gada.
Sulaiman kuwa a hankali yace.
"Abba kayi haÆ™uri a barshi da matarsa tunda yana sontaâ€. Cikin Æ™una Abba yace. "Sulaiman harda kai da nake ganin natsuwarka da nagartarka irin tasu Aminullah ne da Ahmad da Saleh ne, ta ya zakace Mahmoud yana son Fariyda. To idan baka saniba yau ka sani a ranar da iyayenta suka kawota gabanshi a matsayin matarsa da haƙƙin kula da lfyarta ya rataya a kanshi a gabansu ya targaÉ—ata ya gotar mata da Æ™ashi, haka bai ishesaba fa.
A Æ™asar da bata da kowa daga Allah sai shi da Æ´an yaranta ya kuma yi mata duka ya murÉ—e mata hannu da karfin da Allah ya bashi madadin ya kare lfyarta ya targaÉ—ata ya Æ™wace wayarta ya hanata mgna da kowa dan karma a san bata da lfyr a kai mata É—auki, ya barta da targaÉ—e ba uwa ba uba ba yar uwa ko É—an uwa, ta wuni ta kwana a haka tayi kuka har muryarta ta É“ace hannu ya kumbura rauni yayi tsami, bai kulataba bare ya agaza mata aminina mahaifinta ya Æ™irasa ya É—auka yace masa baya gida, alahalin targaÉ—a masa Æ´a yayi ya barta da azabar zogi da zazzzaÉ“i da yunwa, anya za'a iya kiran Mahmoud mai imani kuwa Sulaiman?â€.
Shiru sukayi sai Mahmoud dake ta jujjuya kai, ita kuwa Fariyda kamar yanzu abin ke faruwa haka ya rinka dawo mata a idon zuciya.
Shi kuwa Abba a hankali yaci gaba da cewa.
"Duk wannan bai wadatar masaba fa baiji ya gama gamsuwa da azabtar da itaba. da igiyoyin auren da na cire sadaki na biya masa a ganina na isa dashi aka É—aura musu aure kamar yadda É—an uwansa ya bar wasiya, da igiyoyin aurensa ya rinÆ™a haÉ—ata da maza kamar maiyin kawalcinta badan Allah yayi ita mai tarbiya bace da ya koyawa mata zina, ya take wasiyyar da É—an uwansa yayi dan hana Æ´aÆ´ansa maraici hakan bai isaba ya dawo da ita yaje da ita har gidan mahaifinta ya karya É—an uwanta ya fasa masa baki ya zubda masa haÆ™oran gaba baki É—aya ya targaÉ—a masa agara, a haka ya figota da Æ™arfi ya dawo da ita ya rinÆ™a janta da Æ™arfi har ya kaita parlournsa ya rinÆ™a marinta harda shaÆ™e mata wuya ya cusa mata tsoronsa anan a gabanka da ta gashin kamar zata hau jikina dan firgici a hakane zakace min wai yana sontaâ€. Ya dire mgnar murya cike da baÆ™in cikin tuno abubuwan da Mahmoouud ya aikata, shi kuwa Mahmoud rarrafe ya farayi kamar É—an yaye gaban Abba ya iso murya na rawa yace.
"Nasan nayi kuskure a baya, amman wlh yanzu bazan sake makamancin hakanba Abba kayi haÆ™uri ku bani dama ta biyu zan gyara kuskurenaâ€. Cikin kaushin harshe Abba yace. "Mahmoud dolene fa ka saki Fariyda dolen dole kuma ni zaka bawa takardar a hannunaâ€. Cikin subcewar kuka mai cike da tsoro murya na rawa yace.
"Bazan iya ba Abba wlh tallahi bazan iya ba. Abba ina son Farriyyha ina son rayuwa da ita, Abba ita kaÉ—ai cefa macen da nake raÉ“a ban cutuba.â€
A hankali Sulaiman yace.
"Abba kayi haÆ™uriâ€. Hannu ya É—aga mishi yana kallon Ummi da tayi Æ™asa da kanta hawaye na É—insa ganin Mahmoud ya dawo gabanta da rarrafe guiwowinta ya riÆ™e ido na kwaranyar da hawaye yace.
