Trending Hausa Novels

Sakar Makafi Littafi Na 3 Complete Hausa Novel

Reading file: Sakar Makafi Book 3 Complete Hausa Novel.txt

Chapter 5 of 31

*WOHOHO IN KAJI ANA ƘI GUDU TABBAS SA GUDU NE BEZO BA*

_Ina kuke Ma'aurata masu sha'awar ganin sun zama taurari kuma fitilu a idanun mazajensu Uwar gida,Amarya,Tsakar gida,hadda tan kaɗen gida Shararriya kuma ƙasaitacciya data saba kawo muku nau'ikan sirrin sahihan magungunan ma'aurata wato *AYSHA ALIYU GARKUWA* Garkuwar Marubuta ayau ma ta dawo muku da Ingantattun magungunan mata masu kyau da inganci domin gyara kanki ki zamto tauraruwa a idanun mijinki...Muna da Ingantattun Abubuwa kamar haka_ :_Munada Garin mallaka, garin maɗi, garin Hakkin mayi, garin ɓelɗamhi Garin ilanwaddihi, Gumbar da ba'a baiwa mai kishiya, Gumbar kolli mai kellin al'khairi, Gumbar Riɗi wato 3 in 1, Gumbar makwaranyi, Masin Maliƙi mai masifar ƙarfi da matse mace, ka masin Daɗi har Maɗigan Akwai, kwanon ƙasaitacciyar mace mai masifar kyau da ratsa jiki da samar da inƙantacciyar ni'ima yanada abubuwa masu kyau haɗinsa, Zumar goron tula mai masifar kyau, tsumin dabino, mai ratsa jiki, tsumin Riɗi mai ƙarfi, Furar Mata mai tsastsafo da ni'imantaccen damshi, Cida kaza, Ciccibi Abodi, Tsumin Ɓaure, tuwon ɓauren, kana akwai maganin sanyi sadidan, da dai sauransu...Se kuma fannin ƙamshi kasance da Shu'umin ƙamshi wanda ze gigita ƙwaƙwalwar Oga tare da jin ko wacce mace bata kaiba...._ _Shin ko kina da labarin Miskilinci da ƙasaitar Rayyan Naaan amma lokaci ɗaya ya zamto zautacce sakali akan soyayyar Jannart bakomai Jannart ta riƙe ba face sirrinkan gyara da kuma shu'uman humran da kulaccar sirri na Aysha Aliyu Garkuwa(Tubali) tabbas taga tasirin haka domin Naanunta ya zame mata tamkar bawa_
_Shin ko kinsan sihirtaccen haɗin da Aysha ke sha kenan ta zamto tauraruwa a idanun Hamma Yusuf(Miwasmiti)...Tabbas Mahmud ya zamto zautacce kuma makaho akan sauyayyar Bazawara wato khadijarsa duk da kuwa gashi da budurwa(Namiji Baya Kaɗan) ko kinsan hakan nada alaƙa da amfani da sahihan maganin da kuma shu'uman humran Aysha Aliyu Garkuwa??.Nasan ba zaka ku manta da irin kima da kuma darajar da Aysha ke dashi acikin Idanun Sheik Jabeer ɗin ta duk da kuwa shekaru sunja anma jinta yake tamkar budurwa 'yar sha bakwai(Garkuwa) sirrin hakan na tare da Ingantattun kuma sahihan magungunan Aysha Aliyu Garkuwa Wato Garkuwar Marubuta da kuma Ma'aurata na tabbata kunsan da cewa basirarta ba'a iya rubutun littafi ya tsaya ba hadda inganta rayuwar ma'aurata ta hanyar kawo musu Nagartattun abubuwa Ga duk wacce ta shirya saya seta tuntuɓi number ta 08069423567 muna iya tura kayan mu aduk inda kuke afaɗin Nigeria harma da ƙetare Dan Allah 'yar uwa idan baki shirya siyaba kada kiyi min magana muɓatawa kanmu lokaci...🤝🏻🤝🏻🤝🏻🤝🏻🥰😘sai.kunzo. sayan na gari maida kuɗi gida,

By
*GARKUWAR MARUBUTA**SAƘAR MAKAFI*
Page 92
Na
*Aysha Aliyu Garkuwa*

Yadda yake sauƙe numfashi, haka suma suke sauƙe numfashi cike da ta'ajjudin lamarin Yah Ahmad ya ƙara matsowa kusa dashi, a hankali yake lumshe manyan idanunsa da allurar baccin da akayi masa ya sashi sakewa, murya a karye yace. "Please Yah Ahmad sosa min”. Sai kuma yayi shiru ya haɗi da kwantar da kai, a hankali Dr ya ɗagawa Yah Ahmad hannun cikin natsuwa yace.
"Barshi kada ka ƙaiƙaya masa, yanzu zai bari in sha Allah ai mun samasa allurai a cikin drip ɗin”. Ya ƙare magnar yana ɗauƙar wani cream a cikin ɗam basket ɗin da suka haɗo masa magunguna da allurai da drip matso cream ɗin yayi kan hannun mahamud ɗin da yayi jazir kana yasa tafin hannunsa fara murza mishi cream ɗin kan ƙanana ƙuraje da suka feso duk kuma inda ya sosa yayi ruɗu-ruɗu kamar shatin bulala.
“Hmmmmmmm”. Bappa Lawan da tunda ya shigo ya kasa koda motsi sai yanzu ya saki nannauyan ajiyar zuciya yana kallon Mahmoud dake sauƙe ajiyan zuciya da ƙarfi alamun bai samu ya huceba.
Abba kuwa Dr ɗin dake faɗin. "Waninku ya biyoni Office”. Ya zubawa ido, sai kuma ya kalli Ahmad da yaja kujera ya zauna bakin gadon, Bappa Lawan kuma tuni yabi bayan Dr.
Fitarsu ne ya bawa su Salim damar shiga ciki.
Dai-dai kanshi Amina ta tsaya a hankali ta É—aura hannunta kan goshinsa da taga jijiyar kanshi sun tashi ruÉ—u-ruÉ—u. Goggo Dada kuwa Sulaiman ta nunawa inda Ac yake tana faÉ—in.
"Ƙara masa gudun AC ka sanshi da son sanyi bare kuma in ƙaiƙayi nan ya tashi yafi buƙatar sanyi”. To yace kana ya juya, Salim kuwa Jidda da Mama da suka shigo ya kalla a rai a bace sai kuma ya kauda kanshi dan ganin kallon da maman ke dannan masa.
Cika ɗakin da sukayi ne yasa Abba juyawa ya fita a bakin ƙofar ya haɗu da bappa Lawan haka yasa suka juya tare.
Acan gidan Baba Malam kuwa, ido Aunty Saddiqa ta zuba mata dan tana jin duk abinda Salma ke faɗa mata, baki ta ɗan taɓe a hankali cikin sanyi tace. "To yanzu ni me nawa da kika kirani, me nawa a ciki yaje can ya ƙarata da cutar korokoronsa mana”. Cikin takaici Salam tace.
"Ke kisan Allah a sumefa aka fitar dashi parlour Ummi wai ma bakiji bane waifa aure su Abba zasuyi masa da Jidda ya kamar baki gane me nake gaya mikiba”. Kwaffa tayi cikin rashin kuzari dan yunwar da take ji tana rufe wormas ɗin tace.
"To ya aureta mana ni me ruwana gashi gata ga koro-koronsa ai, ke ni dan Allah barni”. Ta ƙare maganar tana katse kiran.
Wani irin kallo Saddiga ke mata cike da takaici tace.
"Ke anya kuwa kanki ɗaya mijinki fa ake shirin yiwa aure, mijinkifa wata can ballagaza mara aji taje ta goga mishi jiki kina jin halin da yake ciki kina wani cewa to a masa mana ke me ruwanki ni kam anya kuwa kina son Mahmoud ɗin nan”.
A hankali ta lumshe idanta sai kuma ta buÉ—esu tana É—an tauna lip É—inta na sama madadin tsotsa tace.
"Karda ki mancefa ni a gidanmu nake kuma sakina zai yi Abba da kansa zai karbarmin takardata ya kawo, to me nawa a ciki? Aure kuma ai zaɓin iyayensa ne ko bai sakeni bama ni ba ruwana ba hurumina bane su masa auren ai ɗansune su sa ni ya sakeni ba shike nan ba”.
Kwaffa Saddiga tayi ta miƙe tsaye.
Dai-dai lokacin kuma Sadiq ya shigo riƙe da car key da wayarsa kujerar dake manne da table ɗin dake tsakiyar kitchen ɗin ya jawo ya zauna yana kallon yadda ta kwaɓe fuska ta zuba mishi idonta da suka kaɗa sukayi masifar ja har fuskantar duk tayi jazir ganin yadda take kallonsa tamkar zata fasa kuka ne yace.