"Ummi dan Allah da Manzonsa ki tayani bawa Abba haƙuri Goggo Dada kuce masa karya rabani da ita ya bani duk umarni da yakeso zan masa Amman banda rabuwa da Farriyyhah.†kai ta rinƙa jujjuya mishi a hankali alamar bazata iya cewa komaiba, inda Fariyda ke zaune ya juyo, ya zauna kan sawunsa hannunta da take ta jujjuya wayarta ya kamo duka biyu murya na rawan kuka har lips nashi na tsuma tamkar ɗan yaye na kuka yace.
"Farriyyhah karki bari a rabamu Please Farriyyhah kicewa Abba ina sonki su barmu mu raya tare dan Allah my Angel kada ki bari a rabamuâ€. Shar-shar hawayen ke kwaranyo mata, yadda yake kuka da magiyar ne yasa ta É—an É—ago kanta ido cikin ido sukayi dashi, fuskarsa take kallo kamar madubi idanunsa sunyi jazir sai hawaye suke zubdawa lips É—inshi dake rawa ta kalla sunkuyar da kanta tayi tana datse lip É—in.
"Farriyyha ki gaya masa kina sona Please dan Allah karki bari a Æ´anke min farin cikin rayuwata, ke kin sani kece farin cikinaâ€. Kuka mai sanyin sauti ne ya subce mata, haka yasa Abba daka mishi tsawa yace.
"Itafa tsoro kake bata ka matsa daga nan inda take tsoronka takejiâ€. Ya Æ™are maganar yana miÆ™ewa tsaye hannun Fariyda dake kuka ya kamo haÉ—i da miÆ™ar da ita tsaye yace.
"Taso mu tafi in maidaki kuma in sha Allah da kaina zan amsar miki takardar ki, gidanku kuma da yake ta zirganiyar zuwa ya buwayeki wannan karon babu ba gidanku, ko hanyar gindaku yaje zamu gaureya dashi ne in sha Allahâ€. Jiki na rawa ta mike hannunta da yake jane yasa ta bishi.
Shi kuwa Mahmoud da sauri ya miƙe tsaye gaban Abban ya durƙusa ido na tsiyaya yace.
"Abba ka rufa min asiri in ba itabafa bazanyi aureba ita kadaice ko na kasance da ita fatata bata cutuwa da komai in ba itafa babu ni Abba na warke faâ€. A kufule yaja gefe ya fita yana faÉ—in.
"Aure ai dole ne kayisa sati mai zuwan nanma kuwa zakayisa in ma suma zakayi sai kayi tayi ita kuma dai Fariyda ba kai bai itaâ€. Daga nan ya fita da Fariyda.
Da kanshi yayi driving suka tafi gidan Baba Malam.
Zaune Baba Malam É—in da Mamy sun sa Fariyda a gaba Abba kuma na jadda musu laifin Mahmoud ne ba nataba.
Numfashi mai nauyi Abba yaja haÉ—i da cewa Fariyda. "Tashi ki shiga ciki ki kwantar da hankalin ni da kaina zan yi miki maganin Mahmoudâ€. Shiru ta kasa tashi sai kukan da har yanzu yaÆ™i tsaya mata tsawan da Mamy tayi matane yasa ta miÆ™e da sauri ta nufi cikin gidan, a parlour ta samu su Aunty Saddiqa Adda Nana sai Aunty Rashida da Salam dan duk sauran tunda sukayi breakfast suka koma gidajensu.
Acan parlour Malam kuwa a ƙalla 45 minutes to 1 hours Abba da Baba Malam da Mamy suna tattaunawa daga bisani Mamy ta shiga cikin gida, shi kuwa Makam ya raka Abba har bakin mota cikin sanyin jiki ya bashi hannu yace.
"Allah yasa hakan shi yafi alkhairiâ€. Cikin kafiya da yaÆ™ini Abba yace.
"In sha Allah ma hakan ne alkhairi kai dai ka tayani da tsare gidanka a hanashi samun damar zuwa inda takeâ€. Cikin sanyi Malam É—in yace.
"Har yanzu dai kafiyarka na nan nifa ina jin tsoro kar garin neman gira a rasa idoâ€. Hannu ya bashi yace. "Ka bar komai a hannunaâ€. Daga nan sukayi sallama.
Ita kam Fariyda shigowar Mamy ne yasa ta yin ƙasa da kanta tana gyara rungumar da su Zaitoon sukayi mata sai ajiyan zuciya take saukewa.
Chapter Navigation
Use this section to move to any chapter without going back to the top.