"Wallahi naje duk shagunan dake kusa damu ban samu Admiral ɗin nan bafa”. Kamar zata saki ihu ido na kwaranyo da hawaye cikin rawan murya tace.
"Haba Sadiq Admiral ɗin ne zaka cemin babu a duk garin kano, ranar a ina ka samomin?”. Da sauri yace.
"Na rantse da Allah naje mall ɗin dana sama mikishi ranar sunce babu wai dama ai daga Adamawa ake kawo musu shi sai jibi zai iso”.
Ido cikin ido Saddiga ke kallonta sai kuma tace.
"Ai dama Admiral iya Adamawa ne ni nayi mamaki ma da naga an samo miki shi ranar madar shanu da kike cewa ma ni iya Adamawa da taraba nasan ana saidawa da ɗuminsa kamar yadda ake Saida shayi da safe haka ake saida madarar shanu mai zafi a Yola ”.
A hankali tace.
"Wlh yunwa nakeji har jiri nake gani”. Sadiq yace.
"To kici abinci mana ko dole sai Admiral ɗin zaki sha ko madar shanun”. A hankali tace.
"Yauwa na tuna dan Allah ka kira Hafiz ka tambayeshi ina yake seyowa Appiy ya gaya maka sai kaje ka duba min ko Allah zaisa a samu”.
Yana miƙa mata plate yace. "Ok ba matsala zaki bani na mai kuma sai naci abinci”. Tana amsar plate ɗin ta fara zuba masa couscous tana faɗin.
"Ni tun jiya da ranafa ban kuma cin komai ba”.
Saddiqa na fita tace.
"To wai baki da lfy ne, ko dai kewar Mahmoud ɗin ne sai abinda yake sha kikeson sha”. Baki ta tura haɗe da cewa.
"Ni me ruwana dashi”.
A gidan Goggo Dada kuwa Mujahid ne zaune gaban Mamanshi a hankali yake faÉ—in.
"Mama ko yaufa da naje wurin malamin nan da batun mgnar Fariyda cemin yayi da rabofa a tsakanin mu yace min inyi shiru kawai in zuba ido zan sha mmki dan haka ni dai a ɗan bar batun yarinyar nan Murjanatu”.
Cikin mmki take kallonsa dan tama rasa abin cewa, zuwa yanzu tsoro takeji kar son Fariydan ya haukata mata É—anta da kuma rabashi da imaninsa da tsinannun bakayen ke shirin sashi.
A can Hospital kuwa tare Yah Ahmad da Mama da Bappa Lawan da Jidda suka tafi. Sulaiman shi zai zauna dashi.
Abba kuwa tare suka tafi da Goggo Dada.
Ya rage Salim, Amina, Sulaiman, sai Mahmoud dake ta baccn.
Mikewa Amina tayi tana kallon Salim tace.
"Medani gida in samu in muku abinci”.
Miƙewa yayi yana kallon Sulaiman yace.
"Me dame kuke buƙatar in kawo muku”.
Yana gyara zamansa yace.
"Ka sanshi yana farkawa zaice baya son blanket nasu da pillownsu duk a kawo mana da carpet, sai Admiral kasan shi zai fara nema sai jallaniya ko 3 quarter and shirt da phones dinsa.
Kai Salim yake gyaÉ—a mai yana kallon Amina dake tabayarsu me suke so ta dafa musu.
Salim yace. "Komai ma in dai ke kikayi ai zamuci amman kiyi kaɗan zan sa Salma tayi mana miyar Caw tail da tuƙeƙƙen tuwo nasan Sulaiman naso”.
Kai ta gyada kana suka fita.
Haka dai ranar ya wuni bacci sai wuraren ƙarfe ɗaya na dare ya farka zuwa lokacin duk kowa ya tafi sai Sulaiman kawai alwala yayi ya biya sallolin da suka tsere masa yanayi yana layi dan allurar baccin bata sakeshi ba, Admiral ɗin kawai ya sha ya koma ya kwanta.
Washe gari da rana.
Ido Mamy ta zuba wa Saddiga dake cewa.
"Mamy mu shirya muje mu dubashi da jikin ko?”.
Ba tare da ta kalli Saddiga ba tace.
"Ban ceba, ai jikin da sauƙi da safe da mukaje da Malam mun samu yana bacci, kuma kinji yanzuma da Auntynku ta dawo da Sadiq tace sun sameshi a zaune”.
Sai kuma ta maida idonta kan Fariyda dake kwance bisa 3 seatter ta naɗe tayi lip kamar ba mutum a wurin shigowar Sadiq da roll ɗin Admiral a hannunsa duka biyune yasa ta yunƙuro a hankali ta zauna haɗe da lumshe idonta wasu yan siraran hawayen suka ɗan zubo mata da sauri tasa hannunta ta zaro goran Admiral ɗin har jikinta na rawa ta ɓalle marfin tare da kai bakin bottle ɗin bakinta, ido ta lumshe hadi da fara Sipping nashi ba ƙaƙƙautawa, Mamy kuwa da Saddiqa ido suka zuba mata, Sadiq kuwa juyawa yayi ya fita jim kaɗan ya dawo da wasu roll ɗin a hannunsa fridge ɗin dinnin area ya buɗe ya sakasu kana ya dawo cikin parlour dai-dai lokacin ta ajiye gorar kan table ɗin gabanta haɗin da jan numfashi mai nauyi
"Hmm Alhamdulillah”. Ta faɗa tana gyatsa haɗe da jingina bayanta da jikin kujerar tana tanɗe yan lips dinta, hannu Mamy tasa ta jawo gora ɗaya lokacin da Sadiq ya ɗaukesu dan kaisu cikin fridge buɗewa tayi tare da ɗan kurba juyowa tayi tana kallon Fariyda tace.
"Dama wannan ne Admiral ɗin to ai wannan nono ne ko”.
Kai Saddiga ta gyaɗa mata tana kallon Fariyda data kwanta tana ɗan ture Zaitoon gefe Mamy na kara kurɓa tace.
"To ke yaushe kika fara shan nono Fariyda?”. Tana kallon Mamy tace.
"Mamy ai wannan yafi nono daɗi kuma shi baya ƙarni shiyasa nake sha”.
Ido Mamy ta zuba mata ba tare da tace mata komai ba.
Mama da Jidda zaune suke gaban boka yana kallon Jidda dake kora masa jawabin duk abinda ya faru jiyan da kuma matsalar Mahmoud ɗin na yadda yake yi in wani ya taɓasa.
Ido ya zura mata cikin nasa ƙuru-ƙurun idanun jazur dasu har Saida ta gama masa dukkan bayani yace.
"Ku dai kuje ku kawo kuɗin sadakinsa komai zai kare ko mutuwa zai yi in ya kusanceki sai ya aureki kuma da zaran kunyi aure a darenku na farko akwai abinda zan baki ki haɗa da ruwan spm ɗinki ki shafa masa har abada bazai ƙara jin kaikaiyi ko ƙuraje ba dan kin tabashi kuje kawai kusa a baku sadaki ku kawo min shi nan”. Ya ida magnar yana laso shaftareren leɓensa da yake bushe ƙayau.
Ita ma Jidda shi É—in take kallo kamar yadda yake kallonta har saida yace.
"Ya isa haka tashi ku tafi”. Kafin ta iya janye idonta kana suka miƙe suka tafi da bashi tabbacin nan kusa zasu kawo sadakin.
Gab da magrib Dr ya shigo ya ɗaura masa ɗan karamin drip ɗin da sa allurai kala biyu a ciki ya kuma miƙawa Sulaiman cream ɗin yana faɗin a shafa mishi.
Kai ya jujjuya bayan Dr da Nurses ɗin sun fita ne ya kalli Salim da Amina da ke zaune a akan 3 seatter Sulaiman kuma na zaune kan 1 seatter ɗin dake bakin gadon kanshi ya sunkuyar yana ɗan kallon hannunsa da har yanzu yake nan jazir sai dai ƙaiƙayi da ɗan sauƙi ba tare da ya ɗago kanshi ba yace.
"Salim ina jin kunyar Bappa bana son inyi abinda zaiji ban kyauta masaba, yarinyar nan a hanata zuwa inda nake zan ɓallata in tana min wannan iyayinfa”. Cikin takaici Salim yace.
"Ai ka ɓallata kawai Mahmoud zatafi gane cewa baka sonta, dan ni dai nayi nayi har na gaji yarinya kamar mayya”. Amina tace.
"A'a a dai bita a hankali banda duka ba zagi in sha Allah komai zai dai-dai ta”. Sulaiman na katse wayar da yake yi da Humaira yace.
"Masoyi dai baya zama abun gudu yarinyar nan a bita a hankali, muyi ta addu'ar zaɓin Allah shi yafi ko Our Aunty”. Harara Salim ya watsa mishi, shi kuwa Mahmoud kai ya juya ya kwanta.
Washe gari da safe aka sallameshi da tarin magunguna.
Tunda suka koma daya haura sama bai sauƙo ba sai Sulaiman ko Hafiz dake kai mai abinci duk da ba wani ci yake yi ba ƙarfe tara dai-dai ya wuce bedroom ɗinsa ya bar Sulaiman da Salim.
Miƙewa Salim yayi yana faɗin.
"Kai mara matama ka shiga ka barmu bare ni da abata kusa”.
Sulaiman na bin bayansa yace. "Banza nima ɗin na kusa auren shi kuma ya rigaka auren bare ka mai iyayi”.
A hankali yake juyi a kan gadon kiranta ya kumayi a karo na shida a iya wunin yau, tsaki yaja haɗe da riƙe kansa da hannu duka biyu.
Bayan kwana biyu Alhamdulillah jiki kam yayi garau sai dai har yanzu da É—an alamun ja a fatarsa.
Gidan Bappa Lawan kuwa ido ya zuba wa Mama har ta gama batun ƙorafin Ita dai a kawo sadaki ko ƙala baice mataba ya miƙe ya nufi ɗakin.
Yau tun da yamma yake kiran layin Sadiq daya amsa a wurin Hafiz wayar na ringing ba'a ɗagawa tsaki yaja cikin ƙuncin zuciya ya duba time ƙarfe 8:00 Pm a hankali ya miƙe tsaye ya nufi parlour dawnstairs ya sauƙo yana gyara wuyan tattausar jallabiyar jikinsa Black blue mai masifar sheƙi da ƙyalli sai kamshi yake bazawa tamkar fure.
A hankali ya tura ƙofar parlour Ummi ya shiga da sallama Sulaiman Hafiz Huzaifa ne sai Goggo Dada.
Gefen Sulaiman ya zauna yana kallon Hafiz yace. "Layin nan da ka bani ba'a picking call ɗin, ka bani wani layin in akwai”. Yana ajiye plate ɗin da yaci abinci yace.
"Nima ina ta kiransa baya ɗagawa kuma ko kwanan nan baifi kwana shidaba ya kirani da lakin mukayi magna kuma iya layin ne nake dashi”.
Numfashi mai nauyi yaja yana kallon Huzaifa daya amshi plate ɗin da Samira ta miƙawa Huzaifan tana gaida Mahmoud a takaice ya amsa yana amsar plate ɗin a hannun Huzaifa indomei ne yaji naman kaza zuƙu-zuƙu ga uban kifi ga kuma kwai har uku a kai, fuska Huzaifa ya kwaɓe yana kallon kawun nasa dake faɗin.
"Huzy zaka kashe kankafa ga duk wannan zaka labtawa tumbimka a daren nan ta yaya zaka rame in ance maka ƙato kace baka so”. A hankali yace.
"Uncle Mahmoud azumifa nayi sai yanzune zanci abinci”. Hafiz ya kalla dan neman tabbaci fahimtar abinda yake nufu ne yasa Hafiz ɗin cewa. "Eh azumi yayi wai zai maka addu'a Allah ya baka lfy wai ka cika ciwo”. Murmushi yayi yana miƙawa Huzaifa plate ɗin ya fasha kansa yana kallon Goggo Dada dake latsa wayarta tana faɗin.
"Wlh nayi kewarsu Zaid bari in kira in faɗawa Mamy a kawo mana su gobe”. Jin haka ne yasa ya gyara zamansa yana danna wayarsa kamar baijita ba.
Sulaiman kuwa charting yake da Humaira shiyasa hankalinsa baya kansu.
Ido ya zuba mata dan shima yana jiyo sautin kukan Zaid.
"Lfy kuwa suke wannan kukan”. Goggo Dada ta tambaya. Mamy na jijjiga Zaitoon tace. "To gata nan dai yau tun yamma take ta koke-koke shima Zaid ɗin in yaga tanayi sai ya fara wai dole sai uwarsu”. Da sauri tace.
"To ina Fariyda”. Hafiz da Huzaifa duk ita suke kallo dan suna jiyo mgnar Mamy dake faɗin.
"Uwar tasuma gata nan dai kamar mara lfy ko yashe tana kwance”. A hankali ya miƙe tsaye sama ya koma ba tare da yayiwa kowa magna ba, a parlour ya tsaya haɗi da zura hannunsa cikin aljihunsa ya rinƙa ɗan sintiri cikin alamun nazari da neman mafita yesss ya faɗa a hankali kana ya zaro wayarsa ya kira Huzaifa bugu ɗaya ana biyu ya ɗauka.
"Huxy zo parlour na”.
Yana shigowa ya kamo hannunsa yana shafa tumbin Huzaifa cikin raÉ—a yace.
"Kaje parlour Abba ka duba kan Centre table nashi zaka ga car key ɗinsa kayi a hankali ka ɗauko min ka tabbatar bai gankaba Ummi ma bata gankaba”. Dariya yayi haɗi da cewa.
"An gama ai na iya satan car key na Daddy mu ma ina ɗauka na fara koyan mota ai”. Da sauri yace.
"Je ka ɗauko min gobe zamuyi wannan mgnar iya sata da fara joyan motar”.
Jim kaɗan kuwa da fitarsa sai gashi ya dawo da car key ɗin Abba ya miƙa masa.
Kanshi ya shafa kana suka fito a tare.
Huzaifa yayi part ɗin Yah Ahmad inda suke kwana shi kuma ya shiga motar Abba ya fita cike da yaƙini da kewa bege ya nufin gidan Baba Malam.
Numfashi mai nauyi ya fesar lokacin da mai gadin gidan Baba Malam ya buÉ—e masa gate ya shiga.
Har da É—an rusuna masa da faÉ—in.
"Barka da zuwa Alhaji”. Time ya duba lokacin da ya gama yin parking a can nesa kusa da side ɗin Baba Malam inda yake ganin Abba nayin parking in sunzo.
Shi kuwa maigadin gate ɗin ya rufe kana ya koma bakin ƙofar ɗakinsa yaci gaba da cin abincinsa.
Numfashi ya fesar cikin ƙarfin hali ya buɗe motar yana duba time a wayarsa 9:29 Pm maida marfin motar yayi ya rufe a hankali yana kallon window Dinnin area ɗin parlour Malam da yake ta wurin da haske a kunne da alamun da mutum a wurin haka yasa ya ɗan koma ta bayan motar ya nufi cikin gida kai tsaye.
Da sauri Sadiq ya É—an ja da baya haÉ—i da cewa.
"Afwan Yah Mahmoud ban lura da kaiba”. Hannun Sadiq ɗin ya kamo ya riƙe yana ɗan matsewa yace.
"Ina ka wurgar da wayarka ina ta kira baka amsaba”. Yana sosa ƙeyarsa yace.
"Yah Nasir ne ya kwace min waya”. Juyawa yayi ya nufi part ɗin Mamy har lau yana riƙe da hannun Sadiq ɗin yace. "To me kakeyi a wayar”. A hankali yace.
"Wai Aunty Saddiga ne tace masa ina charting da yan mata kuma fa cousmate nane karatu nake koya musu”. Matse hannun yayi da ƙarfi yace.
"Da kai da a bokinka Hafiz duk kanku na rawa shiyasa ake sa muku ido”. Yayi mgnar yana tura Sadiq ɗin gaba lokacin da suka iso bakin ƙofar parlour Mamy gane me yake nufi ne yasa Sadiq ɗin kutsa kai da yin sallama yana turo ƙofar ya hango Yah Nasir a bakin ƙofar bedroom ɗin Fariyda.
"Mamy ga Yah Mahmoud yazo”. Mamy dake tsaye gefen Fariyda dake sanye da wasu tattausan riga da wondon iya sharabarta sai gashin kanta dake zube kan kafaɗunta tana zaune kan gadon ta jingina bayanta da allon gadon ta naɗe sawunta ƙirjinta na kan cinyoyinta kanta na kife kan guiwowinta haka yasa gashinta bajewa a jikinta dake ɗan karkarwa alaman zazzaɓi lips ɗinta sunyi jazir, idonta ta maida kan Saddiga data tasa Fariyda a gaba riƙe da magungunan data ɓare da wata bottle tana magiya ta amsa tasha taƙi sha.
Kwaffa Mamy tayi tana kallon Sadiq tace.
"Mahmoud kuma yaushe yazo yana ina”. Da sauri Dr Nasir da rigada ya hagonshi yace........

Chapter Navigation

Use this section to move to any chapter without going back to the top.